2025-10-27@04:45:12 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1229
«Kungiyar malaman musulmi ta duniya ta»:
Wata tanka ɗauke da man fetur ta kife a kan hanyar Lambata zuwa Lapai zuwa Agaie da ke Jihar Neja, lamarin da ya haifar da tsoro da fargaba a tsakanin mazauna yankin. An gano cewa tankar, wadda ta taso daga Legas tana kan hanyarta na zuwa Kano, ta kife ne da sassafe a garin Takalafiya da ke Ƙaramar Hukumar Lapai ta Jihar Neja. Majalisa ta amince a ƙirƙiro sabbin jihohi 6 a Najeriya Matsalar kashe-kashe a Nijeriya ba ta da alaƙa da addini — Femi Kayode Wani mazaunin garin Lapai, Mallam Mahmud Abubakar, ya shaida wa Aminiya cews lamarin ya faru kimanin kilomita biyu daga garin Lapai. Ya ce kwanan nan aka gyara hanyar NNPCL, amma hanyar ta fara lalacewa...
“Ban taba tunanin zan zama taurariya a duniya ba.” Daga Yobe Zuwa Fagen Duniya An haife ta a Jihar Kano kuma ta tashi a Yobe, labarin Nafisa ba shi da wuya kamar yadda yake da ban sha’awa. Mahaifinta ya rasu tun tana jaririya, kuma mijin mahaifiyarta mai suna Alhaji Yusuf Umar Kaigama ya rene ta, wanda ya dasa mata dabi’u na tarbiyya da azama. Tana kuma ɗauke da tsatson sarautar zuriyar sarakuna biyu masu daraja ta masarautar Kano, wato Sarkin Kano Ibrahim Dabo da Sarki Abdullahi Maje Karofi. Amma bayan jinin sarautar da take ɗauke dasu, yunwar ta na neman ilimi ya sa ta zama daban. A yanki da matsalar staro ta yi katutu wanda kuma yake dakushe duk wani...
Ana haka ne Gwamna Babagana Umara Zulum ya kai ziyara ƙaramar hukumar, inda ya gana da Misis Duaka a cibiyar lafiya da misalin ƙarfe 8 na dare, lokacin da sauran ma’aikatan duk sun tashi. Wannan aiki na sadaukarwa, juriya da biyayya ga aikinta, ya sa Gwamna Zulum ya fahimci cewa ta himmatu wajen kula da lafiyar mutanen Mafa, mahaifar sa. Gwamnan dai a wasu ziyarce-ziyarcen da ya kai har sau biyu, ya ware ta, ya kuma yaba wa sadaukarwar da ta yi, tare da yaba mata kan yadda ta tsaya tare da jama’arsa duk kuwa it aba ‘yar asalin yankin ba ne. Kyautar kwazo da rikon amana da ta samu ya zo ne a lokacin da Gwamna Zulum, wanda ya...
Ba wai nasara kawai ba ce; saƙo ne, cewa masu horarwa na Nijeriya na iya kai wa matakan duniya, kuma ƙwarewar gida har yanzu tana da muhimmanci. Hanyar Da Ba A Yawanta Binta Labarin Madugu ba na nasara cikin dare ɗaya ba ne, yana yi ne sannu a hankali da ƙwarewa mai ɗorewa. Daga farkon ayyukansa na horarwa ya fara da Adamawa United da ƙungiyar mini-football ta Nijeriya, zuwa aiki a matsayin mataimakin mai horarwa a gasar WAFCON huɗu (2012, 2014, 2018, 2022), ya gina suna saboda natsuwa, sassaucin dabaru, da basira. Lokacin da ya karɓi cikakken jagorancin Super Falcons a shekarar 2024, da yawa sun yi shakku kan iya cika takardun zama wasu ƙwararrun masu horarwar na ƙetare da...
Gwamnan Jihar Sokoto, Ahmad Aliyu, wanda Kwamishinan Ruwa, Alhaji Aminu Dodo Iya, ya wakilta, ya jaddada cewa sarautun gargajiya su ne ginshiƙin zaman lafiya da ci-gaban al’umma. Ya ce shugabannin gargajiya na taka rawa wajen haɗa kan jama’a da gwamnati, tare da tabbatar da ɗorewar cigaba a matakin jiha da ƙasa baki ɗaya. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Gwarzon Mawaƙin Shekarar 2025, Skales October 25, 2025 Manyan Labarai Jami’ar ABU Ta Ƙaryata Zargin Ƙera Makamin Nukiliya A Asirce October 25, 2025 Labarai Hukumar Kare Ƴancin Masu Amfani Da Kaya (FCCPC): Tabbatar Da Adalci A Kasuwa October 25, 2025
Hukumar Kwastam Ta Tara Naira Biliyan ₦658.6 A Watan Satumba — DG Na NOA Gwamna Yusuf Ya Buƙaci Hukumar NBC Da Ta Sa Ido Kan Gidajen Rediyo Da Talabijin Na Yanar Gizo Wannan inganci ba wai alama kawai ba ce. Tun daga shekarar 2023, hukumar ta sauƙaƙa sama da Naira biliyan 10 na mayar da kuɗin masu amfani don sulhu kai tsaye, mai iya bin sawu wanda ke nuna cewa dawainiya da gaskiya za a iya auna ta da kuɗi, ba wai da alkawari kawai ba. Jarumta a Zamanin Intanet Wataƙila mafi girman ƙarfin gwiwar FCCPC ya bayyana ne a shekarar 2025 lokacin da ta ɗora tarar Dalar Amurka miliyan 22 kan Meta Platforms saboda ayyukan amfani da bayanai ta...
Kasar Sin Ta Karyata Rahoto Na Zuki-ta-malle Da Wata Cibiyar Binciken Amurka Ta Fitar Game Da Hadin Gwiwar Sin Da Yammacin Afirka
A yau Alhamis 23 ga wata, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun, ya karyata wani rahoto na zuki-ta-malle da wata cibiyar bincike ta Amurka ta bayar kan hadin gwiwar da ke tsakanin Sin da Afirka ta Yamma. Ya yi nuni da cewa, rahoton ya kawo rudani ga ra’ayoyi na kaifin basira, sannan daga bangare guda kawai aka tattaro shi, kuma har ma ya ruwaito wasu bayanan da ba a tantance ba, tare da shafa kashin kaji da kuma muzanta hadin gwiwar da ke tsakanin Sin da kasashen yammacin Afirka. Wannan ya kasance wani bakon abu a fili kuma abin kyama. An ba da rahoton cewa, cibiyar nazarin al’amura ta Amurka ta Atlantic Council, ta fitar...
Masu Tasiri a Kafafen Sada Zumunta sun samu horo kan RMNCAH+N, Tsarin Iyali da Rigakafin Cin Zarafin Mata
Ƙungiyar Centre for Communication and Social Impact (CCSI) tare da haɗin gwiwar abokan aikin ta na EngenderHealth Consortium sun shirya taron horo na yini ɗaya a Kano domin ƙarfafa ƙwarewar ’yan jarida da masu tasiri a kafafen sada zumunta (social media influencers) wajen yada sahihan bayanai da tallafawa manufofin kiwon lafiya da daidaito tsakanin jinsi. Taron, mai taken “Daga Masu Bi zuwa Masu Faɗa Aji: Amfani da Kafafen Sada Zumunta wajen Yaɗa Sawun Lafiya da Daidaito”, ya mayar da hankali ne kan batutuwan Reproductive, Maternal, Newborn, Child, and Adolescent Health plus Nutrition (RMNCAH+N), Family Planning (FP), da Gender, Youth, and Social Inclusion (GYSI). Manufar wannan horo ita ce canza masu tasiri a kafafen sada zumunta zuwa ƙwararrun masu...
Gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf ta bai wa ƙungiyar kwallon ƙafa ta Kano Pillars Football Club sabbin motoci uku domin sauƙaƙa musu matsalolin sufuri a yayin gasar Premier ta shekarar 2025/2026 da ke gudana. Motocin sun haɗa da babbar motar Marcopolo mai kujeru 29 don ɗaukar ’yan wasa, motar samfurin Hummer, da kuma Sharon da za a yi amfani da ita wajen harkokin gudanarwa da sufuri. A lokacin da yake mika makullai da takardun motocin a madadin Gwamnan, Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Malam Ibrahim Umar Farouk, ya roƙi matasan jihar masu son wasanni da su ci gaba da zama masu bin doka da oda tare da guje wa duk wani abu da zai...
Rahotanni su bayyana cewa gwamnatin birtaniya ta sanar a hukumance cire kungiyar tahrirush shams HTS daga cikin jerin kungiyoyin yan ta’adda a wani yunkuri na ganin ta kara kusantar sabuwar gwamnatin siriya bayan faduwar gwamantin Bashar Al-Asad. Gwamnatin birtaniya ta bayyana cewa wannan mataki zai sanya su kara kusanci da gwamnatin siriya da Abu mohammad Al-Jolani ke jagoranta wanda aka fi sani da Ahmed sharaa wanda shi ne shugaban kungiyar Al-Qaida kuma kwamandan Daesh. Wannan sanarwar ta zo ne bayan ziyarar da sakataren harkokin wajen birtaniya David lammy ya kai kasar siriya a watan yuli, wanda ya sanya ya zama shi ne babban jami’in diplomasiya da ya kai ziyara kasar a tsawon shekaru. Kuma mataki yazo ne duk da hujjoji...
Ya ƙara da cewa shirin ya dace da shirin jihar, inda zai mayar da hankali kan bunƙasa samar da abinci a gida da karfafa matan gida wajen kula da abinci mai gina jiki. Gwamnan ya bayyana cewa majalisar kula da abinci ta jihar za ta jagoranci tsara manufofi, haɗin kai da kuma kula da aiwatar da shirin a dukkanin kananan hukumomin jihar. “Mun ƙuduri aniyar tabbatar da cewa wannan shiri ya ɗore tare da haɗin kan gwamnati da abokan hulɗa,” in ji shi. A nasa ɓangaren, kwamishinan kasafin kuɗi da tsare-tsare, Hon. Abdulmalik Gajam, ya ce gwamnatin Gwamna Lawal na taka muhimmiyar rawa wajen inganta harkar lafiya da abinci mai gina jiki ga yara ƙanana. Haka kuma, Misis Uju Rochas...
Ƙungiyar Gwamnonin Nijeriya (NGF) ta bayyana baƙin cikinta game da gobarar tankar mai da ta tashi a ƙaramar hukumar Katcha ta Jihar Neja, inda mutane 38 suka rasa rayukansu. A cikin wata sanarwa da shugaban ƙungiyar, Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq na Jihar Kwara, ya sanya wa hannu, ƙungiyar ta jajanta wa jama’a da gwamnatin Jihar Neja, musamman iyalan waɗanda abin ya shafa da kuma Gwamna Mohammed Umar Bago. Kungiyar IOMed Za Ta Taka Rawar Gani Wajen Gina Al’umma Mai Makomar Bai Daya Babu Rikici A Jam’iyyar APC A Nasarawa — Shugaban Jam’iyya “Tunaninmu yana tare da iyalan da wannan mummunan lamari ya shafa. Muna godiya ga ma’aikatan agajin gaggawa bisa taimakon da suka bai wa waɗanda abin ya rutsa da su,”...
Wasu da ake zargin masu kwacen waya ne sun kashe ma’aikaciyar jinya a Asibitin Gambo Sawaba da ke Zariya a jihar Kaduna mai suna Hadiza Musa. Bayanai sun ce marigayiyar it ace mataimakiyar shugabar sashen haihuwa a asibitin. Majalisa ta soma binciken yadda aka kashe $4.6bn na tallafin kiwon lafiya Gwamna Bala Mohammed ya ƙirƙiri sabbin masarautu 13 a Bauchi Mijinta, Hamza Ibrahim Idris, wanda ke aiki a Abuja, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce an kashe matarsa ne a ranar Asabar yayin da take dawowa daga aiki. “A ranar Asabar, ta kira ni ta ce za ta je wajen gyaran gashi sannan ta ziyarci wani shagon masu magani a Filin Mallawa, Tudun Wada Zariya, kuma na amince.”...
A ranar 30 ga watan Mayun bana, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya halarci bikin sanya hannu kan yarjejeniyar da ta tabbatar da kafuwar kungiyar IOMed, kuma a madadin kasar Sin, ya sanya hannu kan yarjejeniyar aikinta a yankin musamman na Hong Kong. Tun daga watan Agustan bana, kasashe 37 sun sanya hannu kan yarjejeniyar kafuwar kungiyar, kana takwas daga cikinsu sun amince da fara aiwatar da ita. A matsayin wadda ta gabatar da shawarar kafa IOMed, kuma mai masaukinta, kasar Sin na kira ga karin kasashe da su gaggauta shiga kungiyar, su kuma shiga a dama da su cikin hadin gwiwar kut-da-kut na ayyukanta, kana su samar da sabuwar gudunmawa ga wanzuwar zaman lafiya da...
Tsohon shugaban kasar Faransa, Nicolas Sarkozy, ya fara zaman gidan yari na shekara biyar a gidan yarin La Santé da ke tsakiyar birnin Paris. An same shi da aikata laifin hada baki wajen samun kudaden yakin neman zabensa na shekarar 2007 daga tsohon shugaban Libiya, Muammar Gaddafi. Sarkozy ya musanta aikata laifin, kuma ya nemi a sake shi daga gidan yari yayin da yake neman daukaka kara. Wannan dai shi ne karo na farko a tarihin jamhuriya ta biyar da wani tsohon shugaban kasar zai kwana a gidan yari. Magoya bayansa sun taru da sanyin safiyar yau a wajen gidansa na Paris. A shafin sa na sada zumunta ya yi wa magoya bayansa alkawarin cewa .gaskiya za ta yi nasara....
Bayanai daga Falasdinu na cewa a kalla Falasdinawa 97 ne sojojin Isra’ila suka kashe tare da jikkata wasu 230 tun bayan da yarjejeniyar tsagaita bude wuta ta fara aiki a Gaza a ranar 10 ga watan Oktoba. A cikin wata sanarwa da ofishin yada labarai na gwamnatin Gaza ya fitar, ya ce ‘yan mamayar sun aikata laifuka 80 tun bayan ayyana tsagaita bude wuta, wanda hakan ya saba wa dokokin jin kai na kasa da kasa. Laifukan sun hada da harbin bindiga kai tsaye kan fararen hula da gangan, da kama fararen hula. A cewar sanarwar, sojojin na Isra’ila sun yi amfani da motocin soji, tankunan yaki da aka jibge a gefuna da wuraren zama, da jirage marasa, lamarin da...
DSS ta gurfanar da su bisa tuhumar laifuka 32 da suka shafi ta’addanci. Usman ya amsa laifi ɗaya kacal na haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba, amma ya musanta sauran. Abba kuwa ya ƙi amsa dukkanin laifukan da ake tuhumar sa da su. An zarge su da kai hari sansanin soja na Wawa da ke Jihar Neja, sace mutane, samar da kuɗin ta’addanci, da kuma samun horo a ƙasar Mali daga wata ƙungiyar ta’addanci ta waje. Haka kuma DSS ta ce sun sace jami’in Kwastam da wani jami’in Shige da Fice wanda ya mutu a hannunsu, tare da karɓar kuɗin fansa na miliyoyin Naira daga iyalan waɗanda suka sace kafin a kama su. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai NLC...
Sinawa kan ce, bisa mataki mataki ake yin tafiya tsawo. Lallai nasarorin da kasar Sin ta cimma, sun faru ne sakamakon yadda al’ummomin kasar suka hada karfi da karfe a karkashin jagorancin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, kuma suka yi ta yin kokari ba tare da kasala ba bisa shirye-shiryen raya kasa da gwamnati ta tsara na shekaru biyar biyar. Shirye-shiryen cike suke da burikan da kasar Sin ke neman cimmawa, wadanda kuma suka shaida kokarin da al’ummar kasar suka yi da ma wahalhalun da suka sha. Idan aka fara wani sabon shirin, to, an bude sabon babi na bunkasa kasar ke nan. Ma iya cewa, tarihin shirye-shiryen raya tattalin arziki da zaman al’umma na kasar Sin na shekaru...
Kungiyar kare hakkin dan Adama ta Amnesty International ta ce: Gwamnatin Tanzaniya ta wurga yanayin tsoro tare da tsananta danniya gabanin babban zaben kasar Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta zargi mahukuntan Tanzaniya da haifar da yanayin tsoro da kuma tsananta danniya gabanin babban zaben da aka shirya yi a ranar 29 ga watan Oktoba, tare da yin amfani da dabarun yaki da ‘yan adawa, ‘yan jarida, kungiyoyin farar hula, da masu kare hakkin bil’adama. Amnesty International ta bayyana cewa: Gwamnatin shugaba Samia Hassan na ci gaba da ayyukanta na danniya da suka hada da kama mutane ba bisa ka’ida ba, tilasta bacewar mutane, da kuma kashe-kashen ba bisa ka’ida ba, ba tare da hukunta wadanda suka...
Zakaran kyautar Ballon d’Or ta bana, Ousmane Dembele, ya shiga cikin sahun ’yan wasan ƙungiyar Paris Saint-Germain (PSG) da za ta kece raini da Bayer Leverkusen a gasar Champions League, bayan ya shafe makonni shida a jinya. Dembele, wanda ya samu rauni a cinya yayin da yake wakiltar ƙasar Faransa a farkon watan Satumba, ya shafe makonni yana jinya a cibiyar lafiya ta musamman da ke Qatar, kafin komarwarsa atisaye a makon da ya gabata. Gwamnonin Kano, Katsina da Jigawa sun ƙulla yarjejeniyar bunƙasa wutar lantarki Yadda Morocco ta kafa tarihin ɗaga Kofin Duniya na FIFA U20 Kamfanin Dillancin Labarai na Faransa AFP ya ruwaito cewa, kociyan PSG, Luis Enrique, zai yi farin ciki da dawowar Dembele, la’akari da yadda...
Hukumar gudanarwar Kungiyar Kwallon kafa ta Kano Pillars ta dakatar da Babban Kocinta Ahmed Garba Yaro Yaro da bai ba da shawara ga Kocin, Ogenyi Evans, nan take. Ta kuma nada tsohon kyaftin kuma Mataimakin Koci, Gambo Muhammad nan take, ya jagoranci lamuran fasaha na ƙungiyar. Mai horar da masu tsaron raga, Suleiman Shuaibu, zai taimaka masa, yayin da Koci Garzali Muhammad (Kusa) daga Junior Pillars zai ba da ƙarin goyon baya har sai an fitar da sabbin umarni. Kungiyar ta dauki wannan mataki ne bayan abin da ta kira “rashin tagomashinta” a Gasar Firimiyar Najeriya (NPFL) ta 2025/2026 da ake ci gaba da yi. Sanarwa da kulob ɗin ta fitar, hukumar gudanarwar ta ce an ɗauki matakin ne bayan...
Don haka, an nada “tsohon kaftin din kungiyar kuma mataimakin koci, Gambo Muhammad, tare da mai horar da masu tsaron gida, Suleiman Shuaibu, su maye gurbin wadanda aka sallama na dan wucin gadi. Bugu da kari, Koci Garzali Muhammad (Kusa) daga Junior Pillars zai taimakawa wadanda aka nada na dan wucin gadin”. LEADERSHIP ta ruwaito cewa, kungiyar mai taken ‘Sai Masu Gida’ tana fama a ‘yan makonnin nan. Hukumar kwallon kafa ta Nijeriya ta kuma ci tarar kungiyar tarar kudi sama da Naira miliyan 9 biyo bayan rikicin da ya ɓarke a yayin da suke karawa da wata kungiya a filin wasa na Sani Abacha. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Wasanni Kano Derby: Barau FC Ta Doke Kano Pillars A...
Darakta Janar na Hukumar Makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA) Rafael Grossi ya bayyana kwarin gwiwar cewa, za a iya warware takkadama kan shirin Iran na makamashin nukiliya ne ta hanyar diflomasiyya kadai. Grossi ya bayyana hakan ne a wata hira da jaridar Neue Zeitung ta kasar Switzerland a jiya Lahadi. Shugaban hukumar ta IAEA ya ce, masu binciken ba su sami wata shaida da ke nuna cewa Iran ta boye wani adadi na sinadarin uranium da aka inganta ba. Ya kara da cewa, “Yawancin abubuwan da aka samu na Iran an adana su ne a wuraren da aka sani a Isfahan da Fordow, da kuma wani lokaci a Natanz.” in ji shi. Grossi ya bayyana kwarin gwiwa cewa “za a...
Sunana Aisha Isah Abubakar (Mai Waka) Gama: A gaskiya bawa yara kanana kudi wannan ba dabi’a ce mai kyau ba, saboda wata rana idan babu wannan kudi da aka sabawa yaro da shi wallahi illa ce babba. Sabida yau da gobe sai Allah idan suka rasa wannan kudi komai zai iya faruwa za su iya saka hannu su diba ako’ina, saboda su biya wa kansu bukatar su. Shawara ya kamata masu dabi’ar aiken yara su basu kudi dan Allah su daina, gara ku siyi ‘sweet’ idan yaro ya dawo a bashi ya fi a dauki kudi a bashi. Allah ya sa mu dace. Sunana Aminu Adamu, Malam Maduri A Jihar Jigawa: To magana ta gaskiya sam-sam hakan bai dace...
Yanzu kuma za a ci gaba da tattaunawa kan yadda za a aiwatar da sauran sharuddan da ke ke kunshe a yarjejeniyar. Masu sanya ido na ganin cewa aikin sake ginan yankin Gaza wanda aka rushe kusan daukacinsa a yakin da aka yi na shekara biyu, zai zama babban kalubale. Wannan ce ranar da kowa ke jira -Trump A lokacin da Donald Trump ya yi jawabi, ya bayyana yau a matsayin “ranar da kowa ya yi ta hankoro da addu’ar ganin zuwan ta.” Shugaban na Amurka ya ce “Wannan yarjejeniya mai matukar tarihi” wadda gungun shugabannin duniya suka sanya wa hannu, na nuna cewa “addu’ar miliyoyin al’umma ta karbu”. Daga nan sai ya ce shugabannin sun samu nasarar...
A ta bakin shugaban bikin, kuma gwamnan Jihar Tillabery Maina Boukar, taron na wannan karo ya shaida aniyar gwamnatin Nijar, ta bai wa wadanda suka rungumi shirin ajiye makamai damar sauya rayuwarsu, da taimaka musu wajen cimma nasarar komawa cikin al’umma cikin mutunci. Boukar ya ce, “Wannan muhimmin zabi, ya nuna aniyar gwamnatin Nijar ta kare ikon mulkin kai, da wanzar da tsaro, da tabbatar da zaman lafiya karkashin kyawawan manufofin kasa, ba tare da dogaro ga wasu ajandoji daga ketare ba.” ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai ‘Yan Siyasa 11 Da Suka Faɗa Dambarwar Takardar Shaidar Karatu Ta Bogi October 19, 2025 Da ɗumi-ɗuminsa DHQ Ta Ƙaryata Rahoton Yunƙurin Yi Wa Tinubu Juyin Mulki October 18, 2025...
Ya bayyana cewa a ‘yan watannin da suka gabata, rundunar ta kara kaimi wajen kai samame a wuraren da ake zargin yin laifuka a fadin jihar, a wani bangare na kokarinta na rage yawan shan miyagun kwayoyi da laifukan da suka shafi hakan, wadanda hukumomi ke cewa sau da dama su kan zama sanadin tashin hankali da aikata laifuka musamman tsakanin matasa. “Lokacin da barayin suka hango tawagar sintiri na kusantowa, sai suka tsere, suka bar tarin miyagun kwayoyi da wasu haramtattun abubuwa a wurin,” in ji Abdullahi. Mai magana da yawun rundunar ya lissafa abubuwan da aka kwato da suka hada da kwayoyin “Suck and Die,” Tramadol da Diazepam, inda ya ce an kwashe su gaba daya...
Ya ce “Daga wancan lokacin zuwa yanzu, mun rasa Farsesoshi 309,wasu sun je Jami’oi masu zaman kansu a Nijeriya, sauran wasu sun je London, Saudi Arebiya, Kameroon da kuma wasu kasashe.Kwarrunmu wadanda babban jari ne suna barin aiki saboda sharuddan aikinsu babu wani abin jin dadin da zai sasu ci gaba da kasancewa wuraren aikinsu na koyarwa kamar yadda ya ce,”. Sabo ya bayyana cewa kungiyar za ta fara yajin aikin mako biyu daga ranar Litinin, idan har gwamnatin tarayya ta ci gaba watsi da maganar bukatunta da kuma inganta masu sharuddan aiki. “Mun yi shiru har abin ya wuce misali.Hakkin mune nu ceto jami’oin gwamnati. Idan har gwamnati ta ci gaba da yin biris da mu, ba...
Georgieba ta kuma gargadi duniya kan barazanar da fitar da kudade ta haramtacciyar hanya (IFFs) ke yi, inda ta ce wannan matsala ta zama babbar abin da ke lalata tattalin arziki da tsarin kudi na kasashe a fadin duniya. A cewarta, fitar da kudade ta haramtacciyar hanya wacce ta hada da satar kudaden gwamnati, kudaden da suka fito daga ayyukan laifi, da mu’amalolin dijital da ba a iya bibiyarsu na ci gaba da lalata tsarin mulki, rage kudaden gwamnati, da durkusar da kokarin ci gaba, musamman a kasashe masu tasowa. A cikin wani jawabin manufofi na baya-bayan nan, jami’an IMF sun bayyana cewa IFFs yanzu suna zuwa ta fannoni da dama. Wannan ya hada da karkatar da kudaden...
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta fidda bayani kan cewa daga yau Asabar 18 ga watan Octoban shekara ta 2025, kudurin kwamitin tsaro na MDD wanda aka samar don goyon bayan aiwatar da yarjeniyar Nukliyar kasar Iran wacce aka fi sani da JCPOA ya kawo karshe. Don haka daga yau shirin Nukliyar kasar Iran ta koma karkashen yarjeniyar NPT, kuma za’a yi mu’amala da shirin kamar sauran kasashen karkashin kula na hukumar IAEA. Tsahar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ma’aikatar na bada wannan sanarwan a safiyar Asabar ta kara da cewa dama kudurin na tsawon shekaru goma ne daga yau ta gama aiki. Daga yau shirin Nukliyar JMI zai ci gab aba tare da wani karin ka’idojin...
Abokan Yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya Sun Ce: Sake Dawo Da Takunkumin Da Aka Kakaba Kan Iran Baya Kan Doka
Abokan Yarjejeniya ta Majalisar Dinkin Duniya sun bayyana cewa: Sake dawo da takunkumi bayan karewarsa baya da wani tushe na doka ko tsari Kungiyar aminan Yarjejeniya ta Majalisar Dinkin Duniya ta fitar da wata sanarwa game da cikar kudiri mai lamba 2231 kan yarjejeniyar makamashin nukiliyar Iran a ranar 18 ga watan Oktoba, inda ta bayyana cewa matakin da Amurka da Turai suka dauka na sake daukar matakin kakaba takunkumin da ya kare kan wata kasa tsari ne da baya ya kan wani tushe na doka ko yarjejeniyar kasa da kasa. Kungiyar aminan Yarjejeniya ta Majalisar Dinkin Duniya ta fitar da wata sanarwa a ranar Alhamis da ke nuna cikar kuduri mai lamba 2231 na kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya...
An fara gina magudanan ruwa domin dakile afkuwar ambaliyar ruwa a kananan hukumomin Malam Madori da Kaugama dake jihar Jigawa. Tawagar Injiniyoyin jihar karkashin jagorancin Daraktan kula da ambaliyar ruwa da zaizayar kasa, Injiniya Mukhtar Muhammad Usman sun ziyarci kananan hukumomin domin duba yadda aikin ke gudana. Haka zalika Daraktan da mataimakin sa Injiniya Mahdi Isyaku da sauran ma’aikata ssn ziyarci wurin da ambaliyar ruwa tayi ta’adi a garin malam Madori. A lokacin da tawagar ta fara auna fili da tona magudanun ruwan, daraktan ya ce an fara aikin tona magudanar ruwa mai tsawon kilomita 2 a matsayin wani ɓangare na aikin karkatar da ruwan da ya lalata wurare zuwa sabon wurin da aka tsara. Yana mai cewar,...
Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, ya bi sahun dan rajin kare hakkin dan adam kuma tsohon dan takarar shugaban kasa, Omoyele Sowore, wajen yin kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta sakin jagoran kungiyar Biafra (IPOB) Nnamdi Kanu. A cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na D, Atiku, ya bayyana ci gaba da tsare Kanu a matsayin “rashin girmama bin doka a Nijeriya.” Kanu dai, na fuskantar tuhumar ta’addanci ne da cin amanar kasa da kuma nuna tunzura a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja, wanda kuma a lokuta da dama yake musanta hakan. Har ila yau, ya kasance a tsare tsawon shekaru duk da hukuncin da kotu ta yanke na bayar da umarnin...
Rahotanni sun bayyana cewa marziyeh Ja’afari ta kafa tarihi inda ta samu kyautar da hukumar kwallon kafa ta asiya ke bayarwa , inda ta zama kociyar da ta kasance zakara a wannan shekara, yayin da Salar Aghapur kuma ya zamo gwarzo a bangare kwallon Fustal na shekara ta 2025 da hukumar AFC ke bayarwa a duk shekara a wani biki da aka gudanar a birnin Riyadh Biki karo na 29 da hukumar kwallon kafa ta Asiya ke shiryawa a duk shekara don mika kyaututtuka ga wadanda suka yi kwazo, kamar wanda yafi iya taka leda, da kociyan da yafi, da kuma kungiyar kwallon kafa da ta fi a wannan shekarar ya gudana ne a kasar Saudiya. Jaafari an girmamata ne...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar iran Ismail Baqaei yayi maraba da dakatar da bude wuta da aka yi tsakanin kasashen Pakistan da Afghanistan, kuma yayi kira ga kasashen biyu da su warware sabanin dake tsakanin ta hanyar tattaunawa da kuma diplomasiya. Iran ta dade tana ba da shawarwarin magance matsalolin tsaro a yammacin Asiya da kuma Kudancin Asiya, da kuma nuna rashin amincewa kan tsoma bakin kasashen waje kan rashin fahimtar dake tsakanin kasashen musulimi, yace rikicin dake tsakanin Kabul da islam abad barazana ce ga zaman lafiya yankin, kuma zai amfanar da kungiyoyi masu tsattsauran ra’ayi masu so su yi amfani da tarzoma a iyaka. Rikicin kan iyaka tsakanin Pakistan da Afghanistan yayi Kamari a yan kwanakin nan inda...
Kungiyar Euro-Med ta bukaci bangarori su shiga Gaza domin tattara bayanai kan kisan kiyashin Isra’ila
Wata kungiyar kare hakkin bil’adama ta Euro-med mai hedkwata a Geneva ta yi kira ga kasashen duniya da su tabbatar da shiga Gaza ba tare da ‘yan jarida, masu bincike, da masana harkokin shari’a don tattara bayanan kisan kiyashin da Isra’ila a Gaza da kuma hukunta wadanda suka aikata laifin. A cikin wata sanarwa da ta fitar a shafinta na X, Hukumar ta ce, biyo bayan yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka cimma a Masar ranar Litinin, “Dole ne duniya ta ga abinda ya kasance a Gaza.” Kungiyar ta ce a yanzu dole ne a bar duniya ta ga irin barnar da aka yi, wa matsugunai, da kuma haddassa wahalhalun ga bil adama sanadin yakin da Isra’ila ta yi na...
Rundunar ’yan sandan Jihar Katsina ta kama gungun mutane 11 da ake zargi da kasancewa ’yan fashi da makami da ke addabar matafiya a kan hanyar Katsina zuwa Kano. Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, Abubakar Aliyu, ya shaida wa manema labarai a ranar Laraba a Katsina cewa waɗanda ake zargin sun kware wajen tare hanyoyin zuwa Sha’iskawa-Charanchi da Katsina-Kankia-Kano, suna kwace dukiyoyin matafiya. DSS ta cafke tsoffin jami’anta 2 kan aikata zamba Kotu ta daure kocin kwallon kafa a Kano shekara 8 saboda aikata luwadi Ya bayyana sunayen waɗanda aka kama da suka haɗa da Dikko Ma’aru, Dardau Kabir, Muntari Musa, Labaran Amadu, Usman Ma’aru, Lawal Zubairu, Nasiru Sanusi, da Adamu Kabir. Sauran sun haɗa da Abdullahi Zubairu, Muhammad...
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi a jawabin da ya gabatar a taron tsakiyar shekara ta ministocin harkokin wajen kungiyar yan ba ruwammu wato NAM a birnin Kampala babban birnin kasar Uganda a jiya Laraba, ya jadda bukatar hadin kai da goyon baya a tsakanin kasashen kungiyar, wajen fuskantar rashin mutunta dokokin kasa da kasa da kuma nuna iko na bangare guda. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Araqchi yana cewa yana daga cikin manufofin kafa kungiyar NAMA tabbatar da yencin ko wace kasa a duniya. Don haka akwai bukatar nuna wannan a aikace. Dangane da yakin kwanaki 12 wanda Amurka da HKI suka dorawa kasar Iran a cikin watan yunin da ya gabata, Aragchi...
Tsohon ɗan majalisar wakilai, Farouk Lawan, ya ce afuwar shugaban ƙasa ya yi masa, ta ba shi kwarin guiwar yin wata sabuwar tafiyar siyasa. Ya bayyana cewa ya bar tafiyar Kwankwasiyya ne saboda jagorancinta ya yi watsi da shi lokacin da ya fi bukatrsu. ’Yan bindiga sun kashe mutum 1, sun sace dabbobi a Katsina Kaso 92 cikin 100 na ’yan Najeriya ba su iya wanke hannu ba — UNICEF Lawan, wanda ya wakilci mazabar Bagwai/Shanono a Jihar Kano, yana cikin mutane 175 da Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya yi wa afuwa a ranar 9 ga watan Oktoba. An kama shi a shekarar 2021 bayan samun sa da laifin karɓar cin hanci a 2012, domin cire sunan wani kamfani daga jerin...
Shugaban Hukumar Kula da Asibitoci ta Jihar Kano (HMB), Dakta Mansur Mudi Nagoda, ya kai ziyarar ba-zata ta duba aiki a Asibitin karbar Haihuwa na Imamu Wali, na Marmara, da kuma Asibitin Sabon Bakin Zuwo. Ya kai ziyarar ce domin tabbar bin umarnin Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, na wucin gadi wajen sauya wuraren gudanar da ayyukan karbar haihuwa da na yara zuwa wasu cibiyoyi daban. A karkashin wannan umarni, an mayar da sashen haihuwa na Asibitin Koyarwa na Muhammad Abdullahi Wase zuwa Asibitin Haihuwa na Imamu Wali, yayin da aka mayar da ayyukan yara kyauta da ake yi a Asibitin Yara na Hasiya Bayero zuwa Asibitin Haihuwa na Marmara. Wadannan canje-canjen sun biyo bayan ci gaba da...
Ma’aikatar Kasuwancin Sin Ta Yi Kira Ga Amurka Da Ta Shiga Tattaunawar Cinikayya Da Sahihiyar Zuciya
Daga nan sai kakakin ya ce, “Ba zai yiwu bangaren Amurka ya nemi tattaunawa a bangare guda, alhali a daya hannun yana barazanar kaddamar da sabbin takunkumai kan kasar Sin ba. Wannan ba ita ce hanya mai dacewa ta gudanar da cudanya da Sin ba.” (Saminu Alhassan) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Uwar Gidan Shugaban Sin Ta Ziyarci Wajen Nune-nunen Karfafawa Mata Gwiwa A Bangaren Fasahohin Zamani October 14, 2025 Daga Birnin Sin Sin Tana Adawa Da Matakan Kuntatawa Na Amurka Kan Bangarorin Kasar Da Suka Shafi Harkokin Teku Da Jigila Da Ginin Jiragen Ruwa October 14, 2025 Daga Birnin Sin Kowacce Mace Tauraruwa Ce A Kasar Sin October 14, 2025
A halin yanzu, sama da mata da yarinya miliyan 600 a duniya suna cikin rikici da yaki, sannan mata da ‘yan mata biliyan 2 ba su da tabbacin tsaron zamantakewa. Kamar yadda babban sakataren MDD Antonio Guterres ya bayyana, cewar har yanzu ci gaban mata a duniya yana fuskantar “kalubale da ba a taba ganin irinsa ba”, kasashe suna bukatar kuduri da hikima don magance matsalolin mata. A lokacin kaka na shekara ta 2025, daga Beijing za a sake samun ci gaba, wato Sin tana fatan ta kara hada kai da sauran bangarori, don hanzarta cikakken ci gaban mata, da kuma ba da gudummawar mata don ciyar da ci gaban bil’adama gaba. (Amina Xu) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga...
Tawagar Super Eagles ta Najeriya sun kara da Cheetahs na Jamhuriyar Benin a wasan neman cancantar shiga gasar cin Kofin Duniya ta 2026. Wasan da suka fafata a filin wasa na Godswil Akpabio da ke Jihar da Uyo ya kasance tamkar mai zafin gaske kuma an nuna bajinta. Tun kafin a fara wasan, an samu sauye-sauye hudu daga tawagar da ta doke Lesotho, inda Wilfred Ndidi ya hau matsayin kyaftin, yayin da Moses Simon ke shirin yin buga na 85 a wasannin kasa da kasa. A gaba kuma, an hada Victor Osimhen da Akor Adams domin tayar da kura. Wasan ya fara da sauri — ina minti na uku kacal, Osimhen ya zura kwallo ta farko bayan Chukwueze yi mika...
Shugabannin kasashen Amurka, Masar,Katar da Turkiya da su ka halarci taron na “ Herm-Sheikh” a kasar Masar sun sanya hannu akan yarjejeniyar tsagaita wutar yaki a Gaza. A jiya Litinin ne dai aka bude taron na Kasar Masar, wanda kuma ya sami halartar Fira ministan kasar Pakistan da kuma shugaban kasar Faransa. Da yake gabaatar da jawabi, shugaban kasar Amurka Donald Trump yarjejeniyar ta zaman lafiya ta kunshi bangarori da dama, kuma tana tattare da ka’idojin aiwatar da ita. Akan gawawwakin fursunonin Isra’ilawa, shugaban kasar ta Amurka ya ce ba a kai ga warwarewa ba baki daya, domin har yanzu ana ci gaba da kokarin gano inda suke. Shi kuwa mai masaukin baki, Shugaban kasar Masar Abdulfattah al-Sisi, ya bayyana...
Mai bai wa shugaban kasar Iran shawarar akan harkokin mata da iyali Malama Zahra Beruz Azar ta gabatar da shawarar a kulla wata yarjejeniya ta tausayawa a tsakanin matan duniya domin samar da damar gina rayuwa ta jin kai da ‘yan’adamtaka mai dorewa. Malama Zahra Behruz Azar ta gabatar da wannan shawarar ne dai a yayin taron kasa da kasa na mata da aka bude a kasar China. Haka nan ta kuma bayyana cewa; A wannan lokacin muna rayuwa ne a cikin karnin da ci gaba da fasahar kere-kere su ka sauya salon rayuwa, ta yadda kirkirarriyar fasaha ta zama mai matukar tasiri a cikin matakan da ake dauka, kamar kuma yadda Sakandami ( Robot) ya maye gurbin bil’adama a...
“Idan mutum ya shiga jarrabawa kuma Allah Ya kawo dama ta afuwa, dole ne ya yi farin ciki. Ni da iyalina da masoyana mun yi murna ƙwarai,” in ji Lawan. “Na gode wa Allah da kuma Shugaba Tinubu saboda ya yi abin da ya kamata a yaba masa.” Ya bayyana cewa rayuwa a gidan yari ta koya masa juriya da fahimtar cewa komai ƙaddara ce. “Tun kafin na bar kotu na sallama komai ga Allah. Na sani cewa duk inda mutum ya samu kansa, akwai darasi a ciki,” in ji shi. Bayan fitowarsa daga gidan yari, Faruk Lawan ya sauya tafiyarsa ta siyasa. Ya ce ya rabu da tafiyar Kwankwasiyya da aka san shi da ita, duk da cewa har...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Shekara da shekaru kungiyar malaman jami’oi ASUU ta kwashe ta na gudanar da yajin aiki ba tare da samun biyan bukata ba. Irin wannan yajin aiki da kungiyar malaman ke shiga ya jefa dalibai da malaman da ma harkar ilimi cikin halin ni ‘yasu a Najeriya. NAJERIYA A YAU: Kalubalen Da Ke Gaban Sabon Shugaban Hukumar Zabe Ta Kasa DAGA LARABA: Yadda Aka Yi Almajiri Ya Zama Mabaraci Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan wasu hanyoyin da kungiyar malaman ASUU za ta iya bi don warware matsalar ta ba tare da dogaro da gwamnatin tarayya ba. Domin sauke shirin, latsa nan
Jam’iyyun adawa a ƙasar Jamhuriyar Kamaru sun ayyana Issa Bakary Tchiroma a matsayin wanda lashe zaɓen shugaban ƙasar da gagarumin rinjaye. Gamayyar jam’iyyun adawa da ƙungiyoyin fararen hula na Union for Change ta ce sakamakon da suka tattara daga fadin ƙasar da ƙasashen waje ya nuna Bakary ya samu kashi 60 zuwa 80 cikin ɗari na ƙuri’u a rumfunan zaɓe da dama. Sun buƙaci Shugaba Paul Biya, wanda ke neman wa’adin mulki na takwas a zaɓen da ya gaggauta miƙa saƙon taya murna ga Issa Bakary Tchiroma. “Muna kira ga shugaban ƙasa mai barin gado da ya gaggauta taya sabon shugaban ƙasa murna,” in ji ƙungiyar,” in ji wata sanarwa da shugabannin ƙungiyar, Anicet Ekane da Djeukam Tchameni, suka fitar a...
Rundunar ‘yan sandan jihar Neja ta tabbatar wa al’ummar jihar a shirye ta ke ta ci gaba da kare mutuncin daidaikun mutane da kungiyoyin da suka sadaukar da kansu domin samar musu da sahihin bayanan sirri da za su kara kaimi wajen kare rayuka da dukiyoyin al’ummar Nijar. ‘Yan sanda a jihar Neja da ma Nijeriya ƙwararru ne don haka za su ci gaba da aiki da kuma nuna basira da ƙwarewa tare da ƙa’idarta ta sirrin rashin bayyana tushen bayanansu don samun sakamako mafi girma. Kwamishinan ‘yan sandan jihar Neja Adamu Abdullahi Elleman wanda ya bayar da wannan tabbacin a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Minna, ya bayyana cewa a kwanan baya ya halarci wani taron...
Kungiyar ‘Yan Dako ta kasa reshen jihar Jigawa ta kaddamar da Malam Muhammad Tajudeen Maigatari a matsayin sakataren kungiyar na jihar. Da yake jawabin a lokacin bikin kaddamawar a garin Maigatari, Shugaban kungiyar na jihar Malam Nasiru Idris Sara, ya bayyana shugabanci a matsayin rikon amana a maimakon hanyar tara dukiya da alfahari, a don haka akwai bukatar sakataren ya yi aiki tukuru dan kare martabar sana’ar dako da masu yin ta. Yana mai cewar shugabancin kungiyar zai hada kai da shugabannin kananan hukumomi da masu rike da sarautu da jami’an tsaro a matsayin abokan kawo cigaba wajen daga likkafar sana’ar dako. Nasiru Idris Sara ya kuma yi kira ga daukacin ‘yan dako a fadin jihar da su yi rijista...
A cewar NEMA, mutane 135,764 ne suka rasa matsugunansu, yayin da 115 aka bayyana bacewarsu, yayin da wasu 826 suka samu raunuka sakamakon ambaliyar. Bugu da kari, gidaje 47,708 sun lalace, yayin da gonaki 62,653 suka lalace a fadin jihohin da abin ya shafa. Hukumar ta kara da cewa, daga cikin wadanda abin ya shafa sun hada da yara 188,118, mata 125,307, maza 77,423, tsofaffi 18,866, da kuma nakasassu 2,418. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Ta’addanci: Ana Fuskantar Ƙarancin Man Fetur A Mali Sakamakon Datse Hanyoyin Shiga Bamako October 13, 2025 Manyan Labarai Tinubu Ya Isa Birnin Rome Don Halartar Taron Tsaro Na Aqaba October 12, 2025 Manyan Labarai An Sauya Kwamishinan Ƴansandan Abuja Saboda Rashin...
Cibiyar kula da lafiya ta Nasser Medical Complex da ke Gaza ya bayyana cewa: Yara 5,500 ne ke bukatar agajin gaggawa a kasashen waje Daraktan cibiyar kula da lafiya ta Al-Shifa da ke Gaza ya ce: Babu wani agajin jinya da ya shiga zirin Gaza duk da cewa an shafe sa’o’i 72 tsagaita bude wuta. Ya kara da cewa: Mutane 170,000 marasa lafiya da kuma wadanda suka jikkata na bukatar tafiya cikin gaggawa zuwa wajen Gaza domin neman magani. Al-Nasser Medical Complex ya kuma ce: Yara 5,500 na bukatar magani a wajen Gaza. Daraktan asibitin yara na Nasser Medical Complex, Dr. Ahmed Al-Farra, ya bayyana cewa, akwai yara 5,500 a zirin Gaza da ke bukatar agajin gaggawa a wajen yankin...
Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya nuna damuwa kan yadda shugaba Bola Tinubu ya yi wa wasu mutane afuwa, ciki har da waɗanda suka aikata manyan laifuka. A cikin saƙon da Atiku ya wallafa a shafinsa na X, ya ce ana yin afuwa ne ga waɗanda aka yi wa rashin adalci ko waɗanda suka nema gafara bayan sun shafe wani lokaci a gidan yari. Yajin Aikin ASUU: Ba za mu biya duk wanda bai yi aiki ba — Gwamnatin Tarayya ’Yan sanda sun ceto mutum 10 daga hannun ’yan bindiga a Kaduna Ya ce a wannan karon an yi wa masu safarar ƙwayoyi, masu garkuwa da mutane, masu kisan kai, da kuma masu cin hanci da rashawa afuwa. Atiku,...
Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Nijeriya ASUU a ranar Lahadi ta sanar da shiga yajin aiki na makonni biyu, wanda zai kasance cikakke kuma gaba ɗaya, a duka jami’o’in gwamnati na ƙasar. Shugaban ƙungiyar Farfesa Chris Piwuna ne ya sanar da hakan a lokacin wani taron manema labarai da aka gudanar a Jami’ar Abuja, a ranar Lahadi. Asuu ta ce yajin aikin na gargaɗi ne bayan cikar wa’adin da suka bai wa gwamnatin Najeriya a watan Satumban da ya gabata. “Yajin aikin gargadin zai kasance cikakke kuma gaba ɗaya, kamar yadda aka amince a taron NEC na ƙarshe,” kamar yadda Piwuna ya bayyana. RN
Kasashe hudu da suka fi kokari a cikin wadanda suka kare a mataki na hudu za su fafata wasannin raba-gardama, sai wadanda suka samu nasara su sake raba-gardama da wasu kasashen na waje. A yanzu daI manyan kasashen nahiyar ta Afirka irin su Kamaru da Nijeriya suke fuskantar barazanar rasa gurbi, duk da haka suna da wasu damarmakin da idan suka yi sa’a za su iya tsintar kansu a gasar a badi. Kasar Masar ta wuce Burkina Faso da maki biyar, sannan idan ta samu nasara a kan Djibouti shikenan ta samu tikiti. Ita kuma kasar Djibouti tana can karshen teburi ne, domin maki daya tak take da shi a wasa takwas da ta buga. Idan ma...
Nasarorin da kasar Sin ta samu a cikin gida, sun kafa ginshikin jagorancin duniya, wajen samar da ci gaban harkokin mata, musamman ta hanyar fitar da darussa, ta hanyar kyautata mu’amala tsakamnin bangarorin biyu. Babban misali shi ne yadda ake samun bunkasar dangantakar mata tsakanin kasashen Kenya da Sin, wadda aka inganta yayin ziyarar aiki da shugaban Kenya William Ruto ya kai kasar Sin a watan Afrilun bana. Kasashen biyu sun yi alkawarin zurfafa mu’amalar al’adu, ciki har da mu’amalar mata da matasa bisa tsarin dandalin tattauna hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka. Wadannan matakai sun kunshi fannoni kamar su tallafin karatu da horar da sana’o’i, kuma dukkansu sun haifar da babban sakamako. (Safiyah Ma) ShareTweetSendShare MASU ALAKA...
Rundunar sojin Najeriya, ta bayyana cewa dakarunta sun kashe ’yan ta’adda biyar a wani samame da suka kai yankin Magumeri da Gajiram, a Jihar Borno. Kakakin rundunar Operation Haɗin Kai, Kanar Sani Uba, ya ce dakarun sun yi arangama da wasu ’yan ta’adda 24 da ke tafe a ƙafa a ranar Juma’a. Mutane 2 sun rasu a rikicin manoma da makiyaya a Kebbi Rashin wutar lantarki ta kassara kasuwanci a Kaduna, Kano da Katsina A cewar sanarwar da ya fitar, sojojin sun yi nasarar kashe biyar daga cikinsu tare da ƙwato kuɗi Naira miliyan biyar. “An hangi ’yan ta’addan suna ƙone gidaje da kuma kai wa mutane hari, sai dakarun suka fara bin su, inda suka tsere zuwa ƙauyen Damjiyakiri,”...
Rundunar ‘yansanda ta tabbatar da cewa ana gudanar da cikakken bincike domin gano ainihin musabbabin mutuwarta. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Tsaro Sojoji Sun Ƙaryata Rahoton Cewa Ƴan Bindiga Sun Mamaye Sansaninsu A Kwara October 5, 2025 Tsaro Sojoji Sun Kama Ƴan Ta’adda 450, Sun Ceto Mutane 180 A Satumba — DHQ October 4, 2025 Tsaro Bayan Sulhu Da Ƴan Bindiga, An Saki Mutane 70 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Katsina September 22, 2025
Shugabannin Faransa, Jamus, da Biritaniya: Sun kuduri aniyar farfado da tattaunawa da Iran Kasashen Faransa da Jamus da Birtaniya sun bayyana aniyarsu ta farfado da shawarwari da Iran da Amurka dangane da shirin makamashin nukiliyar Iran da nufin cimma cikakkiyar yarjejeniya mai dorewa. A cikin wata sanarwa ta hadin gwiwa, kasashen uku sun yi la’akari da Shirin kunna yarjejeniyar fahimtar juna. A baya dai Faransa da Birtaniya da Jamus sun sanar da cewa za su ci gaba da neman hanyar diflomasiyya don warware rikicin, amma Iran ta tabbatar da cewa ba ta son ci gaba da tattaunawa a halin yanzu idan dai har za a kakaba mata takunkumi. A gefe guda kuma shugabannin kasashen Birtaniya da Faransa da Jamus sun...
Aƙalla mutum takwas ’yan Ƙungiyar tsaro ta Civilian JTF ko ’yan ƙato da gora aka sanar an kashe a ƙauyen Dan Loto da ke Ƙaramar hukumar Tsafe a Jihar Zamfara. Harin dai na zuwa ne makonni biyu kacal bayan da wasu ’yan bindiga suka kai hari a wani masallaci tare da kashe wasu masallata biyar ciki har da wani Limami a ƙaramar hukumar. ’Yan Najeriya miliyan 60 na fama da taɓin hankali — Likita Ɗan Majalisa ya nemi ɗaukar mataki kan dorinar ruwa a Gombe Dan Loto yana cikin yankin Yandoton Daji, unguwar da ’yan bindigar suka kashe masu ibada biyar a ranar 26 ga Satumba, 2025. Binciken Daily Trust ya nuna cewa, ’yan bindigar sun yi wa ’yan ƙungiyar...
Bugu da kari, an rufe shafukan hakar ma’adanai haramtacce 98 a fadin kasar. “An kiyasta cewa Nijeriya na asarar kusan Dala biliyan 9 a kowace shekara sakamakon haramtacciyar hakar ma’adanai. Wannan sata ta albarkatunmu da ya kamata ta bunkasa kasarmu ta wuce kima, kuma lokaci ya yi da za a kawo karshensa,” in ji Abdulraheem. A cewar sa, kwamitin na da alhakin hana asarar kudaden shiga, tabbatar da gaskiya da adalci a harkokin hakar ma’adanai, da tabbatar da cewa dukiyoyin ma’adanin kasar suna ba da cikakken gudunmawa ga ci gaban tattalin arziki. “Yayin da muke ci gaba, daya daga cikin manyan manufofin wannan kwamitin shi ne hana asarar kudaden shiga da haramtacciyar hakar ma’adanai da ayyukanta ke...
Hukumar Kwastam shiyyar bodar Najeriya ta Seme da ke jihar Legas ta ce ta cafke motoci biyar da ke maƙare da buhuna 10,000 na lalatacciyar fulawa da darajarsu ta kai Naira biliyan 1.2. Rundunar ta kuma ce ta tara jimillar kuɗin shigar da ya kai Naira biliyan daya da rabi a watan Satumba, wanda hakan ya nuna kari da kaso 182 cikin 100 idan aka kwatanta da Naira miliyan 531 da aka tara a watan Agustan da ya gabata. NAJERIYA A YAU: Kalubalen Da Ke Gaban Sabon Shugaban Hukumar Zabe Ta Kasa Tinubu ya yi wa Mamman Vatsa, Farouk Lawan da wasu mutum 173 afuwa Kwamandan rundunar a shiyyar, Wale Adenuga, ne ya bayyana hakan a taron manema labarai na...
Hukumar Bunkasa Ma’aikata ta Jihar Jigawa ta shirya taron karawa juna sani na kwana daya ga jami’an kula da dakunan karatu a wani bangare na aikinta na daga darajar ma’aikata da ma’aikatan gwamnati da masu zaman kansu. A jawabinsa na bude taron, Darakta Janar na MDI, Umar Farouk Wada, ya ce makasudin shirya taron shi ne don bunkasa kwarewa da sanin makamar aikin da ake da su ta yadda za a samar da ingantacciyar hidima kamar yadda Cibiyar ta tanadar. Ya kuma bayyana cewa, za a ci gaba da gudanar da irin wannan horon ne domin a baya Cibiyar ta shirya bita ga nau’ukan ma’aikatu masu zaman kansu da na gwamnati. Umar Farouk ya bayyana ɗakin karatu...
A cewar kungiyar, wadannan kalubalen sun hada da takurawar dokoki daga hukumomin gwamnati, karancin isar da danyen mai daga Kamfanin Man Kasa na Nijeriya (NNPC), matsalolin da suka shafi farashin kayayyaki, da kuma tsoma bakin kungiyoyin ma’aikata da na dillalan man fetur. ACF ta fi mayar da hankali ne kan rawar da Kungiyar ’Yan Kasuwar Man Fetur ta Nijeriya (IPMAN), Kungiyar Ma’aikatan Man Fetur da Iskar Gas ta Nijeriya (NUPENG), da Kungiyar Manyan Ma’aikatan Man Fetur da Iskar Gas ta Nijeriya (PENGASSAN) suka taka, tana zarginsu da shiga cikin ayyukan tada hankali, ciki har da zanga-zanga da barazana, wadanda suka kara dagula harkokin aiki na matatar man. “Yanzu abin yana kara bayyana a fili cewa akwai wasu boyayyun kungiyoyi...
Cibiyar Kula da Harkokin kasuwanci ta kasa ta bayyana kafa Cibiyar Gudanar da taron Kasuwanci na Najeriya a wani bangare na ganin ba a samarda cibiyoyi da ke da aiki iri ɗaya ba. Babban magatakardar Cibiyar Mista Victor Olannye, ne ya bayyana haka a lokacin da yake gabatar da takardar a yayin taron jin ra’ayin jama’a na kwamitin majalisar wakilai kan harkokin kasuwanci a Abuja. Mista Victor Olannye ya ce kudurin dokar da ke neman kafa sabuwar cibiyar ya ci karo da ayyukan Cibiyar Gudanarwa ta kasa da tuni Majalisar Tarayya ta 9 ta amince da ita wadda Shugaban kasar na wancan lokacin ya amince da shi. Ya yi nuni da cewa, babban makasudin kafa Cibiyar Kula...
Gwamnatin Isra’ila ta amince da yarjejeniyar tsagaita bude wuta da tsare tsare da shugaban Amurka Donald Trump ya gabatar a hukumance, kamar yadda ofishin Firayim Ministan Haramtacciyar Kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu ya sanar a yau Juma’a. Wannan dai na zuwa ne bayan ci gaba da tsaikon da aka samu na tsawon kwana daya biyo bayan amincewar kungiyoyin gwagwarmayar Falasdinu a ranar Alhamis. Duk da cewa an amince da matakin farko na yarjejeniyar, amma dai Isra’ila ba ta dakatar da hare-harenta a kan al’ummar yankin zirin Gaza, inda a cikin kasa da sa’oi 24 ta kashe Falastinawa akalla 70 da kuma jikkata wasu da dama a yankuna daban-daban na zirin Gaza. Tun da farko hukumar yada labaran Isra’ila ta bayar da...
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bukaci dukkanin bangarorin da su yi aiki da kuma mutunta yarjejeniyar da shugaban Amurka Donald Trump ya gabatar da kuma yin amfani da wannan damar. Da yake jawabi a wurin taron Majalisar Dinkin Duniya, Guterres ya bayyana cewa, “Ina kira ga dukkan bangarorin da su mutunta ka’idojin yarjejeniyar, da kuma rungumar damar da tke cikinta.” Duk da cewa dai a cikin kalaman nasa yafi nuna damuwa a kan fursunonin Isra’ila da ake tsare da su a Gaza, duk da irin mummunan kisan kiyashi da Isra’ila take yi a Gaza, amma mya ce Majalisar Dinkin Duniya ta shirya tsaf domin ba da cikakken goyon bayanta ga aiwatar da yarjejeniyar. A halin da...
Gwamnatin tarayya ta yi asarar jimillar gangar danyen mai miliyan 13.5 wanda kudinsa ya kai dala biliyan 3.3 sakamakon sata da fasa bututun mai tsakanin shekarar 2023 zuwa 2024, in ji wata kungiya mai fafutukar kare masana’antu ta Nijeriya (NEITI). Sakataren zartarwa na NEITI, Dokta Ogbonanya Orji, ne ya bayyana hakan a Legas a taron kungiyar masu ba da rahoto kan makamashi ta Nijeriya (NAEC) na 2025 a Legas ranar Alhamis. Ya koka da cewa, rashin gaskiya da rikon amana ne ya dabaibaye masana’antar mai da iskar gas, yana mai cewa akwai bukatar yin gaskiya da aiwatar da sabon tunani na fasaha wajen tafiyar da harkar mai da iskar gas a kasar. Orji ya lura cewa, kudaden da aka yi...
Adadin Biyan Kudade Ta Intanet Yayin Hutun Bikin Kafuwar Jamhuriyar Jama’ar Sin Ya Kai Yuan Tiriliyan 13.26
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko October 8, 2025 Daga Birnin Sin Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan October 8, 2025 Daga Birnin Sin Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana October 8, 2025
Jami’an Hukumar Shige da Fice ta Ƙasa (NIS) a Jihar Jigawa, sun kama wani matashi da ake zargi da sato motar asibiti daga Jamhuriyar Nijar, yayin da yake ƙoƙarin shigowa da ita Najeriya. Kwanturolan hukumar a jihar, Tahir Abdullahi Musa ne, ya tabbatar wa manema labarai hakan a Dutse. Falasdinawa na murna da tsagaita wutar hare-haren Isra’ila a Gaza Sauye-sauyen Tinubu ba su rage talauci a Najeriya ba — Bankin Duniya Ya ce an kama wanda ake zargin mai suna Yusif Bashir da motar asibiti ƙirar Toyota Land Cruiser mai lambar ONG-0777, bayan ya shigo da ita ta iyakar Babura da Jamhuriyar Nijar. Tahir, ya ce tuni hukumar ta fara shirye-shiryen miƙa sh ga rundunar ’yan sandan jihar, domin ci...
Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya kaddamar da sabuwar cibiyar taro ta Ahmadu Bello da aka gina a Bauchi, inda ya bayyana ta a matsayin alamar ci gaba a gwamnatin Gwamna Bala Mohammed. Da yake jawabi a wajen taron, Obasanjo ya jaddada muhimmancin dunkulewar duniya, inda ya ce babu wata al’umma da za ta iya rayuwa a ware ba tare da yin hulda mai ma’ana da sauran kasashen duniya ba. Ya yaba wa Gwamna Bala Mohammed bisa ayyukan raya kasa, musamman a fannin samar da ababen more rayuwa, wanda a cewarsa hakan zai karawa Bauchi damar karbar bakuncin taron kasa da kasa da kuma jawo hankalin masu zuba jari. Tsohon shugaban kasar ya bayyana cewa irin wadannan...
Ƙungiyar Ma’aikatan Manyan Makarantun Najeriya (SSANU) da Ƙungiyar Ma’aikatan Ilimi (NASU), sun shirya gudanar da zanga-zangar gargaɗi ta rana ɗaya a yau Alhamis saboda Gwamnatin Tarayya ta gaza cika musu alƙawuran da ta ɗauka. Ƙungiyoyin, ƙarƙashin jagoranci Joint Action Committee (JAC), sun gudanar da taron gaggawa a ranar Laraba don shirya zanga-zangar. 2027: Atiku, Jonathan da Obi ba za su iya kayar da Tinubu ba — Kalu ’Yan sanda sun kama ɗan bindiga a kan iyakar Najeriya da Kamaru Sun ce za su gudanar da tattaki a cikin jami’o’i, tare da ɗaukar kwalaye masu rubuce-rubuce, sannan za su yi wa manema labarai jawabi domin bayyana ƙorafe-ƙorafensu. Sun zargi gwamnati da rashin adalci wajen rabon Naira biliyan 50 na alawus-alawus, ƙin...
Wasu da ake zargin ’yan bindiga ne, sun tare hanyar Gusau zuwa Gummi a Jihar Zamfara, inda suka sace mutane da dama. Wata majiya ta bayyana cewa, maharan sun tare motoci sannan suka yi awon gava da fasinjojin da ke ciki. Yadda Obasanjo ya ƙaddamar da cibiyar taron ƙasa da ƙasa a Bauchi Ban yi murabus don ina da laifi ba — Nnaji Wani shaida ya ce ’yan bindigar sun ɗauki lokaci suna sharafinsu kafin daga bisani suka tafi da mutanen da suka kama. Daga cikin waɗanda suka sace akwai Malam Sadis Isa, shugaban Majalisar Malamai ta Ƙaramar Hukumar Gummi, abin da ya jefa al’umma cikin tsoro da damuwa. “Da yammacin ranar Talata, ’yan bindiga sun tare hanyar Gusau zuwa...
Tsohon Shugaban Ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya ƙaddamar da sabon ginin Cibiyar Taron Ƙasa da Ƙasa, wadda aka sanya wa sunan Sir Ahmadu Bello a Jihar Bauchi. An ƙaddamar da cibiyar ne kafin babban taron zuba jari da nufin bunkasa kasuwanci da masana’antu a jihar. Ban yi murabus don ina da laifi ba — Nnaji Kamfanonin rarraba lantarki sun tafka asarar biliyan 358 a cikin wata uku – NERC A jawabinsa, Obasanjo ya yaba wa Gwamna Bala Mohammed, bisa irin ayyukan raya ƙasa da yake aiwatarwa, waɗanda ke inganta rayuwar jama’a. “Na yi farin ciki da abin da na gani da kuma abin da na ji. Ban zata cewa zan dawo Bauchi cikin ƙanƙanin lokaci don buɗe irin wannan katafaren waje...
Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya bai wa wata ma’aikaciyar lafiya ’yar ƙabilar Igbo kuma ‘yar asalin jihar Anambra, Marbel Ijeoma Duaka, kyautar gida mai dakuna biyu. Gwamnan ya kuma ba ɗan ma’aikaciyar aikin yi na dinidindin saboda jajircewarta da sadaukarwa wajen hidimtawa jihar na sama da shekara 20. Matar aure mai ’ya’ya huɗu ta rataye kanta a Jigawa Joash Amupitan na iya zama sabon shugaban INEC Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin rabon gidaje 72 ga malamai da ma’aikatan lafiya a ƙaramar hukumar Mafa. Zulum ya ce Marbel ta shafe fiye da shekaru 24 tana aiki a cibiyar kula da lafiya ta matakin farko da ke Mafa, kuma ba ta taɓa barin wurin ba ko...
Shugaban hukumar makamashin nukiliya ta Iran ya jaddada cewa: Iran ba zata daina samar da magungunan da take yi ta hanyar fasahar makamashin nukiliya ba Kakakin Kwamitin Tsaro da Harkokin Waje na Majalisar Shawarar Musulunci (wato Majalisar Dokoki) Ibrahim Reza’ei, ya tabbatar da cewa ana ci gaba da samar da magungunan ta hanyar fasahar makamashin nukiliya a Iran, kuma ba a taba dainawa ba, kuma za a ci gaba da gudanarwa. Reza’i ya bayyana cewa: Kwamitin tsaron kasar ya gudanar da zaman hadin gwiwa tare da shugaban hukumar makamashin nukiliya ta Iran (AEOI), Mohammad Eslami, da wasu jami’an kungiyar. Islami ya gabatar da wani rahoto kan ci gaban da aka samu a fannin makamashin nukiliya, da hasarar da aka samu...
Haka kuma ya buƙaci a aiwatar da gyare-gyare don farfaɗo da tattalin arziƙi, inganta ilimi da kiwon lafiya, tare da samar da damammaki ga matasa.Ya ƙara da cewa majalisar za ta sake duba Kundin Tsarin Mulki na 1999 domin bunƙasa dimokuraɗiyya da inganta mulki a Nijeriya.ShareTweetSendShareMASU ALAKA Manyan LabaraiDa Ɗumi-ɗumi: Yakubu Ya Miƙa Ragamar INEC Ga Agbamuche-Mbu A Matsayin Shugabar Riƙo October 7, 2025Manyan LabaraiYa Kamata Nijeriya Ta Ayyana Yaƙi Da ‘Yan Ta’adda — Tsohon Hafsan Sojin Ƙasa October 7, 2025Manyan LabaraiTinubu Ya Bayar Da Umarnin Rage Kuɗin Aikin Hajjin 2026 October 7, 2025
Mambobin kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya NUJ reshen jihar Nasarawa sun zabi sabbin jami’anta da za su gudanar da harkokin kungiyar na tsawon shekaru uku masu zuwa. Shugaban kwamitin zaben, Mista Samson Osuo, ya sanar da Abubakar Abdullahi na jaridar Daily Trust a matsayin wanda ya lashe zaben da kuri’u 21 da Danjuma Joseph na National Accord da kuri’u 9 a matsayin shugaban kungiyar. Ya kuma bayyana cewa Mista Chris Nyamtu na gidan rediyon Najeriya ne ya yi nasara da kuri’u 21 yayin da Augustine Kuza na jaridar Pilot na Najeriya ya samu kuri’u 9 a matsayin Sakatare. Mista Abel Daniel na jaridar Guardian a matsayin mataimakin shugaba Awayi Kuje na NAN a matsayin Mataimakin Sakatare, Michael...
Sisi: Samun zaman lafiya na gaskiya a Gabas ta Tsakiya ya dogara da kafa ‘yantacciyar kasar Falasdinu
Shugaban kasar Masar Abdel Fattah el-Sisi ya ce, “Za a samu zaman lafiya na gaskiya a yankin Gabas ta Tsakiya ne kawai idan an kafa kasar Falasdinu mai cin gashin kanta bisa ka’idojin kasa da kasa da kuma hanyar da za ta maido da hakkokin masu hakki.” A jawabin da ya yi na bikin cika shekaru 52 na nasarorin da larabawa suka samu a yakin watan Oktoban 1973, Sisi ya yi nuni da cewa, yin amfani da karfin tuwo domin aiwatar manufa ne ke haifar da tashin hankali, yayin da zaman lafiya da aka gina bisa adalci yana samar da daidaito na gaskiya da kuma dorewar zaman tare a tsakanin al’ummomi.” Ya yi nuni da cewa, tsagaita bude wuta, musayar...
Ya kuma tabbatar da cewa Gwamnatin Tarayya tana aiki don ƙirƙirar yanayi mai sauƙin zuba jari, da zaman lafiya don masana’antu, da haɓaka tattalin arziki mai dorewa. A ƙarshe, ya kira masu ruwa da tsaki da su fifita tattaunawa a wajen neman mafita maimakon rikici, yana cewa, “Nijeriya ƙasa ce mai girma da ke neman mafita a abubuwa da yawa, ya zama dole ne mu haɗa kai wajen kare abin da ke amfanar ƙasa baki ɗaya.” Tags: Aliko DangoteShettima ShareTweetSendShare Abubakar Sulaiman Related Manyan Labarai Talaucin Da Ya Ninku Fiye Da Sau Biyu A Gwamnatin Tinubu, An Ƙuduri Aniyar Kawar Da Shi Nan Da Shekaru 5 4 hours ago Manyan Labarai Uba Sani Ya Amince...
Talaucin Da Ya Ninku Fiye Da Sau Biyu A Gwamnatin Tinubu, An Ƙuduri Aniyar Kawar Da Shi Nan Da Shekaru 5
A cewar Bankin Duniya, talauci a tsakanin mazauna karkarar Nijeriya ya kai kashi 75.5 cikin dari, wanda ke nuna ƙaruwar rashin daidaito da kuma tsananin matsin tattalin arziki a fadin kasar. Ministan ya ce, gwamnati ta kuma kuduri aniyar inganta hasashen tattalin arziki da inganta sauye-sauyen da zai sanya Nijeriya ta samu ci gaba mai ɗorewa. Bagudu ya jaddada cewa, gwamnatin da shugaban kasa Bola Tinubu ke jagoranta tana ba da fifiko wajen samar da ayyukan yi ta fuskar fasahar zamani, noma, tattalin arziki da ƙirƙire-ƙirƙire. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake...
Sanarwar ta ce, hare-haren kakkaɓe maɓoyar ‘yan bindigar na zuwa ne a karkashin shirin ‘Operation Lafiya Nakowa’, da nufin fatattakar ‘yan bindiga da sauran masu aikata laifuka a jihar Taraba. Ya kara da cewa, harin ya biyo bayan sahihan bayanan sirri kan ayyukan ‘yan ta’addan a kusa da Tarhembe, Tornyi, TY Farm, da ɗaukacin yankin Kando da ke yankin Tati, karamar hukumar Takum, da kuma rahotannin lalata gonaki a karamar hukumar Ussa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A karon farko a tarihin kwallon raga ta mata ta Iran ta zami lashe kofin zakarun Asiya, bayan samun galaba akan kawarta ta kasar Uzbakestan. An fara wasan fidda gwani a tsakanin kungiyoyin kwallon raga na mata na Asiya a ranar 2 ga watan nan na Oktoba, a birnin Tashqand wanda ya zo karshe a yau Lahadi da samun galabar Iran. Tun da fari kungiyar kwallon ragar ta Iran ta sami nasarori har sau uku a jere, da a karshe ta kai ga samun nasara akan mai masaukin baki kasar Uzbakestan. Mai bayar da horo ga ‘yan wasan Li Du Hi, ta bayyana jin dadinsa da nasarar da su ka samu, musamman saboda wannan ne karon farko aka sami wannan...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Allah Ya yi wa fitaccen ɗan jarida a Jihar Kano Aliyu Abubakar Getso, rasuwa da safiyar yau Lahadi bayan fama da rashin lafiya. Abubakar Getso ya yi aiki a kafafen yaɗa labarai da dama da suka haɗar da na gwamnati da kuma masu zaman kansu. Ya rasu ya bar mata uku da ’ya’ya da jikoki da dama. Iyalai sun ce za a yi jana’izarsa da misalin karfe 9:30 na safiyar yau Lahadi a gidansa da ke Second Gate a Unguwar Janbulo, Kabuga.
BICTOR IKPEBA – 1997 Dan wasan Nijeriya Bictor Ikpeba, ne da ake yi wa lakabi da suna “Prince of Monaco,” Ikpeba ya samu shiga ne bayan ya taimaka wa kungiyar Monaco ta samu nasarar lashe kofin Ligue 1 ta Faransa. Danwasan ya samu kuri’a 2, inda ya kare a mataki na 32 a cikin jerin wadanda suka samu karramawa a shekarar ta 1997. ADEMOLA LOOKMAN – 2024 A kakar bara, wanda ya lashe gwarzon dan kwallon kafa na Afirka, Ademola Lukman, wanda a lokacin yake buga wasa a kungiyar Atalanta ne ya zo na 14 a bikin karramawar. Lookman ya lashe gasar Europa da Atalanta, inda ya zura kwallo uku rigis a raga, sannan ya taka rawar gani sosai a...
Hukumar sararin samaniya ta kasar Iran ta bada sanarwan shirin cilla tauraron dan’adam a cibiyar cilla taurarin dan’adam na Chabahar tare da amfani da sandarerren makamashi. Kamfanin ndillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto shugaban hukumar Hassan Salarieh yana fadar haka a yau Asabar ya kuma kara da cewa, an kammala bangare na farko na cibiyar cilla taurarin yan’adam na Chabahar kuma hukumar ta fara shirin amfani da sandarerren makamashi don cillan taurarin yan’adam da suke gabanta, wadanda a shirye suke a cillasu. Salarieh y ace a halin yanzu akwai tauraron dan Adam mai suna Pars-2 da ke jiran cillawa, sannan hukumar zata ci gaba da aiki a bangare na 2 na cibiyar don kammala aikin cibiyar cilla tararin...
Da farko za ki wanke tsamiya sai ki dafa ta ki tace sannan ki wanke danyar citta sai ki nika ta, sannan ki samu roba mai kyau sai ki tace tsamiya tare da cittar kisa suga da filebo sai ki juya sosai ki sa a firij ko ki sa masa kankara. Asha dadi lafiya. Hadadden Lemon Shayi: Abubuwan da uwargida za ki tanada: Kankana, kokumba, sitoru beri na ruwa, lemo, tea bag, danyar citta, abarba, Lemon juice, na’a na’a. Yadda zaki hada: Da farko za ki wanke kankana da danyar citta sai ki nika su, sannan ki tace ki zuba a cikin tukunya, sai ki dora akan wuta ki wanke abarba da kokumba, ki yanka ki zuba a cikin tukunya...
Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya yayi tsokaci kan martanin kungiyar Hamas kan yarjejeniyar zaman lafiya a Gaza Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya António Guterres ya bayyana jin dadinsa da martanin da kungiyar Hamas ta mayar dangane shirin shugaban Amurka Donald Trump kan Gaza, yana mai bayyana hakan a matsayin abin karfafa gwiwa. Kakakin babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana a cikin wata sanarwa a yau Asabar cewa: Guterres ya bukaci bangarorin da abin ya shafa da su yi amfani da wannan damar wajen kawo karshen yakin Gaza da kuma kawo karshen bala’in jin kai da fararen hula ke fuskanta. Ya kara da cewa, babban sakataren Majalisar Dinkin Duniyar ya tabbatar da shirin Majalisar Dinkin Duniya na goyon bayan duk...
Mista Fall ya jagoranci tawagar Majalisar Dinkin Duniya da ta kunshi wakilai daga UNICEF, UNESCO, UNDP, UNFPA, da mata na Majalisar Dinkin Duniya a wajen taron. Ya jaddada cewa canjin al’umma ya ta’allaka ne akan jarin dan’Adam musamman ta hanyar ilmantar da ‘ya’ya mata da karfafa wa mata. Ya kara da cewa, “tare da gwamnati da abokan huldarmu, mun himmatu wajen kawar da duk wani cikas da ke hana yara, musamman ma masu rauni damar samun ilimi”. Fall ya gano muhimman abubuwan da ke kawo cikas ga ilimi a Nijeriya, da suka hada da rashin tsaro, tabarbarewar tattalin arziki, sauyin yanayi, da kuma ka’idojin zamantakewa da al’adu. Ya yi kira da a kara himma wajen inganta daidaiton jinsi...
Sabbin Gonakin Da Za A Magance Zaizayewar Kasa A Sin A Karshen Shirin Raya Kasa Na Shekaru Biyar Na 14 Sun Kai Muraba’in Kilomita 340,000
Bisa labarin da ma’aikatar harkokin albarkatun ruwa ta kasar Sin ta bayar a kwanakin baya, ana sa ran cewa, fadin sabbin gonakin da za a shawo kan matsalar zaizayewar kasa a Sin a karshen shirin raya kasa na shekaru biyar karo na 14 ya kai muraba’in kilomita dubu 340, fadin gonakin da aka tabbatar da yanayin ruwa da kasar da ke cikinsu ya kai kashi 73 cikin dari. Wani jami’in ma’aikatar ya bayyana cewa, a yayin gudanar da shirin raya kasa na shekaru biyar karo na 14, an kiyaye kyautata yanayin zaizayewar kasa a kasar Sin, kuma an cimma burin rage fadin gonakin da suka gamu da matsalar, da kuma rage illar da ruwa da iska suka haddasa wa gonaki....
Bayanan sun bayyana cewa; “Jimillar makarantu 228 suka ci gajiyar shirin, inda kimanin dalibai 829,423 suka nema. Ya zuwa yanzu kuma, dalibai 510,378 ne suka samu wannan tallafi na bayar da rance. “Zuwa 10 ga watan Satumba, an biya kimanin Naira 53,801,717,293.00 a matsayin kudaden makaranta na daliban, yayin kuma da aka biya Naira 45,751,360,000.00 a matsayin alawus-alawus na daliban. Idan aka tattara kudaden baki-daya, jimillarsu ta kama Naira 99,553,077,293.00,” a cewar rahoton. Duk da nasarar da aka samu a fadin kasar, shirin ya fuskanci kalubale wajen ganin an yi adalci a rabon a dukkanin shiyoyin fadin kasar guda shida da ake da su. Alkaluman da LEADERSHIP ta tattara a watan Mayun 2025, sun nuna dimbin gibin da ke tsakanin...
Wata gobara da ta tashi a daren Alhamis ta lalata wani ɓangare na ɗakin kwanan dalibai mata a Jami’ar Jihar Gombe, tare da jikkata dalibai uku. Ana zargin gobarar ta tashi ne sakamakon fashewar gas ɗin girki a wani ɓangare na ɗakin kwanan da ke cikin harabar jami’ar. Da yake tabbatar da faruwar lamarin a wata hira ta wayar tarho da wakilinmu a ranar Juma’a, Jami’in Hulɗa da Jama’a na Hukumar Kashe Gobara ta Kasa, reshen jihar, Bashir Mu’azu, ya bayyana lamarin da cewa abin takaici ne. “Lamarin ya faru ne sakamakon fashewar gas ɗin girki. Binciken farko ya nuna cewa daliba ce ta bar girki ba tare da kulawa ba,” in ji Muazu. Sai dai ya bayyana cewa babu...
Ita dai wannan yarjeniyar wadda wanda mamallakin karamin Jirgin Sama, zai bayar da hayar Jirginsa na Sama, ba tare da ma’aikata da kula da Jirgin da kuma yin inshore ba. Akasarin wannan yarjeniyar ana yinta da takardar shedar mamallakan Jiragen Samn wato AOC. “Hakan ya nuna cewa, mun fara shiga cikin matakin fafada harkar kasuwanci mai zaman kansa ne kuma za mu yi hakan a bangaren Kamafnin Jirgin Sama na Air Peace ba ne, sai dai kawai, a bangaren sauran Jiragen Sama,” A cewar Manajin Darakantan. A shekarar 2024 ne dai, aka cire Nijeriya daga cikin jeren kasasshen da suka yi kaurin suna wajen saba yarjeniyar, ta bayar da hayar Jirgin Sama. Kazalika, hakan ya biyo bayan kiyaye daukacin ka’idojin...
Shugaban Gidauniyar Malala, ya jaddada kudirin gidauniyar na bunkasa ilimin yara mata a fadin Najeriya.
Ya bayyana haka ne a lokacin da ya kai ziyarar ban girma ga mai martaba Sarkin Zazzau Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli a fadarsa da ke Zariya. Da yake jawabi, shugaban gidauniyar Malala, Mista Ziouddin Yousafzai ya yaba da kyakkyawar tarba da aka yi masa tare da tawagarsa, inda ya bayyana Masarautar Zazzau a matsayin babbar abokiyar tarayya wajen ciyar da manufofin Gidauniyar gaba. Ya yi alkawarin karfafa hadin gwiwa da cibiyoyin gargajiya domin bunkasa samun ilimi da karfafawa ‘ya’ya mata samun damar da suke da ita. A nasa jawabin, Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli, ya yabawa gidauniyar Malala bisa ci gaba da tallafawa wajen inganta ilimin yara mata, musamman a Arewacin Najeriya. Sarkin ya yi...
Wani abu da ya ja hanklan mutane shi ne, irin muggan makaman da ‘yan bindigar suka hallara da su a wajen kulla yarjejeniyar, wadanda kuma babu wani mahaluki da ke da ikon kwace makaman daga hannunsu, a yayin kulla yarjejeniyar, ta jeka nayi ka. Kazalika, a cikin daya daga cikin faifan Bidiyon, an ga yadda daya daga cikin shuwagabannin ‘yan bindigar ya yi bazaranar shedawa gwamnati da sauran jami’an gwamnatin da suka halarci wajen kulla sulhun cewa, idan har gwamnati ta kuskura ta kashe ‘yan bindiga dubu goma, suma za su hallaka adadin mutane kamar hakan. Wasu ‘yan Nijeriya dai, sun yi ittifakin cewa, kasar nan, ta koma tamkar, a hanun tafin ‘yan bindigar. Kulla wannan yarjeniyra dai, ta nuna...
Mazauna unguwar Sabon Gero, dake bayan Millennium City a Karamar Hukumar Chikun ta Jihar Kaduna, sun roƙi gwamnatin jihar da ta gaggauta kammala aikin gyaran titin unguwar, wanda suka ce an bar shi a cikin mawuyacin hali duk da cewa an bai wa wani kamfani aikin kusan shekara guda da ta gabata. Mazauna yankin sun bayyana cewa halin da hanyar take ciki ya jefa su cikin matsanancin rayuwa, musamman mata masu juna biyu da ke tilasta musu hawa babura domin neman kulawa a wajen unguwar, kasancewar babu asibiti a yankin. Ɗaya daga cikin mazauna, Rashida Shehu, wadda ke da juna biyu, ta ce ta ji rauni a lokacin da take kokarin bin hanyar zuwa gari domin kula...
Kwara ta bukaci a sanya ido sosai, yayin da jami’an tsaro ke kara kai hare-hare a maboyar masu garkuwa da mutane
Gwamnatin jihar Kwara ta shawarci al’ummar da ke kewayen kananan hukumomin Ekiti, Ifelodun, Isin, Oke Ero, da Irepodun, da su yi taka-tsan-tsan tare da takaita harkokin a wuraren da sojoji ke aikin musamman. A wata sanarwa da kwamishinan yada labaran jihar, Bolanle Olukoju ya fitar t cea shawarar ta biyo bayan tsaurara matakan tsaro da hadin gwiwar jami’an tsaro suka yi a garuruwan Kogi da Kwara, inda ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane sun yi garkuwa da su. “Muna kira ga jama’a da su yi taka-tsan-tsan tare da takaita zirga-zirgar ababen da suka dace kawai, wato don gudun kada a kama su ba tare da saninsu ba, yayin da masu garkuwa da mutane ke tserewa maboyarsu, ba...