2025-05-01@11:17:40 GMT
إجمالي نتائج البحث: 389
«Gayyata»:
Gwamnatin Yobe ta bayyana shirinta na mayar da tubabbun mayaƙan Boko Haram cikin al’ummarsu da aka yi wa shirin kawar da tsattsauran ra’ayi, gyara da sake haɗewa da iyalansu ƙarƙashin rundunar Operation Safe Corridor (OPSC). Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni ne ya bayyana haka a ranar Alhamis a Damaturu lokacin da ya karɓi baƙuncin...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Gwamnatin Najeriya ta nuna damuwarta kan yadda masu safarar mutane ke ƙara amfani da kafafen sadarwa na zamani wajen yaudarar mutane da kuma yi musu cin zarafi, inda ta bayyana hakan a matsayin barazana wadda ba ta da iyaka kuma mai saurin yaɗuwa wadda ke buƙatar ɗaukar mataki cikin gaggawa. Da yake jawabi a taron...
Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya nuna kaɗuwar sa bisa rashin da aka yi na ɗan Majalisar Dokokin jihar, Hon. Aminu Ibrahim Kasuwar Daji, ɗan Majalisa mai wakiltar mazaɓar Ƙauran Namoda ta Kudu. Iyalai sun bayyana cewa Hon. Aminu Kasuwar Daji ya rasu ne a cikin barcin sa da asubahin ranar Larabar nan a...
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kaduna ta samu nasarar samo ingantaccen masauki ga alhazan jihar a birnin Makkah, gabanin gudanar da aikin Hajjin 2025. Daya daga cikin mambobin kwamitin musamman da ke kula da aikin hukumar, Malam Buhari Marabar-Jos ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a ranar Talata...
An yi kira ga Gwamna Mohammed Umar Bago na jihar Neja da ya sanya baki kan rikicin fili mai fadin sama da hektar saba’in da biyar da ake zargin Hakimin Tegina da ke karamar hukumar Rafi ya kwace daga hannun mamallakinsa a Pangu Gari. Babban Limamin Pangu Gari, Alhaji Umar Musa Danladi ne ya...
Ministan Lafiya, Farfesa Muhammad Pate ya bayyana cewa, sama da likitoci dubu 16 sun fice daga Nijeriya a cikin shekaru biyar zuwa bakwai da suka gabata zuwa wasu ƙasashen duniya don ci gaba da aiki cikin ingantaccen yanayi. Farfesa Pate ya bayyana haka ne a wurin taron horas da Ƙungiyar Likitocin Afrika da ya gudana...
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya yi martani ga kalaman shugaban Amurka Donald Trump na baya-bayan nan game da yiwuwar tattaunawa da Iran kai tsaye, inda ya yi karin haske kan matsayar Tehran, kamar yadda jaridar Washington Post ta kawo. Araghchi ya bayyana imaninsa cewa irin matakan da Iran ta dauka a baya-bayan nan...
A wani mataki na kara nesanta kanta da Faransa da ta yi mata mulkin mallaka, Nijar ta ayyana harshen Hausa a matsayin yaren ƙasa a madadin Faransanci. Kamfanin dillancin labarin kasar AFP ne ya ruwaito hakan, a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar 31 ga Maris. Boko Haram na sake ƙwace ikon wasu yankuna a...
Li Qiang ya yi nuni da cewa, a kwanakin baya, kasar Amurka ta sanar da kara buga harajin kwastam ga dukkan kasashe abokanta na cinikayya ciki har da Sin da Turai, wanda mataki ne da bangare daya ya dauka, da ba da kariya ga cinikayya, da cin zarafin tattalin arziki. Ya ce, kasar Sin ta...
Hukumar Kula da Jin DDaɗin Alhazai ta Jihar Kwara ta ayyana ranar Juma’a 11 ga Afirilun 2025 a matsayin ranar ƙarshe da za a kammala biyan kuɗin aikin hajjin bana ga dukkan maniyyatan jihar. Shugaban hukumar, Alhaji Abdulkadir Abdulsalam ne ya bayyana hakan a yayin wata hira da manema labarai a Ilori. Alhaji Abdulkadir ya...

Yan Sanda A Saudiya Sun Tsare Wata Bafalasdinya Saboda Bayyana Tutar Kasarta A Kan Jakarta A Masallacin Ka’aba
Jami’an yan sanda a birnin Makka sun tsare wata Bafalasdiniya wacce ta baje Jakarta dauke da tutar kasarta Falasdinu tare da zarginta na bayyana wani abu na siyasa a lokacin aikin umran da take yi. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kamfanin dillancin labaran Mint-Press yana cewa matar ta shiga masallacin haramin...
Jamhuriyar Nijar ta ayyana harshen Hausa a matsayin na kasa, yayin da Faransanci ya zama harshen aiki mai sauki, don haka, Faransanci ba yaren hukuma ne ba. Matakin dai ya dogara ne da shawarwarin da babban taron kasar ya gabatart a watan Fabrairu, wanda kuma shugaban kasar Janar Abdourahamane Tiani ya amince da shi a...
Hakazalika, Lin Jian ya jaddada cewa, ya kamata kasa da kasa su bi ka’idojin yin shawarwari da samun ci gaba da more fasahohi da juna, da kiyaye bin ra’ayin bangarori daban daban, da kin amincewa da ra’ayin bangare daya da ba da kariya ga cinikayya, da tabbatar da tsarin kasa da kasa bisa tushen MDD...
Ya kuma jaddada cewa, manufofin kasar Sin na jan hankalin jari daga waje ba su sauya ba, kuma ba za su sauya ba. Tattaunawar na zuwa ne yayin da ake tsaka da shiga wani sabon zagayen zullumi dangane da cinikayya a duniya inda a baya-bayan nan Amurka ta kara haraji kan abokan cinikayyarta, ciki...
Ƙasar Saudiyya ta musanta batun da ake yaɗawa cewa ta sanya Najeriya a jerin ƙasashen da ta hana biza. Sanarwar da aka yaɗa a kafofin sadarwa ta bayyana cewa daga ranar 13 ga Afrilu, Saudiyan za ta daina bai wa ƙasashen Masar, India, Pakistan, Morocco, Tunisa, Yemen da Aljeria bizar aiki, ta ziyara, da ta...
Sufeto Janar na ’Yan Sandan Najeriya, Kayode Egbetokun, ya janye gayyatar da aka yi wa Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, kan hawan sallah. Maimaikon ya Sarkin ya je Abuja domin yi masa tambayoyi, Sufeto Janar ya umarci rundunar ’yan sandan jihar, yi wa Sanusi II tambayoyi. Gwamnonin Arewa sun yi Allah-wadai da hare-haren...
Wannan ya haifar da wani rikici, wanda ya jawo mutuwar Usman Sagiru da raunata wasu da dama. Wannan shi ne abin da ‘Yansanda suka yi ƙoƙarin hana faruwa, kuma sun ɗauki matakan gaggawa bayan wannan al’amari. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na...
Sufeto Janar na ’Yan Sandan Najeriya, Kayode Egbetokun, ya soke gayyatar da aka yi wa Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, kan hawan sallah. Maimaikon ya Sarkin ya je Abuja domin yi masa tambayoyi, Sufeto Janar ya umarci rundunar ’yan sandan jihar, yi wa Sanusi II tambayoyi. Gwamnonin Arewa sun yi Allah-wadai da hare-haren...
Ƙungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa (NSGF), ta yi Allah-wadai da harin da aka kai wasu ƙauyuka na Ƙaramar Hukumar Bokkos da ke Jihar Filato. Ƙauyukan da abin ya shafa sun haɗa da Ruwi, Manguna, Daffo, Josho da Hurti. Sojoji sun kashe ’yan bindiga 3 a Taraba Fasinja ya yi ƙoƙarin buɗe ƙofar jirgi a sararin samaniya...
Nemi adalci maimakon babakere. Cin zali ta hanyar kakaba haraji da Amurka ke yi, ya haifar da suka da adawa da martani daga kasashe da dama. Takarda mai dauke da matsayar kasar Sin da aka fitar dangane da cin zalin ta samu goyon bayan daga kasa da kasa. Sakamakon wani nazari da kafar CGTN ta...
Ya kuma bukaci jama’a musamman mazauna Damaturu da su kwantar da hankulan su, su ci gaba da gudanar da ayyukansu na yau da kullum ba tare da wata fargaba ba. Abdulsalamu ya bada tabbacin aniyar gwamnati na wanzar da zaman lafiya da tsaro, yayin da ya yi gargadi kan yada labaran karya da ka...
Sakataren Harkokin Wajen Birtaniya, David Lammy, ya soki matakin Isra’ila na hana wasu ‘yan majalisar dokokin Birtaniya biyu shiga ƙasar, yana mai cewa matakin bai dace ba kuma abin damuwa ne. Tsarewa da hana ‘yan Majalisar Wakilan Birtaniya biyu da ke cikin tawagar ‘yan majalisa zuwa Isr’aila shiga cikin ƙasar, abin da ba za a...
Sakatare janar na majalisar dinkin duniya ya ce ba wanda zai ci ribar yakin cinikayya a yayin da ake ta cacar baka kan harajin fito da shugaban Amurka Donald Trump ya lafta wa duniya. Antonio Guitess ya yi wannan gargadin ta bakin kakakinsa inda ya yake bayyana cewa, “ba wanda ke yin nasara a yakin...
Gwamnatin Jihar Borno ta nuna matuƙar damuwarta kan yadda wasu matasa ke amfani da kafafen sada zumunta na yanar gizo wajen yin kalamai masu nuna barazana da al’adunmu na rashin ɗa’a da rashin sanin ya kamata. A cikin wata sanarwa da Ma’aikatar yaɗa labarai da tsaron cikin gida ta jihar Borno ƙarƙashin Kwamishinanta Farfesa Usman...
Gwamnatin kasar Amurka ta sanar da sanya harajin fito na ramuwar gayya kan dukkan kawayen cinikayyarta a ranar 2 ga wata, inda kasar Sin ta mayar da martani nan take, da zummar kiyaye halastaccen hakkinta. Daga baya a ranar 3 ga wata, Sin ta sanar da wasu jerin matakai, ciki har da kara sanya harajin...
Hedikwatar ’yan sandan Nijeriya ta gayyaci Sarkin Kano na 16 Muhammadu Sanusi II domin amsa tambayoyi kan wani lamari da ya faru a lokacin bikin Sallah a Kano. A baya dai rundunar ’yan sanda tare da sauran wasu jami’an tsaro a jihar sun soke duk wani hawan bikin Sallah, musamman jerin gwanon dawakai a jihar,...
Wani jami’in ’yan sanda ya shaida wa Leadership cewa: “Duk da haramta bukukuwan sallah, an gudanar da hawa a motocin Sarkin a rana ta uku bayan Sallah, lamarin da ya haifar da ce-ce-ku-ce.” Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, babu wani bayani daga fadar Sarkin Kano game da gayyatar da aka yi masa. Ga hoton...

Ofishin Jakadancin Sin Da Ke Amurka Da Jakadan Sin A Burtaniya Sun Nuna Adawa Da Matakin Harajin Fito Na Ramuwar Gayya Da Amurka Ta Dauka
A ranar Alhamis ne, ofishin jakadancin kasar Sin da ke Amurka da jakadan Sin a Burtaniya Zheng Zeguang, suka bayyana matukar kin amincewa da harajin fito “na ramuwar gayya” da Amurka ta kakaba. Suna masu nuni da cewa, Amurka ta sanar da karin harajin fito kan kayayyakin da ake shigowa da su daga kasashe da...
Mai magana da yawun jam’iyyar APC a Jihar Ogun, Tunde Oladunjoye, ya rasu. Ya rasu ne a ranar Juma’a, 4 ga watan Afrilu, 2025, yayin da yake jinya a ƙasar waje kan wata rashin lafiya da ba a bayyana ba. An haramta wa Akpabio da Natasha tattaunawa da manema labarai Yadda aka yi jana’izar Dokta...
SShugaban kasa Bola Tinubu ya bayyana alhininsa bisa rasuwar fitaccen malamin addinin Musulunci a jihar Bauchi, Dr Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi, wanda ya rasu a daren Juma’a yana mau shekaru 68 a duniya. Mai ba Shugaban ƙasa shawara na musamman kan Harkokin yada labarai, Bayo Onanuga, ne ya fitar da sanarwar, inda ya jaddada...
Matakan harajin fito na Amurka na haifar da koma-bayan tsarin cinikayyar duniya. Game da wannan batu, kafar CGTN ta babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin, ta gudanar da wani binciken jin ra’ayin al’umma ga masu amfani da intanet na sassan kasa da kasa, inda suka yi tir da irin wannan abun da...
Ya roƙi Allah da Ya ji ƙansa, tare da bai wa iyalansa da almajiransa haƙurin rashinsa. Hakazalika, tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023 kuma jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana kaɗuwarsa game da fitaccen malamin. Ya bayyana haka ne cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafukan sada zumunta. “Ina miƙa...
Kotun Ƙoli ta soke hukuncin da Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Abuja, ta yanke wanda ya amince da Julius Abure a matsayin shugaban jam’iyyar LP na ƙasa. A ranar Juma’a, wani kwamitin alƙalai biyar na Kotun Ƙoli, ya ce Kotun Ɗaukaka Ƙara ba ta da hurumin yanke hukunci kan shugabancin jam’iyyar. APC ta ƙaryata jita-jitar...
Gwamnatin jihar Kwara ta kaddamar da wani shiri na sauya fasalin noma domin habbaka kiwon dabbobi da bunƙasa yankunan karkara a fadin jihar. Jami’in shiri na musamman kan harkar noma wato Special Agro Industrial Processing Zone (SAPZ) a turance, Dr. Busari Isiaka ne ya bayyana hakan ga manema labarai. Ya ce wannan shiri ne da...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun ya bayyana yau Alhamis cewa, kasar Sin ta bukaci Amurka da ta gyara kuskuren da ta yi na kakaba “harajin ramuwar gayya,” kana ta magance sabanin dake tsakaninta da kasar Sin da sauran kasashen duniya dangane da tattalin arziki da cinikayya, ta hanyar yin shawarwari bisa daidaito,...
Kungiyar malaman musulmi ta duniya ta fitar da wata sanarwa inda ta bayyana cewa laifuffukan gwamnatin sahyoniyawa a Gaza sun ketare dukkanin iyakokin kasa da kasa, tare da yin kira da a kawo karshen kashe-kashen mata da kananan yara da makamai masu guba, da yunwa, kishirwa, da cututtuka. A cewar jaridar Arabi 21, kungiyar malaman...
Ƙasurgumin ɗan bindiga, Bello Turji, da mayaƙansa sun kai mummunan hari garin Lugu da ke Ƙaramar Hukumar Isa a Jihar Sakkwato, inda suka kashe manoma 11. Rahotanni sun nuna cewa harin ya faru ne yayin da Turji ke dawowa daga wata ziyarar sallah da ya kai yankin. Najeriya ta yi kuskuren barin Boko Haram ta...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A ranar Talata ne, Allah ya yi wa Alhaji Abbas Sanusi, Galadiman Kano kuma babban mai nada sarki a masarautar Kano rasuwa. A safiyar Laraba, 2 ga watan Afrilun 2025 aka yi jana’izar sarkin wanda ya shafe fiye da shekaru 60 yana hidimtawa masarauta, ya rasu yana da shekara 92 bayan doguwar jinya. Ya bar...
Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu, ya bayyana jimaminsa kan rasuwar Galadiman Kano, Alhaji Abbas Sanusi, wanda yake ɗaya daga cikin masu naɗa Sarki a Kano. Alhaji Sunusi, ya rasu yana da shekaru 92 bayan fama da doguwar rashin lafiya. Uromi: Barau ya ziyarci iyalan waɗanda aka kashe, ya ba su kyautar N16m Basakkwacen da ya yi...
Ƙungiyar matasan Arewa ta yi Allah-wadai da jita-jitar da ake yaɗawa cewa an kashe wani ɗan ƙabilar Ibo a Jihar Kano saboda kisan wasu Hausawa mafarauta da ɓatagari suka yi kwanan a Jihar Edo. A wani taron manema labarai da gamayyar ƙungiyoyin matasa na ƙabilu daban-daban, ta ce abin takaici ne kisan da aka yi...
A wata tattaunawa ta wayar tarho da shugaban hukumar makamashin Nukliya ta duniya Rafael Grossy Abbas Aragchi ministan harkokin wajen kasar Iran ya bukaci hukumar ta bayyana matsayinta dangane da shirin makamashin nukliyar kasar Iran. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ta nakalto ministan yana fadawa Grossy bayyana matsayin hukumarsa dangane da shirin nukliyar...
A yau Talata, kasar Sin ta bayyana cewa, za ta dauki matakan ramuwar gayya domin mayar da martani game da sanarwar da Amurka ta fitar ta saka takunkumin biza a kan jami’an kasar Sin, bisa hujjar hana izinin shiga yankin Xizang mai cin gashin kansa, da ke kudu maso yammacin kasar Sin. A yayin taron...
Yakin cinikayya ba zai taba durkusar da kasar Sin ba, sai dai kaikayi ya koma kan mashekiya. Yayin da wasu kasashen ke aiwatar da kariyar cinikayya da kokarin rufe kofarsu ga sauran sassan duniya, kasar Sin ta kara bude kofarta, tana kuma maraba da ’yan kasuwa daga kasa da kasa. Maimakon kawo cikas, kasar Sin...
Mai Martaba Idi Chiroma, Sarkin Gassol a Jihar Taraba, ya ce Musulmin da suka gudanar da azumin watan Ramadan na shekarar 2025 sun nuna tsayin daka wajen sadaukarwa ga addini. Chiroma ya bayyana hakan ne a ranar Lahadin da ta gabata yayin da yake jawabi ga al’ummar Musulmi a wani bangare na bikin Sallar...
Haka kuma, ya yaba wa Gwamna Okpebholo bisa tattaunawarsa da shugabannin al’ummar Hausa a Edo domin hana rikici da kuma alƙawarin biyan diyya ga iyalan mamatan. “Biyan diyya da aka alƙawarta abu ne mai kyau, amma dole ne a tabbatar da hakan cikin gaggawa domin taimaka wa iyalan da suka rasa masu ɗaukar nauyinsu,” ya...
Da yake tabbatar da afkuwar lamarin, Malam Tanko Isiyaka, shugaban fulani na gundumar Bondon, ya bayyana cewa marigayin ya fito ne daga jihar Bauchi. Ya bayyana alhininsa kan faruwar lamarin tare da yin kira da a yi addu’a tare da tallafa wa iyalan mamacin. An yi jana’izar mamacin kamar yadda addinin Musulunci ya tanada....
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar, ya yi kira ga ’yan Najeriya da su guji cin mutuncin shugabanni yayin da suke bayyana matsalolinsu, inda ya jaddada cewa girmamawa da ladabi suna fi tasiri wajen samun mafita. “Idan ka zagi shugabanka, ta yaya kake so ya taimaka maka?” in ji shi. Masar ta miƙa wa Hamas...