2025-09-17@23:23:17 GMT
إجمالي نتائج البحث: 9010
«cutar Ebola»:
(اخبار جدید در صفحه یک)
Shugaban kasar China Xi Jinping ya bayyana cewa kungiyar BRICS zata ci gaba da ayyukanta duk tare da matsalolin da take fuskanta. Tashar talabijin ta Al-mayadeen ta kasar Lebanon ta nakalto shugaban yana fadar haka a taron kungiyar ta BRICS ta hotunan yanar gizo da aka gudanar a yau litinin. Ya kuma kara jaddada cewa kungiyar da sannu zata wuce wadan nan matsalolin da suke gabatan a halin yanzu, sannan ta ci gaba girma da daukaka. Yace a cikin wuta ne ake gane zinari na gaskiya, don haka matsalolin da suke gabar kungiyar BRICS ne zasu fayyace irin karfin da kungiyar take da shi na fuskantar matsaloli, sannan ta ci gaba girma har zuwa lokacinda zata cimma manufar kafata. Shugaban...
Kasar China ta yi nasarar samun yardar hukumomin kasar Kamaru na gina titi na harkokin kasuwanci tsakanin kasar da Chadi har’ila yau da kasashen makobta a kasashen tsakiyar Afirka zasu amfana da titin.. Tashar talabijan ta almayadeen ta kasar Labanon ta bayyana cewa, nesa da yadda kasashen Afirka suka saba na kulla irin wannan kontragi mai tsoka, a wannan karon kasashen Afirka suna samun karfin tsallaka wadan nan manya-manyan kasashen da suka saba danne su, zuwa ga abinda suka ga zai fi amfanarsu. Wani kamfanin gine-gine na kasar China ya samu nasar samun kontragin gina wani babban titin wanda zai taso daga Duala na kasar Kamaru zuwa Njamena babban birnin kasar Chadi. Wanda masana suna ganin samun wannan titin zai...
Kamfanin Aero Engine Corporation na kasar Sin, ya fitar da sabon injin aiki a manyan na’urori mai aiki da iskar gas mai karfin gaske, wanda ke iya samar da karfin megawatt 110. Kamfanin ya fayyace sashen kirar injin mai suna Taihang 110, a yankin kira na kamfanin a Litinin din nan, kuma ana fatan fara shigar da injin kasuwa. Fitar da injin zuwa kasuwanni na nufin kasar Sin ta cimma nasarar gabatar da inji kirar gida mai matukar karfi, wanda manyan na’urori za su rika amfani da shi ta hanyar sarrafa iskar gas. (Mai fassara: Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku....
Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi Allah-wadai da harin da ’yan ta’adda suka kai a garin Darul Jamal, da ke yankin Bama na Jihar Borno. Harin wanda ya faru a yammacin ranar Juma’a 5 ga watan Satumba ya yi sanadin mutuwar mutum sama da 60 tare da sace wasu da dama ciki har da sojoji da fararen hula. A wata sanarwa da Mohamed Malick Fall, babban jami’i mai kula da ayyukan jinƙai na Majalisar Dinkin Duniya a Najeriya ya fitar, ya bayyana matukar bakin cikinsa kan lamarin. MDD ta yi kira ga hukumomin Najeriya da su gano waɗanda suka kai wannan harin tare da ɗaukar mataki a kansu. Fall ya ce: “Ina kira ga hukumomin tsaro da su kamo waɗanda suka...

Jarin Da Sin Ta Zuba Kai Tsaye A Kasashe Cikin Shawarar Ziri Daya Da Hanya Daya Ya Karu Da Kashi 22.9% A 2024
A yau Litinin, wasu rahotanni na cewa, yayin wani taron manema labaru na musamman kan zuba jari ga sassan ketare da aka gudanar a taron tattauna harkokin cinikayya da zuba jari na kasa da kasa na Sin karo na 25, cewa a shekarar 2024 adadin jarin da kasar Sin ta zuba kai tsaye a kasashen da suka shiga shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya” ya kai dalar Amurka biliyan 50.99, adadin da ya karu da kashi 22.9 bisa dari idan aka kwatanta da makamancin lokaci na shekarar 2023. A dai yau din, ma’aikatar kasuwanci ta kasar Sin, da hukumar kididdiga ta kasar, da hukumar kula da musayar kudin waje ta kasar, sun fitar da sanarwar “kididdiga ta shekarar 2024 kan...
Wasu alkaluma da ma’aikatar masana’antu da fasahar sadarwa ta kasar Sin ta fitar, sun nuna yadda adadin kamfanonin fasahar AI da aka yiwa rajista a kasar Sin suka kai sama da 5000, adadin da ya karu matuka kan sama da 1,400 da kasar ke da su a shekaru biyar da suka gabata. An fitar da alkaluman ne yayin taron kasa da kasa na baje kolin hajoji masu nasaba da na’urori masu basira, wanda ke gudana yanzu haka a birnin Chongqing na kudu maso yammacin kasar Sin. Da yake tabbatar da hakan, mataimakin ministan ma’aikatar Xin Guobin, ya ce an kafa masana’antu masu aiki da na’urori masu basira sama da 40,000 a kasar Sin, da yankunan gwaji na kirkire-kirkiren AI da...
Ya bayyana karya ka’idojin da aka shimfiɗa kan amso basussukan a matsayin “babban abin damuwa da fargaba kan ɗorewar tattalin arzikin kasar,” yana mai jaddada cewa, akwai buƙatar samar da “sabbin tsaruka masu ƙarfi, da za su daidaita hanyoyin karɓar rance na gaskiya, da kuma ƙuduri na bai ɗaya don tabbatar da cewa, duk kuɗin da aka karɓo ya dace da buƙatar shirin inganta zamantakewar ‘yar Nijeriya”. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Yarima Harry wanda ya koma rayuwa a Jihar California ta Amurka, ya ziyarci kabarin mahaifiyarsa, Sarauniya Elizabeth II, a fadar Windsor da ke yammacin birnin Landan a ranar Litinin. Shekaru uku ke nan daidai da rasuwar Sarauniya Elizabeth II wadda ta riga mu gidan gaskiya a ranar 8 ga Satumba, 2022, kuma aka binne ta a cikin cocin St. George’s Chapel da ke fadar Windsor. An fara samun masu zawarcin kujerar Firaministan Japan Matatar Dangote ta musanta dakatar da aiki Mai magana da yawunsa ya tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa Harry ya kai ziyara shi kaɗai domin girmama mahaifiyarsa. A halin yanzu dai abin tambayar shi ne ko Yarima Harry zai gana da mahaifinsa, Sarki Charles III,...
“Don haka, Ma’aikatar Yaɗa Labarai tana aiki kafada da kafada da Ma’aikatar Harkokin Ƙananan Hukumomi, Hukumar Harkokin Addinai, tare da haɗin gwiwar manyan shugabannin gargajiya da na addini, domin tabbatar da cewa wayar da kai da kuma tura saƙon rajista ya isa kowace mazaba, ƙauye, da unguwa a fadin Jihar Kaduna,” in ji Maiyaki. Kwamishinan ya ƙara da cewa jagorancin Gwamnan na bai wa haɗin kan al’umma muhimmanci a matsayin ginshikin shugabanci na dimokuraɗiyya. “Wannan ƙoƙarin wayar da kai yana nuna hangen nesa na Gwamna na gudanar da mulki mai maida hankali kan bukatun jama’a, inda kowace murya ke da muhimmanci, kuma kowane ɗan ƙasa yana da rawar da zai taka wajen gina makomar Jihar Kaduna. “...
Matatar mai ta Dangote ta ƙaryata rahoton da ke cewa za ta iya dakatar da ayyukanta na sarrafa ɗanyen mai har nan da tsawon watanni biyu zuwa uku. Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rukunin kamfanin na Dangote, Anthony Chiejina ya fitar, inda ya bayyana rahoton a matsayin “tsantsar ƙarya” wadda ba ta da tushe balle makama. Sojoji sun kashe kasurgumin dan ta’adda da yaransa 5 a Kogi An fara samun masu zawarcin kujerar Firaministan Japan A wani rahoto da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya fitar, ya bayyana cewa, ‘‘akwai yiwuwar rufe sashen matatar man kamfanin wadda ke samar da ganga 650,000 duk rana tsawon watanni biyu zuwa uku saboda aiwatar da wasu gyare-gyare,...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Hukumar tsaron DSS a Najeriya ta aike da wasika ga dandalin sada zumunta na X, wanda ake kira Twitter a da, inda a ciki ta ke bukatar ya sauke shafin dan gwagwarmaya din nan, Omoyele Sowore ko kuma ya fuskanci mataki mai tsanani . A wasikar da hukumar ta DSS ta wallafa a shafinta na X a safiyar wannan Lahadi, ta zargi Sowore da amfani da dandalin sada zumuntar wajen caccaka da kuma yin kalaman raini ga shugaban kasar Bola Ahmed Tinubu. DSS ta yi ikirarin cewa magoya bayan Tinubu ba su ji daɗin rashin mutuncin da Sowore ya ke yi wa shugaban ba, saboda haka har sun fara zanga-zangaar rashin amincewa da hakan. Lamarin da jawo sabanin siyasa. DSS...
Dakarun sojin Najeriya sun kashe wani kasurgumin dan ta’adda wanda aka fi sani da suna Kachalla Bala da yaransa biyar a Jihar Kogi. Sojojin Birget ta 12 da ke Lakwaja, hedikwatar jihar sun kuma yi nasarar ceto wasu mutanen da gungun ’yan bindigar suka yi garkuwa da su. Mukaddashin kakakin rundunar, Laftanar Hassan Abdullahi ya ce samamen da sojojin ke kaiwa a sassan jihar domin kakkabe ayyukan ’yan binidga yana samun nasara a yankunan Tunga da Aleke da Ungwan Soni da Ungwan Nyaba da kuma Ankomi. Yankin gadar Agbede–Adankoo (Mosalanci Boka) da ke yankunan Lokoja, Kabba-Bunu, da kuma Karamar Hukumar Yagba sun yi iyaka da jihohin Kwara da Neja, wanda hakan ya sa suka zama mafaka ga ayyukan ’yan bindiga....
Tawagar kasar Iran ta maza da mata a wasan wushu a bangaren sanda da taolu ta samu gagarumar nasara inda ta samu lambobin yabo guda guda 10, zinariya 6 Azurfa guda 2 sai kuma tagulla guda 2, a wasan zakarun na washu karo na 17 da aka gudanar a kasar brazil, Gasar Wushu ta duniya ita ce ta farko a gasar da kasar Sin ta mamaye. inda Iran ta samun kambun mataimakiyar zakara ta sha gaban manyan kasashe biyu kamar Malaysia da Hong Kong, ya nuna irin gagarumin sauyi a cikin tsarin wushu na duniya, kuma ya nuna irin kaifin basira da bangarorin biyu suke da shi na maza da mata. Tawagar kasar Iran ta samu lambobin yabo guda 10...
Bayan barazanar da ministan yaki na HKI yayi na yin ruwan bama-bamai kan yankin Gaza wato kai hari kan manyan manyan gine –gine dake yankin , sai gashi kafafen yada labarai na isra’ila sun sanar da wani harin neman shahada da aka kai a birnin Qudus inda yahudawa 5 suka mutu guda 20 kuma suka jikkata Gidajen talabijin na HKI sun sanar da adadin wadanda abin ya shafa sakamakon harin sun bayyana cewa mutane 5 ne suka mutu sai kuma 20 suka yi jikkata, yayin da halin 6 daga cikinsu rai kwakwai mutu kwakwai. Sai dai wannan yana zuwa ne bayan da ministan yaki na HKI Yasrail Katsi yayi barazana ga kungiyar Hamas cewa idan basu mika makamansu ba, kuma...
Sayyid Abbas Araqci ministan harkokin wajen kasar iran a wani sakon mayar da martani da ya aike da shi game da shirun da kasashen turai suka yi kan fadada shirin nukiliyar HKI ya jaddada cewa yin shiru da baki da suka yi ya nuna cewa yanzu basu da wata dama ko kwarin guiwar yin Magana kan hana yaduwar makamin nukiliya kan kowacce kasa . Rahotan ya bayyana cewa Araqchi ya bayyana a shafinsa na x cewa batun samuwa ko fadada shirin makamin nukiliya ba shi ne a gabansu ba, lamarin shi ne waye ya bada dama a samu ci gaban ilimi ko da ma na shirin nukiliya na zaman lafiya ne, Ya jaddada cewa saboda haka wannan ba’a bin mamaki...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Najeriya na iya shiga cikin matsalar ƙarancin man fetur daga yau Litinin, muddin Gwamnatin Tarayya ba ta warware rikicin da ya kunno kai tsakanin Ƙungiyar Direbobin Tankar Mai (PTD) ta ƙarƙashin NUPENG da kamfanin Matatar Mai ta Dangote ba. Direbobin sun sanar da shiga yajin aiki saboda shirin kamfanin Ɗangote na fitar da motoci 4,000 da ke amfani da gas ɗin CNG domin kai mai kai tsaye ga kasuwa ba tare da direbobin da ke ƙarƙashin NUPENG ba. Ƙungiyar ta yi zargin cewa wannan tsari zai rusa ayyukan dubban direbobi, ya hana ’yancin kafa ƙungiya kuma ya haifar da “mulkin danniya” a harkar rarraba man fetur. Gwamnati ta shiga tsakani Ministan Ƙwadago da Ayyuka, Muhammad Maigari Ɗingyadi, ya tabbatar a...
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya jaddada yin kira ga al’ummar Musulmi cewa: Wajibi ne kasashen musulmi su yanke alakarsu da ‘yan sahayoniyya Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya jaddada cewa: Dole ne kasashen musulmi su yanke duk wata huldar kasuwanci da siyasa da gwamnatin ‘yan sahayoniyya azzaluma tare da mayar da ita saniyar ware. Jagoran juyin juya halin Musulunci ya jaddada cewa: Dole ne a fuskanci bala’o’in da muguwar gwamnatin ‘yan sahayoniyya ta haifar a Gaza. Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya yi tsokaci kan mummunan halin da ake ciki a zirin Gaza inda ya ce: Dole ne kasashen da suke gudanar da zanga-zangar a yau musamman kasashen musulmi su yanke duk wata huldar kasuwanci...
Shugaban kasar Iran ya jaddada cewa: Jami’an kasar suna kiyaye shawarwarin Jagoran juyin juya halin Musulunci Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada cewa: Jami’an zartaswa na kasar suna kiyaye shawarwari da umarnin Jagoran juyin juya halin Musulunci a Iran. Shugaba Pezeshkian ya rubuta a shafinsa na yanar gizo a shafin sada zumunta na X cewa: Jami’an zartaswa na kasar suna kiyaye shawarwari da umarnin Jagoran juyin juya halin Musulunci yayin ganawarsa a jiya (Lahadi) da wakilan gwamnati. Ya kara da cewa: Da yardar Allah za a shawo kan matsaloli tare da hadin kan kasa da gwiwar al’umma da taimakon al’umma da kuma saukakawa Jagoran juyin juya halin Musulunci. Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new...
Mataimakin kwamandan rundunar sojin kasar Iran mai kula da harkokin tsaro kasar ya bayyana cewa: Jami’an tsaron Iran suna cikin shirin ko ta kwana Mataimakin kwamandan rundunar sojin kasar Iran mai kula da harkokin tsaron kasar Admiral Habibullah Sayyari ya jaddada cewa: Dakarun kasar da suka hada da sojoji da dakarun kare juyin juya halin Musulunci, da sauran rundunoni sun shirya tsaf domin tunkarar duk wata barazana ta ciki gida da waje da kuma tabbatar da ‘yancin kai da tsaron kasar. Admiral Habibullah Sayyari wanda ya yi jawabi a ranar Asabar a birnin Rasht fadar mulkin lardin Gilan a wajen taro na biyu na tunawa da shahidai dubu 8 daga wannan lardin, ya yi ishara da yakin baya-bayan nan da...
Kungiyar Hamas ta jaddada cewa: Tana maraba da duk wani yunkuri da zai taimaka a fagen dakatar da ta’addanci kan al’ummar Falasdinu Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta jaddada hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a yammacin jiya Lahadin da ta gabata cewa, tana maraba da duk wani yunkuri da zai taimaka a fagen yunkurin da ake yi na dakatar da kai hare-hare kan al’ummar Falasdinu, tana mai bayanin cewa ta samu wasu ra’ayoyi daga bangaren Amurka ta hanyar masu shiga tsakani don cimma matsaya. A cikin wata sanarwa da kungiyar ta Hamas ta fitar ta ce: “Ta samu wasu ra’ayoyi daga bangaren Amurka ta hanyar masu shiga tsakani don cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta. A wannan...
Rundunar sojin Yeme ta sanar da kai hare-hare guda 8 da jirage sama marasa matuka ciki kan muhimman wurare a Isra’ila Dakarun sojin Yemen sun sanar da yammacin jiya cewa, sun kai wasu manya-manyan farmakin soji ta hanyar amfani da jiragen saman yaki marasa matuka ciki guda takwas a kan wasu wurare da dama a yankunan Falasdinawa da aka mamaye. An kai hare-haren ne kan filin jirgin saman Ramon da muhimman wurare da na sojoji da suka hada da Negev, Umm al-Rashrash, Ashkelon, Ashdod, da Jaffa. Domin jaddada goyon baya ga al’ummar Falastinu da ake zalunta da ‘yan gwagwarmayarsu masoya, da kuma mayar da martani kan laifukan kisan kiyashi da kakaba yunwa da makiya yahudawan sahayoniyya suke aikatawa kan ‘yan...
Yayin da makarantu a fadin Najeriya ke dawowa sabuwar zangon karatu ta shekarar 2025/2026 a yau Litinin, iyaye sun koka kan mummunar ƙalubalen tattalin arziki da ke hana su samun sauƙin biyan kuɗin makaranta da sauran kayayyakin karatu. Rahotanni daga jihohi daban-daban sun nuna yadda tsadar rayuwa da hauhawar farashin kaya suka zame wa iyaye da ɗalibai babban cikas, inda wasu ke neman rance domin ganin ’ya’yansu ba su zauna a gida ba. Kukan Iyaye A hirarraki da aka yi da iyaye da dama, sun bayyana cewa duk zangon karatu yanzu yana zama tamkar shiga jana’iza, inda suke binne albarkatunku da nutsuwarsu da farin cikin gida. Misis Victoria Edem, uwa ce mai yara uku daga garin Kalaba a Jihar Kuros...
A cewar ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, bisa gayyatar da shugaban kasar Brazil Luiz Inácio Lula da Silva ya yi masa, shugaban kasar Sin Xi Jinping zai halarci taron koli na shugabannin kasashen kungiyar BRICS da za a yi ta kafar bidiyo, daga nan birnin Beijing a gobe Litinin, tare da gabatar da muhimmin jawabi.(Safiyah Ma) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Jimilar kudin asusun ajiya na kasar Sin a ketare ya kai dala triliyan 3.3222 zuwa karshen watan Agusta, inda ya karu da dala biliyan 29.9 ko kaso 0.91, idan aka kwatanta da na karshen watan Yuli. Hukumar kula da musayar kudi ta kasar Sin ta alakanta karuwar da tasirin sauyin kudi da sauyin farashin kadarori. Ta kara da cewa, tattalin arzikin kasar Sin na ci gaba da habaka yadda ya kamata, cike da juriya da kuzari, da samar da goyon bayan mai karfi ga asusun ajiyar kasar na ketare. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp...
Aƙalla mutum bakwai ne suka rasa rayukansu, yayin da wasu 11 suka jikkata a wani sabon hari da ’yan bindiga suka kai ƙauyen Wake da ke gundumar Agunu, a Ƙaramar Hukumar Kachia ta Jihar Kaduna. Hari ya faru ne da misalin ƙarfe 5:55 na safiyar ranar Lahadi, lokacin da ’yan bindigar suka mamaye garin, inda suka yi ta harbe-harbe. Harin Borno: Dole ’yan Najeriya su haɗa kai su fuskanci Boko Haram — Atiku Ambaliyar Ruwa: NEMA ta ceto mata 2 da jaririya a Kaduna Har ila yau, sun yi garkuwa da wasu mazauna garin, duk da cewa har yanzu ba a tantance adadinsu ba. Waɗanda suka rasu a harin sun haɗa da: Elisha Paul, Japhet Bitrus, Obadiah Joshua, Luka Augustine,...
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya yi Allah-wadai da sabon harin da Boko Haram suka kai a Jihar Borno, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane da dama; ciki har da sojoji. Atiku, ya bayyana halin da ’yan Najeriya ke shiga sakamakon hare-haren ta’addanci. Ambaliyar Ruwa: NEMA ta ceto mata 2 da jaririya a Kaduna Harin Boko Haram: Zulum ya kai ziyarar jaje garin Darajamal A cikin saƙon da ya wallafa a shafukansa na sada zumunta, Atiku ya yi kira ga ’yan Najeriya da su haɗa kai wajen yaƙi da matsalar tsaro ta hanyar haɗin kan al’umma. Ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu, jama’ar Jihar Borno, da kuma Gwamna Babagana Umara Zulum. Ya kuma yaba wa gwamnan...
Ƴan ta’adda sun kai hari a ƙauyen Wake da ke ƙaramar hukumar Kachia, jihar Kaduna, inda suka kashe mutum takwas tare da yin garkuwa da wasu da dama. Bayanan farko sun nuna cewa waɗanda suka samu raunuka a harin an garzaya da su Asibitin Katolika na Saint Gerard domin samun kulawar likitoci. Sulhu Da ‘Yan Bindiga Ya Fara Haifar Da Da Mai Ido A Katsina Gwamnatin Katsina Za Ta Sayo Babura 700 da Motoci 20 Don Samar Da Tsaro Duk da cewa cikakkun bayanai kan lamarin ba su fito fili ba tukunna, majiyoyi sun tabbatar da faruwar harin. Sai dai duk wani yunƙuri na jin ta bakin jami’an ƙaramar hukumar Kachia bai samu nasara ba, domin sun ce za su...
Kasar Sin da Tarayyar Afrika (AU), sun yi alkawarin karfafa goyon bayan juna wajen gina tsarin jagorantar harkokin duniya bisa adalci tare da tabbatar da zaman lafiya a duniya. An yi alkawarin ne a ranar Juma’a yayin wani taron manyan jami’ai a Addis Ababa na Habasha, albarkacin cika shekaru 80 da Sinawa suka yi nasarar turje wa harin Japan da yakin duniya na II. Da yake jawabi ga taron, Jiang Feng, shugaban tawagar kasar Sin a AU, ya nanata bukatar tunawa da tarihi da karfafa hadin gwiwa a duniya domin shawo kan kalubalen tsaro da duniya ke fama da su. Da yake jawabi a madadin kwamishinar kula da harkokin lafiya da jin kai da ci gaban al’umma Amma Twum-Amoah, babban...
Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA), ta ce ta samu nasarar ceto wasu mata biyu da wata jaririya da ambaliyar ruwa ta rutsa da su a Jihar Kaduna. Shugabar hukumar, Hajiya Zubaida Umar ce, ta bayyana hakan a shafinta na Facebook. Harin Boko Haram: Zulum ya kai ziyarar jaje garin Darajamal Tsadar Rayuwa: NLC ta buƙaci gwamnati ta sake duba albashin ma’aikata Ta ce ambaliyar ta auku ne sakamakon ruwan sama mai yawa da aka yi a ranar Juma’a. Ta ce sama da gidaje 160 da magidanta 500 ne ambaliyar ta shafa a unguwanni irin su Kabala Doki, Bachama, Kigo, Ramat, da Unguwar Dosa/Nasarawa/Mali. Rahoton ya nuna cewa ruwan kogin Kaduna ne ya yi sama, ya shiga unguwanni,...

Isra’ila tace Ta Yi Kokarin Kashe Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci A Yakin Kwanaki 12 Da Kasar Iran
Ministan yakin HKI Israel Kazt ya bayyana cewa sun yi kokarin kashe jagoran juyin juya halin musulunci Imam Sayyid Aliyul Khaminae a yakin kwanaki 12 amma bayanan da suke da shi ya kasa kaiwa ga manufarsu. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa wannan shi ne karon farko wanda HKI take tabbatar da cewa ta yi kokarin mai matsayi mafi girma a kasar Iran, wanda kuma ya kasa kaiwa na sarara. Kazt ya bayyana haka wa tasoshin talabijin ta Chennel 13, Kan da kuma Channel 12, kan cewa sun yo kokari har sau 2 amma bayayan da ke hannummu sun kasa tabbatar da abunda muke nema. Yace da mun sami da mun kasheshi tuni. Bayanan da gwamnatin...
Ministan harkokin wajen kasar Iran abbas Aragchi ya yi kira ga kasashen turai 3 EU a takaice su dawo kan hanyar diblomasiyya don warware rikicin shirin Nukliyar kasar Iran wanda ya zo cikin yarjeniyar JCPOA na shekara ta 2015. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Argchi yana fadar haka a yau Lahadi a cikin wani rubutun da yayi a cikin Jaridar Guadian na kasar Burtania. Ministan ya kammala da cewa idan sun ki dawowa kasashen turai ne za’a ware nan gaba, don ba zasu taba cimma manufofinsu a kan Iran tare da sake maida takunkuman MDD kan kasar Iran ba. Tsarin Snpback dai wani tsari ne wanda zai bawa kasashe 6 wanda suke cikin yarjeniyar JCPOA danar...
Zahra Kiana yar wasan Wushu ta lashe lambar Zinari a wasar Wushu ta shekara ta 2025 a kasar Barazil. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa Kiyani ta lashe lambar Zinari ne a dai-dai lokacinda wannan wasan take sabo a kasar Iran, kuma tana cike da masu taka rawa a cikinta da dama daga gabacin kasashen Asia. Labarin ya kara da cewa Kiyani ta daukaka kasar Iran a gasar Wushu, sannan ta kwadaitar da sauran mata wadanda suke sha’awar yi wasar. A rana ta 4 da fara gasar Wushu ta kasa da kasa kuma karo na 17th ta shekara ta 2025 a kasar Brazil Kina ta lashe lambar Zinari, wanda ya bawa Iran matsayi a wannan wasan...
Wani Jirgin Drone wanda ake sarrafashi daga nisa, ya fada kan zauren fisinjoji a tashar jiragen sama na Ramon dake yankin Araya na kudancin haramtacciyar kasar. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa wannan harin ya nuna irin yadda sojojin Yemen suke fadada hare-harensu a kan HKI, da kuma tabbatar mata da cewa Yemenawa suna iya kaiwa ko wani wuri a fadin kasar Falasdinu da aka mamaya. Majiyar yahudawa ta bayyana cewa wai wasu fasinjoji ko kuma yahudawa yan shere wuri zauna ne suka ji ciwa sanadiyyar harin. Sannan babbar abin tambaya ita ce, shin ina makaman kare sararin samaniyar kasar wadanda kasar da kasashen yamma suke tutiya da su. Ta yaya jirgin yaki daga kasar Yemen...
Ali Akbar Vilayati mai bawa jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran Imam Sayyid Aya. Khaminae ya bayyana cewa, yenci da kuma zaman lafiya da tsaron JMI yana da matukar muhimmanci ga kasar Iran. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Wilayati yana fadar haka a lokacin da yake ganawa da Ammar Hakin shugaban Jam’iyyar Hikma na kasar Iraki wanda yake ziyarar aiki a nan Iran a yau Lahadi. Wilayati ya kara da cewa kasashen Iraki da Iran suna da dangantaka mai muhimmanci tsakaninsu wanda ya hada da na addini da al-adu ga kuma makobtaka. Yace Iran tana jin dadin ganin Iraki tana samun ci gaba da kuma zaman lafiya mai dorewa a karkashin jagorancin malaman addini...
Na dauki fim sana’a, kuma sana’ar ce. Dan wallahi sana’a ce me kyau ma, ta ba ni gida, ta ba ni mota, na ci, na koshi. Yanzu idan zan shekara na ce ba zan fita ba, a cikin gidana ne, kuma darajar Kannywood. Ina finafinai na a haka na samu gidana, na gina gidan kuma nake zaune cikinsa. Ko kina da ubangida, a cikin masana’antar Kannywood? Ai ni a masana’antar duk wani sa’a na, ko wanda ya girmen ubangidana ne, ni ba butulu ba ce da zan ce ban da iyayen gida. Ana rade-radin akwai yaranki a cikin masana’antar Kannywood, mene ne gaskiyar maganar? ‘Ya ta guda daya ce take Kannywood, saboda da kanta ta ce “Umma ina...
Bictor Boniface Wani dan wasan da ya tafi zaman aro shi ne Bictor Boniface wanda ya bar Bayer Leberkusen ya koma Werder Bremen a matsayin aro na tsawon kaka guda a ranar da za a rufe cinikin yan wasa, dan wasan na Nijeriya ya saka hannu akan kwantiragin da zai sa ya zauna a Werder har zuwa watan Yuni na shekarar 2026, kungiyoyin biyu ne za su biya albashin Boniface. Tolu Arokodare Wolbes ta sanar da daukar Arokodare daga kungiyar KRC Genk ta kasar Belgium dake buga gasar Belgian Pro League a ranar karshe ta musayar yan wasa, dan wasan mai shekaru 24 ya rattaba hannu kan kwantiragin shekaru hudu da kungiyar ta Firimiya tare da zabin karin shekara,...
Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya ziyarci garin Darajamal da ke Ƙaramar Hukumar Bama, domin jajanta wa iyalan mutanen da Boko Haram suka kashe. Rahotanni sun nuna cewa ’yan ta’addan Boko Haram sun hallaka aƙalla mutum 63, yayin da dakarun soja suka kashe 30 daga cikinsu. Tsadar Rayuwa: NLC ta buƙaci gwamnati ta sake duba albashin ma’aikata Najeriya ce ƙasa ta biyar mafi yawan Musulmai a duniya Da yake magana da mazauna garin Zulum ya ce: “Abin takaici ne sosai. An dawo da wannan al’umma nan ba daɗewa, amma sai ga shi an sake fuskantar mummunan hari a daren jiya.” Gwamnan ya buƙaci Gwamnatin Tarayya ta ƙara ƙarfafa jami’an tsaro a dazuka, inda ya bayyana cewa akwai buƙatar ƙara...
Domin kuwa wasu matan kwanciya kan iya zama sanadi na lalacewar cikin. So, akan ce ma a rage ko a bari a watanni uku na farkon ciki. Don haka idan ka ga wadannan matsalolin kar ka ce wai kirkira take, ko da gangan take. Ba gaskiya bane. Lalura ce babba, kuma da take bukatar kallo na musamman. Idan kaga wannan lokacin yazo, anan ne ake so ka nuna soyayyarka, da kulawarka, da taimakonka. Wajibi ka bata hadin-kai don ta wuce wannan watanni uku na farko din. Domin cikin jikinta a wannan lokacin kamar akan siratsi yake, duk abinda aka ce ana halittarta ’yan Adam a cikinsa ai yaga taka kansa. Komai zai iya faruwa. Namiji dan kirki shine sai kaga...
Alamomin Basir Bayyanar alamomin Basir, ya danganta ga wane irin Basir ne ya bayyana, Basir cikin dubura ko kuma Basir a wajen dubura? Alamomin Basir Cikin Dubura: 1- Zubar jini ba tare da jin ciwo ba, a yayin tsuguno. 2- Basir mai tsiro, wanda ke fitowa wajen dubura; har sai an tura da yatsa, domin mayar da shi. Yana haifar da ciwo da radadi. Alamomin Basir A Wajen Dubura: 1- Ciwo mai radadi 2- Kaikayi 3- Kumburi a kewayen dubura 4- Zubar jini yayin yunkurin tsuguno Abuban da ke kawo Basir: Basir na faruwa ne sakamakon takura jijiyoyin jini a dubura, har su kumbura sannan su yi bulli saboda abubuwa kamar haka: 1- Yawan yunkuri yayin tsuguno 2- Tsawaitar lokacin...
Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya (NLC) da ma’aikatan gwamnati, sun buƙaci Gwamnatin Tarayya, ta sake duba mafi ƙarancin albashi, domin Naira Naira 70,000 da ake biya yanzu ba ta isa wajen tafiyar da al’amuran yau da kullum. A cewarsu tashin farashin kayan abinci, sufuri, haya, da wutar lantarki ya ƙara jefa su cikin wahalar da rayuwa. Sojoji sun bankaɗo mafakar ’yan ta’adda da makamai a Taraba Najeriya ce ƙasa ta biyar mafi yawan Musulmai a duniya A wasu jihohi kamar Imo, Legas da Ribas sun riga sun ƙara mafi ƙarancin albashi sama da wanda gwamnatin tarayya ke biya. Mista Benson Upah, Sakataren riƙo na NLC, ya ce: “Naira 70,000 ba za ta iya ɗaukar nauyin rayuwa a wannan yanayi na tattalin...
Kazalika, an amince da amincewar ne a taron majalisar zartarwa na jihar karo na 12, wanda Gwamna Malam Dikko Umaru Radda, ya jagoranta a gidan gwamnati da ke Katsina. Da yake karin haske ga manema labarai bayan taron, kwamishinan tsaron cikin gida da harkokin gida, Dakta Nasiru Mu’azu Danmusa ya ce, an sanar da matakin ne sakamakon mawuyacin halin da jihar ke ciki, wanda ya kawo babban kalubale ga ababen hawa na yau da kullum wajen shiga wasu yankunan, musamman na karkara da marasa galihu. “Gwamnati ta bayyana matsayinta a fili: tsaro shi ne fifiko na farko, na biyu da na uku na wannan gwamnati shi ne, mun kudiri aniyar magance rashin tsaro baki-daya.” in ji Dakta Danmusa. Baya ga...
Sojojin runduna ta 6 da ke Jalingo, babban birnin Jihar Taraba, sun gano wata mafakar ’yan ta’adda tare da ƙwato makamai da dama a ƙauyen Ikyaior da ke ƙaramar hukumar Wukari, a kan iyakar Taraba da Benuwai. Bayanan sirri da sojojin suka samu ne suka taimaka musu wajen kai farmakin da ya kai ga gano mafakar da kuma ƙwato makaman. Najeriya ce ƙasa ta biyar mafi yawan Musulmai a duniya DSS ta bai wa shafin X wa’adin goge saƙon Sowore da ke ƙaryata Tinubu Mataimakin mukaddashin kakakin rundunar, Laftanar Umar Mohammed, ya tabbatar wa da wakilin Aminiya cewa sojojin sun gudanar da bincike a yankin, inda suka gano makamai masu tarin yawa. “Mun samu makamai daban-daban, ciki har da bindigogi...
A jawabin da ya yi wa shugabannin sashen sintiri, jami’an ‘yansandan motoci, da sauran jami’an da ke aiki a hedikwatar rundunar, CP ya ce halayen jami’an sintiri a fili suke bayyana hoton da al’umma ke da shi game da rundunar ‘yansanda. Adeh ta bayyana cewa CP ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda jami’ai ke gudanar da ayyuka a halin yanzu, yana mai jaddada cewa kula da zirga-zirga na daga cikin manyan alamomin nuna ci gaban gari. Bayan ya yi yawon duba wurare da dama a birnin a lokutan cunkoso, CP ya gano muhimman wurare kusan 30 da ke da matsalar zirga-zirga, ciki har da Wuse, Area 1 Roundabout, Jikwoyi, Karu, Kurudu, AYA, Apo Resettlement, Gudu, Galadima, Dawaki, da Kubwa....
Wasu cibiyoyin bincike na Pew Research da CIA World Factbook sun tabbatar da cewa Najeriya ce ƙasa ta biyar mafi yawan Musulmai a duniya, inda ƙasar ke da Musulmai kimanin mutane miliyan 124. Ƙididdigar ta waɗannan cibiyoyi ta nuna Musulunci na ci gaba da zama addini na biyu mafi girma a duniya, wanda yawan mabiyansa suka kai kusan mutane biliyan 2.45 zuwa shekarar 2023. Firaministan Japan Shigeru Ishiba ya yi murabus DSS ta bai wa shafin X wa’adin goge saƙon Sowore da ke ƙaryata Tinubu Ƙasar Indonesia ce ke kan gaba da Musulmai miliyan 242, sai kuma Pakistan mai miliyan 235. Sai kuma ƙasar India da miliyan 213 sa’annan kuma Bangladesh da miliyan 150. Daga nan kuma sai Najeriya wacce...
Hukumar Tsaron Farin Kaya a Nijeriya (DSS) ta bai wa shafin sada zumunta na X wa’adin sa’o’i 24 da ya goge wani saƙo da mai fafatuka Omoyele Sowore ya wallafa yana ƙaryata Shugaba Bola Tinubu. Hakan na ƙunshe cikin wata wasiƙa da Hukumar DSS ɗin ta aike wa kamfanin X Corp mallakin fitaccen attajirin nan Elon Musk. Firaministan Japan Shigeru Ishiba ya yi murabus ’Yan ta’adda sun kashe mutum 63 a Borno A wasiƙar da DSS ta wallafa shafinta na X ranar Asabar, hukumar ta zargi Mista Sowore da yin amfani da saƙonsa na X wajen cin fuskar shugaban ƙasa Tinubu da yi masa rashin mutunci da ba’a. A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X ranar 25...
Hajiya Sa’ah ta kuma bayyana cewa ita wannan ƙidaya da yin rajistar haihuwa, aure da sauran su, abubuwa ne masu muhimmanci da za su taimaka wa gwamnati ta san yawan su, ta yadda za su sami nasarar ci gaba da lasar romon Dimokraɗiyya mai yawa, musamman a bangaren ilmi, lafiya da dai sauran abubuwan more rayuwa. Daga nan ne ta jinjina wa Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani da cewar jihar Kaduna ce jiha ta farko da gwamnan ta ya yi yunƙurin gabatar da wayar da kan al’ummar sa game da muhimmancin ƙidaya, kuma lallai yana bayar da cikakken goyon bayan sa a kan haka, inda ya ɗauki nauyin hakan a dukkan Ƙananan Hukumomin jihar. A nasa jawabin,...
Ƙungiyar masu dakon Man Fetur da Gas (NUPENG) ta sanar da cewa za ta fara yajin aikin kasa baki daya daga ranar Litinin, 8 ga Satumba, 2025, domin nuna adawa da abin da ta kira tsauraran matakan kin amincewa da kungiyar da Kamfanin matatar Dangote ke yi. NUPENG ta zargi kamfanin da daukar direbobin da za su yi aiki da sabbin motocin CNG da aka shigo da su bisa sharadin cewa kada su shiga kowace kungiya a bangaren man fetur da iskar gas. kungiyar ta ce hakan ya saba wa kundin tsarin mulki na Nijeriya, dokar aiki ta ƙasa, da kuma yarjejeniyar kasa da kasa ta ILO kan yancin kafa ƙungiya. Bayanin hakan ya fito ne bayan wani taro da...
Daruruwan kungiyoyin sa kai ne suka gudanar da zanga-zanga a kasar malesiya domin nuna adawa da ziyarar shugaban Amurka Donal Trump a karshen watan gube saboda nuna goyon bayan isra’ila kan kisan kare dangi da take yi a Gaza, , sun bukaci gwamnati da ta soke gayyatar wanda suka bayyana shi a matsayin babban mai laifin yaki dake da hannu wajen kisan kare dangi da isra’ila ke yi wa alummar Gaza, da hakan ya sabama dukkan dokokin kasa da kasa. Mazu zanga zangar sun daga kwalaye da a ciki aka rubuta cewa trump kada ka zo,kuma mafiywancin wadanda suka halarci zanga-zangar mata ne da yara, kuma kungiyar dake nuna goyon bayan falasdinu ce ta jagoranci zanga-zangar, fira ministan malesiya anwar...
Babban sakataren hukumar samar da hadin kai takanin mazhabobin musulunci hujjatul islam shahriyori ya sanar cewa a gobe litinin 8 ga watan satumba ne zaa bude taron makon hadin kai na 39 a nan birnin Tehran inda zai samu halartar malamai sama a 80 da baki 210 da kuma masu rajin kare hakkin bil adama guda 2800 daga kasashen duniya daban daban. Haka zalika hujjatul islam shahriyari ya kara da cewa taron zai gudana tsakanin 8-10 na watan satumba wanda yayi daidai da lokacin zagayowar ranar haihuwar manzon All.. tsira da aminci su tababta gareshi da Alayensa da aka sanyashi a matsayin makon hadin kai, yace hadin kai tsakanin addinai da kusanto da mazhabobi a yau ya zama wani batun...
Rahotanni sun bayyana cewa dubun dubatan mutane ne suka gudanar da zanga zangar nuna adawa da kisan kare dangi da Isra’ila ke yi a yankin Gaza, da kuma nuna damuwa game da rawar da birtaniya ke takawa na aikewa da isra’ila makamai, kuma zanga-zangar ta nuna irin tashin hankali da ake ciki game da hakkin yancin walwala da kuma fafututar nuna goyon bayan alummar falasdinu da ake zalunta a birtaniya. Sama da mutane 500,000 ne daga sassa daban daban na birtaniya suka taru a birnin London domin yin zanga zangar nuna goyon bayan ga alummar Gaza, inda suka fara tun daga dandalin Russell kuma aka kammala a gaban ofishin prime ministen kasar, wanda suka halarci gangami akwai wakilai daga kungiyoyin...
Rahotani sun bayyana cewa an rufe kamfanin kera makamai na HKI dake birtaniya mai suna Elbit system sakamakon zanga-zangar da kungiyoyin sakai da masu goyon bayan palasdinu suka yi karkashin dokar yaki da ta’addanci a birtaniya. Wannan mataki yayi tasiri sosai a duniya inda dubban mutane ke ci gaba da matsin lamba ga gwamnatocinsu da su yanke duk wata alakar kasuwanci da isra’ila sakamakon ci gaba da kisan kare dangi kan alummar Gaza. Shi dai kamfanin Elbit System dake birtaniya na yanar gizo na Bristol ya fara aiki ne a karkashin wata yarjejeniyar tun a shekara ta 2019 zuwa ta2029 Kamfanin shi ne babban mai samar da jirage marasa matuka da sojojin Isra’ila ke amfani da su, musamman a yankin...
’Yan ta’adda sun kashe aƙalla mutum 63 a wani mummunan hari da suka kai a garin Darul Jamal, kusa da kan iyakar Najeriya da Kamaru, a yankin Bama na Jihar Borno. Gwamnan jihar, Babagana Umara Zulum, ya tabbatar da cewa daga cikin waɗanda suka rasa rayuka akwai sojoji 5 tare da fararen hula 58. Tsagin NNPP na ƙasa ya yi watsi da korar Abdulmumin Jibrin Kofa ’Yan bindiga sun kashe jami’an Sibil Difens 8 a Edo Wannan harin ya faru ne da daddare a ranar Juma’a, inda maharan haye a kan ɗaruruwan babura, suka fara harbe-harbe da ƙone gidaje. Wani mazaunin garin, Malam Bukar, ya shaida wa manema labarai cewa: “Sun shigo suna ta kabarbari da harbi kan mai uwa...
A jawabin ‘yan jaridu wanda darekta na bangaren manema labarai da al’amuran da suka shafi jama’a na ma’aikatar ilimi ta tarayya Folasade Boriowo, abin ya bayyana; “A sashen Firamare , ‘yan aji 1- 3 za su byi darussa 9–10, su kuma wadanda suke aji 4–6 zasu yi darussa 10–12.Sai bagaren karamar Sakandare, abin ya fara ne daga darussa 12–14; Babbar Sakandare kuma dalibanta za su yi darussa 8–9; yayin da su kuma fannin fasaha za su yi darussa 9–11.” Ahmad ya bayyana manhajar an tsara ta ne saboda an rage abubuwan da ta kunsa, aka kara maida hankali ga koyo domin tabbatar da cewa lamarin da ya shafi ilimi ya ci gaba da zama yana tafiya daidai zamanin da...
Wasu ’yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne, sun hallaka jami’ai takwas na Hukumar Tsaro ta Sibil Difens (NSCDC) da ke aiki a kamfanin siminti na BUA da ke Okpella, karamar hukumar Etsako East ta Jihar Edo. An kai harin na kwanton ɓauna ne da misalin ƙarfe 10 na dare a ranar Juma’a, 5 ga Agusta, 2025, lokacin da jami’an suka fita raka wasu ma’aikatan kamfanin ’yan ƙasar China guda biyar bayan kammala aikin gadi a ƙofar kamfanin. Wani babban jami’in rundunar a jihar ne ya bayyana haka a ranar Asabar, inda ya ce ’yan bindigar sun kuma jikkata jami’ai huɗu waɗanda ke karɓar magani a asibiti a halin yanzu.
Tsagin Jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) ya ƙi amincewa da korar ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar mazaɓar Kiru/Bebeji a Jihar Kano, Abdulmumin Jibrin Kofa. Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Sakataren Jam’iyyar na Ƙasa, Oginni Sunday ya raba wa ’yan jarida ranar Asabar. Musulman Kudancin Kaduna sun zargi manyan yankin da juya gaskiya Bikin naɗin Sarkin Ibadan yan hana Musulmi Sallar Juma’a — MURIC Oginni ya yi Allah wadai da korar ɗan majalisar, yana mai cewa babu wata hujja kuma ba su ba da izini ko wani iko na ɗaukar wannan hukunci ba. Sunday ya ce tuni an sallami shugaban jam’iyyar na Kano, Hashim Dungurawa tare da rukunin tsagin Kwankwasiyya daga jam’iyyarsu ta NNPP. A bayan nan ne...
Zulum, wanda ya yi matukar takaici da harin, ya gana da shugabannin al’umma tare da jajantawa iyalan wadanda suka rasu. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ƙungiyar Al’ummar Musulmi ta Kudancin Kaduna mai suna ‘Concerned Muslim Ummah’ ta zargi wasu manyan mutane a yankin da haifar da rarrabuwar kawuna da kuma juya tarihi domin cimma manufofin siyasa. A taron manema labarai da ta gudanar a Kaduna, ƙungiyar ta yi watsi da iƙirarin cewa Kudancin Kaduna na da Kiristoci ne kaɗai. Ta jaddada cewa Musulunci ya daɗe da wanzuwa a yankin tun ƙarnoni da suka gabata, inda ta ce Musulmi sun kai kusan kashi 40 cikin ɗari na al’ummar yankin. Ƙungiyar ta ce tashe-tashen hankula kamar na Zangon Kataf a 1992 da rikicin bayan zaben 2011 sun tabbatar da cewa rikice-rikicen yankin ba wai na yanzu ba ne. Bikin naɗin Sarkin Ibadan yan hana Musulmi Sallar Juma’a...
Ƙungiyar Kare Hakkokin Musulmi ta Kasa (MURIC) ta buƙaci kwamitin shirya bikin miƙa sandar sarauta ga sabon Olubadan na Ibadan da ya soke ranar Juma’a, 26 ga Satumba, da aka shirya gudanar da bikin. Ƙungiyar ta ce wannan rana za ta iya hana ɗaruruwan Musulmi gudanar da Sallar Juma’a da suke yi a kowane mako. Shugaban MURIC na ƙasa, Farfesa Ishaq Akintola, ya yi wannan kira cikin wata sanarwa da aka aika wa manema labarai a ranar Asabar. Farfesa Akintola ya ce sau biyu irin wannan matsala ta taɓa faruwa a baya: lokacin da aka yi bikin miƙa sandar sarauta ga marigayi Olubadan Oba Akinloye Owolabi Olakulehin da kuma lokacin da aka kaddamar da sabuwar hanyar Iseyin zuwa Ibadan...
Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Iran tana ci gaba da musayar saƙon da Amurka ta hanyar masu shiga Tsakani Ministan harkokin wajen kasar Iran Sayyid Abbas Araqchi ya sanar da cewa: Ana ci gaba da musayar sakwanni da Amurka ta hanyar masu shiga tsakani, yana mai jaddada cewa, Iran za ta kasance a shirye don yin shawarwari a lokacin da Amurka ta nuna aniyar ta na shiga tattaunawa bisa mutunta juna, matukar dai an mutunta hakki da muradun al’ummar Iran. A yayin da yake jawabi a zaman taron kasa kan samun damar zuba jari a yankunan ‘yanci da cinikayya a kasar Iran a ranar Asabar, Araqchi ya ce: Yankin Shenzhen na kasar China ya kasance wani karamin kauye...
Kwamandan Sojojin Iran ya jaddada cewa: Dole ne a ko da yaushe Iran ta kasance a shirye don yin yaki Babban kwamandan sojojin kasar Iran ya jaddada wajibcin kasancewa cikin shiri a ko da yaushe domin yaki, yana mai cewa: A yau sun fahimci yaki da gaba da kuma makircin makiya daidai da yadda suke a baya. Babban kwamandan sojojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Manjo Janar Amir Hatami, ya ziyarci rundunonin sojoji a yankunan Isfahan, Tabriz, da Hamadan. A yayin da yake yin nazari kan shirye-shiryen wadannan runduna tare da rakiyar kwamandoji, mayaka, da matukan jirgin sama, ya lura da tsayin daka da al’ummar Iran suka yi wajen tunkarar wuce gona da iri da yahudawan sahayoniyya suka kaddamar na tsawon...
Shugaban hukumar shari’a ta kasar Iran ya jaddada cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba za ta taba mika wuya ga mulkin kama karya ba Shugaban hukumar shari’a ta Iran ya bayyana cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba ta taba kaddamar da yaki kan wata kasa ba, kuma ba za ta taba yin hakan ba, to amma ba za ta taba mika wuya ga tsarin mulkin kama karya ba, yana mai cewa: Iran a koyaushe tana taka-tsantsan kan yunkuri da makirce-makircen makiya. A yayin ganawarsa da shugaban kungiyar Hikma ta kasar Iraki Sayyid Ammar al-Hakim, Hujjatul-Islam Gholamhossein Mohseni Ejei a birnin Tehran ya yi karin haske kan irin karfin dangantakar da ke tsakanin Iran da Iraki, yana mai jaddada cewa: Abubuwan...
Shugaban kasar Tunisiya ya bayyana cewa: Afirka na bukatar sabuwar hanya don tunkarar son ran ‘yan mulkin mallaka Shugaban kasar Tunusiya Qa’is Saeed ya bayyana a ranar Alhamis cewa: Tunisiya tana alfahari da hadin kan kasashen Afirka, kuma ta tsaya tsayin daka kan burin kafa kungiyar tarayyar Afirka mai inganci, duk kuwa da kalubalen da nahiyar ke fuskanta, kamar tashe-tashen hankula, fadace-fadace, laifuffukan safarar bil adama, da rashin samar da muhimman abubuwan rayuwa. A jawabin da ya gabatar a wajen bude taron baje kolin kasuwanci a kasar Aljeriya karo na 4, Saeed ya ce: “Nahiyar Afirka na da dimbin arziki, amma a lokaci guda tana fuskantar talauci da ke sanya matasanta shiga cikin hanyoyin safarar mutane.” Ya ci gaba da...
Ƙungiyoyin Musulmi maza da mata da ƙananan yara daga sassa daban-daban na Jihar Oyo sun gudanar da bukukuwan zagayowar ranar haihuwar fiyayyen halitta, Manzon Allah Annabi Muhammad (SAW), na bana (shekara ta 1447 bayan hijira). Aminiya ta ruwaito cewa an fara gudanar da bukukuwan ne a ranar Asabar daga harabar babban Masallacin Unguwar Sabo, mazaunin Hausawa a Ibadan, babban birnin Jihar Oyo. Khalifofin mazhabobin Darikun Tijjaniyya da Ƙadiriyya a Ibadan su ne suka jagoranci manyan malaman addinin Musulunci tare da dimbin mabiya wajen yin tattaki na tsawon kilomita 10 da ya zagaya wasu sassan birnin domin nuna farin ciki da murnar wannan rana. An ga ƙungiyoyin Musulmi daban-daban masu halartar zagayen Maulidi sanye da sutura iri ɗaya (amko) suna rera...
Shugaban yace jihar Kaduna itace akan gaba daga cikin jihohi 36 da Birnin tarayya Abuja wajen tara kudin fatun layya Wanda ta tara Naira miliyan 23 sai jihar Kebbi wacce tazo ta biyu da Naira milliyan 21 sai kuma jihar Sakkwato wacce tazo ta uku. Yace kudadan da aka tara za’ayi amfani dasu wajen ci gaba da aiwatar da Ayyukan Jami’ar musulunci mallakin kungiyar dake Hadejia a jihar Jigawa wacce ake kan ginawa. Yace irin Wannan sadaka da alumma suke bayarwa zasu tabbatar da cewa anyi amfani da su yadda ya kamata musamman ginin Jami’ar mallakar kungiyar da wasu bangarori domin ciyar da addinin musulunci gaba. Da yake bayani akan taron da kungiyar ta gudanar a jihar...
Wannan ya nuna yadda a halin yanzu irin yanayin da masu zaman a gidajen Yarin ke ci gaba da zama a gidajen, musamman saboda rashin kulawa da su yadda ya kamata. Sai dai, Dakta Essien ya dora laifin kan rashin samu ‘yanci ga masu zaman gidan Jarun din. Gidajen Yarin kasar guda 246 yau shekaru 100 ke nan da gina su, wadanda akasarinsu, duk sun tsufa, inda kuma dakunan da ‘yan jarun din ke kwana, ba su da wani sararin da masu zaman jarun din za su iya wani watayawa. A cewar Essien, jimlar masu zama a gidan jarun ciki har da wadanda aka ajiye da suke jiran Shari’a, sun kai 81,122, wanda a ka’ida kamata ya yi su kai...

Kuri’ar Jin Ra’ayoyi Ta CGTN: Sake Maido Da Ma’aikatar Yaki A Amurka Ya Nuna Babu Dakatawa A Yaki Hatta A Wajen Sa Suna
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Game da babban bikin tunawa da cika shekaru 80 da samun nasarar yakin da al’ummar Sin suka yi da mamayar dakarun kasar Japan da yakin duniya kin tafarkin murdiya, wanda aka gudanar a ranar 3 ga wannan wata, mutane daga kasa da kasa masu halartar bikin sun ba da ra’ayoyinsu ciki har da kalmomin hadin kai, da yin kokari tare, da sauransu don nuna kyakkyawar fata ga makoma. Bayan shekaru 80 da gama yakin duniya na biyu, an canja burin dan Adam. Zaman lafiya da samun bunkasa sun zama babban jigo na halin yanzu, kasa da kasa suna kokarin samun zamanantarwa. Amma a sa’i daya kuma, ra’ayin mai karfi ya cinye maras karfi ya sake bullowa, an kawo illa ga...
Wasanni uku ne kacal suka rage a rukunin. Ƙasar da ta fi kowa maki a ƙarshen zagaye ita ce kawai za ta je gasar Kofin Duniya da za a yi a Amurka, Mexico da Canada. Saboda haka, dole ne Nijeriya ta doke Afirka ta Kudu don cikar burinta. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A jiya Jumma’a 5 ga wannan wata, babban taron MDD karo na 79 ya jefa kuri’a tare da zartas da kudurin hadin gwiwar dake tsakanin MDD da kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai wato SCO da kasar Sin da dukkan kasashe membobin kungiyar SCO kimanin 40 suka gabatar tare. Kudurin ya amince da muhimmiyar rawar da kungiyar SCO ta taka wajen sa kaimi ga samun zaman lafiya da bunkasa da yin imani da juna da kuma hadin gwiwa a yankin, kana ya yaba wa kungiyar SCO bisa kokarin nuna goyon baya ga ayyukan MDD, da kara yin hadin gwiwa a tsakaninta da tsarin MDD. Mukaddashin shugaban tawagar dindindin ta Sin dake MDD Geng Shuang ya bayyana yayin da yake bayani game...
Yawancin waɗanda aka kashe sun fito ne daga sansanin ’yan gudun hijira da ke Makarantar Sakandare ta Kimiyya ta Gwamnati. Wata majiyar ta ce: “Aƙalla mutanen gari 56 da sojoji biyar aka kashe. An ƙone gidaje fiye da 20 da kuma motoci 10. Har yanzu ana neman wasu da suka ɓace.” Har yanzu, babu wata sanarwa da hukumomi suka fitar game da harin. A ranar Asabar, Gwamnan Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ya kai ziyara Bama domin samun cikakken bayani da kuma jajanta wa waɗanda abin ya shafa. A shekarar 2004, Boko Haram ta mamaye garin Bama tare da ayyana shi a matsayin wani ɓangare na “daularsu” kafin daga baya dakarun sojin Nijeriya suka ƙwato garin. Daga kanmu, magana...
Ana zargin mayaƙan Boko Haram sun kai hari ƙauyen Darul Jamal da ke Karamar Hukumar Bama, a Jihar Borno, inda suka kashe gomman mutane da sojoji. Harin ya faru ne da misalin ƙarfe 9 na daren ranar Juma’a. ’Yan bindiga sun kashe mutum 7 a Katsina Yadda makarantu ke tatsar kuɗaɗe daga iyayen ɗalibai Mutane da hukumomin tsaro sun tabbatar da aukuwar harin. A kwanakin baya, Gwamnan Jihar, Babagana Umara Zulum, ya mayar da wasu mutane ƙauyen. Shekaru da dama suna zaman ’yan gudun hijira a sansanoni daban-daban kafin a dawo da su. Wani daga cikin mazauna yankin ya ce: “Rana ce mai matuƙar baƙin ciki. Ɗana da ɗan uwana sun mutu. “Mun kirga gawarwaki 63 kuma mutane da dama...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A wani mataki na tallafawa kasuwanci tsakanin kasashen Afrika an kaddamar da wat kungiyar mai manufartallafawa kasuwanci tsakanin kasashen Afirka tare da saukaka ayyukan raya kasa da sarrafa albarkatun cikin gida. Bankin shigo da kayayyaki na Afirka ne ya kaddamar da kungiyar Don tallafawa kasuwanci, fitar da kayayyaki, da sarrafa albarkatun kasa a Afirka, wanda aka sanar da kirkiro da shi a yayin bikin ranar Afirka. Shugaban bankin Afrexim Bank Oramah Benedict ne ya sanar da hakan a hukumance a birnin Algiers, a yayin bikin ranar ‘yan kasashen Afirka. An gudanar da bikin ne a gefen ranar al’ummar kasashen Afirka, wanda firaministan rikon kwarya na kasar Aljeriya Sifi Ghrib ya jagoranta, tare da halartar jami’ai daga Afirka da dama. Ayman...
Ministan harkokin wajen Iran, Seyyed Abbas Araghchi, ya tattauna ta wayar tarho da takwaroribnsa na kasashen Girka, Slovenia da Saliyo a wannan Juma’a kan batutuwan da suka shafi kasashen. Mista Abbas ya gana ne Georgios Gerapetritis, ministan harkokin wajen Girka, Tanja Fajon, ministan harkokin wajen Slovenia, da Alhaji Musa Timothy Kabba, ministan harkokin wajen Saliyo. Dukkan kasashen uku a halin yanzu mambobi ne a kwamitin sulhu na MDD. Tattaunawar ta ta’allaka ne kan dangantakar da ke tsakanin Iran da kasashen, da kuma ci gaban yanki da na kasa da kasa, musamman dangane da matakin da kasashen Turai uku (Birtaniya, Faransa, da Jamus) suka yi a kwamitin sulhu. Ministan harkokin wajen na Iran ya yi kakkausar suka kan matakin da kasashen...
A cikin sa’o’i 24 da suka gabata, akalla Falasdinawa 68 ne suka yi shahada a Zirin Gaza, wanda ya kawo adadin wadanda suka rasu a yakin kisan kare dangi na Isra’ila tun watan Oktoban 2023 zuwa sama da 64,368. Akalla Falasdinawa tara ne sukayi shahada a wani kazamin harin da aka kai ta sama a birnin Gaza da Khan Yunus, ciki har da takwas lokacin da aka kai hari kan wani gini a unguwar Sheikh Radwan. Kamfanin dillancin labaran iqna, ya nakalto cewa, a ranar Asabar, wani yaro ya yi shahada a wani harin da Isra’ila ta kai kan wata mota a sansanin al-Mawassi da ke Khan Yunis. Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, bayan harin bam da Isra’ila...
Kungiyoyin gwagwarmayar Falasdinawa da dama sun bayyana bacin ransu kan barazanar da ministan yakin Isra’ila ya yi na bude “kofofin jahannama” a zirin Gaza. Wannan martanin ya zo ne a ranar Juma’a bayan da Isra’ila Katz ya ayyana cewa gwamnatin sahyoniyawan na gab da maida yankin jahannama a gabar tekun. Katz, ya bayyana cewa sojojin Isra’ila za su zafafa kai hare-hare har sai kungiyar gwagwarmayar Palasdinawa ta Hamas ta sako mutanen da aka kama. A nata bangaren, Hamas ta ayyana barazanar Katz a matsayin “kalubale da ba a taba ganin irinsa ba ga dokokin kasa da kasa da ka’idojin jin kai.” Kalaman na Katz na zuwa ne a daidai lokacin da kungiyar ta riga ta ba da damammaki don ba...
Kungiyar ba da agaji ta Red Crescent ta Iran ta ce kasar ta aike da kayayyakin jin kai zuwa yankunan da girgizar kasa ta shafa a gabashin Afghanistan. Razieh Alishavandi, jami’i daga kungiyar, ya bayyana cewa, Iran ta tura sama da tan dari na kayayyakin ceton rai zuwa Afghanistan. A cewar Alishavandi, wannan agajin ya hada da abinci, tantuna, barguna, tufafi, da dai sauran abubuwa masu muhimmanci na matsugunin gaggawa da tallafi ga mutanen da girgizar kasar ta shafa a Afghanistan. Kungiyar agaji ta Red Crescent ta Iran “Koyaushe kamar yadda ta saba, za ta tsaya da dukkan karfinta ga mutanen Afghanistan a cikin wnnan lamarin,” in ji shi . A ranar Lahadin da ta gabata, ce girgizar kasa mai...
Rahotanni sun tabbatar da cewa ’yan bindiga sun kashe mutane bakwai, yayin wani hari da suka kai ƙauyen Magajin Wando da ke Ƙaramar Hukumar Ɗandume, a Jihar Katsina. Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11 na daren ranar Juma’a, lokacin da maharan suka afka wa ƙauyen. Mauludi: Ƙungiyoyin addini sun nemi gwamnati ta sassauta dokar hana hawa babur a Gombe Yadda makarantu ke tatsar kuɗaɗe daga iyayen ɗalibai Kwamishinan tsaro na jihar, Dokta Nasiru Mu’azu Danmusa, ya ce jami’an tsaron al’umma na Community Watch Corps (CWC) sun yi artabu da maharan, inda suka daƙile harin. A yayin arangamar, maharan sun ƙone motar jami’an tsaron, amma duk da haka, jami’an sun samu nasarar fatattakar su. Danmusa, ya bayyana cewa, rahotanni...
Rahotanni sun tabbatar da cewa ’yan bindiga bakwai sun mutu a wani hari da suka kai ƙauyen Magajin Wando da ke Ƙaramar Hukumar Ɗandume, a Jihar Katsina. Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11 na daren ranar Juma’a, lokacin da maharan suka afka wa ƙauyen. Mauludi: Ƙungiyoyin addini sun nemi gwamnati ta sassauta dokar hana hawa babur a Gombe Yadda makarantu ke tatsar kuɗaɗe daga iyayen ɗalibai Kwamishinan tsaro na jihar, Dokta Nasiru Mu’azu Danmusa, ya ce jami’an tsaron al’umma na Community Watch Corps (CWC) sun yi artabu da maharan, inda suka daƙile harin. A yayin arangamar, maharan sun ƙone motar jami’an tsaron, amma duk da haka, jami’an sun samu nasarar fatattakar su. Danmusa, ya bayyana cewa, rahotanni sun...
An ce saurayin ya yi wa Ammaye wasa da cewa yana son aurenta domin “cika Sunnah”. Sai dai kuma an ce Ammaye ta yi wata magana da aka dauka a matsayin Batanci. Wannan ne ya fusata matasan yankin. Lamarin aka kai shi fadar Dagacin Kasuwar Garba, inda aka yi mata tambayoyi, kuma a cewar rahoto ta maimaita abin da ta fada tun farko. An ce Dagacin ya mika Ammaye ga jami’an tsaro domin gudanar da bincike, amma taron matasa masu hargitsi suka mamaye jami’an tsaro, suna cewa a kashe ta nan take. Jaridar PUNCH Metro ta gano cewa kafin jami’an tsaro su iso domin kawo dauki, matasan sun riga ya jajjefe Ammaye har ta mutu. Mai magana da yawun ‘yansandan...
Ƙungiyoyin makarantu da na addinin Musulunci a Jihar Gombe, sun roƙi gwamnatin jihar da ta sassauta dokar taƙaita hawa babur daga ƙarfe 7 na yamma zuwa 6 na safe, domin sauƙaƙa zirga-zirga yayin bukukuwan Mauludi. Shugaban ƙungiyar makarantun Islamiyya na Jihar, Alhaji Muhammadu Nuhu, ya ce yawancin masu zuwa wajen bukukuwan na amfani da babura ne. NNPP ta kori Kofa daga jam’iyyar, ta yi barazanar maka shi a kotu ’Yan bindiga sun kashe jami’an NSCDC 8, sun sace ɗan China a Edo Ya ce ana kammala bukukuwan da misalin ƙarfe 10 na dare, amma dokar tana fara aiki tun 7 na yamma, don haka suka roƙi a sassauta dokar saboda muhimmancin Mauludi. Alhaji Nuhu, ya gode wa Gwamna Muhammadu Inuwa...
Ƙaramar hukumar Tureta na fama da matsalar tsaro, inda hare-haren ‘yan bindiga ke yawan faruwa, inda suke kashe mutane. A baya, ɗaruruwan mazauna yankin sun yi zanga-zanga suna neman gwamnati ta kawo musu ɗauki. Matasa kuma sun yi barazanar ɗaukar makamai domin kare kansu idan gwamnati ta gaza samar da tsaro. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Don haka, ana so a dan dakatar da yi masa ban-ruwa har zuwa wasu ‘yan makwanni, wato kafin a yi masa girbi. Sinadaran da ya kamata a yi amfani da su: Sai dai, mangwaro na jurewa yin girma a cikin kowane irin yanayi, sannan kuma bai cika samun wasu kalubale wajen samun harbin kwayoyin cututtuka ba. Sinadaran da ake yi wa mangwaro feshi da su, ya danganta ne da irin cututtukan da suka harbe shi. Wasu daga cikin sinadaran feshin sun hada da kamar irin su ‘Potassium’. Zuba takin zamani: Takin zamanin da ake zuba wa mangwaro, ya danganta da irin matakin da ya kai na yin girma. Wadannan su ne tsarin da aka bayar da shawa kan sinadaran da...
Jam’iyyar NNPP ta Jihar Kano, ta kori Abdulmumin Jibrin Kofa, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazaɓar Kiru/Bebeji. Jam’iyyar ta zarge shi da yi mata zagon ƙasa da kuma gaza biyan kuɗaɗen da ake binsa. ’Yan bindiga sun kashe jami’an NSCDC 8, sun sace ɗan China a Edo APC ta yi barazanar hukunta “Yaran Badaru” a Jigawa Shugaban NNPP na jihar, Hashim Sulaiman Dungurawa ne, ya bayyana haka ranar Asabar a Kano. Ya ce Jibrin ya daɗe yana fitowa a kafafen watsa labarai yana zagin jam’iyya da shugabanninta. Wannan na zuwa ne kwana ɗaya bayan da Kofa, ya ce zai iya barin NNPP, inda ya ce yana da ƙwarewar da zai iya yanke shawara kan makomar siyasarsa. Dungurawa, ya ce Kofa...
Ya kara da cewa, saboda haka; akwai bukatar a kara yawan hektar noman kwakwar manjar zuwa hekta akalla 500,000, domin cike gibin bukatar da ake da ita a kasar nan tare kuma da kara bunkasa nomanta a Nijeriya baki-daya. Shugaban ya ci gaba da cewa, har yanzu a Nijeriya ana ci gaba da fuskantar samun gibi wajen samar da kwakwar, sai dai ya bayyana cewa; sama da shekara 10 zuwa shekara 15 kungiyar ta POFON ta yi namijin kokari, wajen kara yawan noman kwakwar a daukacin fadin kasar. A cewarsa, manyan gonaki a kasar da ke nomanta kamar irin su, Presco da kuma Okomu sun kara dage damtse wajen zuba hannun jari da kuma kara fadada gonakin noman kwakwar manjan...
Gwamnatin jihar Kogi ta tabbatar da aniyarta ta magance matsalolin ambaliya da zaizayar ƙasa ta hanyar aiwatar da muhimman ayyukan gine-gine da aka tsara domin samar da mafita ga matsalolin muhalli a faɗin jihar. Kwamishinan yaɗa labarai da sadarwa na jihar, Kingsley Femi Fanwo, ya bayyana cewa gwamnatin Gwamna Usman Ododo ta ƙuduri aniyar inganta rayuwar al’umma ta hanyar gina muhimman abubuwan more rayuwa da za su tabbatar da tsaro, da ɗorewa da ingantacciyar rayuwa. Hakimin Da Aka Sace A Jihar Kogi Ya Shaki Iskar ‘Yanci Sojoji Sun Ceto Shugaban Fulani, Mutane 5 Daga Hannun Ƴan Bindiga A Kogi Ya bayyana cewa sabbin magudanan ruwa da aka kammala a wurare irin su Etahi, da Omigbo da Olubojo a ƙaramar hukumar...
Wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun kai hari yankin Okpella, da ke Ƙaramar Hukumar Etsako ta Gabas, a Jihar Edo, inda suka kashe wasu jami’an tsaro. Sun kashe jami’an Sibil Difens guda takwas sannan suka yi garkuwa da wani ma’aikacin ƙasar China. APC ta yi barazanar hukunta “Yaran Badaru” a Jigawa Yadda makarantu ke tatsar kuɗaɗe daga iyayen ɗalibai Haka kuma, sun jikkata wasu jami’an Sibil Difens h6udu da wani mutum, waɗanda yanzu haka suna asibiti inda ake kula da ita. Jami’an da lamarin ta shafa suna tsaron ma’aikatan ƙasar China na Kamfanin Simitin BUA. Suna kan hanyarsu na zuwa wajen da suke aikin siminti lokacin da aka tare su a bakin kofar shiga kamfanin. ’Yan...
Ya kuma sanar da ci gaba da bai wa shugabancin Dakta Dantsoho goyon baya, musaman domin kara samar da sauye-sauyen da za su kara bunkasa hada-hadar zirga-zirga, da kuma a bangaren kara bunkasa kasuwancin tatalin azrki na Teku. A nan kuma Kamfanin Rukunonin SIFAD, ya taya Dakta Dantsoho murnar zama Mataimakin Shugaban na kungiyar ta IAPH. Hakan na kunshe ne, a cikin wata wasika da Shugaban Kamfanin Dakta Taiwo Afolabi CON ya fitar ta taya murnar, inda ya danganta zabar Dantsoho kan mukamanin a matsyin abinda ya dace, musamman duba irin salon shugabanci na gari na Dakta Dantsoho, wanda hakan ya sanya ya samar da gagarumar gudunmawa a bangaren sufurin Jiragen Ruwa na kasar. Shugaban sashen samar da bayanai na...
Mambobin kwamitin zartarwar na ADC da suka hada da Bolaji Abdullahi (Sakataren yada labarai na kasa), Babachir Lawal (Mataimakin shugaban jam’iyyar na yankin arewa maso gabas), Usani Uguru Usani (Mataimakin shugaban jam’iyyar na kasa), Farfesa Oserheimen Osunbor (Babban lauyan jam’iyyar na kasa), Bar Chinedu Idigbo (Sakataren shirye-shiryen jam’iyyar na kasa), Sen. Musa Elayo (Mataimakin shugaban jam’iyyar na kasar waje) da Kwamared Nkem Ukandu (Sakataren jin dadi da walwala na jam’iyyar na kasa) da sauransu. Duk da haka, INEC ba ta ki amincewa da sabbin shugabannin tare da kin saka sunayensu da hotunansu a shafinta na yanar gizo. Wannan lamari na ci gaban da damun mambobin jam’iyyar da magoya baya, yana nuna matsaloli a cikin jam’iyyar kafin 2027. Sai dai yayin...
Rahotanni sun bayyana cewa Ammar Al-hakeem shugaban kungiyar national wisdom movement ya gana da shugaban majalisar koli ta tsaron kasa Ali larijani a nan birnin Tehran inda suka tattauna kan hanyoyin da zaa bi wajen kara danko zumunci da kuma yin aiki tare da kuma samar da tsaro a yankin, Sayyed Hakeem ya kawo ziyarar aiki ne a nan kasar Iran inda zai tattauna da jami’an gwamnati kan dangantakar dake tsakaninsu da kuma ci gaban yankin da kuma yadda za su hada kai wajen inganta tsaro da zaman lafiya, A lokacin ganawar dukkan bangarorin biyu sun yi nuni game da muhimmanci dabaru da hadin guiwa da kuma yin aiki tare , kana yayi ishara game da muhimmanci hadin kai kasashen...
Kasashen Duniya da dama ne suka damu game da irin halin da ake ciki a yanki gaza da kuma yadda yake kara ta’azzar inda adadin wadanda ke mutuwa yake kara yawa sosai kullum fiye da kowanne lokaci. Yanayin tsarin ilimi a Gaza yana gab da rushewa baki daya, inda makarantu da dama ko dai an rusa su,ko kuma sun koma sansanin yan gudun hijira, sojojin Isra’ila da gangan suke kai hari Asibitoci da wuraren kula da lafiya, jami’an bada agaji sun yi gargadin cewa idan yanayin ya ci gaba da tafiya a haka zai zama babban balai musamman ga yara kanana,a bangaren kwakwalwa da kuma ci gaba. Sai dai isra’ila ta yi ikirarin cewa dukkan hare-harenta tana kai wa a...
Kungiyar ‘Movement for North East Organization Forum’ ta yi kira ga tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, da ya yi hattara na yin katsalandan game da yakin da ake yi da ta’addanci da ‘yan fashi daji. Shugaban Kungiyar, Alhaji Abdulrahman Buba Kwacham, wanda kuma shi ne Sarkin Fulanin masarautar Mubi a Jihar Adamawa, shi ya yi wannan kira, yayin da yake zantawa da manema labarai a Abuja. Ya lura cewa hukumomin tsaron kasar, karkashin jagorancin Babban Mai Ba Da Shawara Kan Harkokin Tsaro na Kasa (NSA), Malam Nuhu Ribadu, suna aiki tukuru wajen shawo kan matsalolin tsaro. A cewarsa, ci gaban da ake samu wajen dawo da zaman lafiya a sassa daban-daban na kasar ya cancanci yabo maimakon suka....
Dubban magoya bayan kungiyar Hizbullah ta kasar labanon ne suka gudanar da gagarumar zanga-zanar a cikin dare a birnin berut domin nuna adawa game da shirin Amurka da HKI na neman yan majalisar dokokin kasar su amince da batun kwance dammarar kungiyar hizbullah. Bukatar , wanda manzon musamman na Amurka tom barak ya mika, da yan majalisar suka amince da shi wanda ministocin yan shi’a suka yi watsi da ita, sun bakaci ya kasance sojojin gwamnati ne kawai za su rike makamai, wanda ke ishara ga hakkin hizbullah na mallakar makamai don kare kanta, lamarin da yan gwagwarmaya da magoya bayansu suke ganinsa a matsayin wani makatani ne kai tsaye na Amurka da isra’ila don matsin lamba da zai jefa...
Khalil al -Hayya shugaban kungiyar Hamas a yankin gaza dake falasdinu tare da yawa daga cikin mambobin kungiyar Hamas da jagororinta na siyasa sun gana da ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi a birnin Doha na kasar Qatar, inda suka tattauna game da yakin kwanaki 12, da hakan ke nuna irin goyon baya da iran take bawa yan gwagwarmayar falasdinu ,wanda ya sanya wasu kasashen turai suka amince da falasdinu a matsayin kasa Amurka da HKI suna shirin ganin sun kwashe mutanen Gaza sai dai Arqchi ya aike da sako mai karfi zuwa ga Amurka da HKI a taron da suka yi da jami’an kungiyar hamas a gaza, na irin shirin da iran take da shi na ci gaba...
Jam’iyyar APC reshen Jihar Jigawa ta gargaɗi mambobinta da su guji aikata rashin ladabi da halayen da ba su dace ba da za su iya kawo rabuwar kai a cikin jam’iyyar. A cikin wata sanarwa da sakataren jam’iyyar na jiha, Muhammad Dikuma Umar ya sanya wa hannu, APC ta nuna damuwa kan abin da ta kira yawaitar rashin ɗa’a daga wani rukunin magoya bayan tsohon gwamna kuma Ministan Tsaro, Muhammad Badaru Abubakar, da ta kira da suna “Badaru Boys.” Sanarwar ta zargi wannan rukunin da haddasa rikice-rikice a wuraren tarukan siyasa, tare da yunƙurin ɓata sunan gwamnatin Gwamna Malam Umar Namadi. Ta bayyana cewa hakan ya faru a wurare da dama ciki har da Majiya, Gumel da kuma zaben cike...
Kamfanin Kudi na Duniya (IFC) ya ce Afirka na da fa’idar gasa ga al’umma don fadada tattalin arzikin dijital tare da matsayin Najeriya a matsayin kasa mara tushe na ayyuka. Dokta Dahlia Khalifa, Daraktar yankin Afirka ta Tsakiya da kuma Anglophone West Africa, IFC Nigeria, ta bayyana hakan a ranar Laraba a Legas a taron baje kolin fasahar bayanai na Gulf (GITEX) Nigeria 2025. Khalifa ya lura cewa, a duk fadin Afirka, tattalin arzikin dijital yana kara habaka cikin hanzari ta hanyar amfani da intanet, shigar da wayar hannu, da kuma samari masu kirkire-kirkire da ke sake rubuta makomarsu. Ta kara da cewa, haqiqanin al’amuran al’umma a Afirka na nufin jimillar al’ummarta za su karu daga biliyan 1.5 zuwa biliyan...
Ministan harkokin wajen kasar Iran yayi tsokaci kan shurun da kasashen yamma suka yi dangane da bunkasa makaman nukiliyar Isra’ila A yayin da yake tsokaci game da shirun da kasashen yammacin duniya suka yi dangane da fadada kera makaman nukiliyar yahudawan sahyoniya, ministan harkokin wajen kasar Iran Sayyid Abbas Araqchi ya bayyana cewa, yin shiru da suka yi zai kawar musu da duk wani abin da ya dace da su, har ma da yin kalamai dangane da hana yaduwar makaman nukiliya. A cikin wani rubutu da ya wallafa a shafin yanar gizo a dandalin sada zumunta na X, Araqchi ya kara da cewa: Iran ta yi gargadin cewa: Tsananin da kasashen yammacin duniya ke yi na yaduwar makaman nukiliya a...