Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka, Sharhin bayan labarammu zai yi magana a kan “jajircewar mutanen kudancin kasar Lebanon fuskantar sojojin HKI’ yan mamaya’ wanda ni tahir amin.

///…A Jiya lahadi be wa’adin ficewar HKI daga yankuna da garuruwan da suka mammaye a kudancin kasar Lebanon, amma karfe 4 da safe yana cika mutanen wadannan yankuna suka kwarara zuwa gidajensi, amma ko da suka isa sai suka ga cewa sojojin kasar Lebanon sun sha shinge don hana mutane wucewa zuwa wadannan wurare, don har yanzun akwai sojojin HKI a yankin suna iya kashe su.

Banda haka sojojin HKI sun kara wayoyin wasu daga cikin mutanen wadannan yankuna, suna fada masu cewa kada su kuskura su shiga wadannan yankuna.

Amma sai jerin gwanon mutoci da barbura da mutane masu takawa da kafa kake gani suna kwarara zuwa gidajensu. Gwamnatin kasar Amurka ta bukaci gwamnatin Lebanon su amince a kara lokacin janyewar sojojin HKI daga wadannan yankuna na kudancin kasar Lebanon, har zuwa 18 ga watan Fabrayru mai zuwa, amma gwamnatin ta ki amincea da hakan.

A jiya Lahadi sojojin HKI sun bude wuta kan wasu mutanen kudancin kasar Lebanon wadanda suke son komawa gidajensu, inda suka kashe mutane 18 suka kuma raunata wasu kimani 100 a yankunan daban daban da suke mamaye da su a kasar ta Lebanon.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ya nakalto yadda al-amura suka tafiya a kudancin kasar Lebanon a safiyar ranar litinin, inda wasu suke cewa, ai mune makama mafi hatsari na hazbullah, kuma muna nan kassammu ne ba zamu bar kasarmu gay an mamaya ba.

Wasu sun bayyana cewa a shirye suke su yi shahada a kan kasarsu da akamamaye, kamar yadda wasu suka yi amma ba zasu taba ja da baya a kan matsayinsu ba.

A cikin wannan halin ne shugaban kasar faransa Emanuel Macron, wanda kumakasarsa na daga cikin kwamitin da aka kafa don kula da aiwatar da yarjeniyar ta tsagaita budewa juna wuta tsakanin kungiyar Hizbullah da kuma HKI na kwanaki 60.

Daga karshe dai HKI da kuma Amurka sun rasa na yi sai suka fara janyewa daga yankun kasar Lebanin da suke mamaye da su, suna ficewa mutane suna komawa cikin gidajensu a yau Litinin.

Manufar HKI na fara yaki da kungiyar Hizbullah da farko shi ne hanata tallafawa ko shi yakin da ake fafatawa da kungiyoyin masu gwagwarmaya da ita a gaza, ba tare da ta shiga cikekken yaki da kungiyar ba, amma ganin yadda dubabban daruruwan yahudawa a arewacin kasar Falasdinu da aka mamaye sun kasa komawa gidajensu a yankin, kuma sun zama matsala ga gwamnatin HKI, wannan yasa ta shiga yankin. Gadangan da kungiyar Hizbullah musamman bayan sun sami nasarar kashe shugaban kungiyar Sayyed Hassan Nasarallh.

Amma karfin sojoji da makaman da Hizbullah ta nuna ya kara dulmuya HKI a cikin karin musiba, don hizbullah sun yi amfani da makamai masu linzami wadanda suke kaiwa har gaba da birnin Tel’aviv, ko yafa. A nan ne HKI taga cewa ba zata iya tahammulin musibun ba, don haka sai Amurka ta aika jakadan zuwa kasar Lebanon wacce ta sami nasaran gamsar da kungiyar

Don haka tsagaita budewa juna wuta a Lebanon bukatar HKI ce, kuma saboda gazwarsu shiga kasar Lebanon da kuma isar makaman Hizbullah zuwa cikin tsakiya da ma kudancin kasar Lebanon, har a wasu lokacinda HKI ta rasa sojoji masu yawa a wasu hare-haren Hizbullah.

Amma bayan an tsagauita wuta ne, sai wasu sojojin HKI suka shiga wasu kauyuwa a kasar ta Lebanon suna nemna makaman kungiyar da kuma irin ramukan da suka gina a karakashin kasa don adana makamansu.

Sannan yanzun kuma an tilasta masi ficewa daga kudancin kasar ta Lebanon, idan suna sun wannan tsgaita wuta ta dore, idan kuma sun yi taurine kai ta kuwa za’a koma gidan jiya.

Masu sauraro karshen sharhin bayan labaran Kenan.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: a kudancin kasar Lebanon wadannan yankuna da kungiyar

এছাড়াও পড়ুন:

Ya Kamata Shugaba Tinubu Ya Ƙulla Alaƙa Ta Kut-da-kut Tsakanin Hukumar Shige Da Fice Da Kwastam – Babandede

“Iyakar kasa ba wai kawai yanki ne na tsaro ba. Yanki ne na al’adu; yanki ne na tarihi; haka nan ma yanki ne na tattalin arziki. Kula da shige da fice na da matukar amfani ga ci gabanmu. Wajibi ne Nijeriya ta zuba jari a kan kula da nau’in mutanen da take tacewa wajen shiga kasa da kuma irin mutanen da muke tacewa wajen fita daga kasa.

“Dole ne mu yi nazarin nau’in ayyukan da bakin-haure ke yi da kuma yadda suke shafar tattalin arzikinmu. Muna bukatar tsame mutanen da ke kawo cikas ga ci gabanmu”, in ji Babandede.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Rundunar Sojin Nijeriya Ta Shirya Wa Janar Musa Faretin Gama Aiki October 31, 2025 Labarai Gwamnatin Tarayya Da Stellar Steel, Sun Sanya Hannu Kan Yarjejeniyar Habaka Karafan Cikin Gida October 31, 2025 Labarai Ƴansanda Sun Kama  Wani Mai Wasa Da Bindiga AK-47 A Cikin Wani Bidiyo A Adamawa October 31, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kasar Qatar Ta Ba Da Tallafin Gaggawa Ga Al’ummar Sudan Bayan Gumurzun El-Fasher
  • Sojojin Amurka Na Kara Fuskantar Venezuwela Adaidai Lokacin da Trump Ke Musanta Batun Kai Hari
  • Shugaban Kasar Najeriya Ya Mayar Da Martani Ga Takwaransa Na Amurka Akan Rikicin Addini
  • Ministan Wajen Malawi: Tsarin Ci Gaban Kasar Sin Ya Samar Da Darussa Ga Kasashe Masu Tasowa
  • Ya Kamata Shugaba Tinubu Ya Ƙulla Alaƙa Ta Kut-da-kut Tsakanin Hukumar Shige Da Fice Da Kwastam – Babandede
  • Matsalar Talauci Da Rashin Tsawon Rai Da ‘Yan Nijeriya Ke Fuskanta
  • Matsalar Tsaro: Ko Sabbin Shugabannin Rundunar Soji Za Su Kawo Sauyi?
  • Shugaban Lebanon Ya Umarci Sojoji Da Su Fuskanci Kutsen Na Isra’ila A Kudancin Kasar
  • Shugaban Lebanon Ya Umarci Sojoji Da Su Fuskanci Duk Wani Kutse Na Isra’ila A Kudancin Kasar
  • Sin Ta Fitar Da Jerin Sakamakon Tattaunawar Tattalin Arziki Da Cinikayya Da Tawagar Kasar Da Ta Amurka Suka Cimma