Aminiya:
2025-06-15@18:18:53 GMT

Ta kashe saurayinta saboda ya gaisa da tsohuwar abokiyar karatunsa

Published: 9th, February 2025 GMT

Wani matashi ɗan kasar Argentina mai shekara 23 ya rasa ransa a sakamakon daɓa masa wuƙa da budurwarsa ta yi saboda kawai ya gaisa da wata mata a kan titi.

Kishi madaidaici zai iya zama abu mai masu alaka da juna, amma mafi yawanci na iya wuce kima!

Abba ya naɗa sabon Sakataren Gwamnatin Kano Shigo da hatsi daga ƙetare ya karya farashinsa a Neja

Idan aka dubi labarin Mariano Grinspun, ɗan shekara 23 daga González Catán, wani birni a lardin Buenos Aires na Argentina, wanda budurwarsa mai tsananin kishi ta caka masa wuka wanda ya yi sanadiyya mutuwarsa bayan ya gaisa da wata tsohuwar abokiyar karatunsa a titi, za a ga abin akwai ban mamaki.

Abin ya faru ne ranar 21 ga Oktoba 2024, kusa da titin Balboa da La Bastilla, a birnin González Catan.

Mariano da budurwarsa Natacha Palavecino, suna tafiya tare, sai suka ci karo da wata mata da ta gaida Mariano kuma ta tambaye shi halin da yake ciki.

Gaisuwar ta haukata budurwar Mariano, inda ta zaro wuƙa a ɓoye ta afka masa.

Matar da ta gaisa da Mariano Grinspun, tsohuwar abokiyar karatunsa ce, amma hakan ya tunzura budurwarsa.

Natacha ta kai hannu ta ɗauki wata boyayyiyar wuƙa sannan ta yanki matar mai suna LC kamar yadda kafafen yada labarai na kasar Argentina suka bayyana.

Bayan yankar LC da wuƙar ta faɗi kasa ta yi yunƙurin ƙara yankar ta, amma ta sa hannunta ta kare, wanda da watakila ta kashe ta da ba don wani mutumin ba wanda ya yi nasarar daƙile faruwar hakan.

Abin takaici, Mariano Grinspun bai yi sa’a sosai ba, domin bayan da ta gaza kashe matar, Natacha Palavecino ta far wa saurayin nata, inda ta daɓa masa wuƙa a kirji.

Masoyan sun yi ta muhawara ta tsawon mintuna da dama, kamar yadda kyamarorin sa ido na CCTV a yankin suka nuna, wanda a lokacin Mariano ya fadi kasa yana shure-shure.

Zuwa wani lokaci, ya kasa tashi sai budurwarsa mai shekara 32 ta kai masa hari da hannunta.

Shaidun gani da ido sun kira jami’an agajin gaggawa, amma ba su iya yin komai ba wajen ceto rayuwarsa.

Wani bincike da aka gudanar ya bayyana tarihin tashin hankali Natacha Palavecino.

A 2021, an yanke mata hukuncin daurin shekara daya a gidan yari saboda ta dava wa wani tsohon saurayinta wuƙa a kirji, har ma Mariano da kansa ya kai ƙarar ta ga ’yan sanda saboda barazanar da ta yi masa da kuma yi masa rauni a jiki.

A watan Yulin shekarar bara ce aka ba da umarnin hana Natacha duk wata alaka da Mariano.

Sai dai bayan wucewar wa’adin, sai ya yanke shawarar sake dawowa da alakar.

Palavecino mai shekaru 32 za ta iya kasancewa a gidan yari tsawon shekaru saboda wannan laifi na kisan saurayinta da kuma yunkurin kisan matar da ta gaishe shi a kan titi.

 

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Argentina

এছাড়াও পড়ুন:

Masu ƙwacen waya sun kashe ma’aikacin Jami’ar Northwest a Kano

Rahotanni sun bayyana cewa wasu masu ƙwacen waya sun kashe wani ma’aikacin Jami’ar Northwest da ke Kano, Buhari Imam, ta hanyar daba masa wuta.

Bayanai sun nuna cewa barayin sun ritsa shi ne a yankin unguwar Sheka da ke karamar hukumar Kumbotso, inda suka sossoke shi da wuka a ciki kuma suka kwace wayarsa, a ranar Laraba.

BBC ya ruwaito mutumin ya rasu bayan da aka garzaya da shi Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano, a ranar Juma’a.

Shugaban ƙungiyar ma’aikatan jami’ar (NASU), Kwamared Bashir Muhammad, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin ya yi kira ga gwamnatin Jihar Kano da sauran hukumomi da su ɗauki tsattsauran mataki a kan kisan.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Dan Asalin Tudun Loess
  • Yadda wani ɗan sanda ya rasu a hanyar zuwa ɗaurin aurensa
  • Masu ƙwacen waya sun kashe ma’aikacin Jami’ar Northwest a Kano
  • An samu gobara a wasu matatun mai guda biyu na Iran bayan harin da Isra’ila ta kai
  • ’Yan bindiga sun kashe mutum 100 a Benuwe
  • Gwamnati Ta Yi Barazanar Matakai Masu Tsauri Kan Masu Fasa Bututun Mai
  • Dimokuradiyya A Shekara 26: Ba Yabo Ba Fallasa
  • Ambaliyar Mokwa: An sake gano gawar mutum bayan kwanaki 8
  • Ambaliyar Mokwa: An sake gano gawa guda bayan kwanaki 8
  • ICPC Ta Gurfanar Da Ma’aikacin Kotu Bisa Badakalar Naira Miliyan 9.2