Wata Kotun Majistire mai lamba 7 a Kano, ta bayar da umarnin tsare wasu ’yan TikTok biyu kan zargin wallafa wasu bidiyon batsa a shafukansu na dandalin sada zumunta.
Hukumar Tace Fina-Finai ta Kano ce ta gurfanar da ababen zargin biyu — Isa Kabir Brigade da Fatima Adam Kurna — kan wallafa bidiyon da suka saɓa wa tarbiyya da addini.
Sai dai bayan lauyan da ke ɓangaren masu shigar da ƙara, Garzali Maigari Bichi ya karanta musu ƙunshin tuhume-tuhumen, sun musanta wasu daga ciki.
Dangane da hakan ne Alƙalin Kotun, Halima Wali ta bayar da umarnin tsare ababen zargin tare da ɗage zaman kotun zuwa ranar 24 ga watan Afrilu.
Ana iya tuna cewa dai Hukumar Tace Fina-Finai ta Kano ta ɗaura ɗamarar tsaftace dandalan sada zumunta ta hanyar kame da ladabtar da masu wallafe-wallafen duk wani abu da ya ci karo da tarbiyya da addini.
Ko a bayan nan sai da hukumar ta gurfanar da wasu mutum biyu — waɗanda aka yankewa hukuncin ɗauri na shekara guda ko zaɓin biyan tara ta Naira dubu 100 — kan wallafa bidiyon batsa a shafukansu na TikTok.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
An sanya dokar hana fita a Kaduna
Gwamnatin Kaduna ta sanya dokar taƙaita zirga-zirga ta tsawon kwana guda a wasu sassan jihar.
Wannan na zuwa ne bayan wani hargitsi tsakanin jami’an tsaro da wasu ɓata-gari a yankin Kakuri.
Wuraren da dokar ta shafa sun haɗa da Kakuri Bus Stop, Kurmi Gwari, Monday Market, Afaka Road, da Kakuri GRA.
Wata sanarwa da Gwamnatin Kaduna ta fitar ta buƙaci mazauna da su kiyaye umarnin wannan doka.