Iran Ta Bayyana Shirinta Na Halartar Taron Shekara-Shekara Na Hukumar Makamashin Nukiliya
Published: 14th, September 2025 GMT
Cikakkun bayanai kan halartar Iran zuwa taron shekara- shekara na hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA
Shugaban Hukumar Makamashin Nukiliya na kasar Iran Muhammad Islami ya yi karin haske kan yadda Iran za ta halarci taron shekara -shekara na hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA.
Mohammad Eslami ya bayyana dangane da cikakkun bayanai na halartar taron shekara- shekara na hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA inda ya ce: A gobe ne za a fara taron shekara- shekara na hukumar IAEA karo na 69 a birnin Vienna.
Ya kara da cewa: “Iran zata tsara tare da gabatar da wani kuduri na yin Allah wadai da harin da aka kai kan cibiyoyin nukiliyarta na zaman lafiya a wurin taron.”
Shugaban Hukumar Makamashin Nukiliya ya ce: “Suna fatan samun cikakken bayani kan abin da ya faru da cibiyoyin makamashin nukiliyar Iran ta hanyar halartar wannan taro.”
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Ta Bayyana Rashin Halarta Tawagarta A Kada Kuri’a Kan Batun Falasdinu September 14, 2025 Tsananin Masifar Da Falasdinawa Ke Ciki A Gaza Saboda Hare-Haren Gwamnatin Mamayar Isra’ila September 14, 2025 Amurka Ta Ce; Harin Isra’ila Kan Birnin Doha Ba Zai Shafi Kawancenta Da Gwamnatin ‘Yan Sahayoniyya Ba September 14, 2025 Tsohon Kwamandan IRGC Ya Ce Boma-Boman HKI Na Zuwa Kanku Idan Kunki Samar da Kawance September 14, 2025 HKI Tana Ci Gaba Da Rusa Dogayen Gine-Gine A Gaza A September 14, 2025 Dubban Mutanen New Zealanda Sun Fito Jerin Gwanon Goyon Bayan Falasdinawa September 14, 2025 Velayati: Taron Malaman Yahudu A Azerbaijan Tsokana Ce Ga Musulmi Shia September 14, 2025 Wajibi Ne Kasashen Musulmi Su Dauki Mataki Wajen Kawo Karshen Rashin Hankalin Isra’ila. September 13, 2025 Sojojin Isra’ila Sun Kashe Masu Neman Agaji 4 Tare Da Jikkata Da Dama A Gaza. September 13, 2025 Kasar Masar Ta Gano Makircin Isra’ila Na Kashe Shuwagabannin Hamas A Kasar Ta September 13, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: shekara na hukumar taron shekara
এছাড়াও পড়ুন:
Iran Ta Jaddada Bin Hanyar Diflomasiya Ko Da A Lokacin Yaki Ne Amma Ba Zata Amince Da Bin Umarni Ba
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Ana ci gaba da bin hanyar diflomasiyya ko da a ƙarƙashin fada ce amma ba za a yi tattaunawa a ƙarƙashin umarni ba
Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araqchi ya tabbatar a ranar Laraba cewa: Hanyar diflomasiyya za ta ci gaba da kasancewa a buɗe ga Iran, ko da a lokutan mawuyacin hali. Duk da haka, ya jaddada cewa Iran ba za ta yi tattauna da wani maƙiyi mai wuce gona da iri da mai daukar matakin ƙarfi ba, ta hanyar nuna tashin hankali da barazana ba.
Jawabin Araqchi ya zo ne a lokacin da ya halarci zaman taron kan tattaunawar kasa ta Azerbaijan, mai taken “Diflomasiyya ita ce Ingancin Hanyar da Iran ta Amince da ita,” wanda aka gudanar a birnin Tabriz. Ya lura cewa diflomasiyyar Iran na ci gaba da dogaro da gadon tarihi na muhimman ƙa’idodi da sassauci a cikin hanyoyi, kuma ya yi kira da a farfaɗo da rawar da diflomasiyyar gida ke takawa a yankunan biranen arewa da arewa maso yammacin Iran.
Araqchi ya jaddada cewa: Diflomasiyya na nan a fage har ma a lokutan yaƙi, yana mai nuni da cewa manufar Ma’aikatar Harkokin Waje ita ce kare haɗin kan ƙasar Iran, da albarkatun kasa da kuma ‘yancin ƙasar, ikon mallakar ƙasa da kuma muradun jama’arta.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Qalibaf: Amurka Tana Yaudarar Duniya Da Zaman Lafiya, Alhalin Tana Ci Gaba Da Kai Harin Wuce Gona Da Iri October 30, 2025 Ci Gaba Da Killace Gaza Bayan Tsagaita Bude Wuta Ya Janyo Mutuwar Mutane 1000 A Yankin October 30, 2025 Kungiyar Rapid Support Forces Ta Sanar Da Kafa Kwamitin Bincike Kan Cin Zarafin Al’umma A El Fasher October 30, 2025 An Kafa Dokar Ta Baci A Darul-Salam Saboda Tarzoman Zaben Shugaban Kasa A Tanzania October 30, 2025 Rasha Da Amurka Sun Sake Dawo Da Gwaje-gwajen Makaman Nukiliya October 30, 2025 Kasar Czech Ta Hana Wa Wani Sojan HKI Shiga Kasar Bisa Gargadin Faransa October 30, 2025 Sojojin HKI Sun Kutsa Kudancin Lebanon October 30, 2025 Adadin Falasdinawan Da Su Ka Yi Shahada A Cikin Sa’o’i 24 Sun Haura 100 October 30, 2025 Amurka Ta Hana Marubuci Dan Nigeria Wole Soyinka Izinin Shiga Amurka October 30, 2025 Pakistan Tayi Barazanar Daukar Mataki Bayan Rushewar Yarjejeniyar Dakatar Da Bude Wuta Da Afghanistan. October 29, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci