Rashin Tsaro: Ana Ƙoƙarin Ganin Ƙarshen Haƙurin Arewa – ACF
Published: 25th, August 2025 GMT
Ya kuma yi gargadin cewa, “Wannan ba lokaci ba ne da Arewa za ta naɗe hannunta tana kallo yayin da al’amura ke ci gaba da taɓarɓarewa, lamarin tsaro yana kara ta’azzara yayin da ake ci gaba da kwashe albarkatun yankin, ambaliyar ruwa na ci gaba da barazana, dole ne mu tashi tsaye mu hada kai domin kare yankin.
Osuman ya koka da kashe-kashen da ake yi a Arewacin Nijeriya a kullum, yana mai jaddada cewa, babu yadda za a yi, a zura ido ana kallo.
“Mun yi asarar yara, matasa maza da mata, da tsoffi saboda ambaliyar ruwa, bala’o’i, ‘yan bindiga da masu kwacen wayoyi, halin da ake ciki, akwai matukar damuwa, don haka nake kira da a yi tunani mai zurfi kan nemo mafita da kuma addu’a,” in ji shi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Neja Ta Musanta Rahoton Hana Da’awa A Jihar
Rahoton rashin fahimtar da aka fara yadawar, ya biyo bayan taron kwamitin zaman lafiya da kwantar da tarzoma na jihar, wanda Darakta Janar ya jagoranta a ranar 4 ga watan Satumba.
Rashin fahimtar sahihin sakamakon taron ya sa wasu suka rahoto cewa, kwamitin ya dakatar da Malamai daga yin wa’azi.
Sanarwar ta kara da cewa, “Hukumar ba ta da hurumin haramtawa Malaman Addinin Musulunci yin wa’azi sai dai in ya bayyana a fili an taka ƙa’idojin hukumar da ta shimfiɗa”.
A cewar Hukumar, an kira taron ne domin gabatar da fom din rijistar yin wa’azi ko Da’awah da kuma bin tsarin tantancewa.
Ta bayyana shirin a matsayin wani yunkuri na wayar da kan jama’a don “hana rashin fahimtar juna da kuma daƙile yaɗuwar wa’azin yaudara” a faɗin jihar Neja.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp