2025-09-17@20:32:18 GMT
إجمالي نتائج البحث: 877

«Dausayin Musulunci»:

    A yau Laraba ne aka bude bikin baje koli karo na 22, na Sin da kasashe membobin kungiyar ASEAN ko (CAEXPO), da kuma taron dandalin kasuwanci da juba jari na Sin da ASEAN ko CABIS, a birnin Nanning na jihar Guangxi ta kabilar Zhuang mai cin gashin kai dake kudancin kasar Sin. A shekarun baya bayan nan, Sin da kungiyar ASEAN, sun ci gaba da cimma manyan nasarori tare a fannin bunkasa dunkulewar tattalin arzikin shiyyarsu, da fadada damar bai daya ta cudanyar mabambantan sassa, a gabar da ake fuskantar yanayin tangal-tangal a duniya. Wata kuri’ar jin ra’ayin jama’a da kafar CGTN ta kasar Sin ta gudanar, ta shaida yadda kaso 92.8 bisa dari na masu bayyana ra’ayoyi suka amince...
    Ma’aikatar shari’ar kasar Iran ta sanar da zartar da hukuncin kisa kan wani ba’iraniye dan leken hukumar Mossad ta Isra”ila A safiyar yau Laraba ne ma’aikatar shari’ar kasar Iran ta sanar da zartar da hukuncin kisa kan Babak Shahbazi, dan leken asirin Mossad da aka samu da laifin hada kai da yahudawan sahayoniyya a fannin leken asiri da kuma harkokin tsaro da kuma musayar bayanai da jami’an Mossad. An zartar da hukuncin kisar ta hanyar rataya a safiyar yau bayan kammala matakan shari’a kuma kotun kolin kasar ta amince da hukuncin. Babak Shahbazi, dan Rahmatullah, ya yi aiki a matsayin dan kwangilar kere-kere da sanya kayan masana’antu ga kamfanonin da ke da alaka da cibiyoyin tsaro, sojoji, da cibiyoyin sadarwa...
    Sun jaddada cewa dole ne manyan kafafen sada zumunta su kare ‘yancin yin magana. Sun kuma yi kira ga ‘yan Nijeriya, ‘yan jarida, da masu fafutukar kare haƙƙin bil’adama su tashi tsaye don hana abin da suka kira yunƙurin mayar da Nijeriya “mulkin kama-karya a intanet.” Lamarin ya biyo bayan wa’adin sati guda da DSS ta bai wa Sowore da ya goge wasu wasu rubuce-rubuce game da Shugaba Bola Tinubu, wanda ya ƙi amincewa. Hakan ya sa hukumar ta shigar da shi ƙara a kotu. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya...
    Falasdinawa 78 ne aka kashe a yau a Gaza, mafi yawansu a birnin Gaza a yayin da Isra’ila ke ci gaba da kai hare-hare a kasa da kuma umarnin tilastawa mazauna Gaza yin kaura. An bayar da rahoton karin mutuwar mutane uku sakamakon yunwa da killace yankin. Mazauna Gaza sun bayyana tashin bama-baman a matsayin abun tashin hankali da kuma yunkurin shafe wata al’umma. Sojojin Isra’ila sun zafafa kai hare-hare a birnin Gaza, inda suka kai hari kan unguwannin da ke da yawan jama’a. Katangar da Isra’ila ta kakaba mata da kuma karancin abinci na ci gaba da zurfafa rikicin jin kai. Yakin da Isra’ila ta kwashe watanni ana yi a Gaza ya janyo hasarar rayukan fararen hula da dama....
    Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Ondo ta tabbatar da kama wata mata mai suna Iluyemi Bosede bisa zargin kashe yayarta, Tewogboye Omowumi, a Akure, babban birnin jihar. A cewar sanarwar da Jami’in Hulɗa da Jama’a na rundunar, Olayinka Ayanlade, ya fitar a ranar Talata, ya ce lamarin ya faru ne a ranar shida ga Satumba, 2025, bayan wata sa’insa da ta kaure tsakanin matar da marigayiyar kan Naira 800. Tun Tinubu yana Gwamna ba abin da ya fi shahara da shi kamar tara haraji – Adebayo DAGA LARABA: Dalilan Tashin Farashin Doya A Wasu Kasuwannin Najeriya Jami’in ya bayyana cewa Bosede ta ture ’yar uwarta har ta faɗi ƙasa, lamarin da ya haifar da mutuwarta. Ya ce, “Binciken farko ya...
    Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar SDP a zaben 2023, Adewole Adebayo, ya ce Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ba shi da burin da ya wuce na tara haraji tun yana Gwamna a Legas. Adebayo ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels. Sojoji sun harbe mayaƙan ISWAP 8 a Borno DAGA LARABA: Dalilan Tashin Farashin Doya A Wasu Kasuwannin Najeriya A cewarsa, “Kowa ya san cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu sananne ne wajen karbar haraji. Amma wannan tsarin karbar haraji ya fi tsarin da ya tarar da shi wanda ba shi da tsari. “Ya yi hakan a Legas, sannan ya zo Abuja domin ya dora daga...
    Ƙungiyar shugabannin ƙananan hukumomin Jihar Yobe (ALGON) ta karrama Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, da lambar yabo ta karramawa bisa himmar ayyukan raya ƙasa da gwamnatinsa ke gudanarwa a faɗin jihar. Karramawar, wacce aka bayyana a matsayin irinta ta farko a tarihin Jihar Yobe, shugabannin ƙananan hukumomi 17 na jihar suka ba da ita ga gwamna. Gwamnatin Kano ta gayyaci Mai Dubun Isa da Shehi Tajul-Izzi kan shirya muƙabala Sojoji sun harbe mayaƙan ISWAP 8 a Borno Da yake jawabi, shugaban ƙungiyar ALGON a Jihar Yobe, kuma shugaban ƙaramar hukumar Damaturu, Alhaji Bukar Adamu, ya yaba da yadda Gwamna Buni yake gudanar da harkokin mulki na bai ɗaya. Ya ce nasarorin da aka samu sun haɗa da fannoni na...
      Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Mohammad Islami shugaban hukumar kula da makamashin nukiliya na Iran ta fadi a bayan taron da hukumar ta IAEA dake gudanarwa a Vienna yanzu haka cewa yana neman hukumar ta IAEA ta goyi bayan kudurin da ta fitar kuma ta yi Tir da harin wuce gona iri da hki ta kai kan tashoshin nukiliyarta. Wakilai guda 180 a hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya ne suka hallara abirnin viyana daga ranar 15-19 domin gudanar da taron kasa da kasa karo na 69 da hukumar ta duniya ke shiriya a hedkwatarta dake Vienna na kasar Austeria Yace mun bayyana cewa alummar Iran basu da rauni wajen fuskantar duk wata barazana, kuma basu da niyyar mika wuya, ,ya kara da cewa...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Matakin hana malaman da ba su da rajista hawa mumbari a Neja yana ci gaba da yamutsa hazo a ciki da wajen jihar. Yayin da wasu suke ganin wannan mataki bai dace ba, wasu kuwa gani suke faduwa ta zo daidai da zama, wato matakin ya zo a daidai lokacin da ake bukata. NAJERIYA A YAU: Yadda Wasu Al’ummomi Suke Kare Kansu Daga Barnar Ambaliyar Ruwa DAGA LARABA: Dalilan Da Suka Sa Nayi Yunkurin Kashe Kaina Har Sau Uku Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kan tanadin Dokar Kasa game da wannan batu. Domin sauke shirin, latsa nan
    Adadin mutanen da suka yi shahada sakamakon kisan kiyashin da ‘yan sahayoniyya suke yi a Gaza ya doshi 65,000 Adadin mutanen da suka yi shahada sakamakon yakin da yahudawan sahayoniyya suka kakaba wa Falasdinawa a yankin Zirin Gaza ya karu zuwa shahidai 64,871 da kuma jikkatan wasu 164,610 tun daga ranar 7 ga watan Oktoban shekarar 2023. Bisa kididdigar baya-bayan nan da ma’aikatar lafiya ta Falasdinu ta fitar a zirin Gaza a ranar Lahadin da ta gabata, mutane 12,321 ne suka yi shahada yayin da wasu 52,569 suka samu raunuka tun bayan da gwamnatin mamayar Isra’ila ta sake komawa yaki kan Falasdinawa a ranar 18 ga watan Maris. A cikin sa’o’i 24 da suka gabata, Falasdinawa 68 ne suka yi...
    Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa ta Barcelona ta koma matsayi na biyu a kan teburin gasar La Liga ta Sifaniya bayan ta lallasa ƙungiyar Valencia a filin wasa na Johan Cruyff da ke birnin Barcelona. Fermin Lopez, Raphinha da Lewandowski ne suka zura ƙwallaye shida a ragar Valencia a wasan da aka buga da misalin ƙarfe 8 na dare agogon Nijeriya. Da wannan nasara, Ƙungiyar da Hansi Flick ke jagoranta ta tara maki 10 a cikin wasanni huɗu da ta buga a gasar. Kano Pillars Ta Samu Nasarar Farko A Gasar Firimiyar Nijeriya Ta Bana Rashford Na Dab Da Komawa Barcelona A Matsayin Aro An yi tsammanin Barcelona za ta fara buga wasan gidanta a sabon filin Spotify Camp Nou da aka...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ramezan sharif  wani babban jami’I yace idan gwamnatin HKI ta yi kuskure kan kasar Iran, za ta fuskanci mayar da martani mai tsananin, yace ba zamu jira taimakon kowa ba wajen kare kasarmu domin muna da karfi wajen kare kasa. Da yake Magana a gaban manema labarai a wajen bikin cika shekaru 2 na ambaliyar alaqsa wanda dakarun gwagwarmayar yanto palasdinu suka kaddamar kan HKI,yace harin ya fantsama alamarin falasdinu a duniya, Har ila yau ya kara da cewa harin na 7 ga watan oktoban shekara ta 2023 ya nuna cewa isra’ila ba ta da wahalar yin galaba akanta, kuma al’ummar Palastinawa sun kuduri aniyar ci gaba da gwagwarmaya da gwamnatin mamaya da ta shafe shekaru tana aiwatar da kisan...
    Bayan kwashe makonni manyan ‘yan takara a jam’iyyun adawa da sauran jiga-jigan ‘yan siyasa na tuntubar juna domin ganin an fitar da dan takara daya tilo, da yammacin ranar Asabar 13 ga watan nan na Satumba, 6 daga ciki sun amince da tsohon minista kuma mafi kusanci ga gwamnati tsawon shekaru 16, wanda ya taba zama mai magana da yawun gwamnati a matsayin wanda zai fafata da Paul Biya na jam’iyyar RDPC wanda ya kwashe sama da shekaru 42 ya na mulkin kasar da ke tsakiyar Afirka. An zabe shi ne daga cikin ‘yan takara na jam’iyyun adawa 6 cikin 12 da hukumar zabe ta tabbatar da su a matsayin wadanda suka cancanci takara, karkashin inuwar gamayyar Union du Changement....
    Liɓerpool ce mai riƙe da kofin kuma na 20 jimilla da ta lashe a kakar da ta wuce, iri ɗaya da yawan wanda Manchester United take da shi a tarihin gasar premier ta ƙasar Ingila. Ga jerin ƙungiyoyin da suka ci ribar kasuwancin sayen ƴan  ƙwallo da waɗanda suka yi hasara a cikin ƙungiyoyin da suke buga gasar Premier League ta bana. Ƙungiyoyin da suka ci riba; LIVERPOOL Ƙungiyar ce kan gaba a yawan kashe kuɗi wajen sayen ƴan  ƙwallo a bana, wadda karo biyu ta ɗauki ƴan  wasa a matakin mafi tsada a kakar nan. Ta fara da sayen matashin ɗan wasa Florian Wirtz kan fam miliyan 115, sannan ta ɗauki Aleɗander Isak kan fam miliyan 125 ranar da...
    Misali, ya sauya lokacin da aka tsara yin wasan sada zumunta da ƴan  ƙasa da shekara 20 na ƙungiyar Flamengo a lokacin da Leɓerkusen ta je atisaye a Brazil. An buga wasan kwana biyar kafin ranar da aka tsara tun farko, inda Leɓerkusen ta sha kashi da ci 5-1. Haka nan a kusan wannan lokacin ne Ten Hag ya yanke hukunci kan batun tafiyar Granit Ɗhaka, inda ya ce ya kamata ya tsaye saboda Leɓerkusen ta rasa manyan ƴan  wasa da yawa. Sai dai tuni ƙungiyar ta sanar cewa Ɗhaka zai iya tafiya idan aka samu tayi mai kyau. Daga baya ya tafi Sunderland. Haka nan kuma Ten Hag ya soki ƴan  wasansa tare da cewa ba su da kuzarin...
    Amurka ta bayyana cewa: Harin da Isra’ila ta kai wa Qatar ba ya barazana ga kawancenta haramtacciyar kasar Isra’ila da Amurka Sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio ya fada a ranar Asabar din nan cewa: Harin da haramtacciyar kasar Isra’ila ta kai a Doha babban birnin kasar Qatar a makon jiya ba zai shafi dangantakar Amurka da Isra’ila ba, duk da rashin gamsuwar da shugaba Donald Trump ya yi da yakin da gwamnatin mamayar Isra’ila ke ci gaba da yi da kungiyar Hamas a Gaza. Kafin ya tashi zuwa birnin Tel Aviv na Isra’ila, Rubio ya jaddada cewa, gwamnatin Amurka na ci gaba da tallafawa yahudawan sahayoniyawa, yana mai cewa a wasu lokuta ana samun aukuwar lamarin da kan iya...
    Jiragen yakin HKI sun rusa dogon gini kuma gidajen mutane Annoor dake unguwar Tel Hawa na birnin Gaza, a shirinta na rusa dukkan dogayen gine gine a birnin Gaza. Tashar talabijibijin ta presstv ya bayyana cewa sojojin yahudawan sun tilastawa dubban mutane a wasu unguwanni a birnin na Gaza kauracewa gidajen nasu a dai dai lokacin yahudawan suke ci gaba da rusa dogayen gine gine a birnin. Labarin ya kara da cewa manufar yahudawan a wadannan rushe-rushe sun hada da korar falasdinawa daga gidajensu, daga karshe korarsu daga kasarsu. Tun watan da ya gabata ne gwamnatin natanyahu ta fara aiwatar da wannan inda sojojinsa suke amfani da makamai masu karfi don cimma wannan manufar. Ya zuwa yanzo dai sun kashe...
    Wani mahaifi, Mande Achagh, ya ce matsalar ta fi yin ƙamari a gundumarsa ta Agagbe, a ƙaramar hukumar Gwer West inda yawancin waɗanda basu da matsuguni suka samu mafaka, a wurare na musamman, makarantu, da kuma wasu gundumomi na al’umma. “Matsalar tafi matuƙar lalacewa a Gwer ta Yamma abin kuma ya shafi makarantu sosai. Ina fatan gwamnati zata kalli lamarin domin ta ɗauki mataki, wajen samarwa mawaɗanda suka rasa matsuguni wuraren zama ta haka ‘ya’yanmu za su iya koma harkar karatu ta amfani da azuzuwansu. “Irin matsalar da su yaran namu suke fuskanta dangane da karatunsu ba abinda za ayi wa riƙon sakainar kashi bane. Abin yana matauƙara ɓata mani rai, saboda wasu wuraren yara suna karatu ne a ƙarƙashin...
    Babban zauren Majalisar Dinkin Duniya ya amince da gagarimin rinjaye da “Sanarwar New York” da nufin farfado da shawarwarin samar da kasashe biyu a Gabas ta Tsakiya  wato Isra’ila, da kuma Falasdinu a daya bangare – amma ba tare da kungiyar Hamas ba. Kasashe 142 ne suka amince da shi, yayin da 10 suka nuna adawa da shi (ciki har da Isra’ila da Amurka) sai 12 da suka kaurace kada kuri’ar. . Bayan shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron, kasashe da dama sun bayyana aniyarsu ta daukar irin wannan matakin a babban taron Majalisar Dinkin Duniya da za a bude ranar 22 ga watan Satumba, ana kallon wannan tsari a matsayin karin tursaswa Isra’ila ta kawo karshen yakin da take ci...
    Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhakan, sharbin bayan labarammu a yau zasu yi magana dangane da ‘yiyuwar gwamnatin kasar Qatar ta nemi maye gurbim Amurka a bangaren tsaron kasarta, bayan cin amanan da Amurka ta yi a ranar talatan da ta gabata. Kamfanin dillancin labaran Parstoday, ta nakalto wani shafin labarai na yanar gizo a Amurka ‘Axios’. A ranar Alhamis da ta gabata ce, shafin yanar gizo na Acios na labarai ya nakalto Firay ministan kasar Qatar tana fadawa  fadar white House kan cewa, bayan saba alkawalin da Washington ta yi, dangane da hare-haren da HKI ta kaiwa birnin Doha, Qatar zata sake duba yarjeniyar tsaron da ke tsakaninta da Amurka ta kuma nemi sabon abokin aiki a wannan...
    Akalla Falasdinawa 64,756 sukayi shahada a kisan kiyashin da Isra’ila ta yi a Gaza tun daga watan Oktoban 2023, in ji ma’aikatar lafiya a yankin Falasdinawa da ke kewaye. Sanarwar da ma’aikatar ta fitar ta ce an kawo gawarwakin mutane 38 da suka hada da biyu da aka zakulo daga baraguzan gine-gine a cikin sa’o’i 24 da suka gabata, yayin da mutane 200 suka samu raunuka, wanda ya kawo adadin wadanda suka jikkata zuwa 164,059. Ma’aikatar ta kuma bayyana cewa, hare haren Isra’ila sun kashe Falasdinawa 14 tare da raunata wasu 143 yayin da suke neman agaji a cikin sa’o’i 24 da suka gabata, lamarin da ya kai adadin Falasdinawa da aka kashe yayin da suke neman agaji zuwa 2,479,...
    Mai ba da shawara ga Jagora kan harkokin kasa da kasan ya jaddada ccewa; Dole ne duniya ta daina yin shiru game da zaluncin ‘yan sahayoniyya Ali Akbar Velayati mai ba da shawara ga jagora kan harkokin kasa da kasa ya yi Allah wadai da wuce gona da irin da yahudawan sahayoniyya suka kai a kasar Qatar, yana mai cewa: Dole ne duniya ta daina yin shiru kan zaluncin yahudawan sahayoniyya saboda ba su san iyaka kan laifukansu ba. Velayati ya bayyana a shafinsa na twitter game da harin da gwamnatin ‘yan sahayoniyya suka kai wa kasar Qatar yana mai cewa: Keta dokokin kasa da kasa da keta alfarmar kasashe ya zama al’ada ga ‘yan sahayoniyya, kuma dole ne duniya...
    A yau da safe, ofishin yada labarai na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya gudanar da jerin tarukan manema labarai mai taken “Kammala shiri na 14 na shekaru biyar-biyar na raya kasa mai inganci”, inda aka yi karin haske kan ci gaban da aka samu a fannin kafa tsarin shari’a a kasar Sin a wa’adin gudanar da shirin.   An bayyana yayin taron cewa, a wa’adin shirin, hukumomin shari’a sun ci gaba da inganta tsarin kasuwanci bisa shari’a, da cibiyoyin kula da lafiyar jama’a a matakin gundumomi, kuma sun fara aiki gaba daya, kana an hukunta manyan laifuka bisa doka. Taron ya kuma bayyana kasar Sin a matsayin daya daga cikin kasashen da aka amince da su a duniya a...
    “Gwamnatin Jihar Kaduna ta shirya tsaf domin ɗaukar matakin gaggawa kan kowanne yanayi da ka iya tasowa sakamakon wannan hasashen yanayi. An umurci KADSEMA da ta yi aiki tare da dukkan hukumomi masu ruwa da tsaki domin tabbatar da cikakken shiri. Ana roƙon jama’a da su bi dukkan umarnin kariya, su share magudanan ruwa, kuma su guji wuraren da ambaliya ke yawan faruwa a wannan lokaci,” in ji Maiyaki.   Hakazalika, sakataren Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Kaduna (KADSEMA), Dakta Usman Hayatu Mazadu, ya jaddada muhimmancin kasancewa cikin shiri da kuma bin matakan kariya da ke cikin sanarwar.   “Hasashen yanayi ya nuna cewa za a samu guguwar iska da ruwan sama mai yawa musamman a ranakun Laraba...
    Gwamnatin Kano ta ayyana gobe Juma’a, 12 ga watan Satumban 2025, wadda za ta yi daidai da 19 ga watan Rabi’ul Awwal na 1447, a matsayin ranar hutun Takutaha. Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da Sakataren Ofishin Shugaban Ma’aikatan Jihar, Salisu Mustapha, ya fitar a ranar Alhamis. Sanarwar ta bayyana cewa hutun yana cikin girmama ranar bakwai ga haihuwar Annabi Muhammad (S.A.W). Daruruwan magoya bayan NNPP sun tarbi Kwankwaso a Kalaba Kotu ta yanke wa jagoran Ansaru hukuncin ɗaurin shekaru 15 “Mutanen Kano sun shafe shekaru suna bikin wannan rana a matsayin Ranar Takutaha. “Bikin Ranar Takutaha wani tsohon tarihi ne da aka shafe shekaru aru-aru ana gudanarwa.” Gwamnan ya buƙaci al’ummar jihar da su yi amfani da wannan...
    Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran tayi Allah wadai da harin ta’addanci da hki takai kan ginin ma’aikatar sadarwa guda biyu a kasar Yaman da ya kai ga shahadar wasu yan jaridar  guda biyu. Har ila yau tayi tir da hari da isra’ila takai kan muhimman wurare a kasar yamen da yankunan farafen hula ,da haka yayi sanadiyar shahadar wasu mutane kuma ya shafi wasu fararen hula na daban, don haka tayi kira ga kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya data dauki matakin gaggawa na dakatar da  laifukan yaki da HKI take tafkawa. Ta ce gwamnatin Isra’ila tana ci gaba da kai hare-hare a kasashen yankin, tare da ci gaba da kisan Karen dangi a Gaza, da hakan ya sabama dan...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi ya bayyana cewa, sabuwar yarjejeniyar da Iran ta kulla da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA, kan batun dawo da hadin gwiwa, za ta ci gaba da wanzuwa matukar dai ba a dauki wani mataki kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba, ciki har da yunkurin mayar da takunkumin da MDD ta kakaba mata. A ranar 29 ga watan Agusta ne, kasashen Faransa, Jamus, da Biritaniya (E3) suka yunkura ganin an sake dawo da takunkumin Majalisar Dinkin Duniya da manyan takunkumin banki da na ruwa a kan Iran. Iran ta yi Allah-wadai da wannan matakin, inda ta ce kasashen uku sun bi sahun Amurka, wadda ta fice daga yarjejeniyar nukiliyar Iran a...
    Shugabannin kasashen Afirka sun kammala taron kwanaki 3 kan sauyin yanayi na Afirka a babban birnin kasar Habasha a jiya Laraba tare da amincewa da sanarwar Addis Ababa, inda suka yi alkawarin mayar da nahiyar ta zama cibiyar samar da makamashi mai safta da kuma hanyoyin magance sauyin yanayi a yayin da suke neman kudade na gaske. Shugaban kasar Habasha Taye Atske Selassie, wanda ya rufe taron, ya ce taron ya nuna cewa Afirka ba ta shiga cikin rikicin da ba ta haifar da shi ba. ” Mun himmatu wajen samar da wata nahiya mai wadata,” in ji shi. “Zalunci ne cewa sama da ‘yan Afirka miliyan 600 har yanzu suna rayuwa ba tare da samun wutar lantarki ba. Dole...
    Hukumar Zaɓen Nijeriya INEC ta amince da jam’iyyar ’yan haɗaka ta ADC, ƙarƙashin jagorancin tsohon shugaban Majalisar Dattawa, David Mark. Wannan tabbaci na zuwa ne bayan hukumar ta wallafa sunayen shugabannin jam’iyyar a shafinta na intanet, abin da ya kawo ƙarshen dogon jira da aka yi tun bayan ayyana ta a matsayin jam’iyyar haɗin kan ’yan adawa a ranar 2 ga Yuli. Masu zanga-zanga sun ƙone matar tsohon Firaministan Nepal Yadda zanga-zangar adawa da rashawa ta rikiɗe zuwa tarzoma a Nepal Tun a watan Yulin ne dai gamayyar ’yan adawa suka ayyana David Mark a matsayin shugaban jam’iyyar, tare da tsohon Gwamnan Osun, Rauf Aregbesola, a matsayin sakatarenta na ƙasa. Sai dai kafin yanzu, INEC ba ta sanya sunayensu a...
    Babban Layin wutar lantarki na Najeriya ya sake faɗuwa. Wannan matsala ta haifar da katsewar wuta a wasu sassan ƙasar, wanda ya jefa masu amfani da lantarki cikin damuwa. Kotun Ghana ta ɗaure ’yan Najeriya 3 shekaru 96 saboda satar mota Mamakon ruwan sama ya hallaka mutum 3 a Zariya Bayanan da Hukumar Gudanar da Wutar Lantarki, sun nuna cewa wutar ta ragu daga megawat 2,917 zuwa megawat 1.5 daga tsakanin ƙarfe 11 na safe zuwa 12 na ranar Laraba. Kamfanin rarraba wuta na Abuja (AEDC), ya tabbatar da faruwar matsalar a saƙon da ya aike wa kwastomominsa. Ya ce wutar ta ɗauke ne sakamakon matsalar da aka samu daga layin ƙasa da misalin ƙarfe 11:23 na safe. “Saƙonmu zuwa...
    Mark ya ce haɗakarsu na da burin “ceto Nujeriya, gina dimokuraɗiyya”. Manyan ‘yan siyasa a haɗakar sun haɗa da Atiku Abubakar, Peter Obi, Nasir El-Rufai, Rotimi Amaechi, Dino Melaye, Solomon Dalong. Sauran sun haɗa da Dele Momodu, Gabriel Suswam, Ireti Kingibe, Emeka Ihedioha, da Air Marshal Sadique Abubakar (ritaya). Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Babban Layin wutar lantarki na Najeriya ya sake faɗuwa. Wannan matsala ta haifar da katsewar wuta a wasu sassan ƙasar, wanda ya jefa masu amfani da lantarki cikin damuwa. Kotun Ghana ta ɗaure ’yan Najeriya 3 shekaru 96 saboda satar mota Mamakon ruwan sama ya hallaka mutum 3 a Zariya Bayanan da Hukumar Gudanar da Wutar Lantarki, sun nuna cewa wutar ta ragu daga megawat 2,917 zuwa megawat 1.5 daga tsakanin ƙarfe 11 na safe zuwa 12 na ranar Laraba. Kamfanin rarraba wuta na Abuja (AEDC), ya tabbatar da faruwar matsalar a saƙon da ya aike wa kwastomominsa. Ya ce wutar ta ɗauke ne sakamakon matsalar da aka samu daga layin ƙasa da misalin ƙarfe 11:23 na safe. “Saƙonmu zuwa...
    Tawagar Super Eagles ta Nijeriya ta buga kunnen doki da takwararta ta Afirika Ta Kudu da ci 1-1 a filin wasa na Toyota dake birnin Bloemfontein dake kasar Afirika Ta Kudu. Kyaftin din Nijeriya Troost Ekong  shi ne ya ci gida a minti na 25 da fara wasan kafin nan dan wasan bayan Nijeriya Calvin Bassey ya farke kwallon dab da za a tafi zuwa hutun rabin lokaci. Wannan sakamakon ya sa Super Eagles din  rasa tikitin kai tsaye da zai kaisu gasar Kofin Duniya, amma kuma suna da wata damar, idan sukayi kokarin karewa a mataki na biyu a rukunin C. Zuwa yanzu kasashen Moroko da Tunisia ne kawai kasashen da suka samu nasarar zuwa gasar ta Duniya da...
    Sau da dama mukan ji labarai na mutane da suka ɗauki rayukansu saboda damuwa, talauci ko kuma rashin samun mafita a cikin rayuwa.   A cikin wannan shirin, za mu kalli batun kisan kai daga wani ɓangare na daban, ba wai kawai daga alkaluma ba, amma ta hanyar jin labarin wani da ya taɓa  yunkurin kashe kansa har sau uku. NAJERIYA A YAU: Tasirin Takaddamar NUPENG Da Dangote A Kan Tattalin Arzikin Najeriya DAGA LARABA: Yadda Matan Da Ke Auren Gwaji Suke Yamutsa Hazo ko wadanne irin matsaloli ne suka tunzura wannan bawan Allahn yunkurin daukar ransa da kansa har sau uku? Domin sauke shirin, latsa nan
      Zuwa yanzu kasashen Moroko da Tunisia ne kawai kasashen da suka samu nasarar zuwa gasar ta Duniya da za a buga a kasashen Amurka, Mexico da Canada. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ya kuma yi kira ga jami’an tsaro da su tashi tsaye wajen kare rayuka da dukiyoyin ’yan ƙasa, tare da tabbatar da cewa doka ta yi aiki a kan kowa ba tare da nuna bambanci ba. A cewarsa, hare-haren da ake kai wa jam’iyyun adawa barazana ce ga makomar dimokuraɗiyya a Nijeriya, don haka dole a yi magana a kai kafin abin ya zama al’ada. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Kungiyar gwagwarmaya ta Hamas ta yi tir da shiru da kasa tabuka komai da majalisar dinkin duniya ta yi musamman ma kwamitin tsaro game da ci gaba da kisan kare dangi da HKI take ci gaba da yi kan alummar falasdinu. Wannan mayar da martani mai zafi daga hamas yana zuwa ne bayan da fira ministan isra’ila Benjamin Natanyaho yayi barazanar rusa manyan gine –gine dake gaza, da hakan ya haifar da yin kaura daga gidanjensu. Haka zalika kungiyar Hamas ta yi kira ga  dukkan alummomin duniya masu yanci da su kara kaimi wajen yakar  yan ta’adda yahudawa yan fashi da makami , da kuma tilasta mata dakatar da laifuffukan yaki da take tafkawa ba dare ba rana kan alummar...
    Melaye ya kuma yi zargin cewa an ƙara kasafin kuɗin majalisar dokoki don yi wa shugaban ƙasa biyayya Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    An bude taron sauyin yanayi na Afirka karo na biyu a birnin Addis Ababa, na kasar Habasha mai manufar samar da hanyoyin magance matsalolin yanayi a nahiyar. Wannan taro na tsawon kwana biyu, wanda Majalisar Dinkin Duniya da Tarayyar Afirka da gwamnatin Habasha suka shirya, na samun halartar wakilai 25,000 da kuma shugabannin kasashe 45. Haka kuma, taron na neman karfafa murya guda daya ta Afirka a fagen duniya kan rage illolin sauyin yanayi, tare da bunkasa tsare-tsaren da ke da amfani ga kasashen Afirka kafin taron COP da za a gudanar a Brazil a watan Nuwamba mai zuwa. Bayar da kudi da tabbatar da adalci na yanayi a na daga cikin ajandar babban taron. Bankin raya kasashen Afirka ya...
    Kayayyakin da aka samu daga hannun wadanda ake zargin sun hada da wukake adduna almakashi, tabar wiwi, shisha, da sauran haramtattun abubuwan maye.   “Ana kan binciken dukkan wadanda ake tuhuma kuma za a gurfanar da su a gaban kotu bisa laifin aikin dabanci,” in ji Abiodun. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A yau Litinin, wasu rahotanni na cewa, yayin wani taron manema labaru na musamman kan zuba jari ga sassan ketare da aka gudanar a taron tattauna harkokin cinikayya da zuba jari na kasa da kasa na Sin karo na 25, cewa a shekarar 2024 adadin jarin da kasar Sin ta zuba kai tsaye a kasashen da suka shiga shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya” ya kai dalar Amurka biliyan 50.99, adadin da ya karu da kashi 22.9 bisa dari idan aka kwatanta da makamancin lokaci na shekarar 2023. A dai yau din, ma’aikatar kasuwanci ta kasar Sin, da hukumar kididdiga ta kasar, da hukumar kula da musayar kudin waje ta kasar, sun fitar da sanarwar “kididdiga ta shekarar 2024 kan...
    Jagoran juyin juya halin Musulunci ya jaddada yin kira ga al’ummar Musulmi cewa: Wajibi ne kasashen musulmi su yanke alakarsu da ‘yan sahayoniyya Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya jaddada cewa: Dole ne kasashen musulmi su yanke duk wata huldar kasuwanci da siyasa da gwamnatin ‘yan sahayoniyya azzaluma tare da mayar da ita saniyar ware. Jagoran juyin juya halin Musulunci ya jaddada cewa: Dole ne a fuskanci bala’o’in da muguwar gwamnatin ‘yan sahayoniyya ta haifar a Gaza. Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya yi tsokaci kan mummunan halin da ake ciki a zirin Gaza inda ya ce: Dole ne kasashen da suke gudanar da zanga-zangar a yau musamman kasashen musulmi su yanke duk wata huldar kasuwanci...
    Rundunar sojin Yeme ta sanar da kai hare-hare guda 8 da jirage sama marasa matuka ciki kan muhimman wurare a Isra’ila Dakarun sojin Yemen sun sanar da yammacin jiya cewa, sun kai wasu manya-manyan farmakin soji ta hanyar amfani da jiragen saman yaki  marasa matuka ciki guda takwas a kan wasu wurare da dama a yankunan Falasdinawa da aka mamaye. An kai hare-haren ne kan filin jirgin saman Ramon da muhimman wurare da na sojoji da suka hada da Negev, Umm al-Rashrash, Ashkelon, Ashdod, da Jaffa. Domin jaddada goyon baya ga al’ummar Falastinu da ake zalunta da ‘yan gwagwarmayarsu masoya, da kuma mayar da martani kan laifukan kisan kiyashi da kakaba yunwa da makiya yahudawan sahayoniyya suke aikatawa kan ‘yan...
    Aƙalla mutum bakwai ne suka rasa rayukansu, yayin da wasu 11 suka jikkata a wani sabon hari da ’yan bindiga suka kai ƙauyen Wake da ke gundumar Agunu, a Ƙaramar Hukumar Kachia ta Jihar Kaduna. Hari  ya faru ne da misalin ƙarfe 5:55 na safiyar ranar Lahadi, lokacin da ’yan bindigar suka mamaye garin, inda suka yi ta harbe-harbe. Harin Borno: Dole ’yan Najeriya su haɗa kai su fuskanci Boko Haram — Atiku Ambaliyar Ruwa: NEMA ta ceto mata 2 da jaririya a Kaduna  Har ila yau, sun yi garkuwa da wasu mazauna garin, duk da cewa har yanzu ba a tantance adadinsu ba. Waɗanda suka rasu a harin sun haɗa da: Elisha Paul, Japhet Bitrus, Obadiah Joshua, Luka Augustine,...
    Domin kuwa wasu matan kwanciya kan iya zama sanadi na lalacewar cikin. So, akan ce ma a rage ko a bari a watanni uku na farkon ciki. Don haka idan ka ga wadannan matsalolin kar ka ce wai kirkira take, ko da gangan take. Ba gaskiya bane. Lalura ce babba, kuma da take bukatar kallo na musamman. Idan kaga wannan lokacin yazo, anan ne ake so ka nuna soyayyarka, da kulawarka, da taimakonka. Wajibi ka bata hadin-kai don ta wuce wannan watanni uku na farko din. Domin cikin jikinta a wannan lokacin kamar akan siratsi yake, duk abinda aka ce ana halittarta ’yan Adam a cikinsa ai yaga taka kansa. Komai zai iya faruwa. Namiji dan kirki shine sai kaga...
      Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Game da babban bikin tunawa da cika shekaru 80 da samun nasarar yakin da al’ummar Sin suka yi da mamayar dakarun kasar Japan da yakin duniya kin tafarkin murdiya, wanda aka gudanar a ranar 3 ga wannan wata, mutane daga kasa da kasa masu halartar bikin sun ba da ra’ayoyinsu ciki har da kalmomin hadin kai, da yin kokari tare, da sauransu don nuna kyakkyawar fata ga makoma. Bayan shekaru 80 da gama yakin duniya na biyu, an canja burin dan Adam. Zaman lafiya da samun bunkasa sun zama babban jigo na halin yanzu, kasa da kasa suna kokarin samun zamanantarwa. Amma a sa’i daya kuma, ra’ayin mai karfi ya cinye maras karfi ya sake bullowa, an kawo illa ga...
    A cikin sa’o’i 24 da suka gabata, akalla Falasdinawa 68 ne suka yi shahada a Zirin Gaza, wanda ya kawo adadin wadanda suka rasu a yakin kisan kare dangi na Isra’ila tun watan Oktoban 2023 zuwa sama da 64,368. Akalla Falasdinawa tara ne sukayi shahada a wani kazamin harin da aka kai ta sama a birnin Gaza da Khan Yunus, ciki har da takwas lokacin da aka kai hari kan wani gini a unguwar Sheikh Radwan. Kamfanin dillancin labaran iqna, ya nakalto cewa, a ranar Asabar, wani yaro ya yi shahada a wani harin da Isra’ila ta kai kan wata mota a sansanin al-Mawassi da ke Khan Yunis. Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, bayan harin bam da Isra’ila...
    An ce saurayin ya yi wa Ammaye wasa da cewa yana son aurenta domin “cika Sunnah”. Sai dai kuma an ce Ammaye ta yi wata magana da aka dauka a matsayin Batanci. Wannan ne ya fusata matasan yankin. Lamarin aka kai shi fadar Dagacin Kasuwar Garba, inda aka yi mata tambayoyi, kuma a cewar rahoto ta maimaita abin da ta fada tun farko. An ce Dagacin ya mika Ammaye ga jami’an tsaro domin gudanar da bincike, amma taron matasa masu hargitsi suka mamaye jami’an tsaro, suna cewa a kashe ta nan take. Jaridar PUNCH Metro ta gano cewa kafin jami’an tsaro su iso domin kawo dauki, matasan sun riga ya jajjefe Ammaye har ta mutu. Mai magana da yawun ‘yansandan...
    Wani sabon zagaye na shawarwari tsakanin Iran da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya Jakadan kasar Iran kuma wakilin dindindin na kasar Iran a kungiyoyin kasa da kasa a birnin Vienna Reza Najafi ya sanar da fara wani sabon zagaye na shawarwari tsakanin tawagar kasar Iran da jami’an hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA, yana mai cewa, wadannan shawarwarin za su tabbatar da wani sabon salon hadin gwiwa tsakanin Iran da hukumar ta IAEA. Reza Najafi ya yi nuni da cewa, ana gudanar da wadannan shawarwari ne a matsayin ci gaba da tuntubar juna tsakanin Iran da hukumar IAEA domin ayyana hadin gwiwa a cikin tsarin dokar da majalisar dokokin kasar ta amince da shi a cikin...
    Kwamitocin kungiyoyin ‘yan gwagwarmaya sun bayyana barazanar Katz da cewa; Kira ne ga aiwatar da kisan kare dangi da kuma shafe wata al’umma Kwamitin kungiyoyin ‘yan gwagwarmayar Falasdinawa ya tabbatar da cewa: Kalaman ministan tsaron Isra’ila Katz game da “bude kofofin jahannama” kan birnin Gaza ya zama kira ga jama’a na Aiwatar da kisan kiyashi, kawar da wata al’umma daga kan doron kasa da kuma kai hare-haren wuce gona da iri kan ababen more rayuwa da farare hula. Kwamitocin sun bayyana a cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai cewa: Laifukan da sojojin mamaya Isra’ila suka aikata a birnin Gaza, da suka hada da barna, ta’addanci, da kuma kashe jama’a, sun bayyana hakikanin fuskar “hukumar da ke karkashin jagorancin...
    Majalisar Dokokin Jihar Filato, ta haramta wa makarantu a jihar tilasta iyayen ɗalibai sayen sabbin littattafai duk shekara. Wannan mataki ya biyo bayan ƙudurin da Hon. Joseph Bukar, ɗan majalisa mai wakiltar Shendam ya gabatar, tare da goyon bayan Hon. Mathew Kwarpo Sylvanus daga Mangu ta Kudu. Sarkin Zazzau ya jagoranci jama’a domin murnar Maulidin bana Gwamnatin Sakkwato ta bai wa ’yan gudun hijira tallafin kuɗi da shinkafa Bukar, ya ce bai dace ba a ci gaba da tilasta wa iyaye siyan sabbin littattafai duk shekara, inda ya ce hakan cin zarafi ne. ’Yan majalisar sun ce wannan mataki zai rage wa iyaye nauyin kashe kudi. Sun bayyana cewa ana iya sake amfani da littattafai, har ma a raba wa...
    Majalisar Dokokin Jihar Filato, ta haramta wa makarantu a jihar tilasta iyayen ɗalibai sayen sabbin littattafai duk shekara. Wannan mataki ya biyo bayan ƙudurin da Hon. Joseph Bukar, ɗan majalisa mai wakiltar Shendam ya gabatar, tare da goyon bayan Hon. Mathew Kwarpo Sylvanus daga Mangu ta Kudu. Sarkin Zazzau ya jagoranci jama’a domin murnar Maulidin bana Gwamnatin Sakkwato ta bai wa ’yan gudun hijira tallafin kuɗi da shinkafa Bukar, ya ce bai dace ba a ci gaba da tilasta wa iyaye siyan sabbin littattafai duk shekara, inda ya ce hakan cin zarafi ne. ’Yan majalisar sun ce wannan mataki zai rage wa iyaye nauyin kashe kudi. Sun bayyana cewa ana iya sake amfani da littattafai, har ma a raba wa...
    A fannin ƙasa da ƙasa, ya kammala karatun digirinsa na uku (PhD) a Jami’ar Warsaw da ke ƙasar Poland, ƙarƙashin kulawar shahararriyar masaniyar harshe, Farfesa Nina Pawlak. BUK ta miƙa ta’aziyyarta ga iyalansa, abokansa da duk waɗanda rashi ya shafa, inda ta bayyana cewa: “A madadin Uban Jami’ar da Shugaban Jami’ar da Majalisar Gudanarwa da ta Majalisar Malaman jami’ar da Kwamitin Ma’aikata da Dalibai, muna miƙa ta’aziyyarmu ga iyalansa da dukkan al’ummar.” Za a gudanar da sallar jana’iza a ranar Juma’a, 5 ga Satumba, da ƙarfe 9:00 na safe, a gidansu da ke Unguwar Yakasai, kusa da * Makarantar Kwana ta Shekara da ke Kano. Za a ci gaba da tunawa da Farfesa Hafiz Miko Yakasai a matsayin masanin ilimi...
    A fannin ƙasa da ƙasa, ya kammala karatun digirinsa na uku (PhD) a Jami’ar Warsaw da ke ƙasar Poland, ƙarƙashin kulawar shahararriyar masaniyar harshe, Farfesa Nina Pawlak. BUK ta miƙa ta’aziyyarta ga iyalansa, abokansa da duk waɗanda rashi ya shafa, inda ta bayyana cewa: “A madadin Uban Jami’ar da Shugaban Jami’ar da Majalisar Gudanarwa da ta Majalisar Malaman jami’ar da Kwamitin Ma’aikata da Dalibai, muna miƙa ta’aziyyarmu ga iyalansa da dukkan al’ummar.” Za a gudanar da sallar jana’iza a ranar Juma’a, 5 ga Satumba, da ƙarfe 9:00 na safe, a gidansu da ke Unguwar Yakasai, kusa da * Makarantar Kwana ta Shekara da ke Kano. Za a ci gaba da tunawa da Farfesa Hafiz Miko Yakasai a matsayin masanin ilimi...
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna ta gayyaci tsohon Gwamnan jihar, Nasir El-Rufa’i da sauran jagororin jam’iyyar ADC kan zargin yunkurin tayar da zaune tsaye. A cewar takardar wacce Aminiya ta gani, an gayyace su ne domin su yi wa rundunar bayani kan zargin su da hadin baki da tunzura jama’a wajen tayar da tarzoma da kawo wa zaman lafiya tarnaki a jihar. An naɗa Benjamin Hundeyin sabon kakakin ’yan sandan Nijeriya Cin amana shi ne tsarin siyasa a Najeriya — Jonathan Takardar, wacce ke dauke da kwanan watan hudu ga watan Satumban 2025 dai na dauke ne da sa hannun Mataimakin Kwamishinan ’Yan Sanda mai kula da Sashen Binciken Manyan Laifuffuka (SCID), Uzairu Abdullahi. Takardar ta ce, “Wannan sashen namu...
    Mataimakin ministan harkokin wajen Iran mai kula da harkokin siyasa  ya bayyana halin da Iran take ciki kan sabon zagayen tattaunawa Mataimakin ministan harkokin wajen Iran mai kula da harkokin siyasa Majid Takht-Ravanchi ya tabbatar da cewa, ana musayar sakonni tsakanin Iran da Amurka ta hanyar masu shiga tsakani, yana mai cewa maido da zaman tattaunawa da Amurka zai yiwu ne kawai bayan samun tabbacin cewa ba za a kai wa Iran hari makamancin wanda ya faru, kamar yadda ya faru a baya-bayan nan ba. A wata hira da ya yi da kafafen yada labaran Turkiyya, Takht-e Ravanchi ya bayyana cewa: Ana gudanar da magana tsakanin Iran da Amurka ta hanyar masu shiga tsakani na yanki da na kasa da...
    A ranar 20 ga watan Yulin bana, an gano gawarwaki 85 a gefen buhunan abinci masu dauke da tambarin MDD, wadanda suka hada da mata da yara. Wasu na ci gaba da rike buhunan abinci lokacin da aka same su, yayin da wasu yaran ke cikin yanayi na nuna galabaita kafin mutuwarsu. Wannan shi ne mummunan sakamakon harin sama da Isra’ila ta kai a wani wurin rarraba kayan agaji a zirin Gaza. Abun takaici shi ne, ba wannan ne karon farko da aka samu irin wannan abun ba. Wani rahoton MDD ya nuna cewa, mutum guda na mutuwa a duk minti uku a fagen yaki a fadin duniya. Mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon yaki, su ne mafi daukar hankali...
    “A madadin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ina kara tabbatar da tsayin dakar Nijeriya ga manufofin GGC. Babu wanda zai iya gurgunta rawar da hukumar ke takawa wajen samar da hadin kai, zaman lafiya, da ci gaba mai dorewa a mashigin tekun Guinea,” in ji shi.   Ya yaba wa mahukuntan GGC, yana mai ba su tabbacin cewa, “Nijeriya na nan tsayin daka kan kare manufofin hukumar.” Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ya ƙara kira ga ‘yan Nijeriya da su kasance masu bin doka da kula da tsaro tare da goyon bayan manufofin gwamnati da nufin ƙarfafa haɗin kan ƙasa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Juma’a, biyar ga watan Satumban 2025 a matsayin ranar hutu albarkacin ranar haihuwar Annabi Muhammad (S.A.W). Ana dai yin bikin ranar ce dai da ake kira ta Mauludi a duk ranar 12 ga watan Rabi’ul Auwal, wat ana uku a shekarar Musulunci. DAGA LARABA: Yadda Mata Dake Auren Gwaji Suke Yamutsa Hazo ’Yan bindiga sun sace basarake a Kogi Ministan Cikin Gida, Dr. Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa, ranar Laraba a madadin gwamnatin, kamar yadda Babbar Sakatariyar ma’aikatar, Dr Magdalene Ajani ta sanar. Ministan ya kuma taya ’yan Najeriya murna, inda ya bukace su da su yi koyi da kyawawan halayen Annabin na zaman lafiya, kaunar jama’a, hakuri, tawali’u...
    Allah Ya yi wa Shugabar Ma’aikata ta Babban Birnin Tarayya, Abuja, Misis Grace Adayilo, rasuwa a safiyar Litinin ɗin nan. Shaidu sun tabbatar wa wakilinmu cewa ta rasu ne ’yan sa’o’i kaɗan da suka gabata. Kodayake kawo yanzu ba a sanar da rasuwar a hukumance ba. Misis Grace Adayilo ita ce mace ta farko kuma ’yar asalin yankin Babban Birnin Tarayya ta farko da ta riƙe wannan muƙami. ta kasance tsohuwar Sakatariyar Ilimi ta Ƙaramar Hukumar Birnin Abuja (AMAC), kafin Minista Nyesom Wike, ya naɗa ta Shugabar Ma’aikata. Rushe Kasuwar Alaba Rago: Ya kamata a biya ’yan Arewa diyya Gargaɗi kan zagin Sahabban Annabi Muhammad (SAW) Ita ce ta wakilci Wike a babban taron Majalisar Taro ta Ƙungiyar G-7 da...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shugaban ƙasar China, Xi Jinping, na karɓar baƙuncin taron ƙungiyar Shanghai Cooperation Organisation (SCO) a birnin Tianjin, inda shugabannin ƙasashe kusan 20 daga yankin Eurasia suke halarta. Taron, wanda zai gudana har zuwa Litinin, ana kallon sa a matsayin wani babban dandalin da ke ƙara tabbatar da matsayin China a tsakiyar harkokin siyasar ƙasashen Eurasia. Gwamnonin Arewa Maso Gabas sun yi taro kan tsaro da tattalin arziƙi a Taraba Ambaliya: NEMA ta raba kayan tallafi a Yobe  Shugaban Rasha, Vladimir Putin, ya isa Tianjin da manyan jami’an gwamnati da ’yan kasuwa daga ƙasarsa, inda kuma ya yi shirin gudanar da tattaunawa da shugabannin ƙasashe daban-daban a gefen taron. Firayim Ministan Indiya, Narendra Modi, shi ma yana halartar taron, wanda ya...
    Wakilin kasar Sin a fannin cinikayyar kasa da kasa, wanda kuma shi ne mataimakin ministan cinikayya na kasar, Li Chenggang, ya yi musayar ra’ayoyi da jami’an gwamnatin Amurka, dangane da alakar tattalin arziki da cinikayya dake tsakanin sassan biyu. Li, ya jagoranci tawagar kasar Sin yayin zantawa da jami’an ofishin baitulmalin Amurka, da na ma’aikatar cinikayya, da na ofishin wakilin cinikayyar kasar, tsakanin ranakun Laraba da jiya Jumma’a a birnin Washington. Wata sanarwa da ma’aikatar cinikayyar Sin ta fitar bayan ganawar, ta ce sassan biyu sun yi musayar ra’ayoyi dangane da yadda za a aiwatar da kudurorin da shugabannin kasashen biyu suka cimma, yayin zantawarsu ta wayar tarho a ranar biyar ga watan Yunin bana, da ingiza alakar tattalin arziki...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ɗan wasan ɗan shekaru 22 ya zura ƙwallaye 10 ne kawai a wasanni 52 da ya buga a United bara, kuma zuwan Sesko ya ka5ra rage masa damar zama a cikin ƙungiyar. Sha’awar Napoli kan Højlund ta ƙaru ne bayan Romelu Lukaku ya samu rauni a cinyarsa wanda zai sa ya daɗe a jinya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Ƙasa ta Najeriya (NRC) ta fara aikin gyara layin dogon Abuja zuwa Kaduna da ya lalace sakamakon hatsarin jirgin kasa. A ranar Talata da ta gabata ce jirgin mai tarago 10 da ya tashi da misalin karfe 11:00 na safe daga tasharsu da ke Kubwa a Abuja da nufin zuwa Kaduna, rikito daga kan hanyarsa a wata ƙaramar tasha da ke kauyen Asham, ’yan mintoci kalilan bayan fara tafiyar. Hadimin Gwamnan Kano ya maka mawallafin Daily Nigerian a kotu saboda kiransa da ‘ɓarawo’ NAJERIYA A YAU: “Abin Da Ya Sa Muka Dawo Daga Rakiyar Kirifto” Injin jirgin da kuma tarago biyu da ke biye masa sun samu mummunar illa, a yayin da ragowar taragu shida...
    Annabi (SAW), shi ne farkon wanda kasa za ta tsage wa ya tashi a ranar Alkiyama, shi ne farkon wanda zai shiga Aljannah, shi ne wanda Allah ya kebanta da tsani da wasilah, shi kuma ya kebanci muminai masoyansa da ita. Allah ya girmama Manzon Allah (SAW) da abin da bai girmama wani dan Adam da shi ba. Ya daukaka ambatonsa, ta inda ya hada sunansa da sunan Annabi (SAW). Indai an kira sunan Allah, sai an kira sunan Annabinsa. Allah ya yi masa budi (Fatahi) na Zahiri – Sulhu a Hudaibiyya, Fat’hu Khaibara, da Fat’hu Makkah; da Badini – Fatahi a Sifa, Fatahi a Suna da Fatahi a Zati. Allah ya gafarta wa Manzon Allah (SAW), ya tafiyar da...
    Jami’in kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen ya jaddada cewa: A shirye suke su ci gaba da yaki na dogon lokaci da gwamnatin mamayar Isra’ila Jami’in kungiyar Ansarullah ta Mabiya Huthi ta kasar Yemen Mohammed al-Bukhaiti ya bayyana cewa: A shirye al’ummar Yemen su ci gaba da yaki na tsawon lokaci da gwamnatin mamayar Isra’ila, kuma suna farin ciki da arangama kai tsaye da haramtacciyar kasar Isra’ila. Ya kara da cewa, za a ci gaba da daukar matakan soji na goyon bayan Gaza muddin gwamnatin ta ci gaba da yakin da take yi a Gaza. Ya yi nuni da cewa harin da gwamnatin mamayar Isra’ila ta kai kan birnin Sana’a ba zai shafi goyon bayan da al’ummar Yemen ke yi ga...
    “A yau (Ranar Laraba) majalisar zartaswa ta yi la’akari da batun ƙarin kuɗin fansho ga tsofaffin ma’aikatan jiharmu da suka yi ritaya, hakan ya biyo bayan ƙarin mafi ƙarancin albashin ma’aikata da kuma mafi ƙarancin kuɗin fanshi na ƙasa da gwamnatin tarayya ta amince da su,” in ji shugaban ma’aikatan.   Barista Sani ya ƙara da cewa, tun ma kafin wannan ƙarin, hatta adadin mafi ƙarancin fansho da jihar Bauchi ke biya a baya na Naira dubu 12, wasu jihohi da dama ba su ma biyan irin wannan, ga kuma sabon ƙari da suka amince dukkan domin kyautata rayuwar tsofaffin ma’aikata a faɗin jihar.   Ya misalta amincewar a matsayin kyakkyawar yunƙurin gwamna Bala Muhammad na kyautata rayuwa da jin...
    Uzodimma ya ce ƙarin albashi zai inganta rayuwar ma’aikata, sannan ya bunƙasa tattalin arziƙin jihar. Ya kuma bayyana cewa kuɗaɗen shiga na cikin gida sun ƙaru daga Naira miliyan zuwa sama da Naira biliyan uku a kowane wata, yayin da bashin jihar ya ragu daga sama da Naira biliyan 280 a shekarar 2020 zuwa Naira biliyan 100. Ya yaba wa Shugaba Bola Tinubu bisa cire tallafin mai, yana cewa duk da ya jawo tsadar rayuwa, amma ya ƙara yawan kuɗin da ake raba wa jihohi kuma ya bai wa gwamnati damar yin sauye-sauye. Gwamnan ya ƙara da cewa daga ranar 27 ga watan Agusta, gwamnati za ta fara biyan kashin ƙarshe na kuɗaɗen fansho da ake bai wa tsoffin ma’aikata,...
    Fasinjoji na jirgin kasa wanda ya taso daga Abuja zuwa Kaduna ya sauka kan layin dogo da misalign karfe 11:00 nan safe kusa da garin jere. Da dama daga cikin fasinjojin suna cikin tashin hankali saboda matsalolin tsaro da ake fama da shi a kan hanyar. Amma Jaridar Premium times ta Najeriya ta bayyana cewa an kawo jami’an tsaro a yankin don tsaron fasinjojin. Kamfanin jiragen kasa na kasa wato ‘The Nigerian Railway Corporation (NRC) bai bada wani bayani kan al-amarin ba har zuwa lokacin bada wannan labarin. Saukan jirgin daga layin dogon dai bai jiwa wani rauni ba, kuma babu wanda ya rasa ransa. A cikin watan mayun shekara ta 2024 da ya gabata ma, an sami...
    Fasinjoji na jirgin kasa wanda ya taso daga Abuja zuwa Kaduna ya sauka kan layin dogo da misalign karfe 11:00 nan safe kusa da garin jere. Da dama daga cikin fasinjojin suna cikin tashin hankali saboda matsalolin tsaro da ake fama da shi a kan hanyar. Amma Jaridar Premium times ta Najeriya ta bayyana cewa an kawo jami’an tsaro a yankin don tsaron fasinjojin. Kamfanin jiragen kasa na kasa wato ‘The Nigerian Railway Corporation (NRC) bai bada wani bayani kan al-amarin ba har zuwa lokacin bada wannan labarin. Saukan jirgin daga layin dogon dai bai jiwa wani rauni ba, kuma babu wanda ya rasa ransa. A cikin watan mayun shekara ta 2024 da ya gabata ma, an sami...
    shafin Jagoran juyin juya halin Musulunci a cikin harshen Yahudanci ya bayyana cewa: ‘Yan sahayoniyya sune wadanda aka fi kyamata a duniya Shafin Jagoran juyin juya halin Musulunci na yaren yahudanci a shafin sada zumunta na X ya rubuta cewa: Makiyar al’ummar Iran na kan gaba a yau ita ce, gwamnatin ‘yan sahayoniyya wacce ita ce mafi kyamata a tsakanin al’ummar duniya. Shafin yanar gizo na KHAMENEI.IR na yaren yahudanci ya wallafa wani kaso na jawabin Jagoran a jiya litinin a wajen taron juyayin shahadar Imam Ali dan Musa al-Rida Jagoran shiriya na Iyalan gidan Manzon Allah {s.aw}. Sanarwar ta kara da cewa: “Makiyar al’ummar Iran a yau, ita ce gwamnatin ‘yan sahayoniyya, wacce duniya ta fi kyama a duniya....
    Makami mai linzami na Yemen na fission ballistic shi ne babban mafarkin da ke firgita ‘yan sahayoniyya Jaridar Isra’ila, The Jerusalem Post, ta yi bayanin cewa: Harba makamai masu linzami na gungu fission ballistic daga Yemen yana kara yawan barazanar tsaro, tare da dagula Shirin kakkabo shi, kuma yana janyo wahalar murmurewa daga barnarsa. Jaridar ta ce amfani da makamai masu linzami na gungu fission ballistic da ‘yan Yemen suka yi a kan abokan gabar Isra’ila na wakiltar wani gagarumin ci gaba mai kunshe da damuwa, tare da lura da cewa wadannan makamai masu linzami suna mayar da tsarin kariya na makamai masu linzami na gargajiya irin su Arrow ko Sling na David marasa amfani saboda ba su da kayan...
    Mataimakin Ministan harkokin wajen Iran da takwarorinsa na Faransa, Jamus, da Birtaniyya za su gudanar da wani sabon zagaye na tattaunawa a birnin Geneva na kasar Switzerland, a daidai lokacin da kasashen uku ke barazanar aiwatar da abin da ake kira tsarin dawo da takunkumin  Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya a kan Iran. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Esmaeil Baghaei ya fada a ranar Litinin cewa, za a koma  yin shawarwari tsakanin wakilan Iran da E3 a ranar Talata. Ya ce za a gudanar da taron ne a matakin mataimakan ministocin harkokin waje da daraktocin siyasa. Hakan na zuwa ne bayan wata tattaunawa ta wayar tarho tsakanin ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi da babban wakilin kungiyar EU mai...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Kwamitin Zartaswa na Ƙasa (NEC) na jam’iyyar adawa ta PDP ya tabbatar da Umar Damagum a matsayin shugaban jam’iyyar na ƙasa. Wannan dai na zuwa ne a yayin zaman NEC na 102 da ke gudana a hedikwatar jam’iyyar da ke Abuja. A jawabinsa na karɓar shugabanci, Damagum ya gode wa sauran mambobin Kwamitin Gudanarwa na Ƙasa (NWC) bisa taimako da haɗin kai da suka ba shi wajen gudanar da aikinsa. Ya kuma gode wa mambobin NEC bisa yabawa da amincewa da ƙoƙarinsa wajen farfaɗo da jam’iyyar, abin da ya ce hakan ya taimaka wajen tabbatar da shi a matsayin shugaban jam’iyyar.
    Babbar jam’iyyar adawa a Nijeriya, PDP, ta keɓe wa kudancin Nijeriya tikitin takarar kujerar shugaban ƙasa a Zaɓen 2027. Jam’iyyar ta tabbatar da haka ne a babban taron Kwamitin Zartarwa karo na 102 da ta gudanar ranar Litinin a Abuja. PDP ta tabbatar da Damagum a matsayin shugabanta na ƙasa Wata mata ta mayar da N4.8m da aka yi kuskuren tura wa asusunta a Maiduguri A baya-bayan nan dai wasu masu ruwa da tsaki kan sha’anin siyasa sun zafafa kiraye-kiraye ga tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya yi wa jam’iyyar takara a Zaɓen 2027. A yayin taron na yau ne kuma PDP ta tabbatar da Umar Damagum a matsayin shugabanta na ƙasa a hukumance. Damagum wanda ya shafe fiye da...
    Kwamitin Zartaswa na Ƙasa (NEC) na jam’iyyar adawa ta PDP ya tabbatar da Umar Damagum a matsayin shugaban jam’iyyar na ƙasa. Wannan dai na zuwa ne a yayin zaman NEC na 102 da ke gudana a hedikwatar jam’iyyar da ke Abuja. A jawabinsa na karɓar shugabanci, Damagum ya gode wa sauran mambobin Kwamitin Gudanarwa na Ƙasa (NWC) bisa taimako da haɗin kai da suka ba shi wajen gudanar da aikinsa. Ya kuma gode wa mambobin NEC bisa yabawa da amincewa da ƙoƙarinsa wajen farfaɗo da jam’iyyar, abin da ya ce hakan ya taimaka wajen tabbatar da shi a matsayin shugaban jam’iyyar.
    Za a yi amfani da harshen Hausa a matsayin hanyar samar da zaman lafiya a yayin bikin Ranar Hausa ta Duniya karo na goma (10), wanda za a gudanar a Daura da ke Jihar Katsina, a ranar Talata, 26 ga watan Agusta, 2025. Jagoran taron, Abdulbaqi Aliyu Jari, wanda shi ne ya ƙirƙiri wannan rana, ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai a Katsina. Jiragen yaki sun kashe ’yan ta’adda 35 a iyakar Najeriya da Kamaru Jami’an tsaro sun tsare jagoran Falasdinawa mazauna Najeriya Ya ce dukkan shirye-shirye sun kammala, kuma manyan baƙi daga ciki da wajen Najeriya tuni sun fara isowa domin halartar bikin. Jari ya ce an tsara taron ne domin baje kolin al’adun Hausawa...
    Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran ya jaddada cewa: Hadin kan al’umma, jami’ai, da sojojin da ke dauke da makamai, jan layi ne Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya jaddada cewa: Bayan da makiya suka kasa murkushe al’ummar Iran ta hanyar yaki, a halin yanzu suna neman cimma manufarsu ta hanyar haifar da sabani da rarrabuwar kawuna. Ya ce: “Dukkan jama’a, jami’ai, marubuta, da jaridu, dole ne su kare tare da karfafa garkuwar karfe na hadin kan kasa mai tsarki da dukkan karfinsu.” Jagoran ya jaddada bukatar tallafa wa masu yi wa kasa hidima, musamman ma shugaban kasar wanda ya bayyana a matsayin mai jajircewa da kuzari, yana mai jaddada cewa hadin kan al’umma, gwamnati,...
    An tsinci gawar wani saurayi mai suna Daniel Ekanen, mai kimanin shekaru 18, a gefen wani kudiddifi da ke unguwar Ikot Effanga a Ƙaramar Hukumar Kalaba, Jihar Kuros Riba. Lamarin ya jefa firgici a zukata da kuma zaman dar-dar a cikin mazauna yankin, inda aka ruwaito cewa an kawo marigayin ne wurin dangin mahaifinsa daga ƙauyen Ikot Offiong da ke ƙaramar hukumar Odukpani a jihar. Sarkin Musulmi ya ayyana Litinin 1 ga watan Rabi’ul Awwal Dangote ya ci gaba da zama attajiri mafi arziƙi a Afirka — Forbes Rahotanni sun nuna cewa ana zargin masu tsafi da sassan jikin ɗan adam ne suka yi kisan, domin kuwa an yanke kansa kafin a jefar da gawarsa a gefen kudiddifin. Wani daga...
    Fitaccen attajirin nan, Aliko Dangote ya ci gaba da riƙe kambinsa na mutum mafi arziƙi a nahiyar Afirka, inda dukiyarsa ta kai dala biliyan $24.4, a cewar sabuwar ƙididdigar da mujallar Forbes ta fitar a bana. Wannan ya sanya shi zama mutum na 88 a jerin masu kuɗin duniya, inda ya rike wannan matsayi da tazara mai nisa a kan sauran attajiran Najeriya. An kama matashi kan zargin kashe matar ɗan uwansa mai juna biyu An haramta bukukuwan aure a Taraba Abdulsamad Rabiu wanda ya mallaki rukunin kamfanin BUA, shi ne ya biyo bayansa da dukiyar da ta kai dala biliyan $7.2, wanda ya sa shi zama attajiri na 516 a duniya. Sai kuma Mike Adenuga da dukiya mai darajar...
    A yayin zaman majalisar dokokin jihar Katsina, Babban Mai Tsawatarwa na majalisar, Hon. Ibrahim Umar Dikko, ya fashe da kuka a gaban takwarorinsa, yana bayyana yadda ’yan bindiga suka mamaye mafi yawan yankunan da ke cikin Ƙaramar Hukumar Matazu da yake wakilta. Hon. Dikko ya bayyana cewa daga cikin gundumomi 10 da ke cikin Matazu, guda 8 sun faɗa hannun ’yan bindiga, inda ya ce manoma ba sa iya zuwa gonakinsu saboda tsoron harin da ake kai musu. “A jiya da safe, a bakin garin kusa da makarantar sakandare, sun kashe wani matashi sannan suka sace shanu hudu da ake amfani da su wajen noma,” in ji shi cikin hawaye. Ya kara da cewa a cikin kwanaki biyu da suka...
    Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya yi ta’aziyya ga gwamnatin Jihar Kebbi da al’ummar jihar bisa rasuwar Sarkin Zuru, Mai Martaba, Manjo Janar Muhammadu Sani Sami (Gomo II). A cikin wata sanarwa da mai bai wa shugaban ƙasan shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai Bayo Onanuga ya fitar, ya bayyana rasuwar Sarkin  a matsayin “babban rashi ga ƙasa,” inda ya tuno irin hidimar da marigayin ya yi a matsayinsa na tsohon gwamnan soja na Jihar Bauchi da kuma  hidimarsa a matsayin basarake. Shugaba Tinubu ya lura cewa Najeriya za ta daɗe tana tuna gudummawar tsohon janar ɗin, wanda kuma ya yi yaƙi a matsayin ƙaramin hafsan soja lokacin Yaƙin Basasa. Shugaban ƙasa ya kuma yabawa jagorancin...
    Ƙungiyar Gwamnonin Arewa, ta bayyana alhininta game da rasuwar Sarkin Zuru na Jihar Kebbi, Mai Martaba Manjo Janar Muhammadu Sani Sami (mai ritaya) Gomo II, wanda ya rasu yana da shekaru 81. Shugaban ƙungiyar, Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya ce marigayin jagora ne mai kishin ƙasa, dattijo nagari kuma basarake mai daraja wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen yi wa Najeriya hidima. Ta’aziyyar Sarkin Zuru: Muhammadu Sani Sami (1943-2025) Adam A. Zango ya auri jarumar Kannywood A cikin sanarwar ta’aziyyar da mai magana da yawunsa, Isma’ila Uba Misilli, ya fitar, gwamnan ya tuna irin rawar da Sarkin ya taka a aikin soja. Ya ce Sarkin ya taka rawa sosai lokacin da ya yi Gwamnan soja na tsohuwar Jihar Bauchi,...
    Kasashe 31 na duniya sun yi Allah wadai da kalaman fira ministan Isra’ila na shirin mamaye yankunan kasashe don kafa ‘Babbar kasar Isra’ila Kalaman Fira ministan gwamnatin mamayar Isra’ila Benjamin Netanyahu dangane da abin da ake kira “Babbare kasar Isra’ila” ta janyo suka daga Larabawa da Musulunci. Ministocin harkokin wajen kasashen Larabawa da na kasashen musulmi 31, tare da manyan sakatarorin kungiyar hadin kan kasashen Larabawa, da kungiyar hadin kan kasashen musulmi, da kuma kungiyar hadin kan kasashen Larabawan yankin tekun Fasha, sun yi Allah wadai da kalaman Netanyahu dangane da abin da ake kira “Babbar Isra’ila”, tare da la’akari da furucin a matsayin rashin mutunta dokokin kasa da kasa da kuma barazana kai tsaye ga tsaron kasashen Larabawa da...
    Kungiyar Hamas ta Falasdinu ta mayar da martani da cewa: Shigar da ƙungiyar cikin jerin “baƙin littafi’ na Majalisar Dinkin Duniya ba shi da inganci Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta bayyana rashin amincewarta da kakkausar suka ga rahoton da babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya António Guterres ya fitar kan cin zarafin mata da ke da alaka da rikice-rikicen makamai, wanda ya hada da kungiyar ta Hamas a cikin jerin bakin littafin wato “blacklist”, yayin da Guterres ya yi gargadi ga haramtacciyar kasar Isra’ila game da cin zarafin Falasdinawa a gidajen yari. Kungiyar Hamas ta bayyana a cikin wata sanarwa da ta fitar a yammacin jiya Juma’a cewa: Wannan matakin bai dace ba a bisa doka, ta kuma yi gargadin...
    Jami’an tsaro sun kama wani mutum da tsabar kuɗi Naira miliyan 25 da ake zargin kuɗin sayen kuri’a ne a zaɓen cike gurbin da ke gudana a Jihar Kaduna. Da misalin ƙarfe 3 na dare kafin wayewar garin safiyar Asabar da ake gudanar da zaɓen ne ’yan sanda da jami’an hukumar tsaro ta DSS suka kama mutumin a wani otel da ke hanyar Turunku a cikin birnin Kaduna. A cewar rundunar ’yan sandan binciken farko da aka gudanar ya tabbatar da cewa wanda ake zargin ya shirya yin amfani da kuɗaɗen ne wajen sayen kuri’u A yayin da ake yi masa tambayoyi, wanda ke  ya amsa laifinsa kuma ya roki a yi masa sassauci. A wata sanarwa da kakaki rundunar,...
    Wata kotun tarayya a kasar Canada ta ayyana manyan jam’iyyun Najeriya na APC da PDP a matsayin kungiyoyin ta’addanci yayin da ta hana wani tsohon dan siyasa, Douglas Egharevba, mafaka a kasar saboda alakarsa da jam’iyyun. Jaridar Peoples Gazette ta rawaito cewa alkalin kotun, Phuong Ngo, a hukuncin da ta yanke ranar 17 ga watan Yunin 2025, ta hana dan siyasar izinin shiga kasar bayan samun shi da gaza cika sharudan dokar shige da fice ta kasar. A cewar alkalin, “Dabi’ar wasu ’yan siyasa ’yan PDP, wadanda wasu daga cikinsu ma kusoshi ne a jam’iyyar, da wadanda suka aikata laifukan siyasa ko aka yi da yawunsu, ta yi yawan da ba zai yiwu a ki alakanta shugabancin jam’iyyun da ita...
    “Mun amshe bukatun, sannan bayan hakan kwamitin yin nazari kan sake yi wa tsarin mulki garambawul wanda mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Jibrin Barau yake jagoranta zai tattance tare da shirya rahoto ga majalisar. “Da zarar rahoton ya kammala, majalisar dattawa tare da hadin gwiwar majalisar wakilai za su gudanar da cikakken jin ra’ayin jama’a. Wannan zai ba da dama ga dukkan masu ruwa da tsaki da suka hada da masu goyon baya da masu adawa su gabatar da hujjojinsu. Bayan haka, majalisun guda biyu za su yanke shawara kan wadannan bukatun. “Batun kirkirar sabbin jihohi abu ne mai matukar muhimmanci wanda ke bukatar duba batutuwan al’umma, yankuna, da samun alkaluman tarihi. A wasu lokuta, ko a cikin jihohin da...
    A yau Juma’a ne kasar Japan ta gudanar da gangamin tunawa da wadanda suka rasa rayukansu yayin yakin duniya na biyu, sai dai yayin da yake jawabi albarkacin taron, firaministan kasar Shigeru Ishiba, bai tabo batu kan alhakin dake rataye a wuyan kasarsa ba, a matsayinta na wadda ta mamayi wasu kasashen nahiyar Asiya. A hannu guda kuma ya gabatar da addu’a ga wurin ibadar nan na Yasukuni, a matsayin girmmawa ga wurin ibadar da ake kallo a matsayin wurin da aka karrama mutanen da suka tafka danyen aiki yayin yakin duniya na biyu. Kazalika, wasu ministocin kasar sun kaiwa wurin ibadar na Yasukuni ziyarar girmamawa. Jerin wadannan matakai dai na shan suka, da adawa daga sassan kasa da kasa....
    A farkon wannan shekarar da ta gabata, Jaridar LEADERSHIP ta ruwaito Ministan Sufurin Ma’aikatar Jiragen Sama Festus Keyamo, a wani taro ya bai wa kungiyoyin na Sufurin Jiragen Sama tabbacin cewa, Gwamnatin Tarayya za ta tabbatar da bi ka’ida wajen sayar da hannun jarin Tashoshin Jiragen Saman kasa. Keyamo ya kuma bai wa shugabannin kungiyoyin tabacin cewa, suma a sanya kan batun na yarjejeniyar ta sayar da hannun jarin Tashoshin Jiragen Saman. Kazalika, ba su tabbacin cewa, zai umarci hadiminsa domin ya ci gaba da sanar da shugabannin kungiyoyin kan abinda ke tafiya game da yarjejeniyar. Sai dai, a jawabin da shuwagabbin kungiyar da kuma na ma’aikatan suka gabatar a wani babban taronsu a shalakwar Tashar Jiragen Sama da ke...
    Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi sauye-sauyen jagoranci a Hukumar Talabijin ta ƙasa (NTA), inda ya naɗa Rotimi Richard Pedro a matsayin sabon Darakta-Janar. Sauran naɗe-naɗen sun haɗa da Karimah Bello a matsayin Babbar Darakta ta Sashen Tallace-Tallace, Stella Din a matsayin Babbar Darakta ta Sashen Labarai, da Sophia Essahmed a matsayin Manajing Darakta ta Kamfanin NTA Enterprises Limited. Pedro, ɗan asalin jihar Lagos, ƙwararren mai ba da shawara ne a harkar kafofin watsa labarai, mai gogewa sama da shekaru 30 a fannoni da suka haɗa da talabijin, haƙƙoƙin watsa wasanni, da dabarun tallace-tallace a Afrika, da Birtaniya da Gabas ta Tsakiya. Kwararre ne a fannin nishaɗi da mallakar fasaha, tare da digirin na biyu a Gudanar da Zuba...
    Wata kotun tarayya a kasar Kanada ta ayyana manyan jam’iyyun Najeriya na APC da PDP a matsayin kungiyoyin ta’addanci yayin da ta hana wani tsohon dan siyasa, Douglas Egharevba, mafaka a kasar saboda alakarsa da jam’iyyun. Jaridar Peoples Gazette ta rawaito cewa alkalin kotun, Phuong Ngo, a hukuncin da ta yanke ranar 17 ga watan Yunin 2025, ta hana dan siyasar izinin shiga kasar bayan samun shi da gaza cika sharudan dokar shige da fice ta kasar. A cewar alkalin, “Dabi’ar wasu ’yan siyasa ’yan PDP, wadanda wasu daga cikinsu ma kusoshi ne a jam’iyyar, da wadanda suka aikata laifukan siyasa ko aka yi da yawunsu, ta yi yawan da ba zai yiwu a ki alakanta shugabancin jam’iyyun da ita...