’Yan bindiga sun sace makiyaya 5, da shanu 1,200 a Kaduna
Published: 17th, April 2025 GMT
Mazauna gundumar Kufana a Ƙaramar Hukumar Kajuru ta Jihar Kaduna sun shiga cikin fargaba sakamakon jerin hare-haren ’yan bindiga da ya yi sanadiyyar sace mutane biyar da kuma kwashe shanu 1,200 cikin kwanaki hudu.
Babban Jami’in Gundumar, Mista Stephen Maikori, ya tabbatar da faruwar hare-haren a ranar Laraba.
A cewarsa, lamari na farko ya faru ne a daren Talata, 8 ga Afrilu, 2025, lokacin da ’yan bindiga suka kai hari kauyen Mashigi Boka-Libere, wani matsugunin Fulani, da misalin karfe 10 na dare.
Maikori ya ce maharan sun kwashe garken shanu guda 12, inda kowanne garke yake da kimanin shanu 100, wanda ya kai jimillar dabbobi 1,200.
Dangote: Har yanzu gidajen mai ba su rage farashin mai ba Najeriya da gwamnatin sojin Nijar sun sasantaYa ce maharan sun wuce ta kauyen Dogon Noma, inda suka kai hari ga mazauna suka kuma sace babura biyu daga hannun Mista Abednego Samuel da Mista Danjuma John.
A ranar Litinin, 7 ga Afrilu, da misalin karfe 6 na safe, an sace mutane uku daga Ungwan Kaje Afogo.
Maikori ya ce wani harin kuma ya faru a daren Alhamis, 10 ga Afrilu, a al’ummar Afogo Gari, inda aka sace Miss Patience Audi da Mista Arewa Anthony.
Ya ce, “Muna ci gaba da tuntubar jami’an tsaro da iyalai da abin ya shafa.”
Kokarin da aka yi na tuntubar kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna, DSP Mansir Hassan, bai yi nasara ba saboda yana cikin taro kuma bai amsa kiran waya ba a lokacin da ake tattara wannan rahoto.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: hare hare
এছাড়াও পড়ুন:
Kotu Ta Soke Umarnin Kwace Filin Asibitin Tiamin, Ta Umarci Gwamnatin Kano Ta Biya Diyyar ₦2.6bn
A wani hukunci da ya yanke a ranar Laraba, alkalin kotun, Ibrahim Karaye, ya ce soke hakkin wanda ya shigar da kara ya sabawa ka’ida, ya sabawa kundin tsarin mulkin kasa, kuma hukuncin ba shi da tushe balle makama.
Karaye ya ci gaba da cewa, sanarwar kwace shaidar mallakar filin a cikin wata wasika mai dauke da kwanan watan Satumba 3, 2021, daga ofishin kula da filaye na jihar Kano, an yi ta ne ba tare da an yi shari’a ta adalci ba, wanda hakan ya saba wa tanadin dokar amfani da filaye.
Alkalin ya ci gaba da bayyana cewa, takardar shaidar mallakar fili ta asali mai lamba LKN/COM/2017/116 [wacce aka sake shedawa a matsayin LPKN 1188], MLKN01622, da MLKN01837 – suna nan da inganci kuma sahihai.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp