Kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran ya jaddada cewa: Kungiyar Hamas duk da iyakantaccen kayan yakinta ta kalubalanci gwamnatin ‘yan sahayoniyya

Kwamandan dakarun kasa na Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran Birgediya Janar Morteza Miryan ya jaddada cewa: Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta kalubalanci gwamnatin mamayar ‘yan sahayoniyya da suke samun goyon bayan Amurka da kasashen Yamma duk da iyakantaccen kayan yakin da ta mallaka na kare kai.

Birgediya Janar Miryan ya ce a cikin jawabinsa a wajen bikin tunawa da shahidan harin “Wal-Fajir 8” da aka gudanar a lokacin tunawa da shahidan lardin Alborz da ke yammacin birnin Tehran: A lokacin yakin da aka yi na shekara ta 1980 zuwa shekara ta 1988), yana cewa; A lokacin yakin sun ga yadda gwamnatin Saddam na Iraki ta mallaki dukkan nau’o’in makamai, amma kuma al’ummar Iran suka tsaya tsayin daka wajen yaki da ta’addanci.

Yayin da yake nuni da laifuffukan da yahudawan sahayoniyya suke yi a yankunan Falastinu da suka mamaye, Birgediya Janar Miryan ya ce: Duniya ta taimaka wa ‘yan sahayoniyya ‘yan mamaya, kuma dukkanin tsarin makaman sararin samaniyya suna hannunsu, amma kungiyar Hamas ta tsaya tsayin daka da karfinta.

Janar Miryan ya kara da cewa: A yayin harin daukan fansa na “Alkawarin Gaskiya na 1 da na 2, Iran ta tabbatar da cewa: Kashi 85 cikin 100 na makamai masu linzaminta sun kai ga inda aka saita su.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Iran ta yi fatali da kalamman IAEA Kan Shirin Nukiliyarta

Iran ta yi ikirarin cewa Darakta Janar na Hukumar Makamashin Nukiliya Ta Duniya (IAEA), Rafael Grossi, ya “san”sarai da cewa shirin nukiliyar kasar na lumana ne, don haka ya kamata ya guji yin “kalamai marasa tushe” kan lamarin.

A wata hira da ya yi da tashar Al Jazeera, kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Esmail Baghai ya bayyana cewa kalaman da Rafael Grossi ya yi a baya sun share fagen ayyukan ta’addanci da Amurka da gwamnatin Isra’ila suka yi wa Iran a watan Yunin da ya gabata.

Ya kamata Darakta Janar na IAEA ya guji yin kalamai marasa tushe game da shirin nukiliya na Iran, in ji shi.

Rafael Grossi ya bayyana a ranar Laraba cewa IAEA ta gano kwanan nan da sake dawowa da ayyuka a wuraren nukiliya na Iran,” bayan ya amince cewa kasar ba ta nuna alamun kara wadatar da uranium ba.

A cikin wani rahoto na sirri da aka gabatar wa Kwamitin Gwamnonin IAEA a ranar 31 ga Mayu, 2025, Babban Daraktan IAEA ya yi iƙirarin cewa “Iran ta gaza bayyana ayyukanta na nukiliya a wurare uku da ba a bayyana ba” kuma ta bayyana damuwa game da tarin sinadarin uranium da ta wadatar zuwa kashi 60%.

A cewar jami’an Iran, rahoton Grossi game da shirin nukiliya na Tehran ya share fagen kai hari ga Isra’ila kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

A karshen watan Yuni ne, Majalisar Tsaron Iran ta amince da wani kudiri da majalisar dokokin kasar ta zartar wanda ya dakatar da haɗin gwiwa da hukumar ta IAEA.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Trump Ya Umarci Ma’aikatar Yakin Amurka Ta koma gwajin makaman nukiliya October 30, 2025 Isra’ila ta amince da fadada matsugunai a Yammacin Kogin Jordan October 30, 2025 Gaza: hare-haren Isra’ila sun kashe mutane 100 Cikin Kwanaki Biyu October 30, 2025 Sudan : Kasashen duniya na tir da cin zarafi a El-Fasher October 30, 2025 Iran Ta Jaddada Bin Hanyar Diflomasiya Ko Da A Lokacin Yaki Ne Amma Ba Zata Amince Da Bin Umarni Ba October 30, 2025 Qalibaf: Amurka Tana Yaudarar Duniya Da Zaman Lafiya, Alhalin Tana Ci Gaba Da Kai Harin Wuce Gona Da Iri October 30, 2025 Ci Gaba Da Killace Gaza Bayan Tsagaita Bude Wuta Ya Janyo Mutuwar Mutane 1000 A Yankin October 30, 2025 Kungiyar Rapid Support Forces Ta Sanar Da Kafa Kwamitin Bincike Kan Cin Zarafin Al’umma A El Fasher October 30, 2025 An Kafa Dokar Ta Baci A Darul-Salam Saboda Tarzoman Zaben Shugaban Kasa A Tanzania October 30, 2025 Rasha Da Amurka Sun Sake Dawo Da Gwaje-gwajen Makaman Nukiliya October 30, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Larijani: Iran Ba Ta Tsoron Gudanar Da Tattaunawa, Amma Ta Zama Mai Amfani
  • Tsokaci Dangane Da Juyin Mulki A Nahiyar Afirka
  • Hamas ta musanta zargin Amurka na cewa tana sace kayan agaji a Gaza
  • Wasu Yan Ta’adda Sun Kashe Dakarun Sa Kai 2 A Kudu Maso Gabashin Iran
  • Iran Ta Gargadi Isra’ila Kuma Tasha Alwashin Kare Shirinta Na Nukiliya
  • Iran ta damu da halin da ake ciki a yankin El Fasher na Sudan
  • An raba wa iyalan jami’an ’yan sandan da suka rasu a bakin aiki a Borno N63.4m
  • Ƙwallo ta kashe ɗan wasan Cricket
  • Iran ta yi fatali da kalamman IAEA Kan Shirin Nukiliyarta
  • Trump Ya Umarci Ma’aikatar Yakin Amurka Ta koma gwajin makaman nukiliya