A shekara 2 Gwamnatin Tinubu ta ware wa Legas ayyukan N3.9trn
Published: 30th, August 2025 GMT
Jihar Legas, mahaifar Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ta samu ayyukan gwamnati da darajarsu ta kai Naira Turkiya 3.9 a cikin shekaru biyu na gwamnatinsa.
Ayyukan da gwamnatin ta ba wa Jihar Legas ya zarce jimillar abin da aka ware wa jihohin Arewa maso Gabas, Arewa maso Yamma da Kudu maso Gabas baki ɗaya, waɗanda suka haɗa da jihohi 18.
Rahoton binciken da wakilanmu suka gudanar ya bayyana cewa cikin shekaru biyu da suka gabata, Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) ta amince da ayyuka da darajarsu ta kai naira tiriliyan 3.9 a jihar Legas.
A cewar rahoton, cikin lokaci guda, FEC, wadda Shugaban Ƙasar ke jagoranta, ta amince da ayyuka da darajarsu ta kai naira tiriliyan 5.97 ga Kudu maso Yamma, tiriliyan 2.41 ga Kudu maso Kudu, biliyan 407.49 ga Kudu maso Gabas, tiriliyan 1.15 ga Arewa ta Tsakiya (da Abuja), tiriliyan 2.7 ga Arewa maso Yamma, da biliyan 403.98 ga Arewa maso Gabas.
Gwamnan Taraba ya shiryawa gwamnonin Arewa Maso Gabas liyafa Yadda jami’an tsaro suka kashe ’yan ta’adda a musayar wuta 50 a NejaHaka kuma an ware naira tiriliyan 2.70 don manyan hanyoyi da za su ratsa yankuna daban-daban, ba tare da bayani kan takamaiman kuɗin kowanne ba. Wannan ya sa jimillar ayyukan da FEC ta amince da su ta kai Naira Turkiya 15.79.
Minista ya kare Shugaba TinubuWasu ƙungiyoyin da ke kafofin sada zumunta da kuma Kungiyar Kare Muradun Arewa (ACF) sun ta da ƙarar cewa Gwamnatin Tinubu ta fi bayar da filin ayyuka ga yankin Kudu, musamman mahaifasrsa Jihar Legas.
Sai dai Ministan Watsa Labarai, Mohammed Idris, ya ce ba haka lamarin yake ba. “Rarraba ayyuka a ƙarƙashin Shugaba Bola Ahmed Tinubu yana gudana bisa adalci ga dukkan jihohi. Babu wani yanki da aka ba wa fifiko fiye da wani,” in ji shi.
Ya ce gwamnatin ta kuma samar da kuɗaɗen gine-gine na layin dogo na Naira biliyan 150 a Jihar Kano da kuma biliyan 100 a Jihar Kaduna, kana aka ware Naira biliyan 712 don sabunta tashar jiragen sama ta Murtala Muhammed a Legas.
Manyan ayyukan da aka ware wa LegasKuɗaɗe da kuma ayyukan da gwamnatin Tinubu ta ware wa Jihar Legas a shekara biyu da suka gabata sun haɗa da:
– Naira tiriliyan 1.6: Domin gina titin Legas–Kalaba mai tsawon kilomita 55.
– Naira biliyan 712: Domin Sabunta Tashar Jirgin Sama ta Murtala Muhammed.
– Naira biliyan 359: Na gina gadoji da gyaran hanyar Carter Bridges.
– Naira biliyan 176.49: Domin gyaran bakin teku a Ebute-Ero/Marina.
– Naira biliyan 49.9: Katangar tsaro da kuma na’urorin CCTV a filin jirgin Legas.
Akwai kuma ayyuka da dama a sauran jihohin Kudu maso Yamma, ciki har da Ogun, Ekiti da Ondo, waɗanda darajarsu ta kai tiriliyan 1.65 da sauran biliyoyi da dama.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Arewa ayyuka da darajarsu ta kai Naira tiriliyan Naira biliyan ta kai Naira Jihar Legas
এছাড়াও পড়ুন:
Fadar Shugaban Ƙasa Ta Mayar Wa Atiku Martani Kan Cewar ‘Yan Nijeriya Na Fama Da Yunwa
Ya ce kuma kayan da ake fitarwa zuwa waje waɗanda ba man fetur yanzu su kusa yin kai da kai da fetur.
Ya ƙara da cewa ajiyar kuɗaɗen ƙasar a waje ya haura kusan dala biliyan 42, daga biliyan 32 lokacin da Tinubu ya hau mulki.
Har ila yau, ya ce an biya bashin da ya haura biliyan bakwai, ciki har da miliyan 800 da ake bin jiragen saman Nijeriya.
Fadar Shugaban Ƙasa ta ce yanzu jihohi na iya biyan albashi da fansho a kan lokaci, sannan suna da rarar kuɗi don ayyukan raya ƙasa, abin da ba a saba gani ba a baya.
“Bayan shekara biyu da watanni biyar kacal a ofis, Shugaba Tinubu ya cimma abubuwa da dama. Ko da Atiku da magoya bayansa ba su yadda ba, ’yan Nijeriya suna ganin sauyin,” in ji Onanuga.
Fadar Shugaban Ƙasa ta kuma zargi Atiku da jam’iyyar PDP da yaɗa maganganun da za su kawo tashin hankali.
Ya bayyana cewa yawancin matsalolin da ake fuskanta sun samo asali ne daga rashin kyakkyawan shugabanci tun a lokacin PDP, lokacin da Atiku yake mataimakin shugaban ƙasa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp