Gwamnati ta ƙaddamar da jiragen ruwa na zamani 20 a Sakkwato
Published: 18th, September 2025 GMT
Gwamnan Sakkwato, Dakta Ahmad Aliyu, ya ƙaddamar da jiragen ruwa na zamani guda 20, tare da riguna ruwa (life jackets) 2,000, domin rage haɗurran da ke aukuwa sakamakon ambaliya da nutsewar jirage a sassan jihar.
An ƙaddamar da jiragen ne a ƙaramar hukumar Wamakko a ranar Laraba, inda gwamnan ya bayyana cewa wannan mataki na daga cikin shirin gaggawa na tallafa wa al’ummar da ke fama da illar ambaliya da haɗurra a ruwa.
“Mun dauki wannan mataki bayan rahotannin da muke samu na yawaitar hatsarurruka da rasa rayuka da dukiya sakamakon jiragen katako da mutane ke amfani da su,” in ji Gwamna Ahmad Aliyu.
Gwamnan ya miƙa godiya ga shugabar hukumar bayar da agajin gaggawa ta ƙasa (NEMA), Hajiya Zubaida Umar, bisa hadin kai da goyon bayan da hukumar ke bayarwa domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiya, tare da inganta ayyukan ceto da agaji a jihar.
Aminiya ta ruwaito cewa, an horar da direbobin jiragen ruwan da za su riƙa kula da su, kafin a raba su zuwa ƙananan hukumomi goma (10) da suka fi fuskantar barazanar ambaliya da suka haɗa da: Goronyo, Shagari, Sabon-Birni, Wurno, Rabah, Wamakko, Silame, Kebbe, Tambuwal da Isa.
Gwamnan ya kuma yi gargaɗin cewa za a hukunta duk wani da ya ɗauki lodi fiye da ƙima a cikin jiragen, yana mai cewa “wannan jirage da rigar ruwa na jama’a ne, kuma wajibi ne shugabannin ƙananan hukumomi su tabbatar da kula da su yadda ya kamata.”
Sai dai wasu daga cikin mazauna yankunan da za a rabawa jiragen sun bayyana ra’ayinsu dangane da lamarin, inda wani Tanimu Goronyo, daga karamar hukumar Goronyo, ya ce: “Gwamnatin Sakkwato ta kauce hanya.
“Abin da muke bukata a yanzu shi ne hanyoyin mota da magudanan ruwa. Ambaliya tana mamaye yankunan mu ne saboda babu hanya. Idan gwamnati ta kashe wannan kuɗi wajen gina hanya, sai an fi cin moriya.”
Shi ma wani Muhammad Kabiru, daga Silame, ya bayyana farin cikinsa da sayen jiragen, sai dai ya roƙi gwamnati da ta mai da hankali wajen gina hanyoyin mota saboda abin da suka fi buƙata ke nan.
“Mu a Silame jirgi yana da amfani, amma hanyar mota ita ce babbar buƙatar mu. Idan aka samar da ita, ambaliya ba za ta hana mu zirga-zirga ba.”
Yayin da gwamnatin Sakkwato ke ɗaukar matakan gaggawa don rage hatsarurruka da ambaliya ke haifarwa, al’umma na ci gaba da neman tsarin da zai magance tushen matsalar – musamman samar da ingantattun hanyoyi da magudanan ruwa a karkara.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Jihar Sakkwato Jiragen ruwa
এছাড়াও পড়ুন:
An kama ɗaya daga cikin manyan kwamandojin IPOB
Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya ta sanar da samun nasarar cafke Ifeanyi Eze Okorienta, wanda aka fi sani da “Gentle de Yahoo”, ɗaya daga cikin manyan kwamandojin ƙungiyar IPOB, a wani samame da ta kai a yankin kudu maso gabashin ƙasar.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN ya ruwaito wata majiya daga hedikwatar rundunar sojin tana cewa an cafke Gentle de Yahoo ne yayin farmakin da sojojin suka kai a ranar Lahadi kan sansanonin ’yan ƙungiyar a cikin wani dajin da ke ƙaramar hukumar Okigwe a Jihar Imo.
An tattauna yadda za a inganta walwalar malamai a Gombe Tinubu ya janye dokar ta-ɓaci da ya sanya a RibasMajiyar ta ce a yayin cafke jagoran na IPOB, an kuma ƙwato makamai da dama daga hannunsa, ciki har da bindigogi kirar Turai, harsasai, kakin sojoji da na ’yan sanda.
“Cafke wannan kwamanda babban ci gaba ne wajen murƙushe ayyukan ta’addanci da ƙungiyar IPOB ke aikatawa, musamman a yankunan da suke hana zaman lafiya,” in ji majiyar.
Kungiyar IPOB, wacce ke fafutukar ballewa daga Najeriya don kafa ƙasar Biyafara, ta kasance a gaba-gaba wajen aikata hare-hare da ta da tarzoma a jihohin kudu maso gabas, musamman ta hannun sashen rundunar da suka kafa da kansu mai suna Eastern Security Network (ESN).
Ana dai zargin cewa Eze yana ɗaya daga cikin jagororin da ke tsara harin kwantan bauna, da hana zirga-zirga a wasu sassan yankin, wanda hakan ya jefa al’umma cikin fargaba da zaman ɗar-ɗar.
Wannan nasara na zuwa ne bayan makonni kaɗan da wata kotu a ƙasar Finland ta yanke wa Simon Ekpa, wani babban jigo a ƙungiyar IPOB, hukuncin ɗaurin shekaru shida a gidan yari kan laifukan da suka shafi ta’addanci da tayar da zaune tsaye.
Masu sharhi na ganin cewa cafke Gentle de Yahoo wata alama ce da ke nuna cewa ana shirin ragargaza ƙungiyar IPOB gaba ɗaya, duk da cewar har yanzu akwai sauran rina a kaba, musamman ganin cewa wasu sassan yankin na ci gaba da fuskantar matsalolin tsaro.