2025-11-21@05:59:47 GMT
إجمالي نتائج البحث: 2750
«da fara wasa»:
Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya umarci Ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Matawalle, da ya koma jihar Kebbi da aiki sakamakon sace ɗalibai ’yan mata 25 da wasu ’yan bindiga suka yi a jihar. Tinubu ya umurci Matawalle, wanda tsohon Gwamnan Jihar Zamfara ne, da ya zauna a Kebbi domin sa ido kan dukkan matakan tsaro da ake ɗauka domin kuɓutar da ɗaliban da aka sace. Babu wani addini da matsalar tsaron Nijeriya ta ƙyale — Fafaroma Za a aurar da marayu 200 a Zamfara ’Yan bindiga sun sace ɗalibai 25 a Makarantar Sakandiren Mata da ke garin Maga na Jihar Kebbi da misalin ƙarfe 4 na Asubahin ranar Litinin. A cewar mai magana da yawun fadar shugaban ƙasa, Bayo Onanuga wanda...
Hukumar Zakka ta Jihar Zamfara ta sanar da shirye-shiryen aurar da marayu 200 ’yan asalin jihar a wani yunƙuri na tallafa wa marasa galihu. Sakataren hukumar, Malam Habibu Balarabe ne ya bayyana hakan, inda ya ce an kammala dukkan shirye-shirye domin gudanar da bikin auren a ranar Litinin, 23 ga Nuwamba, 2025, a harabar hukumar da ke Gusau. Ya ce an gudanar da cikakken bincike da tantancewa kafin zaɓar waɗanda za su ci gajiyar shirin, domin tabbatar da cewa auren ya kai ga mutanen da suka fi buƙatar taimako na haƙiƙa. Sakataren ya ƙara da cewa, hukumar za ta ba wa amaren kayayyakin tallafi da kayan amfani na gida domin taimaka musu su fara sabuwar rayuwarsu cikin sauƙi da kwanciyar...
Shugaban jam’iyyar NNPP na Jihar Kano, Hashimu Sulaiman Dungurawa, ya ce jam’iyyar APC ba ta da ƙarfin da zai kai ta ga samun nasara a 2027, sai dai idan ta jingina da tasirin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso. Yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a sakatariyar NNPP ta jihar, Dungurawa ya ce APC a Kano har ma da matakin ƙasa “ta rasa shugabanci da tsari”, wanda hakan, a cewarsa, ya sa suke yawan neman kusanci da Kwankwaso. Muna roƙon Tinubu ya ƙawo ƙarshen taƙaddamar gwamnati da ASUU — Ɗalibai IAEA ta buƙaci Iran ta bayyana yawan makamashin nukiliyar da ta mallaka A cewarsa, “Wannan mutanen APC ba su da ƙarfi, kuma a halin yanzu sun shiga ruɗani. Sun san...
Mahukunta a Jahar Kwara sun sanar da rufe makarantu a garuruwan Ifelodun,Ekiti, Irepodun, Isis, da Oke Ero, saboda matsalolin tsaro da ake fuskanta Kwamishinan ilimi na Jahar ta Kwara Lawal Olohungabebe ne ya sanar da daukar wannan matakin saboda abinda ya kira bayar da kariya ga rayuwar daliban da suke fuskantar barazanar masu dauke da makamai da suke karakaina a yankin. Gwamnatin ta Kwara ta dauki wannan matakin ne bayan wani lokaci kadan daga kustawa cikin wata majama’a da masu dauke da makamai su ka yi a Eruku dake karamar hukumar Ekiti. Mazauna yankin dai sun fada cikin frigici da razana haka nan kanan hukumomin da suke makwabtaka. An bayar da umarnin a rufe makarantun kwana na Irepodun saboda rahotanni...
Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta sami jagoran haramtacciyar ƙungiyar neman kafa kasar Biyafara ta IPOB, Nnamdi Kanu, da laifukan ta’addanci da aka zarge shi da aikatawa. Da yake yanke hukunci a ranar Alhamis, Mai Shari’a James Omotosho, ya amince da batutuwa uku da aka gabatar a shari’ar, inda ya yanke hukunci a kan su daga bangaren masu gabatar da ƙara. Gwamnatin Kwara ta rufe makarantu a kananan hukumomi 4 saboda matsalar tsaro Wayar wutar lantarki ta kashe mutum 4 a wajen cashiya a Legas Alkalin ya ce barazanar tashin hankali da Kanu ya yi a cikin jawabansa ta haifar da tsoro da damuwa a zukatan jama’a a yankin Kudu maso Gabas. Justice Omotosho ya ƙara da cewa bisa...
Gwamnatin Jihar Kwara ta bayar da umarnin rufe makarantu a ƙananan hukumomin jihar guda huɗu na saboda ƙaruwar hare-hare a jihar cikin sa’o’i 48 da suka gabata. Aƙalla mutane uku sun mutu a garin Bokungi da ke Ƙaramar Hukumar Edu a ranar Laraba. Wayar wutar lantarki ta kashe mutum 4 a wajen cashiya a Legas Najeriya ta ɗora alhakin taɓarɓarewar harkokin tsaronta kan Amurka Lamarin ya faru kasa da sa’o’i 24 bayan mummunan harin da aka kai coci a Eruku, Ƙaramar Hukumar Ekiti ta jihar, inda aka kashe mutane biyu tare da yin garkuwa da mutum 30. Majiyoyin al’umma sun ce an fara yin garkuwa da mutane huɗu, ciki har da ɗan sa-kai, a cikin waɗannan hare-haren. Ɗaya daga cikin...
An sanar da dan wasan Paris St Germain, Achraf Hakimi a matsayin wanda ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa na Afirka na 2025, mai tsaron baya da ya lashe kyautar karon farko bayan shekara 52. Dan wasan tawagar Masar Mohamed Salah shi ne na biyu mai taka leda a Liverpool da kuma Victor Osimhen na Super Eagles mai wasa a Galatasaray a mataki na uku. Mai tsaron bayan Morocco ya karbi kyautar sakamakon nasarorin da ya samu a 2025 tare da Paris St Geramin ciki har da lashe Champions League da Ligue 1 da Coupe de France da kuma UEFA Super Cup. Shi ne na farko daga Morocco da ya karbi kyautar tun bayan Mustapha Hadji a 1998, kuma...
Wata Kotun Tarayya da ke Abuja, ta sanya ranar 15 ga watan Janairun 2026, don fara shari’ar shugabannin ƙungiyar ’yan ta’adda ta Ansaru; Mahmud Usman da Abubakar Abba. Ana zargin su da jagorantar ƙungiyar ta’addanci ta Ansaru, kuma Hukumar DSS ce ta kama su tare da gurfanar da su a kotu. Ribadu ya jagoranci tawaga zuwa Amurka don ƙaryata zargin yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi Hakimi ya lashe kyautar gwarzon ɗan ƙwallon Afirka na bana An tsara faea sauraren shari’ar a ranar Laraba, amma aka ɗage bayan lauyoyin waɗanda ake tuhuma sun nemi a ƙara musu lokaci. Lauyansu, B.I. Bakum, ya bayyana cewa har yanzu suna jiran takardun zargi da wajen DSS. Haka kuma, ya nemi a mayar da...
Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta yanke wa wani shugaban ISWAP Hussaini Ismaila, hukuncin ɗaurin shekaru 20 a gidan yari bayan samun sa da aikata laifukan ta’addanci. Alƙalin kotun, Mai Shari’a Emeka Nwite, ya yanke hukuncin ne bayan Ismaila, wanda ake kira Mai Tangaran, ya amsa tuhume-tuhume guda huɗu da Hukumar DSS ta gabatar a kansa. Gwamna Abba ya gabatar da N1.36trn a matsayin kasafin 2026 Tinubu ya fasa zuwa taron G20 saboda matsalar tsaro a Najeriya DSS ta ce Ismaila ne, ya jagoranci kai wasu hare-haren ta’addanci a Kano a shekarar 2012. Hare-haren sun haɗa da harin Hedikwatar ’Yan Sanda ta Bompai, Barikin ’Yan Sandan Mopol a titin Kabuga, ofishin ’yan sanda na Farm Centre, ofishin ’yan...
Kasar Saudiyya ta sanar cewa za ta kara hannun jarinta a Amurka zuwa dala tiriliyan daya, daga dala biliyan 600 da kasar ta zuba a baya. Yariman Saudiyyar ne Mohammed Ben Salman ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai tare da Shugaban Amurka Donald Trump a ziyarar da ya kai fadar gwamnatin Amurka, bayan ganawar sirri da suka yi. A baya ne Trump ya bukaci Saudiyya da ta kara hannun jarinta a Amurka, sannan ya bukaci yariman ya tabbatar, inda shi kuma ya amsa da cewa, “tabbas.” Shugaban na Amurka ya ce Saudiyya za ta zama “babbar kawar kawance wacce ba daga NATO ba,” Ya kuma sanar da karfafa hadin gwiwar soja zuwa wani matsayi mafi...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Batun kubutar da ɗalibai mata da masu garkuwa da mutane suka sace na makarantar GGCSS Maga dake karamar hukumar Danko Wasagu a jihar Kebbi na daya daga cikin abubuwan da alumma suka maida hankali a kai. Iyayen wadannan yara, da sauran masu ruwa da tsaki na ganin ya kamata a yi dukkan mai yiwuwa don ganin an ceto wadannan yara ba tare da sun samu rauni ba. NAJERIYA A YAU: Matsayar Doka Kan Taron Da Jam’iyyar PDP Ta Gudanar DAGA LARABA: Tasirin Da Tura Jami’an ‘Yan Sanda Kare Manyan Mutane Zai Haifar Ga Tsaron Al’umma Wannan shine batun da shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari a kai. Domin sauke...
Gwamnan Taraba, Agbu Kefas ya sanar da dakatar da sauya sheƙa daga jam’iyyarsa ta PDP zuwa APC a dalilin sace ɗalibai mata ’yan sakandire da aka yi a Jihar Kebbi. Gwamnan ya ce zai ci gaba da tattaunawa da kuma nazari kan lokacin da ya fi dacewa ya sauya sheƙar tare da magoya bayansa. Mutane 7 sun mutu a hatsarin mota a Jigawa Gwamnonin Arewa sun yi Allah-wadai da sace ɗalibai mata a Kebbi Aminiya ta ruwaito cewa, da sanyin safiyar Litinin, 17 ga watan Nuwambar 2025, mahara suka shiga a makarantar sakandare ta ’yan mata da ke garin Maga a Jihar Kebbi, inda bayanai ke nuni da cewa sun yi awon gaba da ɗalibai 25 tare da halaka mataimakin...
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barau FC ta doke Enugu Rangers da ci 2-0 a wasan mako na 13 na Firimiyar Najeriya da suka buga a filin wasa na Sani Abacha da ke Kofar Mata a Jihar Kano. Umar Bala Mohammed ne ya fara zura ƙwallo ta farko a minti na 25, kafin Joseph Kemin ya ƙara ta biyu a minti na 72 bayan dawowa daga hutun rabin lokaci. HOTUNA: Fada ya barke a Hedikwatar Jam’iyyar PDP ’Yan bindiga sun sako mutane 45 bayan sulhu a Katsina Wannan nasarar ce ta uku da Barau FC ta yi cikin wasanni 12 da ta buga a kakar bana, inda ta yi kunnen doki a wasanni huɗu, aka kuma doke ta a biyar. Yanzu...
Ministan harkokin wajen Najeriya ya ce kasar ta soma tattaunawa da Amurka, bayan barazanar da Shugaba Trump ya yi na kai wa Najeriya harin soji kan kisan kiristoci da ya ce ana yi a kasar. A wata hira da kamfanin dillancin labarai na AFP, yayi da Yusuf Maitama Tuggar ya ce abin da suke tattaunawa a kai shi ne yadda za su hada kai wajen magance matsalolin tsaro don amfanin duniya. A farkon watan Nuwamban nan Trump ya ce ya bai wa ma’aikatar tsaron Amurka umurnin ta soma tsara yadda za ta kai hari Najeriyar. Sai dai ministan ya ce ba ya tunanin Amurka za ta yi hakan, ” muna ci gaba da tattaunawa, kuma ana samun ci gaba a...
“Cikin hukuncin Allah, sojojin Daularmu sun kama ‘Kwamandan Runduna’… bayan ya gudu daga harin kwantan-ɓauna… Bayan mun yi masa tambayoyi, Mujahidai suka kashe shi.” An kuma wallafa wani hoto a kafafen sada zumunta da ya nuna Janar Uba a ɗaure. Har yanzu rundunar sojin Nijeriya ba ta fitar da wata sanarwa game da wannan lamari ba. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai ’Yansanda Sun Tura Tawaga Don Ceto Ɗaliban Da Aka Sace A Kebbi November 18, 2025 Manyan Labarai Bai Dace Adalci Ya Zama Na Sayarwa Ba – Tinubu Ga Alƙalai November 17, 2025 Manyan Labarai Kakakin Majalisar Taraba Da Ƴan Majalisa 15 Sun Fice Daga PDP Zuwa APC November 17, 2025
Masu gabatar da kara a kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa (ICC) a ranar Litinin din nan sun bukaci kotun da ta zartar da hukuncin daurin rai da rai kan Ali Muhammad Ali Abd-Al-Rahman, wanda aka fi sani da Ali Kushayb, kwamandan rundunar Rapid Support Forces (RSF), saboda rawar da ya taka a ta’asar da aka aikata a lokacin harin da aka kai a yankin Darfur na kasar Sudan. An samu Kushayb da laifuka 27 da suka hada da laifukan yaki da cin zarafin bil adama da suka hada da kisan kai, azabtarwa, fyade, da dai sauran manyan laifuka. Shari’ar dai ita ce shari’ar farko da aka shigar a gaban kotun ICC dangane da yakin Darfur. A farkon...
Gwamna Ahmed Idris na Jihar Kebbi ya ba da tabbacin cewa jami’an tsaro za su ƙwato ’yan matan da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a Kwalejin ’Yan Mata ta GGCSS Maga da ke Ƙaramar Hukumar Danko Wasu ta jihar cikin ƙoshin lafiya. Gwamnan ya bayar da tabbacin ne a yayin ganawarsa da iyayen ɗaliban kaɗan bayan harin ’yan bindigar a ranar Litinin. Aminiya ta ruwaito cewar da asubahin ranar ’yan bindiga suka kusta cikin harabar makarantar kwana ta ’yan mata ta GGCSS Maga, suka kwashe ɗalibai 25 daga ɗakin kwanansu zuwa cikin jeji. Maharan da suka riƙa harbi a iska kafin su shiga harabar makarantar sun bindige Matakin Shugaban Makarantar, Malam Hassan Yakubu Makuku, wanda ya yi ƙoƙarin...
Gwamnatin Sin Ba Ta Taba Bukatar Kamfanoni Su Tattara Ko Adana Bayanai Ba Bisa Ka’ida Ba Kuma Ba Za Ta Yi Hakan Ba
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Adadin Motocin Da Sin Ke Fitarwa Waje Ya Karu Da Kashi 15.7 Cikin Watanni 10 Na Farkon Bana November 17, 2025 Daga Birnin Sin An Bude Taron Tattaunawa Kan Wayewar Kai Tsakanin Sin Da Kasashen Larabawa Karo Na 11 A Beijing November 17, 2025 Daga Birnin Sin Firaministan Sin Ya Isa Rasha Domin Halartar Taron SCO November 17, 2025
Ƙungiyar kare haƙƙin bil’adama ta Amnesty International ta yi kakkausar suka kan sabon harin da ’yan bindiga suka kai makarantar sakandare ta ’yan mata da ke garin Maga a Jihar Kebbi, wanda ya kai ga sace ɗalibai mata sama da 25 tare da halaka mai gadi da mataimakin shugaban makarantar. A wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin, Amnesty ta bayyana lamarin a matsayin abin takaici da kuma nuna gazawar gwamnatin Shugaba Bola Tinubu wajen kare rayuka da dukiyoyin ’yan kasa ballantana kawo ƙarshen ta’addancin ’yan bindiga. CAF ta fitar da ’yan wasa uku da suka rage a takarar gwarzon Afirka na bana Gobara ta laƙume rayukan yara biyu ’yan gida ɗaya a Ribas Ƙungiyar ta ce bincikenta ya gano...
A Damaturu, farashin mudun shinkafa ya ragu daga N5,000 zuwa N2,500, yayin da wake, masara da gero suma suka sauka fiye da rabin tsohon farashinsu. Masana tattalin arziki sun ce yawaitar shigo da hatsi kamar shinkafa da alkama ya taimaka wajen rage tsadar abinci da ake fama da ita a watannin baya. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Hauhawar Farashin Kayayyaki A Nijeriya Ta Ragu Zuwa Kashi 16.065% November 17, 2025 Labarai ‘Yansanda Sun Tsaurara Tsaron Iyakokin Kano Bayan Hare-haren ‘Yan Bindiga November 17, 2025 Labarai Rashin Tsaro: Atiku Ya Yi Allah-wadai Da Harin Makarantar ‘Yan Mata Ta Kebbi November 17, 2025
Gobara ta laƙume rayukan wasu yara biyu ’yan gida ɗaya a unguwar Rumuola da ke ƙaramar hukumar Obio/Akpor a Jihar Ribas. Bayanai sun ce ibtila’in ya auku ne da misalin ƙarfe 10 na dare a ranar Lahadi, lokacin da gobarar ta tashi a ɗaya daga cikin wasu ɗakunan haya da mahaifiyar yaran ta kulle ’ya’yanta huɗu ta tafi sayen kayan girki. Mayaƙan ISWAP sun kashe kwamandan soji a Borno ’Yan sanda sun kama ƙunshi 66 na Tabar Wiwi a Gombe A cewar mazauna yankin, cikin yaran huɗun, biyun da suka riga suka kwanta barci sun ƙone su kurmus, yayin da sauran biyun da ke farke suka samu damar tserewa. Aminiya ta ruwaito cewa, mazauna yankin da sun ankara da gobarar...
An samu wannan raguwar ne sakamakon sauye-sauyen da aka samu a shekarar da muke ciki. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai ‘Yansanda Sun Tsaurara Tsaron Iyakokin Kano Bayan Hare-haren ‘Yan Bindiga November 17, 2025 Labarai Rashin Tsaro: Atiku Ya Yi Allah-wadai Da Harin Makarantar ‘Yan Mata Ta Kebbi November 17, 2025 Labarai MACBAN Ta Nemi Amurka Ta Cire Sunanta Daga Jerin Waɗanda Ta Ƙaƙabawa Takunkumi November 17, 2025
Rushewar ramukan hako ma’adinai ta kashe ma’aikata 32 a kudancin Jamhuriyar Demokradiyyar Congo Akalla ma’aikatan hakar ma’adinai 32 ne suka mutu a ranar Asabar sakamakon zaftarewar ƙasa a wani ma’adinan cobalt a kudancin Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo, yayin da ake ci gaba da neman waɗanda har yanzu ba a same su ba a yankin. Zaftarewar ƙasa ta faru ne a wurin Kalandu da ke cikin ma’adinan Mulundu kusa da Kolwezi, wani wuri da kamfanin Bajiklem ke gudanar da shi a hukumance. Ministan harkokin cikin gida na lardin, Rui Kawumba Mayondi, ya ce “masu hakar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba sun kai hari kan wurin duk da haramcin da aka sanya saboda ruwan sama mai ƙarfi da kuma haɗarin zaftarewar ƙasa,” ya...
Ya kuma yi Allah wadai da kisan wani jigo na Jam’iyyar APC, Umar Moriki, da kuma sace-sacen jama’a da aka yi a Karamar Hukumar Tsafe ta Jihar Zamfara, inda aka sace iyalai baki daya, ciki har da mata da yara. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai MACBAN Ta Nemi Amurka Ta Cire Sunanta Daga Jerin Waɗanda Ta Ƙaƙabawa Takunkumi November 17, 2025 Manyan Labarai Bai Dace Adalci Ya Zama Na Sayarwa Ba – Tinubu Ga Alƙalai November 17, 2025 Manyan Labarai Kakakin Majalisar Taraba Da Ƴan Majalisa 15 Sun Fice Daga PDP Zuwa APC November 17, 2025
Hukumar ƙididdiga ta Najeriya (NBS) ta ce hauhawar farashin kayyayaki a ƙasar ya ragu zuwa kashi 16.05 cikin 100 a watan Oktoban 2025. Cikin rahoton wata wata da hukumar ke fitarwa, ta ce hauhawar farashin ya ragu ne da kashi 1.97 idan aka kwatanta da kashi 18.02 da aka samu a watan Satumba. ’Yan Majalisar Dokokin Taraba 16 sun sauya sheka daga PDP zuwa APC An ɗaura auren Sanata Kawu Sumaila da wata jami’ar soji a Kano A watanin baya-bayan an riƙa samun raguwar hauhawar farashin kayyaki a ƙasar. Aminiya ta ruwaito cewa, tun dai daga watan Yunin bana, hauhawar farashin kayayyaki ke ci gaba da sauka a ƙasar har kawo yanzu. Ana iya tuna cewa, tun watanni kadan da...
Bonzena ya ƙara da cewa duk da cewa kafin yanzu APC ce ke da rashin rinjaye a majalisar, an ci gaba da aiki cikin zaman lafiya, amma yanzu yana farin cikin ganin cewa dukkan mambobin majalisar sun haɗe ƙarƙashin tsari daya da ya yi daidai da hangen shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Ƴan Bindiga Sun Sace Ɗalibai Ƴan Mata, Sun Kashe Mataimakin Shugaban Makaranta A Kebbi November 17, 2025 Manyan Labarai Mutane 42 Sun Mutu A Wani Hatsarin Tankar Dizal Da Motar Masu Umrah A Hanyar Makka November 17, 2025 Manyan Labarai Ba Mu Samu Labarin Kai Wa Laftanar Yerima Hari Ba – Ƴansanda November 17, 2025
Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Taraba, Rt Hon. Kizito Bonzena, tare da ’yan majalisar 15 sun sauya sheka daga jam’iyyarsu ta PDP zuwa APC. A saifyar Litinin ne Rt Hon. Kizito Bonzena ya gabatar da takardarsa ta ficewa daga PDP tare da sauran mambobin zuwa APC. Ya bayyana cewa da sauyin shekar tasu, yanzu APC ce ke da daukacin kujeru 24 da ke Majalisar Dokokin Jihar Taraba. Hakan na zuwa ne jim kadan bayan Gwamnan Jihar Taraba, Kefas ya sanar da shirinsa na komawa APC daga PDP. Masu ibadar Umarah 42 sun mutu a hatsarin mota a hanyar zuwa Makka ’Yan ta’adda sun sace dalibai 25 a dakunan kwanansu a Kebbi Sauran mambobin majalisar da suka sauya sheka sun hada da...
Wasu masu ibadar Umara 42 sun mutu bayan da motarsu ta yi taho-mu-gama da wata tankar mai a kusa da birnin Madina da ke kasar Saudiyya. Dukkan masu ibadar ’yan kasar Indiya ne, kuma hatsarin ya ritsa da su ne a kan hanyarsu ta zuwa Makka bayan kammala ziyara a birnin Madina. Ministan harkokin wajen Indiya Dakta S. Jaishankar ya bayyana cewa mutum daya daga cikin fasinjojin ya tsallake rijiya da baya a hatsarin da ya auku da tsakar daren Litinin. Hatsarin ya auku ne a bayan da motar safa mai daukar mutum 43 da masu ibadar suke ciki ta yi karo gaba-da-gaba da wata tankar mai. ’Yan ta’adda sun sace dalibai 25 a dakunan kwanansu a Kebbi NELFUND ya...
Asusun Lamunin Ilimi na Najeriya (NELFUND) ya bayyana cewa ya raba jimillar kuɗi Naira biliyan 116 domin tallafa wa dalibai a faɗin ƙasar nan wajen biyan kuɗin makaranta da kuma kula da rayuwarsu ta yau da kullum. Shugaban NELFUND, Akintunde Sawyerr ya bayyana a Abuja cewa, daga cikin kuɗin, an tura Naira biliyan 65 aka tura kai tsaye zuwa makarantu 239 na tarayya — jami’o’i, kwalejojin fasaha da kwalejojin ilimi — domin biyan kuɗin makarantar ɗaliban da aka amince da buƙatar lamuninsu. Sauran Naira biliyan 51 kuma an tura ne kai tsaye ga ɗaliban a matsayin tallafin kula da rayuwa na wata-wata. Ya ce: “Mun raba Naira biliyan 65 ga makarantu da kuma Naira biliyan 51 ga ɗaliban domin tallafin...
Rundunar Ƴansandan birnin tarayya ta bayyana cewa babu wani rahoto ko bayanin da ta samu game da yunkurin kashe laftanar Ahmed Yerima, jami’in Sojin ruwa da ya yi taƙaddama da Ministan Abuja, Nyesom Wike, kan wani fili da ake jayayya kansa a Abuja kwanakin baya. Jami’ar hulɗa da jama’a ta rundunar, SP Josephine Adeh, ta fitar da sanarwar ne a ranar Litinin tana mai ƙaryata labarin da ya yaɗu a kafafen sada zumunta. Adeh ta ce babu wani lamari da ya faru ko aka rubuta a koda ɗaya daga cikin wata ƙaramar hukumar da ke cikin birnin, don haka ta buƙaci jama’a da su yi watsi da labarin saboda ba shi da tushe. Ta ƙara da cewa irin waɗannan labaran...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Laftanal Yarima Ya Tsallake Rijiya Da Baya A Abuja November 16, 2025 Manyan Labarai Falana Ya Shawarci Waɗanda Suka Biya Kuɗin Fansa Su Kai Gwamnati Kotu Don Ta Biya Su November 16, 2025 Manyan Labarai Ƴan Bindiga Sun Sace Mutane 14 A Wani Sabon Hari A Zamfara November 16, 2025
Gwamnan Jihar Taraba, Agbu Kefas, ya ce zai fice daga jam’iyyar PDP tare da sauya sheƙa zuwa APC a hukumance a ranar Laraba, 19 ga watan Nuwamba. Ya bayyana haka ne yayin da yake duba aikin gyaran Filin Wasanni na Jolly Nyame da ke Jalingo a ƙarshen mako. Ba da yawuna PDP ta kori Wike ba — Muftwang Tsohon Minista Kabiru Turaki ya zama sabon shugaban PDP na ƙasa Yayin da yake magana da ’yan jarida, Gwamna Kefas, ya ce ya yanke shawarar ficewa daga PDP ne saboda nemo hanyar da zai amfanar da al’ummar Taraba. Ya ce: “Zan sauya sheƙa a hukumance daga PDP zuwa APC a ranar 19 ga watan Nuwamba. Wannan sauyi zai amfanar da al’ummar Taraba.”...
“A shekaru goma da suka gabata, ayyukan ta`addanci da tashe-tashen hankula daga masu tsattsauran ra`ayi ya haifar da mummunan koma bayan tattalin arziki da na zamantakewar alummomin dake shiyyar, halin da daliban irin wadannan makarantu suke ciki yana bukatar kulawar gaggawa daga kungiyar ta ECOWAS, abin takaici irin wadannan makarantun allo suna daukar dalibai masu yawan gaske kuma akasari kananan yara daga shiyyar, to amma kuma ba a bai wa makarantun da daliban kulawar da ta kamata, wannan ta sanya kungiyoyin `yan ta`adda ke samun kofar kusantar su domin kwadaita musu shiga cikin kungiyoyin.” ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai APOSUN Ta Jaddada Aniyarta Na Daƙile Hada-hadar Haramtattun Kuɗaɗe November 16, 2025 Labarai NNPP Tana Da Ƙwarin Gwiwar Riƙe Kano...
Ya ci gaba da cewa, “an kama masu laifuka da dama ta hanyar bayanai da muke bai wa jami’an tsaro wanda hakan ya taimaka sosai wajen magance aikata laifuka a POS”, domin a cewarsa “sun sanya tsauraran matakai yadda ko da an tura kudi kafin a zo karɓa mambobinmu suna ganewa idan an tura kudin ta hanyar da ya dace, idan ba su gamsu ba sai a sanar da jami’an tsaro a zo a kama mutum, an kama wasu a Abuja, an kama wasu a Maiduguri da wasu sassa na kasar nan”. Ya bayyana kungiyar a matsayin mai farin jini, inda ya ce dukkan jami’an Nijeriya sun santa kuma sun yi marhaban da ita ta hanyar kai musu ziyara...
Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri na Jihar Adamawa, ya yi watsi da hukuncin da Jam’iyyar PDP ta yanke na korar Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, daga jam’iyyar. Aminiya ta ruwaito yadda PDP ta kori Wike, Sanata Samuel Anyanwu da tsohon Gwamnan Ekiti, Ayodele Fayose, a yayin babban taron PDP da aka gudanar a Ibadan, Jihar Oyo. Cif Olabode George ne, ya gabatar da ƙudirin korarsu, kuma Shugaban PDP na Jihar Bauchi, Samaila Burga, ya mara masa baya. Sai dai bayan sanarwar, Gwamna Fintiri ya fitar da wata sanarwa, wadda ya nesanta kansa daga matakin da jam’iyyar ta ɗauka. Ya ce ba ya goyon bayan korar da aka yi wa Wike, domin hakan zai ƙara haifar da rikici a cikin jam’iyyar....
Sarki Sanusi II, ya yaba da ci gaban da jami’ar ke samu tare da farin ciki kan yawan mata da suka kammala karatu, yana fatan hakan zai ƙara yawan rawar da mata ke takawa a mulki da sauran ɓangarorin rayuwa. Tun da farko, Shugaban Jami’ar, Farfesa Ajith Kumar, ya bayyana cewa cikin ɗalibai 180 da suka kammala karatun 24 sun samu sakamako daraja ta ɗaya (First Class), tare da bayyana cewa wannan bikin yaye ɗaliban shi ne karo na farko da jami’ar ta raba digiri na biyu tun bayan amincewar Hukumar Kula da Jami’o’i ta Ƙasa (NUC), da ta samu. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai NAF Ta Ragargaza Mafakar Ƴan Ta’adda A Zamfara, Ta Halaka Da Dama November 15,...
Wasu mahara sun yi wa wasu matan aure biyu kisan gilla a gidan mijinsu da keunguwar Tudun Yola a Ƙaramar Hukumar Gwale ta Jihar Kano. Aminiya ta samu rahoton cewa maharan banka wa gidan wuta bayan da suka soka wa ɗaya daga cikin matan wuka har lahira, ɗayar kuma an tsinci gawarsa a cikin banɗaki. Matan da aka yi wa wannan kisan gilla — Hauwa’u Yakubu da Zahra’u Aliyu — mata ne ga wani mai suna Alhaji Ashirin Shu’aibu Usaini. Al’unnar unguwar Tudun Yola sun shiga tashin hankali da wannanan ɗanyen aiki. HOTUNA: Yadda Babban Taronjam’iyyar PDP ke gudana Mayaƙan ISWAP sun sace Janar sun kashe sojoji a Borno Ɗan mai gidan, Anas Shu’aibu, ya yi zargin ana yi wa...
Haka zalika, a 2025, an samu kararraki 28 na ‘yan Nijeriya da suka kashe kansu. Shari’ar ta shafi mutane daga kowane jinsi da kuma masu matsayi daban-daban, ciki har da dalibai da kuma ‘yan kasuwa. Da yake zantawa wani dan jarida, masanin ilimin halayyar Dan’adam, kuma kwararre a kan lafiyar kwakwalwa, Dakta Shuab Waidi ya ce; batun kisan kai a halin yanzu, na bukatar da kulawar gaggawa ga mahukuntan kasa. Ya ce, “Kididdigar na nuna cewa, a kowane minti 33; ana asarar rai a Nijeriya sakamakon kashe kai, don haka, akwai bukatar cikin gaggawa a bude tattaunawa game da kashe kai ta hanyar gwajin lafiyar kwakwalwa. “Cutar tabin hankali, wani bangare ne na kisan kai da kai, amma kashe kai...
Rasha Tace Bata Da Shirin Kai wa Kungiyar Nato Hari Amma Za ta Mayar Da Martani Kan Duk Wata Barazana
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Rasha mariya zakhrova ta bayyana cewa Mosko ba ta da wani shirin na kai hari kan wata mamba a kungiyar tsaro ta Nato amma ta shirya mayar da martani kan duk wanda ya kai mata hari daga mambobin kungiyar. Da take taron manenma labarai mariya ta zayyana cewa tana kara maimaitawa babu wani shiri na kai hari kan wata kasa dake mamba a kungiyar tsaro ta nato , sai dai kasar rasha ta riga ta dauki mataken da suka dace na ganin ta samar da tsaronta, adaidai lokacin da abokan hamayya suke gina sansanin soja kusa da iyakar kasarta A cewa Jami’in diplomasiya, bayanan da wasu jami’an kungiyar tsaro ta nato suka fitar bangare ne...
Fashi Da Makami: An Yanke Wa ’Yan Nijeriya Hudu Mazauna Birtaniya Hukuncin Daurin Shekara 55 A Gidan Yari
Ta ce, “Kungiyar ta fi kai hare-hare a shagunan EE, inda suke amfani da barazana da tashin hankali wajen tilasta ma’aikata su bude dakunan ajiya na sirri kafin su gudu da wayoyi masu tsada da sauran na’urori.” A jimlace, sun sace kayayyaki da darajarsu ta kai fam miliyan £240,000. Jami’an tsaro sun gano masu laifin ta hanyar shaidar DNA, da kuma bayanan kira da rikodin motocin da suka yi amfani da su. An ce sun ci gaba da bibiyar kungiyar yayin da take shirin sake kai wani hari, inda a ranar 19 ga Nuwamba, 2024, jami’ai suka yi musu kwanton bauna suka kama mutane hudu daga cikinsu a lokacin da suke kokarin yin fashi a wani shagon EE da ke...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Da ɗumi-ɗuminsa Tsohon Gwamnan Anambra, Willie Obiano, Ya Rasu Yana Da Shekaru 70 November 14, 2025 Manyan Labarai Musulmin da Aka Kashe A Zamfara, Katsina Da Sokoto Sun Ninka Na Kiristoci A Tsakiyar Najeriya: MACBAN November 14, 2025 Manyan Labarai Kotu Ta Yanke Wa Mutum 4 Hukuncin Kisa Kan Kashe Wani Makanike A Kano November 14, 2025
A nasa jawabin, Kwamishinan PPMF, Prince Aliyu Abdulrazaq, ya shawarci kwamitin da su gudanar da aikinsu da amana, gaskiya, da ƙwarewa, yana mai cewa dole ne amincewar da Hukumar ta yi musu ta bayyana a sakamakon aikinsu. Da yake magana a madadin kwamitin, Jagoran Kwamitin, Dr. Haruna Danbaba, ya tabbatar wa Hukumar cewa za su bi dukkann ka’idojin da Ƙasar Saudiyya ta shimfiɗa, tare da tabbatar da cewa ba’a samu jinkirin wajen gudanar da aikin kwamitin ba. Ƙaddamar da kwamitin na daga cikin manyan matakai na farkon shirin NAHCON domin Hajjin 2026, kuma ana sa ran fara aiwatar da muhimman ayyuka nan take. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Kotu Da Ɗansanda NSCDC Ta Cafke Mutum Biyu Bisa Zargin Satar NAPEP Da...
Da misalin karfe 9:00 na safiyar yau Juma’a ne farkon matsakaicin jirgin ruwan yaki dankon jirage masu saukar ungulu na yaki samfurin 076 na kasar Sin, wato jirgin ruwa na Sichuan, ya tashi daga tashar jirgin ruwa ta kamfanin kera jiragen ruwa na Hudong-Zhonghua a Shanghai, zuwa wani yankin teku don gudanar da gwajin sufuri a karon farko. Gwajin sufurin a kan teku, zai mayar da hankali ne kan tabbatar da ingancin tsarin motsi, da sarrafa wutar lantarkin jirgin ruwan na Sichuan. An bayyana cewa, tun lokacin da aka sanya jirgin cikin ruwa a watan Disamban shekarar 2024, an ci gaba da ginin jirgin ruwan na Sichuan bisa tsari, an kuma kammala gwajin tsayawa, da kuma daidaita kayan aiki, wanda...
Babban Taron Kawancen Sin Da Afirka Ya Nuna Hadin Gwiwa Kan Gudanar Da Tsarin Shugabancin Duniya Na Bai-Daya
Babban taron dandalin kafafen yada labarai na kasashe masu tasowa da kwararru na kawancen Sin da Afirka da aka bude a jiya Alhamis a birnin Johannesburg da ke kasar Afirka ta Kudu, zai lalubo hanyoyin karfafa hadin gwiwa, da fadada yin magana da murya daya a tsakanin kasashe masu tasowa da kuma habaka gudanar da tsarin shugabancin duniya na bai-daya. Wanda kamfanin dillancin labarai na Xinhua, da Tarayyar Afirka (AU) da kamfanin Independent Media na kasar Afirka ta Kudu da sauran abokan hulda suka shirya, taron na kwanaki biyu ya samu halartar wakilai sama da 200 daga kafofin watsa labarai fiye da 160, da kungiyoyin kwararru, da hukumomin gwamnati da sauran cibiyoyi daga kasar Sin da kasashen Afirka 41, da...
An sanya ranar 25 ga watan Nuwamba a matsayin ranar da za a fara shari’arsa kan zargin karkatar da biliyoyin kuɗi da EFCC ta gabatar. Obiano ya yi gwamna a Jihar Anambra daga 2014 zuwa 2022. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Musulmin da Aka Kashe A Zamfara, Katsina Da Sokoto Sun Ninka Na Kiristoci A Tsakiyar Najeriya: MACBAN November 14, 2025 Manyan Labarai Kotu Ta Yanke Wa Mutum 4 Hukuncin Kisa Kan Kashe Wani Makanike A Kano November 14, 2025 Manyan Labarai Bayan Barazanar Amurka: Sultan Ya Nemi Hadin Kan ‘Yan Nijeriya Wajen Yaki Da Ta’addanci November 14, 2025
El-Rufa’i ya kara da cewa mutane amintattu za a ba su mukamai idan ADC ta samu nasarar kwace mulki a hannun APC a 2027, yana mai cewa cewa kashi 40 cikin dari na mukamai za su je ga matasa. Ya yi kira ga magoya bayansa da su kiyaye masu yaudara da ke kokarin raba kan jam’iyyar, yana cewa, “APC ba za ta bar ku ku tafi cikin sauki ba, ku yi hankali.” Haka kuma, ADC ta gudanar da taron masu ruwa da tsaki a Jihar Zamfara, wanda mataimakin sakataren gudanarwa na kasa na jam’iyya ya shirya, don karfafa hadin kai tsakanin ‘yan jam’iyya da kuma karfafa musu gwiwar yin rajista da samun katin zabe. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Tambarin Dimokuradiyya Rikicin...
Kasar Sin ta kara azamar kirkiro da fasahar sadarwa mai karfin 6G a cikin ’yan shekarun nan, inda ta samu ci gaba a bangaren binciken fasalin tsarin fasahar ta 6G da kuma zayyanar hanyar sadarwarta, kamar yadda ma’aikatar masana’antu da fasahar sadarwa ta zamani ta kasar ta bayyana a jiya Alhamis. A yayin gudanar da taron bunkasa fasahar 6G na shekarar 2025, mataimakin ministan masana’antu da fasahar sadarwa ta zamani na kasar Sin Zhang Yunming ya bayyana cewa, yanzu haka kasar tana da muhimman fasahohi na kirkiro da fasahar sadarwar 6G sama da 300. Zhang ya kara da cewa, kasar ta hada kan kamfanoni sama da 100 na cikin gida da na waje a fannin tsarin masana’antu, kuma ta gayyaci...
Haka zalika, ya kafa hujjojinsa a kan “Rashin biyan ‘yan fansho a kan lokaci”, “Jigata’Yan-fansho Da Sunan Tantancewa”, “Jefa Razani A Zukatan Maikata”, da ”Salwantar Da Kudaden ‘Yan-fanshon”. Wadannan bayanai na Anwar, sun tabbatar da ko dai bai san abin da ya faru a Hukumar Fansho a lokutan da Kwankwaso ya yi Gwamnan Kano ba, ko kuma shi dan kanzagin wani dan siyasa ne da yake so ya kambama, duk da tauraruwarsa ta disashe. Duk wanda ya san yadda mulkin Kwankwaso ya inganta rayuwar ‘yan fansho a Jihar Kano, ya san cewa; duk abubuwan da Anwar ya fada ba gaskiya ba ne. A tarihin biyan fansho da garatuti a Jihar Kano, babu lokacin da ‘yan fansho suka ji dadi; irin...
A cewarsa, damar kauwancin da ake samu daga fannin an same ta ne, saboda yadda Matatar ta Dangote, ke sarrafa danyen Mai wanda kuma ‘ya’yan kungiyar, ke son ganin sun amafana da hakan daga Matatar ta Dangote. Madugu ya ci gaba da cewa, wasu daga cikin bangarorin da kungiyar za ta amfana daga Matatar ya ce, sun hada da, Man da ake sarrafawa daga danye Mai, Man Dizil, Kalanzir, Man Jirgin Sama da kuma Iskar Gas, samfarin LPG. Sauran ya ce, sun ne, sanadaran naphtha, bitumen, ethylene, propylene da sauransu. Kazalika, ya kuma jinjinawa Shugaban rukunin Matatar Man ta Dangote, Aliko Dangote, bisa namijin kokarin da ya yi, na kafa Matatar Man a kasar nan. Tawagar ta kungiyar MAN, ta...
Kwamatin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya tsawaita da shekara guda wa’adin aikin tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya. Duk da shakkun da Amurka ta yi, Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, ya tsawaita wa’adin aikin tawagar ta MINUSCA, a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya har zuwa ranar 15 ga Nuwamba, 2026. Duk da haka, Majalisar ta nuna yiwuwar rage wa’adin saboda shiryen shiryen zaben da ake yi a shekarar 2026. An amince da kudurin da kuri’u 14 sai kuma kin amincewa daga Amurka. An samar da tawagar ta MINUSCA a watan Afrilun 2014 don kokarin kawo karshen yakin basasar da ya biyo bayan juyin mulkin da aka yi a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya kan...
Kasashen Iran da Turkiyye sun jaddada mahimmancin karfafa zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin. Wannan bayyanin ya fito ne bayan tattaunawar wayar tarho data wakana tsakanin ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi, da takwaransu na Turkiyye Hakan Fidan, game da dangantakar dake a tsakanin kasashen biyu da kuma halin da ake ciki a yankin da ma duniya. A yayin tattaunawar ta wayar tarho, Ministocin Harkokin Wajen Iran da Turkiyya sun yi nazari kan dangantakar kasashen biyu kuma sun jaddada muhimmancin karfafawa da bunkasa dangantaka a dukkan fannoni masu amfani. Yayin da yake yaba wa kokarin rage tashin hankali tsakanin Pakistan da Afghanistan, Ministan Harkokin Wajen Iran ya jaddada muhimmancin karfafa shawarwari don kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a...
Haka zalika, ya buga misali da Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kebbi, da aka yi garkuwa da shi, kuma aka biya wadanda suka sace shi miliyoyin kudade kafin a sako shi, wanda ya bayyana hakan a matsayin babban abin takaici. Dangane da batun Shugaban Amurka Donald Trump, Sultan Sa’ad ya bukaci Nijeriya da kada ta bari wasu kasashe su raba kawunansu, ya kuma bayar da tabbacin cewa; duk da kalubalen da ake fuskanta, Nijeriya za ta ci gaba da kasancewa mai girma da kuma ci gaba da samun hadin kai. Har ila yau, Tsohon Babban Hafsan Sojin Kasa, Abubakar Danbazau, a jawabinsa ya bayar da shawarar cewa; dole ne a magance matsalar rashin tsaro, matsalolin fatara, sauyin yanayi, rashin aikin...
Majalisar Wakilai ta umarci Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya da Hukumar Shirya Jarabawar Afrika ta Yamma (WAEC) da su dakatar da shirin fara amfani da tsarin jarabawa ta kwamfuta a jarabawar kammala sakandare ta shekarar 2026. Umarnin ya biyo bayan amincewa da wani kudiri na gaggawa da Kelechi Wogu ya gabatar a zaman majalisar na ranar Alhamis. Yahudawa sun banka wa masallaci wuta a Yammacin Kogin Jodan HOTUNA: NDLEA ta ƙone tan dubu 52 na miyagun ƙwayoyi a Zariya Kudirin na Wogu mai taken: “Bukatar Daukar Mataki Don Kaucewa Yawan Faduwa a Jarabawar Kwamfuta da WAEC ke Shirin Gudanarwa a 2026,” ya yi gargadin cewa gaggauta amfani da tsarin na iya haifar da yawan faduwa da kuma jefa dalibai cikin damuwa....
NDLEA ta bayyana cewa za ta ci gaba da jajircewa wajen yaƙar wannan matsala, tare da wayar da kan jama’a da kula da masu fama da shan ƙwayoyi, domin kare tsaron rayuka da zaman lafiya a ƙasar nan. Daga cikin waɗanda suka halarci taron akwai wakilin shugaban NDLEA, Birgediya Janar Muhammadu Buba Marwa (mai ritaya), wato Kwamanda Muhammadu Tukur; wakilin Gwamnan Jihar Kaduna, da wakilin Mai Martaba Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli, wato Alhaji Umar Muhammad Fagacin Zazzau. Haka kuma, Kwamandan NDLEA na Jihar Kaduna da wakilai daga ‘yansanda, sojoji, DSS, da sauran hukumomin tsaro sun halarta. Masu jawabi a wajen taron sun nuna farin ciki da wannan nasara, tare da yabawa jami’an tsaro, alƙalai, da jama’ar gari bisa...
Rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna ta cafke wasu mutum uku da ake zargi da safarar bilAdama wadanda aka ceto yara 17 daga hannunsu a garin Zariya. Wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na rundunar, DSP Mansir Hassan, ya fitar, ta bayyana cewa yaran da aka ceto ana zargin an shirya safarar su ne zuwa Abuja da wasu sassan ƙasar da ma ƙetare. An dakatar da Hakimi da Dagaci kan rikicin manoma da makiyaya a Gombe Atiku ya karyata ba sojan da ya yi takaddama da Wike kyautar motar SUV Sanarwar ta bayyana cewa “an tari hanzarin ababen zargin ne da misalin ƙarfe huɗu na yammacin ranar 12 ga watan Nuwamba. “A wannan lokaci ne jami’an sashen Ɗan Magaji da...
Cibiyar Masu Binciken Adadi ta Nijeriya (NIQS) ta yi kira ga gwamnatin tarayya da Majalisar Dokoki ta Kasa da su samar da mafita wajen kayyade kudin hayar gidaje, musamman a manyan birane, kamar Abuja. Shugaban Cibiyar, QS Kene Nzekwe ne ya yi kiran a ranar Laraba a Abuja a wani taron manema labarai don tunawa da taron NIQS karo na 31 da kuma babban taron cibiyar na kasa. Sau Ɗaya Na Taɓa Da-nasanin Fitowa A Cikin Fim – Tanimu Akawu Babu Wani Abu Kuskure Ga Sojan Da Ya Yi Sa-in-sa Da Ministan FCT – Matawalle Nzekwe, wanda ya bayyana cewa, Cibiyarsa tana bai wa gwamnati shawarwari amma ya nanata cewa, alhakin gwamnati ne ta ɗauki mataki da kuma daidaita kuɗin...
Dalilai 5 Da Suka Jefa Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa Ta Kano Pillars Cikin Matsaloli A Kakar Wasa Ta 2024/25
1. Matsalar Mai Zura Ƙwallo Ɗaya daga cikin manyan matsala ga magoya baya da masu nazari a wannan kakar shi ne rashin ɗaukar gogaggun ‘yan wasa, musamman a sashin kai mai zura kwallo. Rashin samun mai cin kwallaye wanda za a dogaro da shi ya bar Pillars ba su da ƙarfin kai hari mai hatsari a gaba. Ko da yake ƙungiyar sau da yawa tana saumn rinjayan samun kwallo da kirkirar damar kai hari, amma kash suna gaza amfani da waɗannan damarmaki zuwa nasara. Wanda hakan yake nuna rashin ‘yan wasa masu ƙwarewa da zasu ci kwallon, wanda ya sa ake dogaro da wanda suka kwana biyu kamar Rabiu Ali, yana iya kokarinsa amma ba aikinsa ba ne kuma tsufa...
Gwamnatin Tarayya ta dakatar da aiwatar da harajin shigo da man fetur da dizal na kashi 15, wanda a baya aka amince da shi domin daidaita farashin shigo da kayayyaki da yanayin kasuwa. Hukumar Kula da Harkokin Man Fetur (NMDPRA) ce, ta sanar da hakan a wata sanarwa da Daraktan Sashen Hulɗa da Jama’a, George Ene-Ita, ya sanya wa hannu. Yadda na yi asarar N120m a gobarar Singa — Ɗan Kasuwar Kano MURIC ta buƙaci Tinubu ya sauke Amupitan daga shugabancin INEC Harajin ya janyo cece-kuce, inda wasu ke ganin zai kare matatun gida, yayin da wasu ke cewa hakan zai ƙara tsadar kayayyaki sannan ya tsauwala wa talakawa. “Hukumar na shawartar ’yan kasuwa da su guji ɓoyewa ko sayar...
Gwamnatin Jihar Kwara ta jaddada kudirinta na ba da ingantaccen kulawa da kuma ƙarfafa matakan rigakafi ga waɗanda suka tsira daga cin zarafin jima’i da na jinsi (SGBV) a fadin jihar. Kwamishiniyar Harkokin Mata, Hajiya Opeyemi Afolashade, ce ta bayyana haka yayin ziyarar sa ido da tantance ayyuka a Cibiyoyin Tallafawa Wadanda Aka Yi wa Cin Zarafi (SARCs) da ke Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jihar Kwara (KWASU) a Ilorin da kuma Asibitin Kwarari ta Sobi da ke Alagbado. Kwamishiniyar ta bayyana cewa cibiyar an kafa ne tare da hadin gwiwar ofishin Uwargidar Gwamna, domin jinya kyauta da kuma kwantar da hankali, da tallafi ga wadanda suka tsira daga cin zarafi a jihar. Afolashade ta ƙara da cewa bincike da tantancewar...
A ci gaba da aikace-aikacen yaki da ta’addanci da laifuffuka a fadin Jihar Taraba karkashin Operation Lafiya Nakowa, sojojin Runduna ta 6 ta Sojan Nijeriya / Sashen 3 na Operation Whirl Stroke (OPWS) sun samu nasarar kama wani wanda ake zargin dillalin makamai, tare da kwato makamai da harsasai daga hannunsa. Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Lieutenant Muhammad, Mai Rikon Mukamin Daraktan Hulda da Jama’a na Rundunar 6, ya sanya wa hannu. A cewar sanarwar, bisa sahihan bayanan leƙen asiri da aka samu, a ranar 12 ga Nuwamba, 2025, sojojin suka kai samame a kauyen Shagada, karkashin gundumar Namnai a Karamar Hukumar Gassol, Jihar Taraba. Samamen ya haifar da kama wani mutum mai suna Abdulmudallabi Audu, mai...
LEADERSHIP ta ruwaito cewa, ministan FCT ya je filin mai lamba 1946 a ranar Litinin inda ya zargi sojoji da hana jami’ai daga Ma’aikatar Kula da Ci Gaban FCT aiwatar da umarnin dakatar da aiki a filin. Ana zargin cewa, filin yana da alaka da tsohon Babban Hafsan Sojojin Ruwa, Vice Admiral Awwal Zubairu Gambo (mai ritaya). Don haka, sojojin da ke wurin suka hana ministan shiga wurin, wanda hakan ne ya haifar da saɓanin. Daga baya, Wike ya yi ikirarin cewa, masu ginin ba su da takardu masu inganci ko izinin doka don gina wurin. Da yake mayar da martani ga lamarin, Matawalle ya ce, ya kamata a magance lamarin ta hanyoyin da suka dace maimakon ta...
Majalisar Tarayya Za Ta Binciki Masaƙa Ta Kaduna Da Sauran Gine-ginen Gwamnati 11,000 Da Aka Yi Watsi Da Su
Ya yi nuni da rahoton 2021 da Cibiyar Binciken kasa ta Nijeriya ta fitar, wanda ya gano kimanin filaye da gine-ginen gwamnatin tarayya 11,866 da aka yi watsi da su a duk faɗin ƙasar. Daga cikin manyan kadarorin da ɗan majalisar ya lissafa akwai Cibiyar Sakatariyar Tarayya da ke Ikoyi, Legas; Ginin Otal na Ƙasa da Ƙasa na Nijeriya, Suleja, Jihar Neja; Millennium Tower, Abuja; Ginin Hukumar Haraji ta Tarayya a Jihar Abia; Hedikwatar Dakin karatu na Ƙasa, Abuja; Kamfanin Masana’antar buga Labarai na Nijeriya, Kaduna; Ginin Masaƙa ta Kaduna; da Kamfanin Narka Alluminium na Nijeriya, Jihar Delta. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Lambar Yabo Da LEADERSHIP Ta Ba Mu, Ta Ƙara Zaburar Da Mu – Gwamna Sule...
A yammacin jiya ne hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar Iraki ta sanar da sakamakon farko na zaben ‘yan majalisar dokokin kasar na shekarar 2025, tare da tabbatar da cewa an gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali da inganci ta hanyar amfani da na’urorin lantarki. A taronta na manema labarai, Hukumar ta bayyana cewa yawan masu kada kuri’a ya kai kashi 56.11% bayan samun sakamako daga kashi 99.98% na rumfunan zabe. Wannan sanarwar ta zo ne sa’o’i 24 bayan kammala babban zaben da aka gudanar a wannan Talata, da kuma zabe na musamman da aka gudanar a ranar Lahadin da ta gabata, domin zaben ‘yan majalisar dokokin Iraki na shekara ta 2025. Jimillar masu kada kuri’a sun kai 20,063,773,...
Gwamnan Sule ya ce irin wannan jaridar da ke kan gaba ta zaɓo shi a matsayin gwarzon gwamna, abun farin ciki ne sannan ya yaba wa kamfanin bisa tabbatar da sahihancin labarai da daidaitasu wanda hakan yasa ta bambanta ta da takwarorinta. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Kashi 74% Na Marasa Lafiya Sun Gamsu Da Ayyukan Kiwon Lafiya Na Nijeriya — Minista November 12, 2025 Manyan Labarai An Kama Direban Gwamnati Da Hannu A Satar Motar Ofishin Mataimakin Gwamnan Kano November 12, 2025 Manyan Labarai Za Mu Kare Sojojin Da Ke Bakin Aiki — Ministan Tsaro November 12, 2025
Sauran sun haɗa da: Hon. Ibrahim Adamu Sarki a jam’iyyar PDP daga shiyya ta biyu sai , Nazifi Jibrin Muhammad na jam’iyyar PDP daga shiyya ta biyu da Haruna Dogo Mabo na.jamiyya NNPP daga shiyya biyu sai Honorable Isah Dan Maryam na PRP daga shiyya ta biyu da , Honarabul Isaac Auta Zankai na jam’iyyar SDP da Wilson Iliya Yange na jam’iyyar PDP, da Honarabul Simon Na Allah na jam’iyyar LP, sai Ibrahim Musa na jam’iyyar ADC daga shiyya ta biyu shi ne Sakataren kwamitin. Da yake jawabi bayan kaddamar da kwamitin, Shugaban jam’iyyar na jihar, Elder Patrick Ambut, ya shawarci mambobin da su kasance masu jajircewa tare da tabbatar da adalci da gaskiya a cikin aikin da aka...
Taron ya hada bijiman masana, da masu tsara manufofi, da masu ilimi,da masu bincike, da abokan hadin gwiwa na haɓaka harkar ilimi daga Afirka, Kudancin Asiya, da Birtaniya don tattauna dabarun inganta ilimi ta hanyar harshe. Dr. Alausa, ya jaddada cewa, yayin da kiyaye harsunan asali har yanzu yana da mahimmanci ga al’adu, amma Turanci ya kamata ya zama babban harshen koyarwa tun daga firamare har zuwa makarantun gaba da sakandare don inganta fahimta da gogayyar ilimi a tsakanin Daliban Nijeriya da takwarorinsu na duniya. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai ‘Yansanda Sun Kama Mutane 4 Kan Zargin Fashi Da Makami A Bauchi November 12, 2025 Manyan Labarai Kashi 74% Na Marasa Lafiya Sun Gamsu Da Ayyukan Kiwon Lafiya...
Ya kuma yi nuni da cewa, a binciken da za a yi na gaba, akwai bukatar gudanar da manyan gwaje-gwaje da za su mayar da hankali ga fadada nemo samfuran da za a yi aiki a kansu. Yana mai cewa, “har yanzu muna bukatar kara tabbatar da tasirin maganin da aka yi amfani da shi da kuma samar da nagartattun hanyoyin warkarwa ta yadda jami’an lafiya za su nakalci sahihin zabin da za su yi amfani da shi wajen magance matsalolin rashin haihuwa mabambanta, da kuma tabbatar da cimma muradun samun haihuwar.” Tabbas, kamar yadda kasar Sin take da sa kwazo cikin abubuwan da take yi, ina da yakinin za a zurfafa wannan bincike domin cike gibin da aka gano...
A cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Laraba, Sakataren Yada Labarai na ofishin mataimakin gwamna, Ibrahim Shu’aibu, ya bayyana lamarin a matsayin “cin amana a fili da direban da aka kama ya yi.” “Ofishin Mataimakin Gwamna ya yaba wa binciken gaggawa da rundunar tsaron ta yi ta hanyar amfani da kaifin basira da kwarewa,” in ji sanarwar. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Za Mu Kare Sojojin Da Ke Bakin Aiki — Ministan Tsaro November 12, 2025 Manyan Labarai Bayanan Da Muka Samu Sun Nuna An Fara Samun Tsaro A Nijeriya – Hafsan Sojin Ƙasa November 12, 2025 Manyan Labarai Yadda Ɓarawo Ya Shiga Gidan Gwamnatin Kano Ya Saci Motar Ayarin Mataimakin Gwamna November 12,...
Daga Usman Muhammad Zaria Majalisar Zartarwa ta Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da Naira Biliyan daya da miliyan dari uku domin gyara da inganta tsofaffin ayyukan wutar lantarki a fadin jihar. Kwamishinan yada labarai, matasa, wasanni da al’adu na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed, ne ya bayyana haka ga manema labarai a Dutse. A cewarsa, wannan mataki na daga cikin jajircewar gwamnatin Malam Umar Namadi wajen inganta samar da wutar lantarki da kuma bunkasa ci gaban al’umma musamman a yankunan karkara. A cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai bayan zaman majalisar, Alhaji Sagir Musa Ahmed ya kara da cewa, aikin na nuna kudirin gwamnatin jihar na tabbatar da karin samun wutar lantarki, kara habakar tattalin arziki,...
Ya bayyana cewa mutanen sun fita da sassafe don wani aiki, amma ‘yan bindigar suka tare su suka kashe su tare da tserews da babur ɗinsu . Mista Ajeh, ya roƙi hukumomin tsaro da su gano waɗanda suka aikata wannan ɗanyen aiki tare da gurfanar da su a gaban kotu. Haka kuma, ya buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta jiha da su ɗauki matakin gaggawa domin kawo ƙarshen matsalar rashin tsaro da ke ƙara ta’azzara a Jihar Nasarawa. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai ‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi Sama Da 200 A Katsina November 12, 2025 Manyan Labarai Bayanan Da Muka Samu Sun Nuna An Fara Samun Tsaro A Nijeriya – Hafsan Sojin Ƙasa November 12, 2025 Manyan Labarai...
Gwamnatin Tarayya ta ce za ta kafa ka’idoji da jagorori da za su tsara samarwa da amfani da injinan noma a fadin Najeriya. Ministan Noma da Tsaron Abinci, Sanata Abubakar Kyari, ya bayyana haka a taron shekara-shekara na 45 na Ƙungiyar Injiniyoyin Noma ta Najeriya (NIAE), mai taken “Kafa Ka’idoji da Ƙarfafa Fasahohin da Aka Gwada Don Samar da Abinci da Ƙara Darajar Kayayyaki a Najeriya”, da aka gudanar a Ilorin. Ya ba da shawarar kafuwar cibiyoyin injinan noma a kowanne yanki na ƙasa, domin horo, gyara, da tsara fasahohin aikin gona. A cewarsa, bayan samun injina, mafi muhimmanci shi ne kafa tsarin daidaitawa, haɗa na’urori a gida, da tsarin kulawa, domin tabbatar da cewa kowanne injin da aka tura...
Gwamnatin Jihar Nasarawa ta bayyana shirin ta na faɗaɗa gonakin shinkafar Jangwa daga hektar 3,300 zuwa hektar 5,000 a kakar noma mai zuwa, domin haɓaka samar da shinkafa da kuma ƙarfafa tattalin arziki a jihar. Gwamna Abdullahi Sule ya bayyana haka yayin ziyarar duba girbin shinkafa a garin Jangwa, ƙaramar hukumar Awe. Gwamnan ya ce faɗaɗa gonakin zai ƙara hektar 3,000 daga yawan da ake da shi yanzu, domin inganta ci gaban tattalin arziki ta hanyar aikin gona. Ya kuma nuna yadda jihar ta samu ci gaba a fannin noma, inda gonar ta faɗaɗa daga hektar 2,000 a bara zuwa hektar 3,300 a wannan shekarar. Gwamna Sule ya sanar da haɗin gwiwar gwamnatin jihar da kamfanin Silvex International, babban kamfani...
A wani muhimmin mataki na inganta harkar lafiya a matakin ƙasa, Karamar Hukumar Gwarzo ta kaddamar da sabuwar Cibiyar Kiwon Lafiya ta Farko (PHC) da aka gina a garin Dankado, da ke cikin gundumar Sabon Birni. Taron kaddamarwar, wanda ke nuna wani sabon ci gaba a tsarin raya jama’a, ya samu halartar manyan jami’an gwamnati, sarakunan gargajiya, da wakilan al’umma. Shugaban Karamar Hukumar Gwarzo, Dakta Mani Tsoho Abdullahi, wanda Mataimakinsa, Alhaji Abdulmumin Garba Lakwaya, ya wakilta, ya tabbatar da jajircewar gwamnatin sa wajen tabbatar da cewa kowane yanki a cikin karamar hukumar na da damar samun ingantacciyar kiwon lafiya mai sauƙin samu da araha. Ya yaba wa Kakakin Majalisar Dokoki ta Gwarzo, Ahmad Shehu Sabon Birni, da sauran kansiloli bisa...
Hukumar Tsarawa da Raya Birane ta Jihar Kano (KNUPDA) ta gudanar da horon cikin gida na farko ga ma’aikatanta, wanda ya mayar da hankali kan aiwatar da dokokin aikin gwamnati, kyawawan ɗabi’un aiki da kuma ingancin ayyuka. Wannan horo, wanda ya zama muhimmin mataki a shirin ƙarfafa ƙwarewar ma’aikata na hukumar, an shirya shi ne domin haɓaka inganci a ayyuka da ƙarfafa ƙwararru da tabbatar da bin ƙa’idojin aikin gwamnati yadda ya kamata. A jawabinta, Manajiyar Darakta ta KNUPDA, Arc. Hauwa Hassan Tudun-Wada, ta bayyana horon a matsayin muhimmiyar hanya ta gina al’adar ladabi da biyayya da nagarta a cikin ma’aikatan gwamnati. Ta yaba da jajircewa da himmar ma’aikata wajen halartar shirin, inda ta jaddada cewa fahimta da bin dokokin...
An kama diraben da ke jan motar Shafiu Sharp-Sharp, domin yi masa tambayoyi. “An riga an fara bincike. Ana yi wa direban tambayoyi, yayin da Babban Jami’in Tsaro (CSO) ke duba bidiyon CCTV,” in ji wata majiya. “An miƙa bayanan motar ga jami’an tsaro domin su gano motar da kuma kama ɓarawon.” Kakakin gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa, bai amsa kiran waya da saƙonnin da aka tura masa ba. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Zargin Kisan Kiristoci: Dalilan Da Ya Sa Trump Ba Zai Iya Kai Wa Nijeriya Hari Ba November 12, 2025 Manyan Labarai Bayan Ganawa Da Tinubu, COAS Ya Tabbatar Wa ‘Yan Nijeriya Samun Ingantaccen Tsaro November 11, 2025 Manyan Labarai Cikin Wata Ɗaya,...
Gwamnan Jihar Legas, Babajide Olusola Sanwo-Olu, ya ce a wannan zamanin na mulkin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, babu wani gwamna ko shugaban ƙaramar hukuma da zai yi ƙorafi kan ƙarancin kuɗi. Sanwo-Olu ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin wani taron ƙarawa juna sani na yini ɗaya da ƙungiyar Arewa Think Tank (ATT) ta shirya albarkacin cikar Nijeriya shekaru 65 da samun ’yancin kai, wanda aka gudanar a Arewa House da ke Kaduna. An buƙaci tsige shugaban APC na Kuros Riba ’Yan bindiga sun kashe mai juna biyu da wasu mutum 4 a Sakkwato Taken taron shi ne: “Shekaru 65 da samun ’yancin kai: Tafiyar Najeriya zuwa yanzu a ƙarƙashin Tsarin Sabunta Fata (Renewed Hope Agenda)”, inda aka haɗa...
Gwamna Lawal ya tabbatar da cewa gwamnatinsa tana da niyyar haɗa kai da hukumar wajen inganta jin daɗin ‘yan sanda da kyautata yanayin ayyukansu. Ya ce, “Gwamnatina na ɗaukar matakan da suka dace don tabbatar da cewa an kula da walwala da jin daɗin ‘yan sanda. Wannan ne dalilin da ya sa muke gyaran hedikwatar ‘yan sanda ta Zamfara a halin yanzu. “Haka kuma, muna gina wasu muhimman gine-gine a hedikwatar rundunar ‘yan sanda na Moble. Mun samu nasarori da dama a wajen, kuma muna da ƙarin shirye-shirye na gaba. “Na ji daɗin yadda sakataren hukumar ya ambaci batun ginin sabon unguwar ma’aikatan ‘yan sanda. Idan ka duba halin da barikin ‘yan sanda ke ciki yanzu, za...
Wasu ’yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun kashe mutum biyar, ciki har da wata mata mai juna biyu a ƙauyen Alkalije da ke Ƙaramar Hukumar Yabo ta Jihar Sakkwato. Lamarin ya faru ne da sanyin safiyar Litinin lokacin da maharan suka mamaye ƙauyen, inda suka fara harbe-harbe kan mai uwa da wabi. An buƙaci tsige shugaban APC na Kuros Riba Mai cutar HIV ya yi wa ’yar shekara 4 fyaɗe a Yobe Wani mazaunin yankin da ya buƙaci a sakaya sunansa, ya ce maharan sun daɗe suna shigowa daga Jihar Kebbi suna kai hare-hare kan al’ummomin yankin. “Sun saba zuwa daga Kebbi da Silame, suna kashe mutane ko su yi garkuwa da su. A wasu...
Ana fargabar cewa an yi wa wata yarinya ’yar kimanin shekara huɗu fyaɗe a ƙaramar hukumar Jakusko ta Jihar Yobe. Da yake zantawa da manema labarai fyaɗe da safiyar Litinin, mahaifin yarinyar ya bayyana cewa ta samu mummunan rauni a al’aurarta. John Cena ya lashe kambun Intercontinental karon farko a tarihi An ceto mutane 86 daga hannun ’yan ta’adda a Borno Mutumin da ake zargi da wannan aika-aikar mai suna Rabilu Sani, ɗan kimanin shekara 22, an gano cewa yana ɗauke da cutar kanjamau (HIV), kamar yadda mahaifin yarinyar ya tabbatar wa manema labarai. A wata hira da aka yi da mahaifin ta ta wayar tarho, ya bayyana cewa an kai yarinyar asibitin Jakusko tare da wanda ake zargi, inda...
A shekarar 2023, Ronaldo, wanda ke taka Leda tare da Al Nassr ta Saudiyya, ya tabbatar da maganar da ya yi na cewa, zai rataye takalminsa nan ba da jimawa ba, “Idan ina nufin nan ba da jimawa ba, watakila shekara daya ko biyu zan ci gaba da kasancewa a wasan,” in ji shi. Ronaldo wanda ya lashe kyautar Ballon d’Or sau biyar yana da burin buga Kofin Duniya na shida a shekara mai zuwa, ya kusa lashe kofin a shekarar 2006, lokacin da Portugal ta sha kashi a hannun Faransa a wasan kusa da na karshe, a halin yanzu, Portugal ba ta sami gurbi a gasar 2026 ba, wadda za ta gudana a Amurka, Kanada, da Mexico, amma...
Alƙalin ya jaddada cewa wajibi ne a bi doka da oda domin kare tsarin dimokuraɗiyya, inda ya yi gargaɗin cewa karya doka na iya jefa ƙasa cikin ruɗani. A baya, Mai shari’a James Omotosho, ya taɓa bayar da irin wannan umarni, inda ya dakatar da PDP da INEC daga gudanar ko amincewa da sakamakon taron saboda rashin bin ƙa’idojin doka, ciki har da gaza bayar da sanarwar kwanaki 21 kafin gudanar da taron kamar yadda doka ta tanada. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Tinubu Ya Aika Wakilai Don Tattaunawa Da Birtaniya Kan Dawo Da Ekweremadu Nijeriya November 11, 2025 Manyan Labarai Faɗa Ya Kaure Tsakanin Boko Haram Da ISWAP, An Kashe Mayaƙa Sama Da 170 November 11, 2025...
DSP Aliyu ya gargaɗi jama’a da su guji yaɗa labaran ƙarya, inda ya bayyana cewa duk wanda aka samu da laifin aikata hakan za a hukunta shi. Ya kuma roƙi mutane su dogara da sahihan bayanai daga hukumomi, tare da tabbatar da cewa rundunar ‘yansandan ƙarƙashin CP Bello Shehu tana ƙoƙarin kare rayuka da dukiyoyin jama’a a faɗin jihar. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Wasanni Katsina United Ta Shiga Komar Hukuncin Hukumar NPFL November 9, 2025 Wasanni Me Ke Haddasa Yawaitar Farmakar Ƴan Wasa A Gasar Firimiyar Nijeriya November 9, 2025 Wasanni Yadda Aka Tsara Gudanar Da Gasar Kofin Afirka A Moroko November 8, 2025
An kuma bayyana cewa gwamnatin Tinubu tana ƙoƙarin amfani da wannan tattaunawa wajen ƙarfafa dangantaka da Birtaniya, musamman wajen harkokin shari’a, musayar bayanan tsaro, da kula da ‘yan Nijeriya da ke fuskantar matsaloli a ƙasashen waje. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Faɗa Ya Kaure Tsakanin Boko Haram Da ISWAP, An Kashe Mayaƙa Sama Da 170 November 11, 2025 Manyan Labarai Obasanjo Ya Buƙaci Matasa Su Karɓi Ragamar Shugabanci A Ƙasashen Afrika November 11, 2025 Manyan Labarai ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 2 A Ƙauyen Katsina November 11, 2025
’Tsohon Ministan Harkokin Cikin Gida, Laftanar Janar Abdulrahman Bello Dambazau (ritaya), ya bayyana damuwarsa kan yadda matsalar tsaro ta ta’azzara a Arewa, inda ’yan bindiga da ’yan ta’adda suka mamaye wasu yankuna suna kafa dokoki tare da karɓar haraji daga hannun jama’a. Janar Dambazau ya yi wannan jawabi ne a taron farko na kan tsaro da aka gudanar a Birnin Kebbi, Jihar Kebbi, mai taken “Barazanar Rayuwa da Tsaron Ƙasa.” Ya ce matsalar tsaro a Arewa ba sabuwa ba ce, domin ta wanzu tsawon sama da shekaru 20. “Ana kashe mutane a masallatai a Katsina, Borno, Zamfara da Kano. Arewa ta sha fama da rikicin manoma da makiyaya, ta’addanci da kuma hare-haren ’yan bindiga. “Mun kai wani matsayi da ’yan...
A wajen taron, tsohon Babban Hafsan Tsaron Nijeriya, Janar Martin Luther Agwai (mai ritaya), ya ce barazanar da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi kan zargin kisan Kiristoci a Nijeriya, ya zama gargaɗi ga shugabanni su ƙara ƙaimi wajen yaƙi da rashin tsaro. Obasanjo ya ce, “Ku ne shugabannin yau, domin idan kuka bar gobe a hannun shugabannin yau, za su lalata komai, kuma ba za ku samu gobe mai kyau ba. Ku duba ƙasar Kamaru, shugabanta Paul Biya yana da shekara 92, to me za a ce game da matasan ƙasar?” Tsohon shugaban ya jaddada cewa lokaci ya yi da matasa za su tashi tsaye su jagoranci nahiyar Afrika domin makomarsu ta dogara da abin da suka yi a...
Gidauniyar Sarkin Musulmi kan Zaman Lafiya da Ci-gaba ta bayar da tallafin kayan da darajarsu ta kai Naira biliyan 1.3 domin tallafa wa makarantun Jihar Kebbi. Kayan da aka bayar sun haɗa da kujeru da teburan karatu da aka samar karkashin shirin gidauniyar, domin rabawa makarantun jihar a matsayin gudummawa don inganta yanayin ilimi. Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, wanda ya samu rakiyar Sarkin Argungu, Alhaji Sama’ila Muhammadu Mera ya miƙa kayan ne a hukumance a ranar Litinin ga Gwamnan Jihar Kebbi, Dakta Nasir Idris, a Bulasa Warehouse da ke kusa da Birnin Kebbi. Sarkin Argungu, wanda ya yi jawabi a madadin Sarkin Musulmi, ya bayyana cewa wannan kyauta na cikin manufofin Gidauniyar Sarkin Musulmi na inganta ilimi da...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Gwamnati Ta Nemi Ƴan Nijeriya Su Ƙwantar Da Hankali Kan Barazanar Trump November 10, 2025 Manyan Labarai Rundunar Sojin Sama Ta Kai Hari Kan ISWAP Da Ƴan Bindiga A Borno, Kwara Da Katsina November 10, 2025 Manyan Labarai Sojoji Sun Fatattaki Boko Haram, Sun Ceto Mutane 86 Da Aka Sace A Borno November 10, 2025
Gwamnatin Tarayya ta nemi ƴan Nijeriya da su ƙwantar da hankali duk da tutsun diflomasiyya da ya taso tsakanin Nijeriya da Amurka. Ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a, Mohammed Idris, ya bayyana hakan a Dutse, Jihar Jigawa, yayin ziyarar gaisuwa ga Gwamna Umar A. Namadi. Barazanar Amurka Na Kawo Wa Nijeriya Hari Mabiya Mazhabar Shi’a Sun Yi Zanga-Zanga A Kano Kan Barazanar Trump Ga Nijeriya “Shugaba Bola Ahmed Tinubu na da dukkan abin da ya kamata wajen tabbatar da tsaron Nijeriya daga duk wata barazana da zata kawo ruɗani, da kuma gyara duk wani tarnaki a dangantakar mu da abokan hulɗarmu na ƙasa da ƙasa, don haka, ƴan Nijeriya su samu nutsuwa,” in ji Idris. Ministan ya ziyarci...
Hukumar kula da jin daɗin alhazai ta birnin tarayya (FCT) ta saka ranar 1 ga Disamba, 2025, a matsayin ranar ƙarshe da za a biya kuɗin Hajji na shekarar 2026, wanda aka tsara a N7,696,769.76. Wannan sanarwa ta fito ne daga ofishin hukumar a yayin wata ganawa da manema labarai a ranar Litinin, inda jami’in hulɗa da jama’a, Muhammad Lawal Aliyu, ya buƙaci duk masu niyyar zuwa Hajji daga Abuja su bi ƙa’idojin da aka shimfida. An bayyana cewa tabbataccen kuɗin Hajjin ya samu ne bisa ƙayyadadden tsari daga Hukumar Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON), sannan duk biyan kuɗin za a yi ne ta hanyar Banki, domin tabbatar da gaskiya da rikon amana, ba tare da karɓar kuɗi a hannu...
Maiyaki ya ce, “Gwamna Uba Sani kwanan nan ya ba da izinin daukar ma’aikatan lafiya 1,800 nan take a karkashin rukunoni daban-daban. “Za a ci gaba da yin hakan a cikin shekaru biyar masu zuwa, da nufin inganta harkar lafiya a jihar.” Maiyaki ya ci gaba da cewa, Gwamna Sani ya fifita harkar kiwon lafiya a gwamnatinsa, inda take gaba-gaba. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Wani Sabon Hari Kan Al’ummar Da Ke Iyaka Da Katsina A Kano Ya Rutsa Da Mata 5 November 10, 2025 Labarai Yadda Sojoji Suka Tarwatsa Haramtattun Matatun Mai 14 A Yankin Neja Delta November 10, 2025 Labarai Ɗan Majalisar Wakilai, Jibrin Ƙofa Ya Sauya Sheƙa Daga NNPP Zuwa APC November 10,...
Da yake sanar da sauya sheƙarsa a ranar Litinin ta hanyar shafukansa na sada zumunta da aka tabbatar, Jibrin ya ce magoya bayansa sun yanke shawarar barin jam’iyyar NNPP da kuma kungiyar Kwankwasiyya don shiga APC da kuma yin aiki tuƙuru don marawa Shugaba Tinubu baya a zaɓen 2027. “A yau, a cikin nuna goyon baya, dubban ‘yan mazaɓarmu a garinmu na Ƙofa, Bebeji, Kano sun yi min maraba sosai. Taron ya tabbatar barinmu jam’iyyar NNPP/Kwankwasiyya, zuwa APC, da kuma goyon bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu a karo na biyu a kan mulki,” in ji Jibrin. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Sojoji Sun Fatattaki Boko Haram, Sun Ceto Mutane 86 Da Aka Sace A Borno November 10, 2025...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Da zarar damuna ta fara bankawana, yanayi na sanyi da zafi kan fara sallama, wanda hakan kan zo da rashin lafiya dake yaduwa a cikin alumma. Ko wadanne dalilai ne suka sa ake samun yaduwar rashin lafiya a wannan lokaci? NAJERIYA A YAU: Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Cutar Basir DAGA LARABA: Yadda ‘Yanbindiga Ke Amfani Da Hakar Zinare Wajen Mallakar Makamai Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kai. Domin sauke shirin, latsa nan
Hukumar gasar firimiya ta Nijeriya (NPFL) ta ƙaƙabawa Katsina United tara mai tsanani bayan samun ta da laifin gazawa wajen samar da tsaro a wasan da ta kara da Barau FC a filin wasa na Muhammad Dikko dake Katsina a ranar Asabar. Wannan hukunci na zuwa ne bayan makonni kaɗan da irin wannan aka kakabawa Kano Pillars saboda rashin ɗa’a da saɓa doka a gasar. Rahotanni sun nuna cewa rikici ya ɓarke a filin wasan bayan Barau FC ta farke ƙwallo, inda wasu magoya bayan Katsina United suka kutsa cikin fili, lamarin da ya janyo mummunan rauni ga ɗan wasan Barau, Abraham, a wuyansa. Wannan ya jawo tayar da tarzoma da ta jefa ƴan wasan cikin ruɗani. Ranar Foliyo Ta...
Shugaban reshen Akure na NBA, Mr. Friday Umar, wanda ya yi wannan kira, ya lura cewa “wani lokacin, yanke hukuncin masu karo da juna, suna tasowa ne daga bambance-bambancen ra’ayoyin alkalai” kuma ya amince cewa Majalisar Shari’a ta Ƙasa (NJC) tana ƙoƙarin kawo ƙarshen wannan yanayi. Ya ƙara da gargaɗin cewa, ya kamata a riƙa shigar da ƙara a inda aka yi laifi don kiyaye mutuncin shari’a. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kebbi Bagudo Ya Shaƙi Iskar ‘Yanci Daga ‘Yan Bindiga November 9, 2025 Labarai Soludo Ya Sake Lashe Zaɓen Gwamnan Anambra November 9, 2025 Manyan Labarai Zargin Ɓatanci Ga Annabi: Alaƙar Triumph Da Gwamnatin Kano Da Majalisar Shura November 9,...
Babban mai tattara zaɓe da hukumar ta turo, Farfesa Edogah Omoregie, kuma shugaban jami’ar Benin, shi ne ya karanta sakamakon na karshe a hedkwatar zaɓe da ke Awka. Nasarar Soludo ta nuna cewa APGA na ci gaba da daƙile siyasar yankin, tare da samun cikakken goyon bayan jama’ar jihar. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kebbi Bagudo Ya Shaƙi Iskar ‘Yanci Daga ‘Yan Bindiga November 9, 2025 Manyan Labarai Zargin Ɓatanci Ga Annabi: Alaƙar Triumph Da Gwamnatin Kano Da Majalisar Shura November 9, 2025 Labarai Turkiyya Na Karbar Bakuncin Wasu Kasashen Musulmai Game Da Makomar Gaza November 8, 2025
Gasar cin kofin Afirka ta 2025 za a fafata tsakanin kasashe 24 da aka raba rukuni shida dauke da hurhudu kowanne. Da zarar an kammala fafatawar cikin rukunin, duk wadda ta yi ta daya da ta biyu za ta kai wasan zagaye na biyu wato na ‘yan 16 da kuma hudun da suka kare a mataki na uku a rukuni da maki mai yawa. Sai dai zagaye na biyu za a buga ne ziri daya kwalle, duk wadda aka doke sai dai ta tattara kayanta zuwa gida. Gabaki dayan gasar wasanni 52 za a buga, 36 a karawar cikin rukuni da takwas a zagaye na biyu da hudu a kwata fainal da biyu a zagayen daf da karshe da neman...
Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Jibrin Barau, ya nemi Shugaban Amurka, Donald Trump, ya janye barazanar da ya yi wa Najeriya kan zargin yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi. Trump, ya yi barazanar ɗaukar matakin soji a kan Najeriya saboda zargin ana zaluntar Kiristoci. Barazanar Trump: Ya kamata shugabannin Najeriya su farka daga bacci — Bishop Kukah Tinubu ya gana da Sarkin Musulmi a Aso Rock Barau ya ce maganar da Trump ya yi ba ta dace ba, kuma ta saɓa wa dokokin ƙasa da ƙasa. A cikin wani bidiyo da aka fitar a ranar Juma’a, Mataimakin Shugaban Majalisar, ya ce Najeriya, a matsayinta na ƙasa mai cin gashin kanta, ba za ta yadda a ci zarafinta ko a tsangwame...
Sunana Lawan Isma’il (Lisary), Rano, A Jihar Kano: Haduwa da kawayen banza da kuma kuntatawa da wasu malaman suke nuna musu, saboda kin amincewa da su na bukatun da suke nema a wajensu. Da yawa iyayen ba sa tsayawa su saurari matsalolin ‘ya’yansu kan abin da ke damunsu a makaranta, da kuma rashin bibiyar karatunsu da abokansu. Iyaye su tabbatar da suna bawa yara kudi da kayan abincin da zai ishesu idan a makarantun kwana suke, sannan su tabbatar da tarbiyyar malaman da za su kai yaran nasu. Sunana Aisha Isah Gama (Mai Waka), Jihar Kano: A gaskiya abin da ke janyo wa baya wuce gurba tattun abokai, har da lefin malamai saboda malami ne za ka ga ya kulla...
Barau Zai Yi Ƙarar Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Gawuna/Garo Kan Zargin Karɓar Cin Hancin Dala Miliyan 10
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Bisa Rakiyar Jami’an Tsaro Na Ke Ganawa Da Ƴan Bindiga – Sheikh Gumi November 8, 2025 Manyan Labarai Shugaba Tinubu Da Shugaban Ƙasar Saliyo, Sun Yi Ganawar Sirri A Abuja November 8, 2025 Manyan Labarai Majalisa Ta Ƙaryata Karɓar Dala Miliyan 10 Don Daƙile Tantance Shugaban NERC November 8, 2025
Ya ƙara da cewax gwamnatinsa ta fara gyara daga tushe, inda ilimi ya zama ginshiƙin farko. “Shekaru takwas kafin mu hau mulki, ɗalibanmu ba su samun takardun WAEC, sannan tsawon shekaru biyu suna fama da matsalar NECO. Na biya Naira Biliyan huɗu don magance wannan matsala,” inji shi. Gwamnan ya bayyana irin matsalolin da ya gada, yana mai cewa: “Na samu asusun gwamnati da naira miliyan huɗu kacal. Ma’aikata suna karɓar albashi cikin rashin tabbas, babu ruwa, asibitoci kuwa suna cikin mummunan yanayi.” Lawal ya ce, ya sake fasalin tsarin gwamnati, inda ya rage yawan kwamishinoni da manyan sakatarorin don rage ɓarna da ƙara inganci. “Yanzu muna daga cikin jihohi mafi ci gaba wajen tara haraji, inda kuɗaɗen...