Saura ƙiris Bello Turji ya zo hannu – Ministan Tsaro
Published: 5th, February 2025 GMT
Ministan Tsaro, Muhammad Badaru Abubakar, ya bayyana cewa sun kusa da kama ƙasurgumin ɗan ta’addan nan da ya addabi yankin Arewa Maso Yamma, Bello Turji.
Ministan ya ƙara da cewa Gwamnatin Tarayya tana da tabbacin cewa matsalar tsaro za ta zama tarihi kafin ƙarshen shekarar 2025.
Sarkin Jiwa a Abuja ya yi rashin mahaifiya Tinubu ya ƙara kasafin kuɗin 2025 zuwa N54.2trn
“Shugaban ƙasa na cewa yaushe matsalar tsaro za ta ƙare, saboda lokacin da ya kamata ta ƙare ya yi.
“A wani zama da muka yi da shi da shugabannin hafsoshin tsaron, an tattauna sosai, kuma shugaban ya ce su faɗa masa yaushe matsalar za ta ƙare, suka ce da yardar Allah zuwa ƙarshen shekarar nan,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa: “Sun ce ko matsalar ba ta ƙare gaba ɗaya ba, to za a ga sauƙin da kowa zai gani ya kuma ji daɗi.”
A wani taron da aka yi tare da shugabannin tsaro, Badaru, ya ce Shugaban Ƙasa ya bayyana cewa yana tsammanin matsalar tsaro za ta ƙare kafin ƙarshen shekara mai zuwa.
Hakazalika, ya ce idan matsalar ba ta ƙare, gwamnatin za ta ɓullo da sabbin dabaru domin murƙushe ta’addanci a yankin da ma Najeriya baki ɗaya.
A yayin tattaunawa da BBC Hausa, Ministan ya bayyana cewa duk da a yanzu ba a kama Turji ba, amma suna da labarin ya fara guje-guje, kuma nan ba da jimawa ba zai shiga hannu.
Ministan ya tabbatar da cewa tsare-tsaren da Gwamnatin Tarayya da hafsoshin tsaro suke aiwatarwa, za su kai ga gagarumar nasara wajen inganta tsaro a Najeriya.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Arewa maso yamma Ministan tsaro Muhammad Badaru Abubakar
এছাড়াও পড়ুন:
Ribas: Duk wani rikici tsakanina da Fubara ya ƙare – Wike
Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya tabbatar da cewa tattaunawar da suka yi da Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ta kawo ƙarshen duk wata rigima da ke tsakaninsa da Gwamnan Jihar Ribas da aka dakatar, Siminalayi Fubara.
A daren ranar Alhamis ne Shugaba Tinubu, ya jagoranci wani zaman sulhu a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja, tsakanin Wike da Gwamna Fubara da kuma wasu daga cikin ’yan majalisar Ribas da aka dakatar.
NDLEA ta kafa cibiyar kula da masu shaye-shaye a Yobe Tinubu ya rattaba hannu kan sababbin dokokin harajiBayan ganawar, Wike ya yi magana da manema labarai, inda ya tabbatar da kawo ƙarshen rikicinsa da Fubara.
“Dukkaninmu mun amince mu yi aiki tare da Gwamna, kuma shi ma ya amince zai yi aiki da mu. Dukkanninmu ’yan gida ɗaya ne.
“Rigimarmu ta daɗe, amma zamanmu na ranar Alhamis ya kawo ƙarshenta. Dama ɗan Adam yana iya samun saɓani, amma daga baya a sasanta.”
Ya ƙara da cewa: “Kuma yau ne muka kammala komai, mun zo mun shaida wa Shugaban Ƙasa cewa mun daidaita. Don haka a gare ni, komai ya wuce.”
Wike, ya kuma yi kira ga mabiyansa da su kwantar da hankali tare da haɗa kai don ciyar da Ribas gaba.
“Ina kira ga kowa da kowa da mu haɗa kai da sauran jama’a. Babu sauran rigima, babu wani abu da za a sake yin faɗa a kai.”
Abin da rikicin ya haifarA baya dai rikicin siyasa a Jihar Ribas, ya haifar da barazanar tsige Gwamna Fubara a watan Oktoban 2024, yayin daga bisani Shugaba Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci a watan Maris a jihar
Sai dai yanzu ɓangarorin sun ce komai ya wuce, kuma za su ci gaba da aiki tare domin ci gaban jihar.