Gwamnan Taraba ya shiryawa gwamnonin Arewa Maso Gabas liyafa
Published: 30th, August 2025 GMT
Gwamnan Jihar Taraba, Dokta Agbu Kefas, ya shirya wa Gwamnonin yankin Arewa maso Gabas inda ya shirya musu ƙasaitaccen biki da liyafar dare a Jalingo, a gabanin taron gwamnonin da za a gudanar yau Asabar.
An gudanar da liyafar ne a daren Juma’a a babban ɗakin fadar gwamnati, inda aka nuna raye raye na al’adu daga kungiyoyin gargajiya na Taraba da sauran jihohin yankin.
A jawabinsa, Gwamna Kefas ya bayyana cewa haɗin kan Arewa maso Gabas na da matuƙar muhimmanci wajen shawo kan matsalolin tsaro, talauci da rashin ingantattun ababen more rayuwa.
Ya kafa da cewa taron gwamnonin na bayar da dama ta musamman don tsara manufofi da inganta zaman lafiya da ci gaban yankin.
Editan BBC Hausa ya magantu kan zargin musguna wa ma’aikciya 2027: ’Yan Najeriya suna fama da yunwa, sun san abin da za su yi — KwankwasoA cewar sanarwar da mai magana da yawun fadar gwamnatin Gombe, Isma’ila Uba Misilli ya fitar, Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya nanata kudirin gwamnonin na yin aiki tare domin ci gaban Arewa maso Gabas baki ɗaya.
Shugaban taron, Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya jinjinawa Gwamna Kefas bisa shirya wannan liyafa, yana mai cewa baje kolin al’adu da zumunci za su ƙara karfafa haɗin kai da fahimtar juna tsakanin jihohin yankin.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Gombe ta saurari ra’ayoyin jama’a kan kasafin kuɗin 2026
Gwamnatin Jihar Gombe ta ƙaddamar da taron sauraron ra’ayoyi jama’a kan shirye-shiryen tsara kasafin kuɗin shekarar 2026 a wani yunƙuri na jaddada ƙudirinta na gudanar da mulki cikin gaskiya da haɗin kai.
Da yake jawabi a wajen taron, Mataimakin Gwamnan Jihar, Dakta Manassah Daniel Jatau, ya bayyana cewa wannan mataki na nuna jajircewar Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya wajen tabbatar da cewa ra’ayoyin jama’a na taka muhimmiyar rawa a tsara kasafin kuɗi da aiwatar da shi.
Za a rataye wanda ya kashe ɗan uwansa a Ekiti Gobara ta tashi a babban kanti a AbujaYa ce tattaunawar ta bai wa gwamnati damar haɗa kai da sarakunan gargajiya, mata, matasa, ƙungiyoyin farar hula da sauran masu ruwa da tsaki, domin bayar da shawarwari kan muhimman fannoni kamar ilimi, lafiya, noma da gine-gine, da za su amfanar da al’umma baki ɗaya.
Dakta Jatau ya ƙara da cewa gwamnatin jihar ta samu ci gaba wajen alkinta kuɗaɗe cikin tsari da gaskiya, wanda hakan ya sa Gombe ke samun matsayi mai kyau a ɓangaren ingantaccen gudanar da kuɗi da sauƙin kasuwanci a Najeriya.
“Kasafin kuɗin 2026 zai mai da hankali ne kan ci gaba da ayyukan da ake yi, tare da ƙara zuba jari a muhimman fannoni, da tabbatar da daidaito da manufofin ci gaban ƙasa da na duniya,” in ji shi.
A nasa ɓangaren, Kwamishinan Kasafi da Tsare-Tsaren Tattalin Arziki, Alhaji Salihu Baba Alkali, ya bayyana taron a matsayin wata hanya ta buɗe ƙofa tsakanin gwamnati da jama’a domin samun fahimta da amincewa.
Ya buƙaci mahalarta taron da su bayar da shawarwari masu amfani da za su taimaka wajen samar da kasafin kuɗin da zai kasance mai ɗorewa kuma mai amfani ga kowa da kowa.
Kwamishinan ya kuma gode wa mahalartan bisa yadda suka bayar da gudunmawa, yana mai tabbatar da cewa za a yi la’akari da shawarwarinsu a cikin tsarin ƙarshe na kasafin kuɗin jihar.