Za A Samar Da Ababen Hawa Ga Malaman Sakandare A Jigawa
Published: 12th, April 2025 GMT
Gwamnatin jihar Jigawa ta ce za ta samar da ababen hawa ga shugabannin makarantun babbar sakandare a fadin jihar.
Kwamishinan ilimi na jihar, Farfesa Isa Yusuf Chamo, ne ya bayyana hakan yayin wani taro da ya gudanar da shugabannin makarantu a garin Dutse.
A cewarsa, za a gyara gidajen ma’aikatan makarantun sakandare domin saukaka matsalar masauki ga malamai da sauran ma’aikata da ba malamai ba.
Farfesa Chamo, wanda Mataimaki na Musamman ga Gwamna kan Harkokin Ilimi, Malam Abdullahi Hudu, ya wakilta, ya ce taron ya na da nufin tattauna shirin dawowa makarantu bayan hutun da aka yi a jihar.
Ya bayyana cewa, gwamnatin jihar ta sanya bangaren ilimi a sahun gaba saboda muhimmancinsa ga ci gaban jihar.
Kwamishinan ya nuna cewa gwamnatin jihar ta dauki malamai 7,000 domin inganta tsarin koyarwa a makarantu, inda ya kara da cewa za a dauki ma’aikatan girki na J-Cook domin kara karfafa harkar gudanarwar makarantu.
A jawabansu daban-daban, wasu daga cikin Daraktoci da Shugabannin makarantu, sun bukaci a sake duba kudaden gudanar da makarantu, da samar da kwamfutoci da kayan aikinsu, da bayar da tallafi da kuma samar da malamai domin inganta ayyukan koyarwa.
Usman Muhammad Zaria
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Jigawa
এছাড়াও পড়ুন:
Hajjin 2025: An Fara Yi Wa Maniyyata Allurar Rigakafi A Jigawa
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Jigawa ta ƙaddamar da shirin rigakafin mahajjata na shekarar 2025 a yankin Hadejia da ke shiyyar arewa maso gabas ta jihar.
Shugaban hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo, ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Hadejia.
Alhaji Ahmed Umar Labbo ya jaddada kudirin hukumar na ba da fifiko ga lafiya da kuma tsaron mahajjatan jihar.
Ya ce, kare lafiyar mahajjatan jihar nauyi ne da ya rataya a wuyan hukumar.
“Shirin rigakafin da muka fara yana nuna shirinmu na tabbatar da nasarar aikin Hajjin shekarar 2025. Ina ƙarfafa mahajjata su ba da haɗin kai tare da bin ƙa’idojin lafiya yayin wannan tafiya mai albarka.”
“Ina kuma ƙarfafa ku da ku zama masu bin doka da haƙuri yayin aikin Hajji. Da fatan za ku halarci dukkan tarukan bita da kai da aka shirya, domin muhimmanci su Alhazai” In ji shi.
Labbo, wanda ya sa ido a kan shirin rigakafin tare da bai wa wani mahajjaci daga Hadejia allurar farko, ya bayyana cewa aikin rigakafin zai ci gaba har zuwa lokacin tafiyar su zuwa ƙasa mai tsarki.
Haka kuma, Shugaban cibiyar lafiya a matakin farko, Dr. Bala Ismaila, ya bayyana muhimmancin allurar rigakafin da ake bayarwa, wanda ya haɗa da rigakafin cutar sankarau, cutar shan inna, da kuma cutar zazzabin cizon sauro (yellow fever).
Ya kuma yi bayani kan yiwuwar fuskantar rashin lafiya bayan rigakafin, inda ya shawarci mahajjata da su nemi kulawar likita cikin gaggawa idan suka fuskanci hakan ko wata matsala da ta wuce kima.
Wakilinmu ya ruwaito cewa, ana gudanar da aikin rigakafin a dukkan kananan hukumomi 27 na jihar.
Usman Muhammad Zaria