Ci Gaban Tattalin Arzikin Sin Na Taimaka Ga Bunkasa Al’adunta Da Mu’amalar Al’adu Tsakaninta Da Kasashen Duniya
Published: 18th, September 2025 GMT
Hukumar Kididdiga ta kasar Sin ta samar da alkaluman tattalin arziki na watan Agusta a kwanan nan, alkaluman da suka nuna cewa, tattalin arzikin Sin yana ci gaba da bunkasa ba tare da tangarda ba, musamman a fannin sana’o’in ba da hidima, inda ma’aunin ISP game da ayyukan ba da hidima ya karu da kashi 5.
Abin lura shi ne, a matsayin wani muhimmin bangare na sana’o’in ba da hidima na zamani, sana’ar al’adu ita ma tana nuna gagarumin ci gaba. A taron dandalin kasa da kasa kan harkokin al’adu na “Golden Panda” da aka gudanar kwanan nan, ministar fasaha, al’adu, yawon bude ido da tattalin arzikin kirkire-kirkire ta Najeriya, Hannatu Musawa, ta yaba wa saurin ci gaban sana’o’in kirkire-kirkire ta Sin, inda ta bayyana cewa, Sin tana hada hangen nesa da kirkira, wanda ya sa ta zama hasken gwarazan al’adu a duniya. Ta kuma bayyana fatan kara karfafa hadin gwiwa tsakanin Najeriya da Sin a fannoni na kirkire-kirkire da al’adu.
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya taba bayyana cewa, “Tattalin arziki shi ne tushen al’adu, inda karfin tattalin arziki ke aza tubali mai inganci ga ayyukan raya al’adu.” Ci gaban tattalin arzikin Sin ba tare da tangarda ba ya kafa tushe mai karfi ga bunkasar al’adu, bunkasar al’adu ta kuma samar da gadar fahimtar juna a tsakanin Sin da sauran kasashe. (Mai zane da rubutu: MINA)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
An Bude Dandalin Tattauna Batutuwan Tsaro Na Xiangshan Karo Na 12 A Beijing
Da safiyar yau 17 ga watan Satumba, aka bude dandalin tattauna batutuwan tsaro na Xiangshan karo na 12 da zai dauki kwanaki 3, daga raneku 17 zuwa 19 ga wannan nan, bisa jigon “daukaka tsarin duniya da inganta neman ci gaba cikin lumana”, a nan birnin Beijing.
Tawagogi sama da 100 na gwamnatocin kasashe daban-daban da yankuna da wakilan kungiyoyin kasa da kasa ne ke halartar taron, inda yawan masu rajista ya wuce 1,800.
Da safiyar yau, taron ya shirya tarukan tattaunawa guda 6 bisa jigon “ma’anar cimma nasarar yakin duniya na kin tafarkin murdiyya” da “madaidaitan hanyoyi da manyan kasashe za su bi na yin mu’ammala”, da “hanyoyin warware rikice-rikicen shiyya-shiyya”, da “cika shekaru 80 da kafuwar MDD: samun ci gaba cikin sauye-sauye”, da “amfani da sarrafa sabbin fasahohi”, da kuma “kirkire-kirkire a bangaren kimiyya da fasaha da sauye-sauyen yanayin yaki”. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp