2025-10-16@18:54:58 GMT
إجمالي نتائج البحث: 22
«tarayyar turai»:
Bayan tattaunawa ta wayar tarho da ministan harkokin wajen kasar iran Abbas Araqchi yayi da babbar jami’ar diplomasiyar kungiyar tarayyar turai kaja kallas ta maimaita bukatar kungiyar na sa ido kan tashohin nukiliyar iran, kana tayi gargadin cewa kofar diplomasiya tana gab da rufewa, matsayin da iran taki amincewa da shi kuma ta bayyana shi a matsayin mara inganci, Iran a matsayinta na member a NPT ta yi aiki da nauyin da ya rataya akanta, karkashin yarjejeniyar JCPOA yayin da Iran ke jiran kungiyar tarayyar turai ta yi aiki da abin da ya hau kanta kuma ta cire takunkumi, amma hakan bai samu ba, kasashen turai da hadin bakin Amurka suna barazanar sake dawo da takunkumai don matsin lamba ga...
Hukumar tarayyar turai ta gabatar da shawara ga kasashe mambobi da su jingine aiki da yarjejeniyar da aka kulla ta kasuwanci da HKI saboda yakin Gaza. A yau Laraba ne dai hukumar tarayyar turai din ta bijiro da wannan shawarar ga kasashen mambobi,sai dai kuma babu cikakken goyon baya daga mafi yawancin kasashen kungiyar da zai sa a yi aiki da shi. Ita kuwa jami’ar harkokin wajen ta tarayyar turai din Kaya Kalas ta gabatar da shawarar a kakaba takunkumi akan wasu ministoci biyu na HKI da kuma ‘yan share wuri zauna da suke amfani da akrfi akan Falasdinawa. Da akwai kungiyoyin kare hakkin bil’adama guda 84 da suke yin kira a yanke duk wata alaka ta kasuwanci da zuba...
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya sanar da yiwuwar sake yin wani taro da babbar jami’ar kungiyar tarayyar Turai kan harkokin waje Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya sanar da yiwuwar sake ganawa da babbar jami’ar harkokin wajen kungiyar tarayyar turai Kaya Kalas. A cikin wata sanarwa da ya fitar a yammacin jiya Juma’a, Araqchi ya ce, “Akwai yiwuwar sake yin wani taro da jami’ar harkokin wajen kungiyar tarayyar Turai, kuma hakan ya dogara ne da shawarar Turai. Dangane da tattaunawar da aka yi a birnin Alkahira, ya ce, wadannan shawarwarin masu muhimmanci ne sosai, da kuma shawarwarin da ake yi a bayan yaki, inda hotunan shahidai ke wucewa a kan idonun mutane daya bayan daya, ba tattaunawa...

Kasar Sin Na Fatan EU Za Ta Yi Aiki Da Ita Bisa Alkibla Guda Da Tsara Hadin Gwiwa Na Shekaru 50 Masu Zuwa
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun, ya bayyana a yayin gudanar da taron manema labaru na yau da kullum da aka yi yau Litinin cewa, bana shekara ce ta cika shekaru 50 da kulla huldar diflomasiyya tsakanin Sin da Tarayyar Turai EU. Kuma taron kolin kasar Sin da EU karo na 25 na karatowa. Kasar ta Sin tana fatan kungiyar EU za ta yi aiki tare da ita bisa alkibla guda, da cimma matsaya, da kawar da bambance-bambance, da kuma tsara shirin hadin gwiwa tare cikin shekaru 50 masu zuwa. Bayan cimma yarjejeniya tsakanin Sin da kungiyar EU, shugaban majalisar Tarayyar Turai António Costa da shugabar hukumar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen, za su...
Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da lafta wa Tarayyar Turai da kuma Mexico harajin kashi 30 kan kayayyakin da ake shiga da su da su ƙasar daga ranar 1 ga Agusta. Bayanai sun ce ana ganin wannan matakin zai iya haddasa rikici mai tsanani tsakanin Amurka da biyu daga cikin manyan abokan kasuwancinta. An sanya dokar hana fita a Adamawa Tinubu ya dawo Najeriya bayan ziyarar aiki a Saint Lucia da Brazil Trump ya yi cikakken bayani kan wadannan haraje-harejen ne a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, yana mai cewa matuƙar ba a cimma wata tartibiyar matsaya ba, ba shakka zai ƙara lafta musu harajin. Wannan na daga cikin jerin sabbin haraje-haraje da...

Kazem Sajjadpour Ya ce: Iraniyawa Suna Daukan Tarayyar Turai Ma Goyon Bayan Harin Zaluncin Isra’ila Kansu
Mai ba da shawara ga ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Tarayyar Turai ta zama abokiyar gudanar da ta’addancin ‘yan sahayoniyya kan kasar Iran Kazem Sajjadpour, mai baiwa ministan harkokin wajen kasar Iran shawara ya bayyana dabi’ar Turai a lokacin da yahudawan sahayoniyya suke kai wa Iran hari a matsayin abin da ba za a amince da shi ba, saboda matakin da suka dauka na goyon bayan ‘yan sahayoniyya lamarin da mayar da ita mai hannu wajen kai hare-haren. Sajjadpour ya ce: Turai ba ta da wani matsayi a manufofin ketare na Amurka kuma Donald Trump bai ma ambaci Turai ba a cikin wannan tsari. A wani taron karawa juna sani na yanar gizo da aka gudanar a...
Kasar China ta maida martani ga takunkuman tattalin arziki na wasu kayakin kiwon lafiya wadanda tarayyar Turai da dorta maya. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto majiyar kasar ta Chaina na fadar haka ta kuma kara da cewa gwargwadon takunkuman da suka dorawa kasar gwargwadon maida martanin kasar ta China. Labarin ya kara da cewa wannan haramcin ba zai shafi kamfanonin turai da suke samar da kayakin aikin kiwo lafiya a cikin kasar China ba. A cikin watan Yunin da ya gabata ne kungiyarn EU ta hana gwamnatocin kasashe kungiyar sayan kayakin aikin likita fiye da dalar Amurka miliyon 5 tare da bukatar kasar china ta daina nuna bambanci a cikin ahrkokin kasuwanci da ke tsakaninsu.
Minstan harkokin wajen Iran Abbas Arakci ya mayar da martani da kakkausar murya akan furucin jami’ar diplomasiyya ta tarayyar turai Kaya Jallas na cewa Iran ta dakatar da shirinta na makamashin Nukiliya, yana mai cewa; Jallas ta jahilci abinda dokokin NPT su ka kunsa. Abbas Arakci ya ce; Idan manufar ganawa da kwamitin hadin gwiwa akan yarjeniyar Nukilar iran shi ne kawo karshen Shirin makamashin Nukiliyar Iran, to kuwa Jallas ta jahilci abinda yake kunshe a cikin yarjejeniyar hana yaduwar makaman Nukiliya. Ita dai babbar jami’ar harkokin wajen tarayyar turai Jallas ta rubuta sako a shafinta na X cewa; Ya zama wajibi a bude tattaunawa da sauri da Iran akan yadda za ta kawo karshen shirinta na makamashin Nukiliya, kuma...
Wasu jami’an diplomasiyyar turai sun yi wa gwamnatin Benjamin Netanyahu da cewa za ta fuskanci Karin matsin lamba idan har ba ta sauya halayyarta akan Gaza ba. Jaridar “Washington Post” ta Amurka ta ambato jami’an diplomasiyyar turai suna cewa; sabon tsarin da ake yin aiki da shi na raba kayan agaji a Gaza, ya juya ya zama harigitsi kuma ana bude wuta akan mutane da hakan ya yi sanadiyyar jikkatar Falasdinawa da dama.” Har ila yau jami’an diplomasiyyar na turai sun ce, ko kadan ba su da aniyar bayar da kayan agajinsu ga masu tafiyar da tsarin da su ne Isra’ila da Amurka.” Bugu da kari, majiyar diplomasiyyar ta tarayyar turai ta ci gaba da cewa; Hotunan masu ban tsoro...
Bayan sabon farmakin da Isra’ila ta kai a zirin Gaza, kasashen Yamma na kokarin kara matsin lamba kan Isra’ila, wacce ta kauda kai kan kiraye kirayen da duniya ke yi na ta dakatar da yakin a Gaza. Kungiyar ta EU, ta kara mastin lamba ta hanyar sake nazari kan yarjejeniyarta da Isra’ila ta tsawon shekaru 25 dake a tsakaninsu. Tunda farko dama kasashen kasashen Canada-Faransa da Ingila sun sanar da yin Allah wadai da farmakin kasa na soja na sojojin Isra’ila a Gaza. Baya ga hakan kuma Birtaniyya a ranar Talata ta sanar da kawo karshen yarjejeniyar ciniki cikin ‘yanci da Isra’ila. Ita ma kiasar Sweden, ta yi kira da a kakaba takunkumi ga membobin gwamnatin Isra’ila. Bayanai sun ce...
Bayan sanarwar ba-zata da Amurka ta yi a makon da ya gabata, Tarayyar Turai ta ce za ta dage takunkumin da ta kakaba wa Syria. Ministocin harkokin waje da ke taro a Brussels ne suka yanke shawarar dage dukkan takunkumin tattalin arzikin kan Siriya. “Muna son taimakawa al’ummar Siriya wajen sake gina sabuwar Siriya,” in ji jami’ar kula da harkokin wajen Tarayyar Turai Kaja Kalas. Tarayyar Turai ta kuma yi alkawarin bayar da Yuro biliyan biyu da rabi domin sake gina kasar. Matakin dage wannan takunkumin da aka kakabawa gwamnatin Bashar al-Assad tun daga shekara ta 2011, zai bada damar sakin kadarorin kasar da har yanzu ke daskare, sannan kuma zai baiwa hukumomin kasar damar neman zuba jarin da suke...
Jami’ar siyasar waje ta tarayyar turai Kaja Kallas ta bayyana cikakken goyon baya ga warware batun makamashin Nukiliyar Iran ta hanyar diplomasiyya. Jami’ar ta wallafa a shafinta na X cewa: Na tattauna da ministan harkokin wajen Iran Abbas Arakci domin tabbatar da goyon bayan kungiyar tarayyar turai akan aiki da hanyar diplomasiyya domin warware batun Nukiliyar Iran da kuma rage rikice-rikice a cikin wannan yankin.” Haka nan kuma Kallas ta jaddada abinda a baya tarayyar turai din ta rika riyawa da ba shi da tushe na cewa, Iran tana bai wa Rasha taimakon soja tana mai cewa: ” Na kuma yi kira ga Iran da ta dakatar da bai wa Rasha taimakon soja.” Iran dai ta sha yin watsi da...
Kasashen kungiyar Tarayyar Turai sun amince da cewa kungiyar za ta kaddamar da matakan yaki da harajin da shugaban Amurka Donald Trump ya dora mata. Kungiyar mai kasashe mambobi 27 tana fuskantar kashi 25% na harajin shigo da kayayyaki kan karafa, aluminium, da motoci, da kuma karin harajin kashi 20% akan kusan duk wasu kayayyaki karkashin manufofin Trump. Domin mayar da martani, Tarayyar Turai za ta aiwatar da ayyuka, galibi an saita su a kashi 25%, kan nau’oin kayayyakin da ake shigo da su daga Amurka, wanda zai fara daga ranar Talata mai zuwa a matsayin martani na musamman ga harajin karafa na Amurka. Kungiyar har yanzu tana kimanta tsarinta na magance tasirin karin haraji. Kayayyakin na Amurka da tsarin...

Tarayyar Turai Ta Yi Maraba Da Tattaunawa Tsakanin IRAN da Amurka Kan Shirinta Na Makamashin Nukliya
Kungiyar tarayyar Turai ta yi maraba da tattaunawa tsakanin Amurka da JMI dangane da shirinta na makamashin Nukliya, tare da kara jaddada cewa hanyar diblomasiyya kadai ta rage don warware wannan matsalar. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa a halin yanzu dai kungiyar tarayyar ta Turai ta na ci gaba da takurawa JMI da takunkuman tattalin arziki, masu tsanani, a lokaci guda tana fadar cewa hanyar Diblomasiyya ce kadai ta rage wajen warware matsalar shirin makamashin nukliya na kasar Iran, wanda ya tabbatar da fuska biyu na kasashen na Turai. Labarin ya kara da cewa, wani mai magana da yawun kungiyar ta EU wanda kuma baya son a bayyana sunansa, ya fadawa kamfanin dillancin labaran IRNA...
An kori jakadan Isra’ila a Habasha Avraham Neguise daga taron kungiyar Tarayyar Afirka da aka gudanar a wannan Talata a Addis Ababa domin tunawa da kisan kiyashin da aka yi a Rwanda. An fitar da Neguise daga dakin taro na Mandela da ke hedikwatar Tarayyar Afirka bayan da kasashe da dama suka nuna rashin amincewarsu da halartarsa a taron shekara-shekara kan kisan kiyashin da aka yi a kasar Rwanda. Jakadan na Isra’ila ya shiga wurin taron ne ba zato ba tsammani, ba tare da an gayyace shi ba, a cewar majiyoyin diflomasiyyar da suka halarci taron. Majiyar ta kara da cewa tawagogin kasashen Afirka da dama sun nuna rashin amincewa da zuwansa, lamarin da ya sa aka dakatar da taron...
Jami’ar kula da manufofin ketare ta Tarayyar Turai, Kaya Kalas, ta tabbatar da cewa, EU za ta iya sake kakaba takunkumi kan kasar Syria, idan aka samu tabarbarewar lamurra, tana mai nuni da yadda ake cin zarafin fararen hula a gabar tekun Syria. Kaya Kalas ta shaidawa kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya cewa, “Muna shirye-shiryen mayar da takunkumi kan Syria, idan muka ga tabarbarewar lamurra na ci gaba, inda ta jaddada cewa, dole ne mika mulki ya kasance cikin lumana da kuma hadin kai, kuma dole ne a kare fararen hula a kowane hali.” Ta bukaci dukkan masu ruwa da tsaki na waje da su mutunta hadin kan Syria, da kuma iko da iyakokinta.”

Shuwagabannin Kasashen Kungiyar tarayyar Turai Sun Bukaci Karin Kudade A Bangaren Tsaro A Rigimarsu Da Amurka
Shuwagabannin kasashen Turai, sun amince da kara kudade mai yawa a bnaren tsaro da kuma tallafawa kasar Ukraine, a yakin da take yi da kasar Rasha, saboda janyewar Amurka dukkan taimakon da take bawa kasar ta Ukraine. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar taron shuwagabannin kasashen na Turai, sun zuba kudade dalar Amurka biliyon $860 (Euro 800bn) don karfafa kasashen Turai da kuma Ukrania. Shugaban kungiyar ta EU Ursula von de Leyen yace a karon farko tsaron kasashen yake komawa kansu bayan da Amurka ta dauki nauyin hakan tun bayan yakin duniya na II. A halin yanzu gwamnatin kasar Amurka tace ba zata ci gaba da kashewa wadannan kashe kudade don tsarunsu ta kungiyar tsaro ta...
Kungiyar Hamas ta jinjinawa kungiyar tarayyar Afrika ta AU kan yin Allah wadai da kisan kiyashin da Isra’ila ke yi a Gaza bayan da kungiyar ta soki Isra’ila da keta dokokin kasa da kasa a jawabin rufe taron da ta yi na kwanaki biyu a Addis Ababa. Hamas ta ce tana matukar godiya da matsayin da kasashen Afirka suka dauka a kan Isra’ila da “mummunan” ayyukanta a Gaza. A cikin sanarwar da ta fitar, kungiyar ta AU ta ce tana adawa da keta dokokin kasa da kasa da kuma “kai hari kan fararen hula da kayayyakin more rayuwa da Isra’ila ke yi”. Kungiyar dai ta yi Allah Wadai da duk wani Shirin tilastawa Falasdinawa gudun hijira daga muhallinsu Batun neman...
Kungiyar Tarayyar Afirka ta yi Allah Wadai da duk wani Shirin tilastawa Falasdinawa gudun hijira daga muhallinsu Batun neman tilastawa Falasdinawa gudun hijira daga kasarsu ta gado yana ci gaba da fuskantar tofin Allah da Allah wadai a duk fadin duniya da kuma a taruka daban-daban, kuma batun Falasdinu shi ne kan gaba a ajandar taron kolin Afirka karo na 38 da aka yi a birnin Addis Ababa fadar mulkin kasar Habasha. A yayin bude zaman taron kolin kungiyar tarayyar Afirka, shugaban hukumar Tarayyar Afirka, Moussa Faki, ya yi gargadi game da kiraye-kirayen da ake yi na tilastawa Faladinawa gudun hijira, yana mai jaddada cewa ci gaba da tauye wa Falasdinawa ‘yancinsu abin kunya ne ga bil’Adama, yana mai sukar...
Kungiyar Tarayyar Turai EU ta yaba wa ƙoƙarin Gwamna Babagana Umara Zulum wajen farfado da harkokin rayuwar al’ummar Jihar Borno bayan tashe-tashen hankulan ’yan ta’adda da jihar ta yi fama da shi. EU ta buga misali da cibiyar koyar da sana’o’i ta Muna da ke horar da matasa musamman waɗanda rikicin Boko Haram ya shafa na tsawon fiye da shekaru goma. Ya je Maiduguri daga Legas a kan keke Rikicin rusau ya yi ajalin mutum 4 a Kano Shugaban tawagar Tarayyar Turai a Borno, Ambasada Gautier Mignot ne ya yi wannan yabon a Maiduguri a lokacin da yake zantawa da manema labarai a cibiyar koyar da sana’o’i ta Muna. Ambasada Mignot ya ce tawagarsa ta yi matuƙar farin ciki da...

Majalisar Dokokin Tarayyar Turai Ta Amince Da Bukatar Kawo Karshen Rikicin Jin Kai Cikin Gaggawa A Gaza
Majalisar Dokokin Tarayyar Turai ta yi kira da a kawo karshen rikicin jin kai na Gaza cikin gaggawa Majalisar dokokin Tarayyar Turai ta amince da wata shawara a jiya Larabar da ta aka gabatar da ta bukaci kawo karshen rikicin jin kai na yara, mata da fursunoni a Zirin Gaza, sakamakon kisan kare dangi da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta yi a yankin sama da watanni 15. Cibiyar yada labarai ta Falasdinu ta watsa rahoton cewa: An tattauna shawarwarin da suka yi kira da a kawo karshen rikicin jin kai da ya shafi yara, mata da fursunoni a Gaza, a babban taron Majalisar Dokokin Tarayyar Turai. A kuri’ar da aka kada, an amince da kudurin da rinjayen kuri’u 90, inda...