An kaddamar da makon nuna fina-finai da shirye-shiryen talabijin na kungiyar hadin kai ta Shanghai (SCO), ranar Juma’a a Qingdao mai taken “Duniya ta hadu ta hanyar haske da inuwa a Qingdao”, lamarin da ya mayar da birnin zuwa cibiyar musayar al’adu da bukukuwan nuna fina-finai.

 

Shirin wanda babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin CMG da gwamnatin birnin Qingdao suka shirya, da taimakon hukumar kula da shirya fina-finai ta Sin, zai gudana tsawon mako guda, inda ya hada mashirya fina-finai da jagororin masana’antar da jami’ai kamar sakatare janar na SCO da shugabannin CMG da manyan jami’an diplomasiyya da masu wakiltar al’adu da taurarin fina-finai da masu tsara shirye-shirye a shafukan sada zumunta da ‘yan kallo daga kasashe mambobin kungiyar SCO, domin zurfafa musayar al’adu da lalubo damarmakin hadin gwiwa a masana’antar shirya fina-finai.

(Fa’iza Mustapha)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Sojoji Sun Kashe Mayaƙan ISWAP 11 A Borno Da Adamawa

Nijeriya dai ta daɗe tana fama da ta’addancin Boko Haram da ISWAP a Arewa Maso Gabas.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Al’ajabi: Yadda Aka Shirya Bikin Haihuwar ‘Ya’yan Awaki Biyar A Garin Dakasoye
  • Karamar Hukumar Birnin Kano Ta Kaddamar Da Kula Da Lafiyar Ido Kyauta
  • Tinubu bai shirya gudanar da sahihin zaɓe ba a 2027 – Buba Galadima
  • Sojoji Sun Kashe Mayaƙan ISWAP 11 A Borno Da Adamawa
  • Ana zargin mace da kashe ’yar uwarta a kan N800 din barkono
  • Shawarwarin Sin: Ingantattun Hanyoyi Masu Sauki Na Warware Sabani
  • An Yi Garkuwa Da Wani Mai Hidimar Ƙasa Da Ɗalibi A Jos
  • Gwamnatin Kano ta gayyaci Mai Dubun Isa da Shehi Tajul-Izzi kan shirya muƙabala
  • NDLEA ta kama ɗan Indiya da ƙwaya ta Naira biliyan 3 a Legas
  • Ɗan Majalisar Tarayya Ya Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-haren Ta’addanci A Sakkwato