Sojojin Sudan Sun Fara Shirye-Shiryen ‘Yantar Da Birnin Khartoum Fadar Mulkin Kasar
Published: 9th, February 2025 GMT
Sojojin Sudan suna kokarin canza ma’aunin yaƙin kasar bayan da suka sun tunkari birnin Khartoum fadar mulkin kasar domin yantar da shi gaba daya
Babban birnin kasar Sudan, Khartoum, shi ne tushen rikicin kasar da a halin yanzu aka shafe makonni ana gwabza fada tsakanin sojoji da mayakan dakarun kai daukin gaggawa, amma fadan ya kara kamari a ‘yan kwanakin da suka gabata.
Sojoji suna kara ci gaba da tunkarar babban birnin kasar bayan fitattun sojojin kasar da suka hada da sojoji da mayaka masu goyon bayan sojoji da hukumar leken asiri da dakarun tsaron Sudan da suke sansanin Haddab da ke bangaren arewa maso gabashin yankin Gabashin Nilu a arewa maso gabashin Khartoum suka doshi birnin na Khartoum da nufin ‘yantar da shi gaba daya daga hannun mayakan dakarun kaidfaukin gaggawa.
Wata majiyar sojan ta bayyana cewa: Sojoji da dakarun da ke mara musu baya sun tunkari hedikwatar bataliya ta dabarun yaki a yankin Maqran Al-Nilu biyu a birnin Khartoum.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Xi Ya Gabatar Da Rubutaccen Jawabi Ga Taron Kolin Shugabannin Masana’antu Da Kasuwanci Na APEC
Ya kuma bayyana cewa kasar Sin wuri ne mai kyau ga harkokin zuba jari ga ‘yan kasuwa na duniya. Ya ce hadin gwiwa da kasar Sin yana nufin hadin gwiwa da damammaki, imani da kasar Sin yana nufin imani da kyakkyawar makoma, zuba jari a kasar Sin yana nufin zuba jari mai riba ta dogon zango.(Safiyah Ma)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA