2025-09-18@06:59:32 GMT
إجمالي نتائج البحث: 148
«kayan gwari»:
(اخبار جدید در صفحه یک)
Yanzu da ya rasu, Hauwa ta ce ba ta da tabbas kan yadda za ta yi rayuwa da ‘ya’yanta. Lamarin mai tayar da hankali ya faru ne a ranar 27 ga watan Maris, lokacin da wasu matafiya 16 ‘yan asalin Arewacin Nijeriya suka faɗa tarkon wasu ‘yan sa-kai a Uromi, a Jihar Edo, inda suka kashe su. Wani rahoto na musamman da gidan talabijin na News Central TV, ya bayyana halin da Hauwa ke ciki, wanda ya nuna irin tasirin da wannan lamari ya haifar. Yanzu tana fuskantar babban ƙalubale na kula da ‘ya’yanta bakwai, tare da neman mafita game da rayuwa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da...
Ofishin jakadancin Amurka da ke Damascus ya fitar da wata sanarwar gaggawa, inda ya yi kira ga daukacin Amurkawa da su gaggauta ficewa daga kasar Syria, sakamakon karuwar hare-haren da ake kai wa a lokacin bukukuwan sallar Idi, wanda ke kawo karshen azumin watan Ramadan mai alfarma. A cikin wata sanarwa da ta fitar ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta daukaka tafiye-tafiye zuwa Syria zuwa mataki na 4 mafi girman inda aka gargadi, Amurkawa da kada su je kasar Siriya bisa kowane dalili. Ofishin jakadancin ya gargadi ‘yan kasar game da yiwuwar kai hari kan “ofisoshin jakadanci, kungiyoyin kasa da kasa da cibiyoyin jama’a na Syria” a Damascus. Halin tsaro a Syria ya tabarbare bayan da kungiyoyin ‘yan ta’adda, karkashin jagorancin...
A ranar Juma’a kasuwar ta rufe a cikin makon makon inda masu zuba hannun jarin, suka yi asarar Naira biliyan 166.43. Duk a cikin makon, saye da sayawar da aka yi ta shiyar ta kai ta jimlar Naira biliyan 3.281 da kuma wata shiyar ta Naira biliyan 63.517, duk a cikin hada-hada guda 60,782 da masu zuba hannun suka yi. Wannan ya nuna, savanin jimlar shiyar da aka yi hada-hadar ta kasuwar da ta kai Naira biliyan 1.818 sai kuma wata shiyar da ta kai ta Naira biliyan 47.226, wato wacce aka yi musayarta a makon da ya wuce wadda ta kai 64,222. Misali, manyan kamfanonin da suka yi hada-hada a kasuwar sune, kamfanin Inshora na Sovereign Trust Insurance da...
Sojojin Iran sun fitar da bayani a daidai lokacin da ake shirin raya ranar Kudus ta duniya, suna masu bayyana cewa; Hanyar da za ta warware matsalar Falasdinu ita ce yin gwgawarmaya da kuma samun goyon baya daga al’ummun duniya. Bayanin ya kuma kara da cewa; A daidai lokacin da al’ummar Falasdinu suke fuskantar zalunci,ta’addanci, da amfani da karfi a kansu, da kuma yin barna a masallacin Kudus, da majami’u, makarantu, asibitoci da kuma cibiyoyin MDD, da kuma shiru din da duniya ta yi, hakan yana nufin cewa ‘yan sahayoniya masu aiki da duk wata ka’ida ko doka ta kasa da kasa balle kuma halayyar kwarai, a dalilin hakan, hanya daya tilo da za a iya sauya wannan yanayin shi...
Har ila yau, masu bincike sun gano wasu tsoffin dabarun hana koguna da madatsun ruwa ambaliya da yadda aka tsaga manyan hanyoyin ruwa da aka yi amfani da su shekaru 5,000 da suka gabata, a wani tsohon yanki na Zhejiang ta hanyar amfani da kayan binciken muhalli. Binciken ya fayyace wayewar kai na tsara birane da kula da koguna da hanyoyin ruwa irin na Liangzhu a tsohon zamani. Babu shakka, amfani da wayewar kan magabata a zamaninmu na yanzu yana daga cikin sirrin nasarorin da Sinawa ke samu ta fuskar wayewar kai da bunkasa ci gaban kimiyya da fasaha da kere-kere da kirkire-kirkire. Ina fatan kasashenmu na Afirka su dau hannu domin jifar tsuntsu biyu da dutse daya, tabbatar da...
Gwamnonin Arewa sun aike wa Gwamna Dikko Umar Radda na Jihar Katsina, saƙon ta’aziyya game da rasuwar mahaifiyarsa, Hajiya Safara’u Umaru Baribari, wadda ta rasu tana da shekaru 93. Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa (NSGF) kuma Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya bayyana Hajiya Safara’u a matsayin uwa mai tausayi da riƙon gaskiya, wadda ta rayu bisa turbar Allah da hidima wa al’umma. ’Yan bindiga sun kashe jami’an tsaro 10, sun jikkata 14 a Zamfara Mahaifiyar Gwamnan Katsina ta rasu A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Ismaila Uba Misilli, ya fitar, Gwamna Yahaya, ya iyalanta da shugabanni za su yi kewarta. Ya kuma buƙaci Gwamna Radda da iyalansa da su ci gaba da girmama tarihinta ta...
Wasu ’yan bindiga sun kai hari Kasuwar Kayan Miya ta Akinyele, kusa da Ibadan, Babban Birnin Jihar Oyo, inda suka sace Shugaban Kasuwar, Alhaji Usman Yako. Bayanan da muka samu daga shugabannin kasuwar sun nuna cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 7 na dare, jim kadan bayan an idar da sallar Magriba. Ƙungiyoyin ƙwadago sun buƙaci Tinubu ya mayar da Fubara kan kujerarsa Goman Ƙarshe: Dama ta ƙarshe ga mai neman rahamar Allah Mataimakin Shugaban Kasuwar, Alhaji Abdul’aziz Abdulwasi’u (Dan Kashi), ya tabbatar da faruwar lamarin. “Bayan na koma gida domin shan ruwa, sai yarona ya kira ni ta waya ya shaida min cewa wasu mutane ɗauke da bindigogi sun shigo kasuwa suna harbe-harbe. “Sun tilasta Shugaban Kasuwa...
Gwamnatin HKI ta bayyana damuwarta da jibge sojojin da gwamnatin kasar masar take yi a yankin Sinaa kusa da kan iyakar kasar da HKI. Tun bayan da gwamnatin HKI ta gama lalata makaman gwamnatin kasar Siriya bayan ta taimaka ta kawo dan Daesh kan kujerar shugabancin kasar ta Siriya, kuma ta bayyana cewa yankunan da ta mamaye a kasar Siriya sun zama HKI ne har abada.take nuna damuwa da kasar Masar. Banda haka mun ga yadda sabon shugaban kasar ta Siriya Julani ya yi shiri da bakinsa a kan mamayar da HKI takewa kasar Siriya da kuma yadda ta kai hare-hare fiye da dubu guda kan kasar tana lalata makamanta, ko wa ya fahinci cewa, siriya ta gama yawo,. Kuma...
An sanya dokar hana fita a Jihar Jigawa tare da kafa wuraren bincike domin magance matsalar rashin tsaro da ta biyo bayan kisan wata amarya mai shekaru 22, Zainab Ibrahim. An yanke wannan shawara ne a taron da aka gudanar a Hadejia, wanda ya haɗa jami’an majalisar masarautar da hukumomin ƙananan hukumomin Malam Madori da Kirikasamma. Sojoji sun kashe ’yan bindiga 31, sun lalata sansaninsu a Katsina HOTUNA: NDLEA ta kama hodar iblis da aka ɓoye a cikin carbi da takalma Manufar taron ita ce samo mafita ga matsalolin tsaro da ke ƙara ta’azzara a yankin. Da yake jawabi a madadin majalisar masarauta, Galadiman Hadejia, Usman Abdul’aziz, ya nuna damuwa matuƙa game da yawaitar hare-haren da ake kai wa jama’a....
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Kafofin yada labaran kasar Rasha sun yi ta jinjina wa wani sojan kasar a matsayin jarumi saboda ci gaba da fafatawa a yankin Kursk tsawon mako guda bayan harbin da aka yi masa a ka. Mutumin da ba a bayyana sunansa ba, wanda aka ruwaito cewa yana cikin Brigade na 155 na Marine na Rukunin Pacific Fleet na Rasha, ya ci gaba fafatawa da sojojin Ukraine a Kursk lokacin da aka harbe shi. Nijar ta kori wasu kamfanonin China 3 daga ƙasar Faɗuwar farashin kayan abinci a watan azumi ta shammace mu – ‘Yan kasuwa A lokacin an harbi hular kansa, amma yana tunanin tabbas harsashin ya huda cikinta. Ya samu kumburi a saman idonsa, wanda daga ƙarshe ya sa...
’Yan kasuwa na ci gaba da neman mafita bayan karyewar farashin kayan masarufi, musamman abinci da ake ci gaba da samu, sabanin yadda aka saba fuskantar tashin gwauron zabon farashi a lokacin azumi a Nijeriya. Farashin kayan abincin ya karye ne a lokacin da wasu ’yan kasuwar suka riga suka saye amfanin gona suka boye tun a lokacin kaka, da nufin rubanya kudinsu idan farashinsa ya yi tashin gwauron zabo daga musamman a lokaci irin wannan na azumin watan Ramadan, da wasu bayin Allah suke saya don raba wa mabukata. ’Yan bindiga na neman N30m domin fansar gwarzon gasar Al-Qur’ani a Katsina ’Yan Nijeriya su ƙara haƙuri kan matakan da muke ɗauka — Tinubu Kudin hatsi irin su shinkafa da...
Jami’ar kula da manufofin ketare ta Tarayyar Turai, Kaya Kalas, ta tabbatar da cewa, EU za ta iya sake kakaba takunkumi kan kasar Syria, idan aka samu tabarbarewar lamurra, tana mai nuni da yadda ake cin zarafin fararen hula a gabar tekun Syria. Kaya Kalas ta shaidawa kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya cewa, “Muna shirye-shiryen mayar da takunkumi kan Syria, idan muka ga tabarbarewar lamurra na ci gaba, inda ta jaddada cewa, dole ne mika mulki ya kasance cikin lumana da kuma hadin kai, kuma dole ne a kare fararen hula a kowane hali.” Ta bukaci dukkan masu ruwa da tsaki na waje da su mutunta hadin kan Syria, da kuma iko da iyakokinta.”
Adelaja ya jaddada mahimmancin ƙarfafa musayar bayanan sirri da haɗin gwiwar hukumomi, duba da irin kaifin basira da masu fasa-kwari ke amfani da wasu a ‘yan kwanakin nan wurin cimma muradunsu. “Masu fasa kwauri na ci gaba da bunkasa a ayyukansu, kuma don tunkararsu yadda ya kamata, dole ne mu hada kai ta hanyar bayar da bayanan sirri don cimma nasarar ayyukanmu,” in ji shi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ministan harkokin wajen kasar Sin, Wang Yi ya bayyana a wajen taron manema labaru na ministan harkokin waje da aka shirya a harabar manyan tarukan kasar Sin guda biyu, lokacin da yake magana kan batun Taiwan cewa: suna daya tilo na Taiwan a Majalisar Dinkin Duniya shi ne “Lardin Taiwan na kasar Sin”. Kuma wasu sun yi amannar cewa, hakan ne ya sa manufar babban yankin kasar Sin a kan Taiwan ta zama mai tsaurin gaske. Da take mayar da jawabi game da wannan batu, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Mao Ning, ta bayyana a wani taron manema labarai da aka saba gudanarwa da ya gudana yau 10 ga wata cewa, wannan shi ne daidaitaccen matsayin...
A Talatar nan ne ofishin yada bayanai na majalissar gudanarwar kasar Sin, ya fitar da takardar bayani game da batutuwan da suka shafi sinadarin Fentanyl. Takardar mai taken “Shawo kan sinadarai masu alaka da sinadarin Fentanyl-Gudummawar kasar Sin.” Ta yi fashin baki game da yadda a ‘yan shekarun baya bayan nan, kasar Sin ke ta kara dora muhimmanci kan matakan shawo kan bazuwar sinadarai dangin Fentanyl, kana take ta karfafa hadin gwiwa da sauran sassan kasa da kasa, wajen dakile bazuwar miyagun kwayoyi, da zurfafa hadin kai da sauran kasashe masu ruwa da tsaki, ciki har da Amurka, wajen shawo kan bazuwar sinadarai dangin Fentanyl, da sinadaran da ake samar da shi daga gare su, inda kuma aka cimma manyan...
Ƙamshi abin so ne a wurin kowa. Mata su kasance suna saka turaren wuta a kullum. Su mayar da shi dole kamar yin wanke-wanke. Ko kun san cewa, wannan turaren wutar za a iya amfani da shi da kabbasa domin turara zanin gado da rigar sawa? An horas da masu unguwannin Katsina kan sasanta jama’a Ramadan: Gwamnatin Jigawa ta rage lokacin aiki Bayan haka, akwai turaren humra wadda za a iya shafa shi a gashin kai. Akwai na hammata daban sannan akwai na shafawa kamar mai, wanda aka fi sani da kulacca da kuma na riga. Lallai duk macen da ta kasance cikin ƙamshi, za ta sami girmamamwa a cikin al’umma da kuma mai gidanta. Kuma akwai turaren kanti kamar...
Allah Ya yi wa Sarkin Sasa, Alhaji Haruna Maiyasin rasuwa bayan shafe shekaru 125 a duniya. Fadar Sarkin Sasa da ke Ibadan, babban birnin Jihar Oyo, ce ta bayar da sanarwar rasuwar Sarkin wanda ke riƙe da muƙamin Sardaunan Yamma. HOTUNA: Gobara ta laƙume shaguna 100 a Kasuwar Sakkwato An raba wa ma’aikatan gona babura 200 a Yobe Bayanin rasuwar Sarkin Sasa yana ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Ɗan Masanin Sasa, Alhaji Kasim Ado Yaro ya raba wa manema labarai a ranar Asabar. Ɗan Masanin na Sasa ya ce Alhaji Maiyasin ya rasu ne a yau Asabar bayan fama da rashin lafiya a wani asibiti mai zaman kansa da ke Ibadan. Sarkin Sasa wanda kuma yake riƙe da muƙamin...
Assalamu alaikum uwargida tare da fatan alheri kuma kuna cikin koshin lafiya. Kamar yadda a kullum nake ba da shawarar cewa, yana da kyau uwargida ta ƙware wajen girke-girke, wato yana da matukar muhimmanci ta ƙware wajen girkin gargajiya da na zamani da kuma na ƙasashen waje. Ramadan: Saudiyya ta bai wa Kano da wasu jihohi kyautar dabino katan 1,250 Falalar Ramadan: Wata na rahama, gafara, da tsira daga wuta Don haka ne a yau na kawo muku yadda ake ‘spring roll’. Bayan abincin buɗe baki, uwargida za ta iya koyan wannan girki a matsayin sana’a da za ta iya kawo mata kuɗi. Abubuwan da ake bukata: · Karas · Albasa · Attaruhu · Tafarnuwa · Kabeji · Kayan dandano...
Sakamakon wannan ragin da aka samu, yanzu gidan mai na MRS zai sayar da man a jihar Legas a kan naira 860, sai mutanen da suke yankin kudu maso yamma kuma da za su saya a kan naira 870, sai kuma mutanen Arewa da za su saya a kan naira 880, sai mutanen kudu maso kudu da kudu maso gabas da za su saya akan naira 890. Kamfanin ya yi kira ga ‘yan kasuwa da su taimaka wajen ganin sauƙin ya je inda ake bukata, domin an yi ragin ne don sauƙaƙawa al’umma. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp...
Rundinar kare juyin juya halin musulinci ta Iran, ta bayyana bikin jana’izar sakataren kungiyar Hezbollah ta Lebanon mai rasuwa Sayyed Hassan Nasrallah da kuma Sayyed Safiedinne da aka gudanar a matsayin wani babban sako na ‘yan gwagwarmaya ga duniya baki daya. Wannan babban taron da akayi a Beirut abun tarihi ne ga duniyar musulmi, ya kuma nuna cewa kungiyar Hizbullah, na da karfinta da kuma akidar kyamar sahyoniyawan. Sanarwar ta kara da cewa: “Bikin da ya samu halartar miliyoyin mutane, a daidai lokacin da ake barazana da jiragen yakin Isra’ila, ya zama wata alama ta karfin Musulunci da cikakken hadin kan al’ummar kasar Labanon. Sanarwar ta yi nuni da cewa, gagarumin taron makoki daga kasashe daban-daban, addinai da kabilu, da...

Gwamnatin Iraki Ta Kokawa Sabuwar Gwamnatin Siriya Dangane Da Barazanar Mayakan Daesh Da Suka Rage A Kasar
Shugaban hukumar Leken asiri na kasar Iraki Hamid al-Shatri ya bayyana cewa gwamnatin kasar Iraki ta isar da sako ga sabuwar gwamnatin kasar Siriya dangane da samuwar ragowar mayakan kungiyar yan ta’adda ta Daesh a wasu yankunan kasar. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta Nakalto Hamid al-Shatri ya na fadar haka ga kafafen yada labarai a birnin Bagdaza, sannan ya kara da cewa al-amuran tsaro a kasashen biyu suna hade juna ne, don haka dole ne gwamnatocin kasashen biyu su yi aiki tare don ganin bayan wadannan yan ta’adda, masu kafirta musulmi. Kamfanin dillancin labaran INA na kasar Iraki ya nakalto al-Shatri yana fadar haka a taro na 7TH na tattaunawar Bagadaza a jiya Lahadi. Ya kara da...
Dakarun gwagwarmaya a Iraki za su ci gaba da ayyuka bisa tafarkin babban sakataren kungiyar Hizbullah Sayyid Hasan Nasrallah, wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen kare wadanda ake zalunta, kamar yadda Qais al-Khazali, babban sakataren kungiyar Asa’ib Ahl al-Haq ya bayyana. Da yake magana a ranar wannan Lahadin, al-Khazali ya jinjinawa Sayyed Nasrallah, yana mai bayyana shi a matsayin babban mutum wanda ya shafe tsawon rayuwarsa a tafarkin jihadi da kare wadanda ake zalunta. Ya kara tabbatar da cewa babu makawa wa’adin Sayyed Nasrallah na samun nasara a kan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila yana zuwa. “Mun yi alkawarin shrda ma Nasrallah cewa, za mu ci gaba da tafiya a kan wannan tafarki har zuwa lokacin da za a tsarkakae kasar...
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa matukar aka samu mamaya to za a samu manyan mutane irin shahid Sayyeed Hasan Nasrallah da za su tsaya tsayin daka kan yaki da hakan, kuma ba za su bari ‘yan mamaya su cimma manufarsu ba. Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya tabbatar da cewa, Hizbullah tana nan a raye kuma tana ci gaba da bin tafarkinta mai daraja fiye da kowane lokaci a baya. A yayin zaman majalisar ministocin kasar Iran, Pezeshkian ya bayyana cewa, matukar dai abin ake yi na zalunci da danniya a kan masu rauni zai ci gaba, to kuwa tabbas ba za a rasa mutane irin Nasrallah ba, masu tsayin daka da jajircewa wajen tunkarar zalunci da...
Babban sakataren kungiyar Hizbullah Sayyid Hassan Nasrallah Sheikh Na’im Kassim ya bayyana Shahidin al’umma Sayyid Hassan Nasrallah da cewa, jagora ne na musamman na al’ummun larabawa da musulmi kuma shugaban gwgawarmaya. A cikin jawabin da ya gabatar a lokacin jana’izar Shahid Sayyid Hassan Nasrallah, da Shahid Hashim Safiyuddin, inda ya bayyan cewa: A wannan rana muna yin ban kwana da jagora na tarihi na musamman wanda kuma yake a matsayin alkiblar ‘yantattun na duniya. Sheik Na’im Kassim ya kuma ce; Sayyid Hassan Nasrallah ya kasance wanda ‘yan gwgawarmaya suke kauna, wanda Falasdinu da birnin Kudus ne manufarsa, ya kuma taka rawa wajen farfado da batun kare hakkokin Falasdinawa. Babban sakataren kungiyar ta Hizbullah Sheikh Na’im Kassim ya kuma ce; Sayyid...

Ministan Wajen Sin Ya Yi Kiran Hadin Gwiwar Kasashen G20 Don Gina Duniya Mai Adalci Da Ci Gaba Na Bai-daya
Taron na farko na ministocin harkokin wajen G20 a karkashin shugabancin Afirka ta Kudu ya kasance mai cike da tarihi, domin shi ne taron ministocin wajen kungiyar na farko a nahiyar Afirka, kamar yadda ministan huldar kasa da kasa da hadin gwiwa na Afirka ta Kudu, Ronald Lamola ya bayyana, yayin da yake yabawa da taron, a wani taron manema labarai bayan kammala taron, inda har ila yau ya kara da cewa, taron “mai matukar fa’ida” ya yi gagarumar tattaunawa a kan dabarun da suka shafi yanayin shiyyoyin duniya da tasirinsu a kan gudanar da ayyukansu. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Kocin Manchester United Ruben Amorim ya bayyan cewar Kocin ƙungiyar ƙwallon kafa ta Everton David Moyes ba mutum ne wanda za a raina iyawarshi a harkar kwallon ƙafa ba, David Moyes ya na yin aiki mai kyau na farfado da Everton fiye da yadda na ke yi cikin ƙanƙanin lokaci a Old Trafford inji Amorim. Amorim zai fafata da Kocin Everton Moyes a ranar Asabar yayin da yake kokarin fitar da United daga koma bayan da ta ke fuskanta, tsohon kocin na Sporting Lisbon ya lashe wasanni huɗu ya yi rashin nasara a wasanni takwas a wasannin gasar Firimiya 12 da ya jagoranci Manche’ster United tun bayan zuwanshi a watan Nuwamba. Juma Bah: Balladolid Za Ta Kai Manchester City Kara...

Binciken Ra’ayoyi Na CGTN: Watan Daya Da Dawowar Trump Mulki, Mutanen Duniya Sun Ce Da Wuya A Ce An Gamsu Da Salonsa
Binciken Ra’ayoyi Na CGTN: Watan Daya Da Dawowar Trump Mulki, Mutanen Duniya Sun Ce Da Wuya A Ce An Gamsu Da Salonsa
Gwamnatin Tarayya, ta bayyana cewa ba ta shigo da kayan abinci daga ƙasashen waje ba, duk da cewa farashin kayan abinci ya ragu a kasuwanni. Ministan Aikin Gona da Samar da Abinci, Farfesa Abubakar Kyari, ya bayyana cewa, ko da yake gwamnatin ta yi tunanin shigo da abinci a lokacin da farashinsa ya yi tashin gwauron zabo, daga bisani ta janye wannan shawarar. An ƙwace miliyoyin daloli, gidajen da ke da alaƙa da Emefiele Babban mai kai wa Bello Turji makamai ya shiga hannu Ministan ya danganta saukar farashin kayan abinci da ƙoƙarin manoma da suka koma gonaki a daminar bara, wanda ya sa amfanin gona ya yi yawa. Ya kuma buƙaci ‘yan kasuwa da su rage farashi domin jama’a...

Babban Jami’i A Kungiyar JIhadul-Islami Ya Ce: Gudumawar Marigayi Sayyid Hasan Nasrullahi Ba Zai Fadu Ba
Jimi’in ofishin siyasa na kungiyar jihadul-Islami ya bayyana cewa: Marigayi Sayyid Hasan Nasrallah ya baiwa Falastinu da gwagwarmaya abin da harshe ba zai iya siffanta shi ba Mamba a ofishin siyasa na kungiyar gwagwarmaya ta Jihadul-Islami ta Falasdinu Ihsan Ataya ya yaba da irin tsayin dakan da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi a fagen goyon bayan hakkokin Falasdinawa da gwagwarmayarsu, yana mai jaddada cewa: Shahidin al’ummar Sayyed Hassan Nasrallah ya gabatar wa Falasdinu da gwagwarmaya abin da harshe ba zai iya ambata ba. A cikin wata hira ta musamman da ya yi da tashar talabijin ta Al-Alam, Adaya ya yi cikakken bayani kan yarjejeniyar musayar fursunoni tsakanin ‘yan gwagwarmayar Falasdinawa da yahudawan sahyoniya, yana mai jaddada cewa: Gwagwarmaya...
Da yake jawabi ga manema labarai a Abuja a ranar Laraba, Ogbugo Ukoha, Babban Darakta a sashen rarraba mai tare da adanawa na NMDPRA, ya ce matakin ya biyo bayan karuwar firgicin hadurran da ke tattare da manyan motocin dakon man. “Kwamitin fasaha na masu ruwa da tsaki ya gana a yau don cimma wasu muhimman kudurori guda 10 da nufin rage karuwar yawan hadurran tankokin mai da ke janyo asarar rayuka,” in ji Ukoha. An cimma wannan matsaya ne bayan tattaunawa da manyan masu ruwa da tsaki da suka hada da DSS, hukumar kashe gobara ta tarayya, hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC), kungiyar masu sufurin mota ta kasa (NARTO), kungiyar ma’aikatan man fetur da iskar gas...
Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Gwamnatin mamayar Isra’ila ta fuskanci cewa dole ta mika wuya tare da amincewa da sulhu da ‘yan gwagwarmaya da ta nemi murkushe su Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa: Yahudawan sahayoniyya ba su cimma ko daya daga cikin munanan manufofinta ba, kuma daga karshe ya zama tilasta su mika wuya tare da amincewa da sulhu da bangarorin da suke son kawar da su. Babban sakataren kungiyar jihadul-Islami ta Falasdinu Ziyad Nakhalah, da ya ziyarci birnin Tehran a karkashin jagorancin wata tawaga don tuntubar hukumomin kasar Iran ya gana da ministan harkokin wajen kasar Sayyid Abbas Araqchi a yammacin jiya Talata. Haka nan yayin da yake ishara da halaltacciyar gwagwarmayar...
Shi kuwa tsohon Janar Manaja na Hukumar ta NPA Joshua Asanga, ya jaddda mahimmancin amincewa da karin biyan harajin wanda ya sanar da cewa, sahalewar za ta taimaka wajen samar da kayan aiki a Tashar Jiragen Ruwan, inda kuma shi ma wani mai ruwa da tsaki a fannin ya yi kira da a zuba hannun jari a wasu bangarori na Tashar. Mahukunta a bangaren tafiyar da Tashohin Jiragen Ruwa a fadin duniya, sun dogara ne, wajen samar da kudaden shiga domin su samu damar ci gaba da kula da kayan gudanar da ayyukansu da kuma kara tabbatar da tsaro, a Tashohin Jiragen Ruwan su. Bugu da kari, wasu kararru a fannin sun bayyana cewa, harajin da Hukumar NPA ke karba...
Jami’ai a yankin kudu masu yammacin Pakistan sun ce aƙalla mutum 11 sun mutu sakamakon fashewar wata motar da ke ɗauke da masu haƙar ma’adinai a yankin Harnai da ke lardin Balochistan. Jami’an yankin sun ce suna ci gaba da bincike kan abin da ya haifar da fashewar, to amma ana kyautata zaton abubuwan fashewa ne da ƴanbindiga ke amfani da su. Lardin Balochistan mai albarkar ma’ainai ya shafe gomman shekaru yana fama da matsalolin ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai na ƙabilar Baloch.

’Yan Wasan Motsa Jiki Na Asiya Sun Yi Murnar Bikin Sabuwar Shekara Bisa Kalandar Gargajiya Ta Sin A Harbin
An gabatar da bikin mu’ammalar al’adu a jiya Litinin a birnin Harbin da ake wa lakabin “Birnin kankara”, yayin da ake gudanar da gasar wasannin motsa jiki na lokacin hunturu ta Asiya karo na 9 a birnin. An yi wannan gaggarumin biki ne bisa jigon “bikin sabuwar shekara ta kalandar gargajiya ta kasar Sin, wato bikin bazara karo na farko bayan shigar da shi jerin bukukuwan gargajiya da aka gada daga kaka da kakanni a duniya, wanda ya zo a kan gabar gasar wasannin motsa jiki ta lokacin hunturu ta Asiya.” ’Yan wasan motsa jiki 20 daga kasar Mongoliya da Thailand da Philipphines da Vietnam da Indiya da Nepal da dai sauran wakilan tawagogin wasannin motsa jiki da ’yan jarida...

Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci Ta Iran Ya Ce; Kasashen Iran Da Iraki Zasu Kare Kungiyoyin Gwagwarmaya
Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran ya jaddada cewa: Iran da Iraki sun kuduri aniyar kare kungiyoyin gwagwarmaya Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran Muhammad Baqir Qalibaf ya jaddada cewa: Iran da Iraki sun kuduri aniyar kare wannan gwagwarmaya da ta hana makiya numfasawa a yankin. Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran Muhammad Baqir Qalibaf a wani taron manema labarai da ya yi da takwaransa na Iraki Mahmoud al-Mashhadani, ya bayyana cewa: Kasashen Iran da Iraki sun kuduri aniyar kare gwagwarmaya, yana mai jaddada cewa: Iran da kawarta Iraki sun kuduri aniyar marawa bangaren gwagwarmaya baya domin kare Musulunci da martabar al’ummar musulmi. Baqir Qalibaf ya kara da cewa: Sun ba da muhimmanci wajen raya hanyar layin dogo, musamman sabuwar...
Bisa kididdigar da aka samu daga dandalin yanar gizo, adadin kudaden da aka samu daga fina-finan kasar Sin da suka yi zarra a kasuwa wato box office a 2025 ya zarce yuan biliyan 5.047, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 696, wanda ya zarce rawar da manyan fina-finan Arewacin Amurka suka taka a kasuwa, wanda ya kasance a matsayi na daya na wucin gadi a kasuwar fina-finan duniya. (Mai fassara: Mohammed Yahaya)
Shugaban kasar Iran Mas’ud Fizishkiyan ya bayyana cewa; babbar matsalar da duniyar musulmi ke fuskanta ta samo tushe ne daga yin isa daga koyarwar musuluncin, da babu abinda hakan ya haddasa sai rabuwar kawuna da sabani, ya kuma bai wa makiya kafar da za su shiga. Shugaban kasar ta Iran wanda ya aike da sako zuwa wurin rufe ‘gasar karatun akur’ani mai girma karo na 41 da aka yi a birnin Mashhad, ya bayyana cewa; Alkur’ani mai girma yana yin Magana ne da musulmi a matsayin al’umma daya dunkulalliya, yake kuma yin kira a gare su da su yi riko da igiyar Allah da hadinkai, domin hana rabuwar kawuna. Shugaban na kasar Iran ya kuma ce; Shakka babu, wani sashe...
Wani direba da ake zargin yana cikin maye ya kutsa da motarsa cikin wani gungu na sojoji daga barikin Myoung da ke Yaba dake jihar Legas, yayin da suke atisayen motsa jiki da safiyar yau Juma’a, lamarin da ake jin tsoron cewa ya yi sanadiyyar mutuwar Sojojin da dama. Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya haifar da tashin hankali a cikin sansanin Sojojin. Wani Soja da ya tsira daga harin ya bayyana cewa, “Jini ne ko’ina. Na tsira ne kawai saboda ina baya.” Mun Kashe Ƴan Ta’adda Sama Da 70, Kafin Mu Yi Rashin 22 – Sojoji Sojoji Sun Ƙwato Makamai, Sun Ci Gaba Da Neman Bello Turji A Zamfara Sojan (wanda ba a bayyana sunansa ba) ya ce a...
Kungiyar Hamas ta yaba da rawar da Iran ke takawa wajen tallafawa al’ummar Falasdinu masu neman ‘yanci kai Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya gana da wata tawaga daga jagororin kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas, karkashin jagorancin shugaban majalisar gudanarwa (wanda aka kafa bayan kisan jagoran kungiyar Yahya Sinwar) Mohammed Darwish, a babban birnin Qatar, Doha a jiya Alhamis. Sanarwar da kungiyar Hamas ta fitar ta bayyana cewa, tawagar kungiyar ta hada da shugabannin Khalil Al-Hayya, Hussam Badran, Izzat Al-Rishq da Basem Na’im. Darwish ya yaba da rawar da Iran ta taka wajen tallafa wa al’ummar Falasdinu masu neman ‘yancin kai, yana mai jaddada cewa: “Harin Daukan Fansa naAmbaliysar Al-Aqsa Mai Albarka” wani ci gaba ne a yunkurin al’ummar...

Kafafen Yasa Labaran Sweden Sun Tabbatar Da Mutuwar Selwan Momika Wanda ya Kona Alkuranai A Kasar A shekarum Baya
Kafafen yada labarai na kasar Sweden sun bayyana cewa an sami gawar Selwan Momika dan shekara 38 a duniya a wani gida daga kudancin birnin Stokhom na kasar. Selwan dai dan asalin kasar Iraki ne, wadanda yake gudun hijira a kasar ta Sweden tun, amma ya bayyana kansa a kafafen watsa labarai a shekara ta 2023 inda yake kona alkur’ani mai girma don wulakanta shi. Saboda kuma nuna kiyayyarsa ga addinin musulunci da musulmi. Gwamnatin kasar Sweden dai ta halattawa Selwan yin haka a karkashin dokar yencin fadin albarkacin baki wanda kasashen yamma musamman a turai suka amince da ita. Sai dai wannan aikin nasa ya gamu da fushin musulmi a duk fadin duniya. Yansan da a birnin Stokhom sun...
Firai ministan HKI Banyamin Natanyahu Ya bada umurnin a dakatar da musayar fursinoni da kungiyoyi masu gwagwarmaya a Gaza. Bayan da Falasdinawa sun Saki mutane 8 ya zuwa yanzu, yahudawa 3 da kuma wasu yan kasar Thailand 5. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kafafen yada labaran yahudawan suna fadar haka. Sun kara da cewa firai ministan ya ce a dakatar da sakin fursinoni Falasdinawa 110 wadanda yakamata HKI ta sallamesu a yau. Kafin haka dai Falasdinawan sun salami wadannan fursinonin yahudawan 8 ne a zagaye uku na musayar fursinoni da kuma janyewar sojojin yahudawan daga yankunan gaza. Majiyar ofishin firay ministan ya bayyana cewa an dakatar da musayar fursinonin ne har sai abinda hali yayi. Da...
Jami’an tsaro sun mamaye Sakatariyar Jam’iyyar PDP, bayan rikici ya ɓarke kan shugabancin jam’iyyar. Rikicin ya kunno kai ne tsakanin Samuel Anyanwu da Sunday Ude-Okoye kan wanda ke da haƙƙin zama Sakataren jam’iyyar na ƙasa. Matashiyar da ta watsa wa mai naƙuda tafasasshen ruwa ta shiga hannu Me kuka sani game da ficewar Mali, Nijar, da Burkina Faso daga ECOWAS? Rikicin ya fara ne lokacin da duka mutane biyun suka iso taron kwamitin amintattun. A lokacin taron, wani hadimin Anyanwu ya tilasta wa Ude-Okoye fita daga zauren taron, wanda hakan ya janyo gardama tsakanin magoya bayan ɓangarorin biyu. Jami’an tsaro sun shiga tsakani domin kwantar da tarzoma. Matsalar ta samo asali ne bayan Anyanwu ya yi murabus daga kujerarsa don...
Babban sakataren kungiyar Hizbullahi ta kasar Lebanon ya ce: Batun rusa gwagwarmaya ta zama tatsuniya kuma batun Falasdinawa ya dawo cikin fagen siyasar duniya Babban sakataren kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta kasar Lebanon, Sheikh Na’im Qassem ya jaddada cewa: Harin daukan fans ana “Ambaliyar Al-Aqsa” ta cimma burinta na mayar da al’ummar Falastinu a fagen kasa da kasa, yana mai cewa; Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta zame a matsayin kungiyar ta’addanci ta masu aikata laifuka da kisa kiyashi a idon duniya. Babban sakataren kungiyar ta Hizbullah Sheikh Na’im Qasem ya bayyana a wani jawabi da ya gabatar a yammacin jiya Litinin game da sabbin abubuwan da ke faruwa a kasar Lebanon da kuma yankin, inda ya ce: “Hare-haren wuce...
Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka, Sharhin bayan labarammu zai yi magana a kan “jajircewar mutanen kudancin kasar Lebanon fuskantar sojojin HKI’ yan mamaya’ wanda ni tahir amin. ///…A Jiya lahadi be wa’adin ficewar HKI daga yankuna da garuruwan da suka mammaye a kudancin kasar Lebanon, amma karfe 4 da safe yana cika mutanen wadannan yankuna suka kwarara zuwa gidajensi, amma ko da suka isa sai suka ga cewa sojojin kasar Lebanon sun sha shinge don hana mutane wucewa zuwa wadannan wurare, don har yanzun akwai sojojin HKI a yankin suna iya kashe su. Banda haka sojojin HKI sun kara wayoyin wasu daga cikin mutanen wadannan yankuna, suna fada masu cewa kada su kuskura su shiga wadannan yankuna. Amma...

Sanarwar Yiwuwar Kai Harin Ta’addanci Kano Lokacin Maulidi: Mun Cafke Wani Da Bama-bamai – Kwamishina
Ya bayyana cewa, wadanda ake zargin sun tsere daga jihar biyo bayan tona musu asiri, amma an cafko daya an dawo da shi Kano bayan ya tsere da farko. CP Dogo, ya jaddada mahimmancin samun rahoton leken asiri wajen dakile barazanar da ake iya fuskanta, tare da yin cikakken bayani kan yadda ‘yansanda suka hada kai da masu ruwa da tsaki don inganta tsaro a lokacin taron.
Shugaban kasar Sin Xi Jinping da sauran jagorori na kasar Sin sun ziyarci ko kuma sun gayyaci wasu su ziyarci tsoffin jami’ai da suka yi ritaya, sun mika gaisuwa gabanin bikin Bazara na al’ummar Sinawa na ranar 29 ga watan Janairun nan. Xi, wanda kuma shi ne babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, kuma shugaban kwamitin koli na sojan kasar, da sauran jagororin kasar, sun taya tsoffin jami’an da suka yi ritaya murnar bikin Bazara, tare da musu fatan karin lafiya da kuma tsawon rai. A nasu bangaren kuwa, tsoffin jami’an da suka yi ritaya sun yaba da ayyukan kwamitin koli na jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin a shekarar da ta gabata, tare da bayyana goyon bayansu...