Sheikh Kassim: Gwagwarmaya Za Ta Ci Gaba Da Dukkanin Karfinta
Published: 23rd, February 2025 GMT
Babban sakataren kungiyar Hizbullah Sayyid Hassan Nasrallah Sheikh Na’im Kassim ya bayyana Shahidin al’umma Sayyid Hassan Nasrallah da cewa, jagora ne na musamman na al’ummun larabawa da musulmi kuma shugaban gwgawarmaya.
A cikin jawabin da ya gabatar a lokacin jana’izar Shahid Sayyid Hassan Nasrallah, da Shahid Hashim Safiyuddin, inda ya bayyan cewa: A wannan rana muna yin ban kwana da jagora na tarihi na musamman wanda kuma yake a matsayin alkiblar ‘yantattun na duniya.
Babban sakataren kungiyar ta Hizbullah Sheikh Na’im Kassim ya kuma ce; Sayyid Shahid Hassan Nasrallah ya narke a cikin yi wa musulunci hidima da kuma a cikin riko da wilaya, ya kuwa yi shahada ne a sahun gaba na fagen daga, kuma zai ci gaba da zama a cikin zukatanmu da ruhinmu, za kuma mu yi riko da amana mu ci gaba da tafiya akan wannan tafarkin.
Shekih Na’im Kassim wanda ya yi Magana da sayyid Nasrallah, ya ce: Kai ne kake fadin cewa, tare za mu kammala wannan tafiyar,ko da kuwa za a kashe mu baki daya. Ya Sayyid Nasrallah muna nan akan wannan alkawalin.”
Sheikh Kassim ya kuma ce; Taron da aka yin a jana’iza, yana a matsayin bayyana ra’ayi ne akan riko da gwagwarmaya wanda irinsa ya yi karanci a tarihin Lebanon.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Sayyid Hassan Nasrallah
এছাড়াও পড়ুন:
Iran ta sha alwashin ci gaba da aiwatar da manufofinta na raya dangantakarta da Nijar
Iran ta sha alwashin ci gaba da aiwatar da manufofinta na raya dangantakarta da Jamhuriyar Nijar.
Mataimakin shugaban kasar na farko Mohammad-Reza Aref ya ce Iran na ci gaba da aiwatar da manufofinta na raya dangantakarta da Nijar da sauran kasashen nahiyar Afirka bisa tsarin juyin juya halin Musulunci.
Aref ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da ministan man fetur na kasar Nijar Sahabi Oumarou wanda ke Tehran, inda yake jagorantar wata tawaga, domin halartar taron hadin gwiwar tattalin arzikin Iran da Afirka karo na uku.
Ya ce da gaske ne gwamnatin Iran mai ci a yanzu tana son raya dangantakar da ke tsakaninta da kasashen Afirka ciki har da Nijar dangane da batutuwan da suka dace.
Ya kara da cewa, “Kasancewar manyan jami’an Nijar a taron da kuma kwamitin hadin gwiwa wani mataki ne mai ban sha’awa na inganta hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu.”
Mataimakin shugaban kasar ya jaddada cewa, bunkasa alaka da Nijar abu ne mai matukar muhimmanci, “idan aka yi la’akari da matsayinta kan ci gaban yanki da na kasa da kasa da kuma ra’ayi daya kan batutuwan Falasdinu da Lebanon.”
A yayin da yake tsokaci ga kiran da ministan na Nijar ya yi na inganta alaka a fannin noma, man fetur, da makamashi mai dorewa, Aref ya bayyana wadannan fannoni guda uku a matsayin muhimman batutuwan da suka shafi dangantakar Iran da Nijar, wadanda ya ce kwamitin hadin gwiwa zai duba su.
Yayin da yake tsokaci kan dangantakar tattalin arziki, ya ce, ya kamata kamfanoni masu zaman kansu na kasashen biyu su zuba jari don ciyar da matakin hadin gwiwa zuwa matsayi mafi girma.