Yadda ’yan Arewa suka yi Maulidin bana a Ibadan
Published: 7th, September 2025 GMT
Ƙungiyoyin Musulmi maza da mata da ƙananan yara daga sassa daban-daban na Jihar Oyo sun gudanar da bukukuwan zagayowar ranar haihuwar fiyayyen halitta, Manzon Allah Annabi Muhammad (SAW), na bana (shekara ta 1447 bayan hijira).
Aminiya ta ruwaito cewa an fara gudanar da bukukuwan ne a ranar Asabar daga harabar babban Masallacin Unguwar Sabo, mazaunin Hausawa a Ibadan, babban birnin Jihar Oyo.
Khalifofin mazhabobin Darikun Tijjaniyya da Ƙadiriyya a Ibadan su ne suka jagoranci manyan malaman addinin Musulunci tare da dimbin mabiya wajen yin tattaki na tsawon kilomita 10 da ya zagaya wasu sassan birnin domin nuna farin ciki da murnar wannan rana.
An ga ƙungiyoyin Musulmi daban-daban masu halartar zagayen Maulidi sanye da sutura iri ɗaya (amko) suna rera zikiri da ambaton sunayen Ubangiji (TWT), da salatin Annabi Muhammad (SAW), tare da wako6kin yabon sa. Aminiya ta ce kamar yadda aka saba a duk shekara, a bana ma an gudanar da wannan zagaye cikin tsauraran matakan tsaro.
Boko Haram sun kashe gomman mutane da sojoji a ƙauyen Borno Mauludi: Ƙungiyoyin addini sun nemi gwamnati ta sassauta dokar hana hawa babur a GombeAttajiran Musulmi ’yan Arewa da masu hali sun tallafa da dukiyoyinsu wajen karfafa guiwar gudanar da wannan biki da al’ummar Musulmi ke yi duk shekara. Haka kuma, Aminiya ta gano cewa iyaye masu hali sun gwangwaje iyalansu da naman dabbobi, kaji da talo-talo, suna dafa nau’ukan abinci iri-iri domin ci a gidajensu da kuma rabawa makwabta da sauran jama’a don nuna farin cikinsu da zagayowar ranar haihuwar Annabi Muhammadu (SAW).
Tun kafin wannan rana, manyan malaman Darikun Tijjaniyya da Ƙadiriyya sun jagoranci mabiyansu zuwa masallatai daban-daban a Unguwar Sabo, inda suka shafe dare-daren watan Rabi’u Awwal suna yin wa’azi kan tarihin fiyayyen halitta, matsayin sa da girmansa, tare da jaddada bukatar Musulmi su yi koyi da halayensa domin samun tsira a duniya da lahira, kamar yadda Ubangiji (TWT) ya umarta.
Gwamnonin jihohin Kudu maso Yamma, Sanatoci, masu fada a ji da Sarakuna sun aike da sakonnin taya murna ga al’ummar Musulmi. A cikin sakonninsu sun jaddada bukatar yin koyi da kyawawan halayen Annabi Muhammad (SAW) wajen gudanar da rayuwa. Haka kuma sun yi kira ga Musulmi su yi amfani da wannan dama wajen yi wa Najeriya addu’ar samun zaman lafiya da kwanciyar hankali baki ɗaya.
Ends
Kana so in rage tsawon labarin zuwa sigar takaitacciya (ƙasa da rabin wannan tsawon) domin ya dace da salo irin na Aminiya, ko ka fi so a bar shi cikakke haka?
Na duba rubutun, na yi gyare-gyare kadan don inganta tsari, daidaita nahawu da rage maimaitawa ba tare da canza ma’anar labarin ba. Ga sigar da aka gyara:
—
Dubban Musulmi ‘Yan Arewa Sun Yi Maulidin Bana a Ibadan
Daga Kabir Yayo Ali, Ibadan
Kungiyoyin Musulmi maza da mata da kananan yara daga sassa daban-daban na Jihar Oyo sun gudanar da bukukuwan zagayowar ranar haihuwar fiyayyen halitta, Manzon Allah Annabi Muhammad (SAW), na bana (shekara ta 1447 bayan hijira).
Aminiya ta ruwaito cewa an fara gudanar da bukukuwan ne a yau Asabar daga harabar babban Masallacin Unguwar Sabo, mazaunin Hausawa a Ibadan, babban birnin Jihar Oyo.
Khalifofin mazhabobin Darikun Tijjaniyya da Qadiriyya a Ibadan su ne suka jagoranci manyan malaman addinin Musulunci tare da dimbin mabiya wajen yin tattaki na tsawon kilomita 10 da ya zagaya wasu sassan birnin domin nuna farin ciki da murnar wannan rana.
An ga kungiyoyin Musulmi daban-daban masu halartar zagayen Maulidi sanye da sutura iri ɗaya (amko) suna rera zikiri da ambaton sunayen Ubangiji (TWT), da salatin Annabi Muhammad (SAW), tare da wakokin yabonsa. Aminiya ta ce kamar yadda aka saba a duk shekara, a bana ma an gudanar da wannan zagaye cikin tsauraran matakan tsaro.
Attajiran Musulmi ’yan Arewa da masu hali sun tallafa da dukiyoyinsu wajen karfafa guiwar gudanar da wannan biki da al’ummar Musulmi ke yi duk shekara. Haka kuma, Aminiya ta gano cewa iyaye masu hali sun gwangwaje iyalansu da naman dabbobi, kaji da talo-talo, suna dafa nau’ukan abinci iri-iri domin ci a gidajensu da kuma rabawa makwabta da sauran jama’a don nuna farin cikinsu da zagayowar ranar haihuwar Annabi Muhammadu (SAW).
Tun kafin wannan rana, manyan malaman Darikun Tijjaniyya da Qadiriyya sun jagoranci mabiyansu zuwa masallatai daban-daban a Unguwar Sabo, inda suka shafe dare-daren watan Rabi’u Awwal suna yin wa’azi kan tarihin fiyayyen halitta, matsayin sa da girmansa, tare da jaddada bukatar Musulmi su yi koyi da halayensa domin samun tsira a duniya da lahira, kamar yadda Ubangiji (TWT) ya umarta.
Gwamnonin jihohin Kudu maso Yamma, Sanatoci, masu fada a ji da Sarakuna sun aike da sakonnin taya murna ga al’ummar Musulmi. A cikin sakonninsu sun jaddada bukatar yin koyi da kyawawan halayen Annabi Muhammad (SAW) wajen gudanar da rayuwa. Haka kuma sun yi kira ga Musulmi su yi amfani da wannan dama wajen yi wa Najeriya addu’ar samun zaman lafiya da kwanciyar hankali baki ɗaya.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Fiyayyen Halitta Kadiriyya Tijjaniya zagayowar ranar haihuwar Darikun Tijjaniyya da gudanar da bukukuwan gudanar da wannan al ummar Musulmi jaddada bukatar manyan malaman Unguwar Sabo kamar yadda wannan rana duk shekara
এছাড়াও পড়ুন:
Arewa Ba Zata Ƙarɓi Mulki A 2027 Ba, Gwamna Bago
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp