Mutum 11 sun mutu bayan fashewar wata mota a Pakistan
Published: 14th, February 2025 GMT
Jami’ai a yankin kudu masu yammacin Pakistan sun ce aƙalla mutum 11 sun mutu sakamakon fashewar wata motar da ke ɗauke da masu haƙar ma’adinai a yankin Harnai da ke lardin Balochistan.
Jami’an yankin sun ce suna ci gaba da bincike kan abin da ya haifar da fashewar, to amma ana kyautata zaton abubuwan fashewa ne da ƴanbindiga ke amfani da su.
Lardin Balochistan mai albarkar ma’ainai ya shafe gomman shekaru yana fama da matsalolin ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai na ƙabilar Baloch.
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Fashewa
এছাড়াও পড়ুন:
An Tsare Wani Mutum A Gidan Yari Kan Zargin Kashe Matarsa Saboda Ƙuli-Ƙuli A Kano
Mai shari’a Dahiru ya amince da buƙatar, ya kuma ɗage shari’ar zuwa ranar 12 ga watan Disamba, 2025, domin ci gaba da sauraron shari’ar.
Ƙuli-ƙuli dai nau’in abin ci ne mai taushi da ake yi da gyaɗa, ana soyawa har sai ya zama ƙura-ƙura ta yadda za a ci cikin nishaɗi.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA