Aminiya:
2025-11-02@17:18:28 GMT

An kashe shugaban Lakurawa, Maigemu a Kebbi

Published: 8th, March 2025 GMT

Jami’an tsaro da ’yan sa-kai sun kashe shugaban ’yan ta’addan Lakurawa, Maigemu, a Jihar Kebbi.

Daraktan Tsaro na Jihar Kebbi, AbdulRahman Usman Zagga ne, ya shaida wa manema labarai a ranar Juma’a cewa an kashe Maigemu a ranar Alhamis.

PDP ta soki dakatar da Natasha, ta nemi a binciki Akpabio Fashewar tankar mai: Mutum 7 sun mutu, gonaki sun lalace a Neja

Ya ce an kashe shi ne yayin musayar wuta da jami’an tsaro a garin Kuncin Baba da ke Ƙaramar Hukumar Arewa.

Mutuwarsa ta zo ne mako guda bayan da Gwamna Nasir Idris ya kai ziyarar jaje ƙauyukan Bagiza da Rausa Kade, inda ’yan ta’adda suka kashe mutum shida.

“Ƙoƙarin gwamna ya haifar da ɗa mai ido, domin yanzu an kashe wannan babban shugaban ’yan ta’adda. Gawarsa tana nan a matsayin shaida,” in ji Zagga.

Ya yaba wa gwamnan bisa ƙoƙarinsa na tabbatar da tsaro da kuma tallafin da yake bai wa jami’an tsaro a kai a kai.

Zagga ya kuma roƙi jama’a da su ci gaba da haɗa kai da jami’an tsaro ta hanyar ba su bayanai da kuma kai rahoton duk wani abun zargi domin samar da zaman lafiya mai ɗorewa a jihar.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Jami an Tsaro Lakurawa musayar wuta

এছাড়াও পড়ুন:

Tsaro: Taimakonmu Amurka ya kamata ta yi maimakon ba barazana ba — Kwankwaso

Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana damuwarsa kan kalaman da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi game da Najeriya.

Kwankwaso, ya yi wannan magana ne bayan Trump ya yi barazanar ɗaukar matakin yaƙi game da zargin kisan kiyashi da ake yi wa Kiristoci.

Kisan Kiristoci: Ba zan yaƙi ƙasar iyayena kan labaran ƙarya ba — Sojan Amurka Kisan Kiristoci: Lauyoyi sun nemi Gwamnatin Tarayya ta tattauna da Amurka

A cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Kwankwaso, ya ce Najeriya ƙasa ce mai cikakken ’yanci, wadda ke fama da matsalar tsaro daga miyagu a sassa daban-daban na ƙasar.

“Matsalar tsaron da muke fuskanta ba ta bambanta tsakanin addini, ƙabila ko ra’ayin siyasa,” in ji shi.

Ya buƙaci gwamnatin Amurka da ta tallafa wa Najeriya da sabbin fasahohi domin yaƙar matsalar tsaro maimakon yin kalaman da za su iya raba kan ’yan ƙasa.

“Amurka ya kamata ta taimaka wa hukumomin Najeriya da ingantattun fasahohi don magance matsalolin tsaro, maimakon yin barazanar da za ta ƙara raba ƙasar,” in ji Kwankwaso.

Haka kuma, ya shawarci Gwamnatin Najeriya da ta naɗa jakadu na musamman domin inganta hulɗar diflomasiyya da Amurka da kare muradun ƙasar a matakin duniya.

Ya kuma yi kira ga ’yan Najeriya da su zauna lafiya, inda ya bayyana cewa wannan lokaci ne da ya dace a fifita haɗin kan ƙasa ba abin da ke raba ta ba.

“Wannan lokaci ne da ya kamata mu mayar da hankali kan abin da zai haɗa kanmu ba wanda zai raba mu ba. Allah Ya albarkaci Najeriya,” in ji shi.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Tsaro: Taimakonmu Amurka ya kamata ta yi maimakon barazana — Kwankwaso
  • Tsaro: Taimakonmu Amurka ya kamata ta yi maimakon ba barazana ba — Kwankwaso
  • Dalilin Gwamnatin Jihar Kuros Riba Na Raba Wa Manoma Taraktoci
  • Tinubu Ya Kaddamar Da Ayyuka Bakwai A Jami’ar Ilori
  • Dalibin Jami’ar Jos Ya Kashe Abokinsa Ya Binne Gawar A Rami
  • Gwamna Namadi Ya Bada Motocin Aiki Goma Ga Rundunar ‘Yan Sanda
  • Gwamnatin Jigawa Ta Bada Motocin Aiki Goma Ga Rundunar ‘Yan Sanda
  • An yi garkuwa da Mataimakin Shugaban Majalisar Dokokin Kebbi
  • Matsalar Talauci Da Rashin Tsawon Rai Da ‘Yan Nijeriya Ke Fuskanta
  • Matsalar Tsaro: Ko Sabbin Shugabannin Rundunar Soji Za Su Kawo Sauyi?