’Yan Wasan Motsa Jiki Na Asiya Sun Yi Murnar Bikin Sabuwar Shekara Bisa Kalandar Gargajiya Ta Sin A Harbin
Published: 12th, February 2025 GMT
An gabatar da bikin mu’ammalar al’adu a jiya Litinin a birnin Harbin da ake wa lakabin “Birnin kankara”, yayin da ake gudanar da gasar wasannin motsa jiki na lokacin hunturu ta Asiya karo na 9 a birnin. An yi wannan gaggarumin biki ne bisa jigon “bikin sabuwar shekara ta kalandar gargajiya ta kasar Sin, wato bikin bazara karo na farko bayan shigar da shi jerin bukukuwan gargajiya da aka gada daga kaka da kakanni a duniya, wanda ya zo a kan gabar gasar wasannin motsa jiki ta lokacin hunturu ta Asiya.
’Yan wasan motsa jiki 20 daga kasar Mongoliya da Thailand da Philipphines da Vietnam da Indiya da Nepal da dai sauran wakilan tawagogin wasannin motsa jiki da ’yan jarida sun yi murnar bikin bazara tare, a dakin watsa labarai na CMG, a bikin baje kolin kayayyakin kankara dake Harbin bayan sun fafata a gasanni daban-daban. (Amina Xu)
এছাড়াও পড়ুন:
Barcelona Na Shirin Ɗauko Victor Osimhen Na Galatasaray
Matsalar, kamar ko yaushe, ita ce gaskiyar cewa Osimhen ba zai yi arha ba kuma Barcelona za ta yi fama da biyan manyan “yan wasa a bazara mai zuwa, Julian Alvarez da Erling Haaland sun riga sun kasance cikin wadanda kungiyar ta Catalonia ta fara nema, yayin da kuma ta ke kallon Etta Eyong da Serhou Guirassy na Borrusia Dortmund.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA