2025-04-21@00:54:48 GMT
إجمالي نتائج البحث: 442
«rage farashin man fetur»:
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya yi watsi da barazanar HKI na kaiwa cibiyoyin makamashin nukliyar kasar don hana kasar abinda take kira makaman Nukliya. Ministan ya kara da cewa kasar Iran zata iya kare kanta ko da Amurka ce ta takaleta, kuma Amurka ta san hakan. Sannan ya ce HKI bata taba...
Gwamnaton kasar Kongo Democradiyya ta bada sanarwan haramta jam’iyyar Josept Kabila tsohon shugaban kasar. Shafin yanar gizo na labarai, Africa News ya nakalto ma’aikatar harkokin cikin gida na kasar tana bada wannan sanarwan. Labarin ya kara da cewa, Josept Kabila ya shugabanci kasar ta kwango har zuwa shekara ta 2019, karkashin Jam’iyyarsa ta ‘the People’s...
A faransa ana ci gaba da tsare wata ‘yar Iran mai goyan bayan Falasdinu, bis azarginta da iza ta’addanci. Mahdieh Esfandiari (mai shekaru 35) ana tsare da ita tun ranar 28 ga watan Fabrairu, bayan kama ta a binrin Lyon, inda ta ke da zama. Iran ta bakin kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar, Esmail Baghai,...
Kungiyar Hamas ta yi watsi da kudirin baya bayan nan na Isra’ila na kwance damarar kungiyoyin gwagwarmayar Falasdinawa domin tsagaita bude wuta a Gaza, tana mai kiran hakan a matsayin wani yunkuri na gurgunta ‘yancin Falasdinu. Tattaunawar da ake ci gaba da yi tsakanin Isra’ila da Hamas ta tsaya cik, inda Isra’ila ta matsa kaimi...

An Fara Bikin Ranar Sojin A Iran 18 Ga Watan Afrilu Tare Da Gudanar da Fareti A Gaban Shugaban Kasar
An fara gudanar da bukukuwan ranar soji a Iran a ranar 18 ga watan Afrilu ta hanyar gudanar da faretin soja a gaban shugaban kasar Mas’ud Pezeshkian An fara faretin soji na sojojin kasar Iran a kusa da hubbaren Imam Khumaini (r.a) da ke kudancin birnin Tehran fadar mulkin kasar a daidai lokacin da ake...
Dakarun gwagwarmayar Yemen sun kaddamar da hare-haren daukan fansa kan yankin Jaffa da ke kusa da birnin Tel Aviv na Isra’ila Dakarun gwagwarmayar Yemen sun sanar da aiwatar da wasu matakan soji masu inganci kan yankin Jaffa da aka mamaye, da kuma kan jiragen ruwan Amurka masu dauke da jiragen saman yaki na Truman da...
Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya bukaci Kiristoci da su yi tunani a kan darussa, muhimmaci, da kuma kyawawan dabi’u na makon Easter. Gwamna AbdulRazaq a wani sako da ya aike a Ilorin, ya taya mabiya addinin kirista a jihar da ma fadin Najeriya murnar bikin Easter. Gwamnan ya ce nasarar da Yesu...
Wannan nasarar ta nona irin namijin kokarinda Bankin ya yi na kara habaka samar wa da kansa kudaden shiga duk da matsin tattalin arzikin da kasar nan ke fuskanta. Bugu da kari, kadarorin Bankin sun karu zuwa jimmlar kaso 47 daga Naira tiriliyan 20 a shekarar 2023 zuwa Naira tiriliyan 30, a shekarar 2024. Kazalika,...
Sojojin kasar Yemen sun bada sanarwan cilla makamai masu linzami kan birnin Telaviv da kuma kan jirgin yakin Amurka saboda tallafawa falasdinawa a Gaza, da kuma maida martani kan hare-haren Amurka kan kasar a jiya Alhamis. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kakakin sojojin kasar na Yemen Burgediya Janar Yahayah Saree yana...
Ita Jihar Yobe,rashin biyan sabon mafi krancin albashi da tsohon na Naira 30,000 ga Malaman makarantun ta na Firamare da Sakandare, hakan ta kasance ne saboda rashin amincewa tsakanin Kungiyar NUT da kuma Kungiyar ma’aikatan Kananan Hukumomi ta kasa (NULGE). A ma’aikatar ilimin bai daya ta Jihar Abia, bangaren Kungiyar Malaman makaranta NUT, da reshen...
Hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya (NSCDC) reshen jihar Zamfara, ta tura jami’ai 415 a fadin jihar domin tabbatar da tsaro a duk lokacin bukukuwan Easter. Hakan ya fito ne a cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar jihar, ASCII Umar Mohammad M. ya fitar, ya ce jami’an sun jibge a...
Hakazalika, kamfanoni 43 da aka bayyana sun ba da shawarar raba jimillar Naira tiriliyan 1.678 ga masu hannun jarinsu, tare da yaba wa abokan huldarsu. A cikin 2024, bangarori na kasuwancin Nijeriya ya gamu da kalubale masu yawa na tattalin arziki da samar da ababen more rayuwa wadanda suka yi matukar tasiri ga ayyukansa. Masana’antun...
Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya jaddada cewa, Iran a shirye take yin aiki tare da Saudiyya a dukkanin bangarori, domin cin gajiyar al’ummomin kasashen biyu da ma duniyar musulmi, tare da yin ishara da cewa, dukkanin ci gaban da Iran ta samu a dukkanin bangarori na ilimin kimiyya da fasaha,...
Mata da ’yan mata da suka tsira daga tashin hankalin ‘yan Boko Haram a Arewa Maso Gabashin Nijeriya na fuskantar matsaloli masu yawa, ciki har da shiga tsananin damuwa da fuskantar nuna wariya da rashin samun dama na neman kuɗi da kuma uwa-uba rashin samun kulawar gwamnati da na al’umma. A lokacin tashin hankali da...

Wata Cibiyar Kare Hakkin Bil’Adama Ta Bukaci Kama Jami’in Haramtacciyar Kasar Isra’ila A Kasar Birtaniya
Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Hind Rajab ta yi kira ga Birtaniya da ta kama ministan harkokin wajen haramtacciyar kasar Isra’ila Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Hind Rajab ta gabatar da bukatar fitar da sammacin kame ministan harkokin wajen haramtacciyar kasar Isra’ila Gideon Sa’ar da yake ziyara a Birtaniya. Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto...
Hare-haren sojojin mamayar Isra’ila sun kona kananan yara a garin Khun-Yunis da ke kudancin Zirin Gaza Hukumar tsaron fararen hula a Zirin Gaza ta fitar da wani faifan bidiyo a yau alhamis, inda ta ke nuna irin mummunan halin da ‘yan gudun hijiran Falasdinawa suka shiga a Khan Yunis, bayan da jiragen saman yakin gwamnatin...
Tsohon shugaban jam’iyyar APC a Jihar Enugu, Dr. Ben Nwoye, ya ajiye muƙaminsa daga jam’iyyar. Nwoye, wanda ya sanar da haka a wani taron manema labarai ranar Alhamis, ya ce wannan shawara ta biyo bayan rushewar jagorancin jam’iyyar a jihar. Kafin yanke wannan shawara, Nwoye ya ce ya tattauna da magoya bayansa da sauran...
A karo na biyu a cikin mako guda, matatar mai ta Dangote ta sanar da rage farashin man fetur. Daga ranar 16 ga Afrilu, 2025, farashin man fetur zai tashi daga N865 zuwa N835. Wannan dai shi ne karo na biyu da aka rage farashin a cikin mako guda yayin da matatar man Dangote a...
Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa ta shirya taron horaswa gaa malamai daga dukkan kananan hukumomi 27 domin shirya su, su horar da maniyyata aikin hajjin 2025 na jihar. Darakta Janar na hukumar Alhaji Ahmed Umar Labbo ya bayyana hakan a yayin wani taron karawa juna sani na kwana daya ga sabbin masu wa’azin...
Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa ta shirya taron horaswa gaa malamai daga dukkan kananan hukumomi 27 domin shirya su, su horar da maniyyata aikin hajjin 2025 na jihar. Darakta Janar na hukumar Alhaji Ahmed Umar Labbo ya bayyana hakan a yayin wani taron karawa juna sani na kwana daya ga sabbin masu wa’azin...
Majalisar kasa ta kasar Rasha ta amince da yarjeniyar dangantaka ta musamman tsakanin kasar da JMI a ranar 8 ga watan Afrilun da muke ciki sannan ana saran shugaban kasa Vladimir Putin zai sanyawa yarjeniyar hannu a nan gaba. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa yarjeniyar ta musamman mai kuma dogon...
Hukumar UNICEF ta MDD mai kula da yara ta bada sanarwan cewa kimani yara 3,500 suka rasa rayukansu a kokarin ketara tekun Medeteranina a cikin shekaru 10 da suka gabata. Kamfanin dillancin labaran Spunic na kasar Rasha ya nakalto hukumar tana fadar haka a wani rahoton da ta fitar dangane da hakan. Labarin ya kara...
An bukaci gwamnatocin jihohi da su kara samar da tsarin kula da kiwon lafiya na bai daya (UHC) ga ‘yan kasa domin tabbatar da samar da ingantaccen kiwon lafiya a kasar. Jami’ar Ayyuka, Kula da Lafiya ta Duniya ga Mata a Lafiya ta Duniya, Najeriya (WGH), Dokta Sienne Oluwatosin Orogun, ta yi wannan kiran...
Gwamnatin Tarayya ta nemi kafafen watsa labarai da su daina kawo rahoton ayyukan ‘yan ta’addan da ke tada hankali a jihohin Filato, Borno, Zamfara, Binuwai, da sauransu. Aminiya ta rawaito cewa jihohin na fama da tashe-tashen hankula musamman a baya-bayan nan in da aka yi asarar rayuka da dukiyoyin al’umma. Dangote ya karya farashin fetur...
Mako guda bayan rage farashin fetur da Naira 45, matatar mai ta Dangote ta sake karya farashin man ga ‘yan sari da ragin Naira 30 duk lita. Aminiya ta rawaito cewa matatar na sayar da man ne a ranar Laraba akan ₦835, saɓanin makon da ya gabata da ta sayar da shi akan ₦865 bayan...
Gwamnan Filato, Caleb Mutfwang, ya sanar da haramta kiwo da daddare tare da taƙaita amfani da babura a faɗin jihar sakamakon yawaitar hare-haren da ake kai wa a wasu sassan jihar. A cikin wani jawabi da ya yi a jihar a ranar Laraba, Mutfwang ya bayyana hare-haren a matsayin “ayyukan ta’addanci” da ke da nufin...
Don su wuce zuwa zagaye na gaba, Real Madrid na buƙatar ta zura ƙwallaye huɗu ba tare da ta bari Arsenal ta zura ƙwallo ko ɗaya ba. Idan kuma suka ci ƙwallo uku, kamar yadda Arsenal ta ci su, za a ƙara lokaci domin a fidda wanda yi nasara. Fitaccen ɗan wasan Faransa, Kylian Mbappe,...
Paris St Germain ta kai zagayen daf da na ƙarshe a Gasar Zakarun Turai duk da rashin nasara da ta yi a hannun Aston Villa ranar Talata a Villa Park. Aston Villa ta yi nasarar cin PSG 3-2, inda Tielemans da McGinn da kuma Konsa suka ci mata ƙwallayen a wasa falle na biyu a...
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Neja ta kaddamar da rabon sutura da jakunkunan hannu masu nauyin kilo 8 ga maniyyatan bana, a matsayin wani ɓangare na shirye-shiryen aikin Hajji na shekarar 2025. A lokacin da yake jawabi yayin kaddamar da rabon, Shugaban Hukumar, Sheikh Muhammad Awwal Aliyu, ya bayyana cewa rabon kayayyakin na da...
Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu ya yi barazanar korar sojojin da ke neman kawo karshen yakin Gaza bayan sun rattaba hannu kan wasu takardu da ke nuna bukatar hakan. A bayan nan dai fiye da sojoji 1,500 na rundunar da ke kula da tankokin yaƙi ta Isra’ila, ciki har da janar-janar, suka sanya hannu kan wata...

Lauyoyin London Suna Tattara Bayanai Kan ‘Yan Birtaniya Da Suka Yi Yaki Cikin Sahun Yahudawan Sahayoniyya A Gaza
Lauyoyin Landan suna tattara bayanai kan ‘yan Birtaniya da suka yi aiki a cikin rundunar sojojin mamayar Isra’ila Kwararru kan harkokin shari’a na kasar Biritaniya sun ce gurfanar da wasu ‘yan kasar masu takardar ‘yan kasa biyu da ke aiki a cikin sojojin mamayar Isra’ila a gaban kuliya bisa zargin hannu a tafka laifukan yaki...

Firaministan Malaysia: Xi Jinping Babban Jagora Ne Mai Matukar Mayar Da Hankali Kan Abubuwan Dake Shafar Zaman Rayuwar Jama’a
Gabanin ziyarar aiki da shugaban kasar Sin Xi Jinping zai yi a Malaysia, firaministan kasar Datuk Seri Anwar Ibrahim, ya zanta da manema labarai na CMG a jiya Litinin, inda ya darajanta bunkasar huldar kasashen biyu. Anwar Ibrahim ya kuma bayyana matukar amincewa da tunanin Xi Jinping na ingiza al’adu da wayewar kan...
Wasu kafofin yada labarai a duniya na ganin cewa, idan gwamnatin Amurka ta ci gaba da saka shingayen haraji, to sauran kasashe za su maye gurbinta a bangaren samar da hidimomi. Abin da gwamnatin ta yi biris da shi yayin da take kididdigar harajin da za ta kakabawa sauran sassa, har yanzu wannan bangare na...
Babban daraktan hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya zai ziyarci Tehran a ranar Laraba mai zuwa. Ziyarar ta Grossi na zuwa ne gabanin sabuwar tattaunawar da za’ayi tsakanin Iran da Amurka a ranar Asabar mai zuwa kan batun shirin nukiliyar Iran na zaman lafiya. Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran mai kula da harkokin...
Wata ’yar kasar Jamus mai suna Alexandra Hildebrandt mai shekara 66 ta ja hankalin jama’a bayan ta haifi ɗanta na 10 ba tare da maganin haihuwa ba. Haihuwar ta faru ne a ranar 19 ga Maris a Asibitin Charité da ke Berlin da taimakon likita. Bello Turji ya kashe manoma 11 a Sakkwato ’Yan bindiga...

Kasashen Larabawa Na Yankin Tekun Farisa Sun Yi Fatan Al-Khairi Ga Iran Da Amurka A Tattaunawar Shirin Nukliyar Kasar
Babban sakataren kungiyar kasashen Larabawa na yankin tekun Farisa (PGCC) ya yi fatan alkhairi ga kasashen Iran da Amurka a tattaunawa ba kai tsaye ba a tsakaninsu dangane da shirin Nukliya ta kasar Iran na zaman lafiya wanda suka fara, a birnin Mascat na kasar Omman a ranar Asabar da ta gabata. Kamfanin dillancin labaran...
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Makiya suna cike da takaici da fushi kan ci gaban da Jamhuriyar Musulunci ta Iran take samu A yayin ganawarsa da manyan kwamandojin sojojin kasar Iran a yau Lahadi, Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya jaddada cewa; Ci gaban da Iran ta samu...
Gwamnatin Amurka ta sanar da cewa: Ba ta neman tada tashin hankali tsakaninta da Iran Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Amurka Samuel Werberg ya bayyana cewa: Kasarsa ba ta neman kara ruruta wutar rikici da Iran, yana mai jaddada cewa har yanzu kofar diflomasiyya a bude take, duk kuwa da kakkausar murya da Amurka ta yi...

Ukraine na Fuskantar Wata Barazana, Dangane Da Bukatar Amurka Na Kwace Iko Da Cibiyar Gas Na Rasha A cikin Kasar
Labaran da suke fitowa daga kasar Ukraine sun bayyana cewa, gwamnatin kasar tana son karban iko da bututun iskar gas na kasar Rasha wanda yake yammacin kasar da Turai, wanda kuma yake kai iskar gasa zuwa kasashen Turai. An gina bututun tun zamanin tarayyar Soviet kuma kasashen biyu suna samun kudade masu yawa daga wannan...
Kungiyar kare hakkin bil’adama ta kasa da kasa ” Amnesty International” ta bayyana cewa, rundunar kai daukin gaggawa ta “RSF” ta bautar da mata da kuma cin zarafinsu. Kungiyar ta yi tir da abinda rundunar ta “RSF” ta yi akan mata da su ka manyanta da kuma ‘yan mata a tsawon lokacin yakin na Sudan...
Kasashen duniya da kungiyoyin kasa da kasa na fatan nasara ga tattaunawar Iran da kuma Amurka. Kasar Iraki ta bayyana fatan tattaunawar za ta aifar da kwanciyar hankali a yankin Ministan harkokin wajen Iraki ya bayyana goyon bayansa ga tattaunawar tsakanin Iran da Amurka, yana mai bayyana fatan Bagadaza na ganin cewa hakan zai samar...
Isra’ila ta ce ta karbe iko da wata muhimmiyar hanya a zirin Gaza a wani mataki da ya yanke gaba daya yankin kudancin Rafah mai yawan jama’a daga sauran yankunan Falasdinawa da aka yiwa kawanya. A cikin wata sanarwa da Isra’ila ta fitar yau Asabar ta ce dakarunta sun yi wa Rafah kawanya gaba daya...
Shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da dokar albashi na naira 70,000 a ranar 29 ga watan Yuli na 2024, bayan shafe watanni ana muhawara da kungiyoyin kwadago. Sabon mafi karancin albashin na wata-wata ya karu da kaso 133 daga naira 30,000 zuwa naira 70,000, sakamakon matsin tattalin arziki da ake fama da shi a...
Wasu mahara sun harbe wasu mata biyu har lahira tare da banka musu wuta a gonakinsu da ke ƙauyen Okete a Ƙaramar Hukumar Dekina ta Jihar Kogi. Lamarin ya faru ne a lokacin da kowacce daga cikin matan biyu ke tsaka da kula gonarta. An ce maharan sun yi musu ruwan harsasai baya wata taƙaddama...
Sanata Oluremi Tinubu yt gana da sarakunan Taraba, ta kuma ba da gudummawar naira miliyan 50 don tallafa wa mata 1,000, da kayan aiki dubu 10,000 ga ma’aikatan lafiya Uwargidan shugaban Najeriya, Sanata Oluremi Bola Ahmed Tinubu, ta bukaci shugabannin gargajiya da su marawa shirin ta na sabon fata ta hanyar wayar da kan...
Kazalika, a wani binciken kwanan baya na gama gari kan yawan alummar kasar, ya gano cewa, kaso 53 na wasu matasan kasar, a kullum suna rungumar wannan dabi’ar. Sai dai, muna sane da cewa, wasu ‘yan Nijeriya, na kallon yin cacar tamkar wata aba ce, ta nishadi kawai, amma wasu bincike sun bayyana cewa, wani...
Sojojin kasa na kasashen Iran ta Armenia sun fara atisayen soje na hadin guiwa a tsakaninsu, don kyautata tsaro na kan iyakar kasashen biyu na kuma tsawon kwanaki biyu. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa dakarun kare juyin juya halin musulunci na kasar Iran ne suke jagorantar wannan atisayen. Da nufin...
Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo, ya jagoranci wata tawaga zuwa Jihar Edo domin binciko gaskiyar abin da ya faru game da kisan mafarauta ’yan asalin jihar a ƙauyen Uromi. Gwamna Abba Kabir Yusuf ne, ya umarci a kafa wannan tawaga, wacce ta ƙunshi manyan shugabanni irin su Sarkin Rano, Kwamishinonin ma’aikatu da...
Kasashen kungiyar Tarayyar Turai sun amince da cewa kungiyar za ta kaddamar da matakan yaki da harajin da shugaban Amurka Donald Trump ya dora mata. Kungiyar mai kasashe mambobi 27 tana fuskantar kashi 25% na harajin shigo da kayayyaki kan karafa, aluminium, da motoci, da kuma karin harajin kashi 20% akan kusan duk wasu kayayyaki...
Matatar Mai ta Ɗangote ta rage farashin litar man fetur zuwa Naira 865 ga dillalai masu saya daga wurinta. A safiyar Alhamis hukumomin Matatar Ɗangote suka sanar da dillalai dangane da ragin naira 15 daga tsohon farashin man na naira 880.