Wani Harin Amurka kan Yemen ya kashe fararen hula akalla 12
Published: 21st, April 2025 GMT
Amurka ta sake kai wani hari ta sama kan babban birnin kasar Yemen, Sana’a, inda ta kashe fararen hula akalla 12 tare da jikkata wasu fiye da 30 na daban.
Mummunan harin na Amurka an kai shi ne a wata kasuwa mai cike da cunkoson jama’a a unguwar al-Farwa da ke gundumar Sha’ub a safiyar ranar Litinin.
Ana fargabar adadin wadanda suka mutu zai karu yayin da mutane da dama ke makale a karkashin baraguzan gine-gine da aka wargaza a harin.
A gefe guda kuma, Amurka ta kai hare-hare a yankunan lardin Sa’ada, a arewa mai nisa na kasar, da tsakiyar Ma’rib, da yammacin Hudaydah.
Dama kafin hakan a ranar Lahadi, Amurka ta kai wasu hare-hare ta sama a Yemen, ciki har da Sana’a, inda aka kashe akalla uku.
A cikin watan da ya gabata ne dai sojojin Amurka suka zazafa kai hare-hare a kasar Yemen, bisa ikirarin dakile hare-haren kungiyar Ansarullah dake kai farmakin goya bayan falasdinu kan jiragen ruwa masu alaka da Isra’ila.
Fiye da mutane 200 ne aka kashe a harin da Amurka ta kai kan Yemen tun cikin watan Maris.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Mutanen Sweida Na Kasar Siriya Suna Fama da Rashin Abinci da Ruwa
A yankin sweida na kudancin kasar Siriya mazauna wurin sun bayyana cewa abinci da ruwa da kuma kayakin bukatu nay au da kullum sun fara karanci sosai a yankin saboda yakin makonni uku da suke fafatawa da sojojin sabuwar gwamnati a Damascus.
Jaridar The National ta Amurka ta bayyana cewa yankin sweida na kudancin kasar Siriya wanda kuma HKI ta dade tana shigowa yankin ta fita a halin nyanzu yana fama da karancin abinci da ruwansha. Sannan da alamun har yanzun sojojin sabuwar gwamnatin kasar Siriya tana ci gaba da hana shigowar abinci da ruwa yankin duk tare da shelanta tsagaita wuta da aka yi.
Labarin ya kara da cewa. an kashe daruruwan mutane a fafatawar da mayakan hTI suka yi da drsawa da suka fi rinjaye a yankin da kuma wasu kananan kabilu a yankin.
Tun lokacinda HKI tare da taimakin kasashen turkiya da sauran kasashen yamma suka kifar da gwamnatin Bashar al-asad, kasar Siriya take fama da karin kashe-kashe na kabilanci da na addini a kasar.