Saudiyya ta sanya wa masu Umarah wa’adin ficewa daga ƙasar
Published: 8th, April 2025 GMT
Gwamnatin Saudiyya ta ayyana 1 ga watan Dhul Qada, wadda za ta yi daidai da 29 ga watan Afrilu, a matsayin ranar ƙarshe da duk wani baƙo da ke ƙasar da zummar aikin Umarah da ya fice daga ƙasar.
Sanarwar da ma’aikatar aikin Hajji da Umarah ta Saudiyya ta fitar ta ce ta ɗauki matakin ne domin fara gudanar da shirye-shiryen aikin Hajji mai zuwa.
Cikin wata sanarwa, ma’aikatar ta ce ranar 15 ga watan Shawwal, da ya yi daidai da 13 ga watan Afrilu, ita ce ranar karshe da masu shiga ƙasar domin aikin Umrah za su daina shiga, sai dai a fita.
Ma’aikatar ta jaddada cewa duk wanda aka samu ya ci gaba da zama a ƙasar har ya wuce lokacin da keɓe, to ko shakka babu ya saɓa ka’ida sannan kuma zai fuskanci hukunci.
Mahukuntan sun buƙaci mutane da ma kamfanonin da ke shirya zuwa aikin Umrah da su kiyaye da waɗannan lokuta da aka ƙayyade.
An kuma yi gargaɗin cewa duk wani jinkiri na barin mutane, ƙasar za a ɗauke shi kamar karya doka.
Ta ce duk kamfanin da aka samu da ƙin bayyana mutanen da suka ƙi koma wa ƙasashensu to za a ci tararsu riyal dubu 100.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Za a kammala shimfiɗa layin dogo daga Kaduna zuwa Kano a 2026 — Gwamnatin Tarayya
Gwamnatin Tarayya ta sanar da cewa za ta kammala aikin shimfiɗa layin dogo wanda ya taso daga Kaduna zuwa Kano a cikin shekarar 2026 mai zuwa.
Ministan Yaɗa Labarai, Mohammed Idris ne ya bayyana hakan cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na X a yau Laraba.
Kazalika, takwaransa na sufuri, Sa’idu Ahmed Alkali ya jaddada hakan ne a yayin jawabinsa a wajen wani taron tuntuɓa tsakanin ’yan ƙasa da gwamnati da ke gudana a Jihar Kaduna.
Tattalin arzikin Nijeriya zai ci gaba da bunƙasa har zuwa baɗi — IMF Tinubu ya naɗa sabon shugaban hukumar kashe gobara ta ƙasaA cewar ministan, lokacin da Shugaba Bola Tinubu ya hau mulki kashi 15 cikin 10 na aikin kawai aka kammala.
Wata sanarwa da ma’aikatar yaɗa labarai ta fitar ta ambato ministan yana cewa “amma zuwa yanzu an kammala kashi 53 cikin 100.”
A 2024 Gwamnatin Nijeriya ta bayyana cewa ta samu rancen kuɗin da za ta kammala aikin daga wani bankin kasuwanci na ƙasar China, abin da ministan ya jaddada a yau ɗin.
Kazalika, ministan ya ce Gwamnatin Tarayyar ta samu duka kuɗin gudanar da aikin gina layin dogo daga birnin Maiduguri na Jihar Borno zuwa garin Aba na Jihar Abiya.
“Layin dogon mai tsawon kilomita 1,443 zai ratsa jihohin Borno, da Yobe, da Gombe, da Bauchi, da Filato, da Kaduna, da Nasarawa, da Binuwai,” in ji sanarwar da kakakin ministan Rabiu Ibrahim ya fitar.
Sai dai sanarwar ba ta bayyana inda gwamnatin ta samo kudin ba.
Ministan ya kuma bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta gyara layin dogo na dakon kaya tsakanin Legas zuwa Kano.