Ƴan Siyasar Arewa Na Rigima Da Juna, Tinubu Na Murna — Jibrin
Published: 4th, September 2025 GMT
Ɗan majalisar wakilai, Abdulmumin Jibrin, ya ce Shugaba Bola Tinubu ba ya damuwa da maganganun ‘yan siyasar Arewa da ke ayyana niyyar ƙalubalantar shi a zaɓen 2027, duba da yadda yankin Arewa ya kasa dunkulewa wuri guda.
Jibrin, wanda ke wakiltar mazaɓar Kiru/Bebeji ta jihar Kano a ƙarƙashin jam’iyyar NNPP, ya bayyana haka a shirin Politics Today na gidan talabijin ɗin Channels a ranar Laraba.
Ya tunatar da yadda tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya samu saɓani da tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo, sakamakon adawar da wasu ƴan Arewa suka yi masa wajen neman ƙarfafa tushen siyasa. Haka kuma ya ambaci tsohon mataimakin shugaban ƙasa Namadi Sambo da mai ci yanzu, Kashim Shettima, da su ma suka taɓa fuskantar irin wannan matsin lamba daga yankin Arewa.
Jibrin ya yi wannan bayani ne a daidai lokacin da shirye-shiryen siyasa suka fara ɗaukar zafi kafin 2027, inda batun rabon mulki (zoning) da neman haɗin kai ke ci gaba da jan hankali a fafutukar neman shugabanci.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Jamus ta shiga sahun ƙasashen da ke neman kawo ƙarshen yaƙin Sudan
Jamus ta shiga sahun ƙasashen duniya da ke kiran a gaggauta tsagaita wuta a yaƙin da ke ci gaba da salwantar rayuka a ƙasar Sudan.
Sama da shekaru biyu ke nan Sudan na fama da yaƙin da ya ɗaiɗaita fararen hula baya ga asarar rayuka.
Rikicin PDP: Tsagin Wike ya dakatar da Damagum Kisan Kiristoci: Za mu kai hari Najeriya — TrumpMinistan Harkokin Wajen Jamus, Johann Wadephul, ya bayyana halin da Sudan ke ciki a matsayin “mummunan bala’i,” yana mai cewa babbar matsalar jinkai ta duniya a yanzu ta tattara ne a Sudan ɗin.
A taron da aka gudanar a Bahrain, ƙasashen Birtaniya da Jordan su ma sun yi magana kan rikicin, suna kiran da a kawo ƙarshen tashin hankalin.
A ƙarshen makon da ya gabata, RSF ta kori rundunar soji daga sansanin ta na ƙarshe a yammacin Darfur.
Rahotanni daga garin El-Fasher sun bayyana cewa ana samun kashe-kashe ba tare da shari’a ba, da fyaɗe da fashi har ma da hare-hare kan ma’aikatan agaji.
Wata Kungiyar Likitoci ta MSF a ranar Asabar ta ce ana fargabar dubban fararen hula sun maƙale sannan suna cikin mummunan haɗari a birnin Al Fasher wanda ya koma hannun dakarun RSF.
Rikicin Sudan ya fara ne a watan Afrilun 2023, bayan taƙaddama ta siyasa tsakanin Janar Abdel Fattah al-Burhan, shugaban sojin ƙasar, da Mohamed Hamdan Dagalo (Hemedti), Kwamandan RSF.
Bayanai sun ce rikicin ya samo asali ne daga saɓani kan yadda za a haɗa rundunar RSF da sojojin ƙasar bayan juyin mulkin 2021 da ya hamɓarar da gwamnatin farar hula.
Tun daga lokacin, yaƙin ya zama wani mummunan bala’i na jin kai, inda Majalisar Ɗinkin Duniya (UN) ta ce fiye da mutane miliyan bakwai sun tsere daga gidajensu, yayin da dubbai ke buƙatar taimakon gaggawa.