HausaTv:
2025-11-02@17:13:04 GMT

Iran: IRGC Sun Kama Ma’aikatan Mosad A Arewa Maso Gabacin Kasar

Published: 30th, August 2025 GMT

Dakarun kare juyin juya halin musulunci a nan Iran sun bada labarin kama ma’aikatan Mosad na HKI a lardin Khorasan Razavi  da ke arewa maso gabacin kasar, wadanda suka taimakawa HKI a kan hare-haren da ta kaiwa kasar na kwanaki 12 a cikin watan Yunin da ya gabata.

Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto sanarwan da dakarun suka bayar a jiya Jumma;a na cewa, bangaren leken asiri na su ya sami nasarar kama wasu mutane 8 a cikin lardin wadanda suke da hannu dumu-dumi a cikin yakin kwanaki 12 a cikin watan Yunin da ya gabata.

Kuma suna aiki kai tsaye da HKI a cikin yakin.

Labarin ya kara da cewa gungun mutanen guda 8 suna aiki aikawa Mosad wurare masu muhimmanci a yankin da kuma gidaje da wuraren manya-manyan dakarin na IRGC a lardun Khurasan radawai.

Banda haka suna shirin kai hare-hare a cikin lardin tare da amfani da abubuwan fashewa da kuma wasu kayakin aikin soje wadanda aka kwace daga hannunsu. Daga karshen labarin ya kammala da cewa, an tabbatar da cewa kungiyar tana aiki kud da kud da kungiyoyi masum adawa da JMI da suke kasashen yamma.  Dakarun na IRGC dai sun yabawa bangaren leken asirin nasu kan wannan kokarin nasu, na tabbatar da zaman lafiya da kuma kare kasar daga makiya daga kasashen waje.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iran Ta Yi Watsi Da Shirin ‘SnapBack’ Na Kasashen Turai August 30, 2025 E3 sun gindaya sharudda 3 kan dakatar da dawo da  takunkuman MDD a kan Iran August 30, 2025 Amurka ta hana izinin shiga kasarta ga shugaban Falastinawa don halartar taron MDD August 30, 2025 Rwanda ta dauki bakin haure kashi na farko da aka kora daga Amurka August 30, 2025 Jami’in Sojin Isra’ila: Masu Tunanin Hizbullah Ta Yi Rauni Suna Mafarki Ne August 30, 2025 Mali: Kungiyar Al-Qaeda ta kwace iko da garin Farabougou da ke tsakiyar kasar August 30, 2025 Mutum Guda Ya Yi Shahada Sanadiyar Harin Isra’ila A Kudancin Lebanon August 29, 2025 Malasiya Ta Bukaci A Kori Isara’ila (HKI) Daga MDD August 29, 2025 Iran: China Ta Zuba Jari A Aikin Samar Da Wutar Lantarki Ta Hasken Rana A Bushar August 29, 2025 MDD Ta Yi Tir Da Dirar Mikiyan Da Jamus Takewa Masu Goyon Bayan Falasdinawa August 29, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Sudan Ta Yi Kira Ga Kwamitin Tsaro Da Ya Ayyana RSF A Matsayin Kungiyar ‘Yan Ta’adda

Sudan ta yi kira ga Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya  da ya sanya rundunar  Rapid Support Forces (RSF) a matsayin kungiyar ‘yan ta’adda bisa ga ka’idojin yaki da ta’addanci na duniya, sannan ya dauki mataki a kan duk wanda ya yi mu’amala da ita, ko ya samar mata da makamai da sojojin haya, ko jiragen sama marasa matuki, ko kuma kasar da ta bar ta ta tsallaka iyakokinta.

A cikin wata sanarwa da ya fitar a lokacin zaman gaggawa na Kwamitin Tsaro don tattauna yanayin da ake ciki a Sudan, Wakilin dindindin na Sudan a Majalisar Dinkin Duniya, Al-Harith Idris, ya bukaci Majalisar da ta yi Allah wadai da kisan kiyashin da ‘yan bindigar RSF, sojojin haya na kasashen waje, da masu goyon bayanta na yankin suka aikata a El Fasher da kuma sauran wurare a cikin Sudan.

Idris ya yi kira ga Kwamitin Tsaro da ya sanya takunkumi mai tsauri ga dukkan kasashe  da daidaikun mutane da Majalisar ta sani wadanda ke bayar da kudi ga  RSF, samar mata da makamai, ko samar mata da mafaka, sannan a fara bincike kan kisan kiyashin da ake yi wa mazauna El Fasher don ci gaba da kokarin daukar mataki. Ya kara da cewa “‘yan bindiga suna yin barazanar kashe mutane a kullum rana ta Allah.”

Wakilin na Sudan ya yi kira da a tabbatar da an aiwatar da kudurorin Majalisar Tsaro na 2736 da 1591, “kamar yadda shaidu a Darfur suka tabbatar da cewa wasu ƙasashe maƙwabta sun shiga cikin kisan fararen hula don tallafawa ‘yan bindiga.”

Bugu da ƙari, Al-Harith ya yi kira da a goyi bayan taswirar da gwamnatin Sudan ta gabatar wa Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, wadda ta dogara ne akan dakatar da yaƙi na dindindin da kuma kwance damarar makamai na ‘yan bindiga, sannan kuma su mika wuya.

Idris ya fayyace cewa ba za a yi tattaunawa da RSF ba har sai sun ajiye makamansu su kuma sun daina kai hari kan al’ummar Sudan.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Araqchi: Gwajin Makaman Nukiliya Na Amurka Babbar Barazana Ce Ga Duniya October 31, 2025 Masar da Eritrea Sun Tattauna Bukatar Tallafawa Kasar Sudan October 31, 2025 Shugaban Lebanon Ya Umarci Sojoji Da Su Fuskanci Kutsen Na Isra’ila A Kudancin Kasar October 31, 2025 Madagascar Ta Sanar da Kafa Sabuwar Gwamnati Tare da Manyan ‘Yan Adawa October 31, 2025 Iran ta yi fatali da kalamman IAEA Kan Shirin Nukiliyarta October 30, 2025 Trump Ya Umarci Ma’aikatar Yakin Amurka Ta koma gwajin makaman nukiliya October 30, 2025 Isra’ila ta amince da fadada matsugunai a Yammacin Kogin Jordan October 30, 2025 Gaza: hare-haren Isra’ila sun kashe mutane 100 Cikin Kwanaki Biyu October 30, 2025 Sudan : Kasashen duniya na tir da cin zarafi a El-Fasher October 30, 2025 Iran Ta Jaddada Bin Hanyar Diflomasiya Ko Da A Lokacin Yaki Ne Amma Ba Zata Amince Da Bin Umarni Ba October 30, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Araqchi: Da Hadin Bakin Amurka, Gwamnatin Isra’ila ta kaddamar Da Hari Kan Kasar Iran
  • Kasar Qatar Ta Ba Da Tallafin Gaggawa Ga Al’ummar Sudan Bayan Gumurzun El-Fasher
  • Wasu Yan Ta’adda Sun Kashe Dakarun Sa Kai 2 A Kudu Maso Gabashin Iran
  • Isra’ila Ta Kashe Mutane 4 Tare Da Jikkata Wasu Guda 3 A Kudancin Labanon
  • Iran Ta Gargadi Isra’ila Kuma Tasha Alwashin Kare Shirinta Na Nukiliya
  • Iran ta damu da halin da ake ciki a yankin El Fasher na Sudan
  • Iran Ta Sanya  Da Ranar 30 Ga Watan Nuwamba A Matsayin Ranar Kasa Ta Tsibirai 3
  • Sudan Ta Yi Kira Ga Kwamitin Tsaro Da Ya Ayyana RSF A Matsayin Kungiyar ‘Yan Ta’adda
  • Gaza: hare-haren Isra’ila sun kashe mutane 100 Cikin Kwanaki Biyu
  • Sudan : Kasashen duniya na Allah wadai da cin zarafi a lokacin kama El-Fasher