2025-10-15@15:13:26 GMT
إجمالي نتائج البحث: 7020
«garkuwa da mutane»:
(اخبار جدید در صفحه یک)
Li ya ce kasar Sin za ta ci gaba da nuna goyon baya ga jam’iyyar WPK, don ta bayar da jagoranci ga al’ummun kasar Koriya ta Arewa, wajen neman ci gaba bisa halin da kasar take ciki. A sa’i daya kuma, kasar Sin tana fatan karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu a fannoni da dama, kamar aiwatar da ra’ayi daya da shugabannin kasashen biyu suka cimma, tare da kara musayar manyan jami’ai, da mu’amala kan manyan tsare-tsare, ta yadda za a inganta fahimtar siyasa a tsakanin kasashen biyu, tare da cimma sakamako mai kyau bisa hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Koriya ta Arewa. (Mai Fassara: Maryam Yang) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Ma’aikatar Wajen...
Rahotanni sun tabbatar da rasuwar wasu sojoji huɗu, bayan ’yan ta’adda sun kai hari yankin Ngamdu na Jihar Borno. Jihar Borno ta daɗe tana fama da hare-haren ta’addanci, musamman daga ƙungiyar Boko Haram. Sojoji sun hallaka ’yan ta’adda 5 a Borno An yi jana’izar sojojin da ’yan bindiga suka kashe a Kebbi Ko da yake wasu mazauna yankin sun ce sojoji 10 ne suka mutu, sai dai mai magana da yawun rundunar Operation Haɗin Kai, Laftanar Kanar Sani Uba, bai tabbatar da hakan ba cikin sanarwar ya fitar a ranar Juma’a. Amma rahotanni sun bayyana cewa sojoji huɗu ne suka mutu, yayin da wasu biyar suka jikkata a yayin harin. A cewar Kanar Sani, ’yan ta’addan sun yi amfani da...
A cikin nuna jajircewa da hadin kai tsakanin gwamnati jiha da ta tarayya, Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, a ranar Juma’a ya gana da Ministan Ayyuka, Sanata David Umahi, CON, domin yin cikakken bitar aikin titin Abuja–Kaduna–Abuja Taron, wanda aka gudanar a birnin Abuja, ya nuna irin salon jagorancin Gwamna Uba Sani na jajircewarsa wajen tabbatar da kammala wannan muhimmin titi wanda ke da matuƙar tasiri ga tattalin arzikin ƙasa. Tattaunawar ta mayar da hankali ne kan yadda za a hanzarta kammala ɓangaren Abuja–Jere da Kaduna, wanda ke da muhimmanci ga miliyoyin ‘yan Nijeriya da ke amfani da shi kullum wajen sufuri, kasuwanci da hulɗar zamantakewa. Gwamna Uba Sani ya jaddada cewa wannan titin ba...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Sanatan Bauchi Ta Arewa Ya Fice Daga Jam’iyyar PDP October 11, 2025 Siyasa Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu October 9, 2025 Labarai Kotu Ta Yi Watsi Da Ƙarar Da Aka Shigar Da Tinubu Kan Sanya Dokar Ta-Ɓaci A Ribas October 2, 2025
Tukur Muhammad Fakum, daya daga cikin jagororin al’ummar ya shaida wa BBC cewa an riga an kai makura, don haka a yanzu fatan su kawai bai wuce neman wa kai mafita ba. Ya ce ”Mu yanzu muna nan muna gangami, mai ‘yar karamar gona ya sayar, mai dan karamin gida ya sayar, in muka sayi bindigogi a ba matasa su ma su yi kokari su kare mu. ”Gwamnati ta ba mu kariya, idan kuma ba ta iyawa to ta bamu makamai a ba matasa, su matasa na iya kare rayukansu da garuruwan su,” in ji Tukur Muhammad Fakum. Dangane da halin da irin barnar da ‘yan bindigar suka yi masu kuwa, Tukur Muhammad Fakum ya ce ”Babu dai...
Ya bayyana cewa an riga an hada wadanda aka ceto da iyalansu, kuma ana ci gaba da gudanar da bincike da aikin ceton domin gano wadanda suka aikata laifin da kuma kubutar da sauran wadanda ake tsare da su, idan suna nan. A halin da ake ciki kuma, kwamandan Runduna ta 6 ta Sojan Nijeriya, Birgediya Janar Kingsley Chidiebere Uwa, ya yaba da saurin daukar mataki da hadin kai tsakanin sojoji da ‘yansanda wanda ya kai ga nasarar aikin ceton. Ya sake jaddada kudirin rundunar wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a a Jihar Taraba. Sai dai, ya bukaci jama’a da su ci gaba da bai wa sojoji da sauran hukumomin tsaro goyon baya ta hanyar...
Mataimakin shugaban kasar Iran Mohammad Reza Aref ya bayyana cewa, batun kifar da gwamnatin JMI bayan yakin kwanaki 12 ya kuma fita daga abinda makiya zasu iya. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar yanakalto mataimakin shugaban kasa na farko yana fadar haka a ranar Alhamis da ta gabata, ya kuma kara da cewa a cikin yakin kwanaki 12 wanda kasashen Amurka da HKI suka dorawa kasar sun so su kifar da gwamnatin JMI a cikin kwanaki 3 zuwa 4 amma suka kasa. Ya ce hatta babban sakataren MDD Antonio Guterres ya tabbatar da haka a wata tattaunawa da shi dangane daha. Ya kuma tabbatar da cewa makiyan JMI ba zasu iya tumbuke tsarin ba. Yasashen yamma musamman Amurka suna kokarin...
Masu zanga-zanga a nan Iran a jiya jumma’a a manya-manyan garuruwan kasar bayan sallar Jumma’a sun bayyana goyon bayansu ga al-ummar Falasdinu a Gaza, sannan sun bukaci HKI ta aiwatar da yarjeniyar da ta cimma da kungiyoyi masu gwagwarmaya. Har’ila yau sun bukaci a gaggauta shigo da abinci da magungunacikin zirin Gaza. Tashar talabijin talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto masu zanga zangar wadanda suka hada da mata da maza, malaman addini, daliban jami’o’i da sauransu suna tattaki daga dandalin inkilab zuwa dandalin azadi. Har’ila yau sun rera wakoki na goyon bayan masu gwagwarmayar, dauke da hotunan shahidai da kuma shuwagabannin kawancen masu gwagwarmaya a yankin. An gudanar da jerin gwanon a cikin manya manyan biranen...
Majiyar asbitoci a yankin gaza na kasar Falasdinu da aka mamaye ta bada labarin cewa HKI ta kashe falasdinawa 19 a safiyar yau Asabar duk tare da cewa an fara tsagaita budewa juna wuta a yankin. Tashar talabian ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar asbitoci a gaza na cewa bayan janyewar sojojin HKI daga wasu yankuna a Gazar sun zakulo gawakin falasdinawa 155 daga burbushin gine-gine wadanda HKI ta rusa a bayan. Banda haka an kawo masu sabbin gawaki 19 wadanda sojojin HKI suka kashe a safiyar yau duk tare da cewa an fara yarjeniyar dakatar da budewa juna wuta. Labarin ya kara da cewa gawaki 135 daga cikin 155 da aka kawo na kashe-kashen...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Tsaro ‘Yansanda Sun Tabbatar Da Mutuwar Wata Ba’amurkiya Da Ta Ziyarci Saurayinta A Jihar Delta October 11, 2025 Tsaro Sojoji Sun Ƙaryata Rahoton Cewa Ƴan Bindiga Sun Mamaye Sansaninsu A Kwara October 5, 2025 Tsaro Sojoji Sun Kama Ƴan Ta’adda 450, Sun Ceto Mutane 180 A Satumba — DHQ October 4, 2025
Wadanda suka amfana da horon, an ba su horon ne a fannoni daban-daban da suka hada da yin noma da takin gargajiya da kuma yin noman kayan lambu da sauransu. Kajin gidan gona da tare da kuma tallafa masu da kayan aikin noma. Bisa tsarin wannan haron, kowace mace daya da ta amfana da horon, an ba su tallafin Naira Naira 50,000. Kazalika, Adeleke ya danganta wannan tallafin kudin a matsayin mayar da hankalin gwamnatinsa na taimaka wa matan jihar. Gwamnan ya kuma jaddada muhimmcin tallafa wa mata, wanda ya sanar da cewa; hakan na da muhimanci domin inganta gobensu. Shi kuma shugaban gidauniyar, Dakta Deji Adeleke a nasa jawabin ya bayyana cewa, shirin wanda...
A cewarta, shirin ya taimaka wajen noman shinkafa da ta kai kimanin tan 99,452, wacce kuma kudinta ya kai kimanin Naira biliyan 13.527 tare kuma da noman rogo da ya kai kimanin tan 87,237, wanda kudinsa ya kai Naira biliyan 3.925, musamman domin a kara samar da wadataccen abinci da kuma kara bunkasa fannin tattalin arzikin jihar. Sai dai, ta bayyana cewa; har yanzu a jihar ba a samar da wani cikakken tsari a hukumance ba, a kan tsarin na shirin na CAF wanda hakan ke haifar wa da shirin koma baya a jihar. Ta yi kira ga sauran masu ruwa da tsaki a fannin bunkasa aikin noma, domin samun riba a jihar da su bayar da hadin...
Duk da Najeriya na cikin yanayin damina, wanda ake ganin a lokacin ta fi samar da wutar lantarki ga ’yan ƙasarta, amma jama’a a jihohin Kaduna da Kano na ci gaba da kokawa kan ƙarancin wutar. A duk shekara jama’a na more wutar lantarki a Nijeriya a lokacin damina saboda tashoshin ruwa na samar da wutar lantarki suna aiki da cikakken ƙarfinsu. Amma, wasu masana a ɓangaren wutar sun shaida wa wakilinmu cewa duk da matsalolin masu nasaba da lalata kayan aiki da kuma ƙin biyan kuɗin wuta da wasu masu amfani da ita ke yi, kamfanonin rarraba wutar (DisCos) suna yin iya bakin ƙoƙarinsu wajen cike giɓin. Masu ruwa da tsaki sun bayyana cewa ana ƙoƙarin daidaita rarraba wuta...
Ya kara da cewa, ana ci gaba da kokari don ganin an iske masu yin kiwon shanu a kasar nan, domin fadakar da su kan muhimmancin rungumar wannan tsari na zamani. Sai dai, ya yi nuni da cewa; wasu al’adu na haifar da tarnaki a tsakanin wasu masu kiwon a kasar na rungumar wannan tsarin. “Na ga wasu gidajen gona da ake yin irin wannan dabara ta zamani, sannan kuma ana bayar da kulawar da ta kamata; wanda hakan ya sanya ake iya samar da litar madarar shanu daga tsakanin lita 15 zuwa 30,” in ji Jatau. “Akwai wasu Fulani Makiyaya ‘yan kalilan da suka rungumi wannan tsari, misali a Jihar Bauchi; inda wani makiyayi ya rungumi...
Bangarorin kungiyoyin gwagwarmayar Falasdinawa sun fitar da sanarwar hadin gwiwa kan tsagaita bude wuta a Gaza Kungiyar Hamas, Jihad Islami, da kuma Popular Front mai fafatukar ‘yantar da Falasdinu, sun fitar da sanarwar hadin gwiwa a jiya Juma’a, inda suka bayyana matakin farko na yarjejeniyar tsagaita bude wuta a zirin Gaza, inda suka yi maraba da gwagwarmayar al’ummar Falastinu, musamman a Gaza wajen fuskantar laifukan yahudawan sahayoniyya. Kungiyoyin Hamas da na sauran kungiyoyin Falasdinu sun yaba da jarumtar gwagwarmayar da ta janyo hasara ga makiya, suna masu jaddada cewa: “Muradin jama’a da ‘yan gwagwarmaya ya fi duk wani yunkuri na murkushe su.” Har ila yau, sun jinjinawa “bangarori masu goyon bayansu a Yemen, Lebanon, Iran, da Iraki saboda goyon bayan...

Venezuala Ta Bukaci Kwamitin Sulhun M.D.D Da Ya Tabbatar Da Cewa: Amurka Tana Barazana Ga Zaman Lafiya
Kasar Venezuela ta yi kira ga Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya da ya tabbatar da cewa Amurka tana yin barazana zaman lafiyar duniya Kasar Venezuela ta yi kira ga kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da ya amince cewa; Lallai Amurka tana yin barazana ga zaman lafiya da tsaro na kasa da kasa, saboda yadda sojojin Amurka suke shisshigi a tekun Caribbean, wannan batu ya zo ne a yayin zaman gaggawa na majalisar a jiya Juma’a. Wakilin dindindin na Venezuela a Majalisar Dinkin Duniya, Samuel Moncada, ya ce: “Suna ba da shawarar ayyuka uku ga kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya: Na farko, amincewa da barazanar zaman lafiya da tsaro na kasa da kasa da sojojin Amurka suka haifar a cikin...
Jiragen saman yaki sun yi luguden wuta kan birnin Kabul fadar mulkin kasar Afganistan, kuma rahotanni masu karo da juna suna cewa an kashe shugaban Taliban na Pakistan Kafofin yada labaran Afghanistan sun yi ikirarin cewa: Sojojin Pakistan ne ke da alhakin harin da aka kai a Kabul babban birnin kasar Afganistan a yammacin ranar Alhamis. Tashar Talabijin ta Tolo News da Khabar Online Afganistan sun ruwaito cewa: Sojojin Pakistan sun dauki alhakin hare-haren da aka kai cikin daren jiya a Kabul. Kakakin Taliban Zabihullah Mujahid ya rubuta a dandalin X a yammacin ranar Alhamis cewa: An ji karar fashewar wani abu a birnin Kabul. Ya kara da cewa: “Babu wata damuwa, lamarin dai kamar yadda aka saba, ana ci...
Ministar wadda ta je kamfanin domin daukar sabuwar motarta ta alfarma kirar Nord Demir SUB da kamfanin ya hada nataimakin Shugaban jami’ar na sashen kula da ilimi da gudanar da bincike Farfesa Bola Oboh da kuma Shugaban kamfanin Mista Oluwatobi Ajayi ne, suka karbi bakuncinta. A jawabin da ta gabatar a lokacin ziyarar ministar ta bayyana cewa,Duba da yarjejeniyar hada-hadar kasuwanci wajen fitar da kaya zuwa ketare kamfanin zai iya yin amfani da wannan samar waken fitar da motocinsa zuwa ketare. Ta kara da cewa, Nijeriya na da gurare biyu ne da ake hada motoci da suka hada da, na wannan jami’ar da kuma na EPs, inda ta yi nuni da cewa, karfin da kamfanin ya ke da...

Ma’aikatar Wajen Sin Ta Yi Tsokaci Kan Amincewar Da Isra’ila Ta Yi Da Yarjejeniyar Kawo Karshen Rikicin Gaza
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Sojojin Ruwan Sin Za Su Gudanar Da Aikin Sintiri A Zirin Tekun Aden Da Yankin Tekun Somaliya October 10, 2025 Daga Birnin Sin CMG Ya Kaddamar Da Shirin “Dabarun Tallata Kayayyakin Sin” A Tafarkin Gina Kasa Bisa Hadin Gwiwa October 10, 2025 Daga Birnin Sin Sin Za Ta Fara Cajin Kudi Na Musamman Ga Jiragen Ruwan Amurka October 10, 2025
Shugaban ya ci gaba da cewa, a karkashin shugabancinsa, Hukumar za ta yi namijin kokari wajen bayar da goyon bayanta, wajen fitar da kayan da ba su shafi dangogin Mai ba, zuwa kasar waje, musamman ta hanyar cin giyar albakatun yanayin na Abuja da kuma na bangaren aikin noma, da birnin ke da shi. Ya kara da cewa, ta hanyar wadannan alkatun kasar da birnin ke da su, Hukumar za ta kara bayar da gudunmwarta, wajen kara bunkasa fannin tattalin arzikin kasar nan da kuma kara fitar da kayan da ba su shafi Man ba, zuwa ketare. A cewarsa, domin Hukumar ta tabbatar da na kara mayar da hankalin wajen ganin ana bin ka’ida da kuma tabbatar da ingancin...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin CMG Ya Kaddamar Da Shirin “Dabarun Tallata Kayayyakin Sin” A Tafarkin Gina Kasa Bisa Hadin Gwiwa October 10, 2025 Daga Birnin Sin Sin Za Ta Fara Cajin Kudi Na Musamman Ga Jiragen Ruwan Amurka October 10, 2025 Daga Birnin Sin Kasar Sin Ta Samu Manyan Nasarori A Fannin Inganta Walwalar Yara Da Tsoffi Cikin Shekaru 5 Da Suka Gabata October 10, 2025
Hukumar Tsaro ta Sibil Difens a Jihar Kano, ta cafke wasu mutum uku da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi a Ƙaramar Hukumar Doguwa. Hukumar ta miƙa su ga Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA), domin ci gaba da bincike da gurfanar da su a kotu. ’Yan bindiga sun kashe Civilian JTF 8 a Zamfara Sojoji sun mutu yayin da Boko Haram ta kai hari sansanin soji a Borno Kwamandan hukumar na Jihar Kano, Bala Bawa Bodinga ne, ya bayyana hakan yayin da yake magana da ’yan jarida a hedikwatar hukumar a ranar Juma’a. Ya ce an kama mutanen ne da sanyin safiyar ranar Talata, 7 ga watan Oktoba, 2025, bayan samun sahihin bayaai. Jami’an hukumar daga...
A yau Jumma’a 10 ga watan Oktoba, an kaddamar da wani shiri na aikin hadin gwiwa mai lakabin “Dabarun Tallata Kayayyakin Sin” na rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin (CMG) na shekarar 2026 a birnin Beijing. Shen Haixiong, babban darektan CMG, ya gabatar da jawabi a wajen taron, inda ya bayyana cewa, CMG ya samu damar zamowa kan gaba a fagen yada labarai na kasa da kasa bisa kayayyakin aiki da ma’aikata, kuma shi ne muhimmin dandali na tallata kayayyakin kasar Sin. Kamfanin a shirye yake ya dauki shirin a matsayin wata damar yin aiki kafada da kafada da abokan kawance daga kowane bangare na rayuwa, tare da rubuta sabon babi a fagen gina kasa mai kunshe...
“Ta yaya Jonathan zai zama barazana? Mun doke shi a baya lokacin da PDP take kan mulki. “Idan mutum yana ganin cewa PDP ita ce kololuwar jam’iyya a Nijeriya, kuma ya sha kaye a lokacin da yake ganiyarsa, ina ganin sai makiyinsa ne kawai zai tilasta masa ya kara tsayawa takara a zaben 2027,” in ji shi. Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa ya ce a yanzu haka Jonathan ya kasance dan siyasa mai daraja, yana mai cewa komawa fagen siyasa na iya rage masa kima da kuma zubar masa da darajar da yake da shi a idon duniya. Ya jaddada cewa Jonathan ya samu damar nuna cewa mulki bai tsole masa ido ba, domin haka ne...
Falasdinawan da HKI ta kora daga gidajensu a birnin Gaza sun kama hanyar komawa gidajensu a birnin Gaza dake arewacin yankin Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kamfanin dillancin labaran reuters na cewa ya zuwa tsakiyar rana a yau jumm’a sojojin HKI sun janye makamansu daga babban titi wanda ya taso daga arewacin zirin Gaza zuwa kudancin yankin , wanda kuma ake kira Titin Rasheed. Sun janye zuwa inda aka amince zasu koma a wannan matakin na sabon yarjeniyar. Hotunana daga yankin ya nuna falasdinawa gungu-gungu suna takawa da kafa zuwa arewacin zirin Gaza, daga inda sojojin yahudawan suka koresu a farkon watan da ya gabata, suka kuma hana kowa bin kan titin Rasheed. A wani bangare...
Tawagar da ke karkashin jagorancin, Barry Andrews ta kuma ziyarci hedkwatar hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), inda shugabanta, Mahmood Yakubu, ya yi gargadin cewa jinkirin da ‘yan majalisa ke yi wajen gyaran dokar zabe ta 2022 na iya kawo cikas ga shirye-shiryen gudanar da zabe a 2027. Wakilan, wadanda suke Nijeriya tun kusan makonni uku domin nazarin matakin aiwatar da shawarwarin da ke cikin rahotonsu na bayan zaben 2023, sun kuma yi tattauna da babbar jam’iyyar adawa ta PDP. Abbas, a cikin wata sanarwar da sakataren yada labaransa, Leke Bayeiwu, ya shaida wa tawagar EU cewa rahotanninta kan zabukan shekarar 2023 ana la’akari da su a cikin sauye-sauyen gyara dokar zabe da na dimokuradiyya da...

Kasar Sin Ta Samu Manyan Nasarori A Fannin Inganta Walwalar Yara Da Tsoffi Cikin Shekaru 5 Da Suka Gabata
Ministan kula da harkokin al’umma na kasar Sin Lu Zhiyuan, ya ce cikin wa’adin shirin raya kasa na shekaru 5-5 na 14 tsakanin 2021 zuwa 2025, walwalar yara da tsoffi a kasar, ta samu gagarumin ci gaba. Lu Zhiyuan, ya bayyana yayin wani taron manema labarai a yau Juma’a cewa, yayin wa’adin shirin, an samar da wani cikakken tsarin bayar da kariya da kulawa ga yara mabukata, wanda ya shafi yaran da ba sa gaban iyayensu saboda wasu dalilai, da yaran da iyayensu suka yi nesa da gida, da yaran da suka kaura, inda a yanzu dukkansu ke cin gajiyar hidimomin kariya da kulawa na kasar. Har ila yau a wa’adin, kasar Sin ta kammala gyarawa da sake fasalin kayayyakin...
“Muna kira ga majalisar kasa da ta yi la’akari da shirin gyaran tsarin kudurorin zabe cikin gaggawa. Amincewa da dokar cikin lokaci yana da muhimmanci ga shirinmu na gudanar da zabe a 2027. “Rashin tabbas game da tsarin doka na zabe na iya kawo matsaloli masu yawa ga ayyukan hukumar INEC yayin da lokacin zabe ke karatowa,” in ji shi. Shugaban INEC ya bayyana cewa hukumarsa ta aiwatar da shawarwarin da aka mika mata kai tsaye a rahoton EU na zaben 2023. “An dauki mataki kan wasu bangarori na shawarwarin da ake bukatar hukumar ta aiwatar da su. Haka kuma, ana daukar mataki kan shawarwarin da suka shafi fannoni da dama wadanda ake bukatar hadin gwiwa tsakanin...
Wani Likitan ƙwaƙwalwa a Asibitin Neuropsychiatric Aro, a Abeokuta, Jihar Ogun, Dokta Emmanuel Abayomi ya ce kimanin mutane miliyan 60 ne ke fama da taɓin hankali a halin yanzu. Ya yi wannan jawabin ne a ranar Juma’a a Abeokuta a wajen wani taron ƙarawa juna sani da Ƙungiyar likitoci ta NAS ƙarƙashin Ƙungiyar masu ruwa da tsaki ta ƙasa ta shirya domin tunawa da ranar kiwon lafiyar ƙwaƙwalwa ta duniya ta bana. Ɗan Majalisa ya nemi ɗaukar mataki kan dorinar ruwa a Gombe ’Yan sanda sun ceto mutum 3 da aka sace a Kano da Kaduna Shirin da Ash Montana Deck tare da haɗin gwiwar Atlantis, Americana 1 da Longhorn Deck suka yi wanda ya ja hankalin ‘yan sanda da...
Wannan lamari ya haifar da tambaya kan yiwuwar dorewar shirin sauye-sauye da na zamani da ake gudanarwa a karkashin jagorancin Babban Kwanturola Janar, Adewale Adeniyi. Adewale Adeniyi, wanda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kara wa wa’adin mulki na shekara guda, shima zai yi ritaya daga hukumar a watan Agusta, 2026. A halin yanzu, za a dauki babban mataki kafin a cike gibin ma’aikata da ake bukata a hukumar kwastam, musamman idan aka yi la’akari da cewa jami’ai 825 za su bar aiki ba tare da sabon daukar ma’aikata ba. Binciken da leadership Hausa ta gudanar ya gano cewa ritayar ta shafi kowane mataki a hukumar daga manyan shugabanni, zuwa matsakaita, har da kananan jami’ai. Daga cikin...
Ana fargabar sojoji da dama sun rasu yayin da mayaƙan Boko Haram suka kai hari sansanin soji da ke Ngamdu, a Ƙaramar Hukumar Kaga a Jihar Borno. Rahotanni sun nuna cewa mayaƙan sun kai wa sojojin hari a sansanin da ke kan hanyar Maiduguri zuwa Damaturu. Ɗan Majalisa ya nemi ɗaukar mataki kan dorinar ruwa a Gombe Kwastam ta kama buhunan lalatacciyar fulawa 10,000 ana ƙoƙarin shigo da ita Najeriya Biyo bayan harin, sojoji sun rufe hanyar Ngamdu har zuwa ƙarfe 11:20 na safe, wanda hakan ya sa matafiya suka maƙale na tsawon lokaci. “Na tashi daga Damaturu da sassafe ina fatan isa Maiduguri kamar ƙarfe 9 na safe, amma da na isa Ngamdu sai muka tarar da hanya a...
Bugu da kari, Xi Jinping ya yi wa jam’iyyar WPK fatan samun karin nasarori, yana mai fatan abotar Sin da Korea ta Arewa za ta dore har abada. (Fa’iza Mustapha) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin An Jinjinawa Tallafin Kamfanonin Sin Ga Tsarin Bunkasa Masana’antun Senegal October 9, 2025 Daga Birnin Sin Masu Kallon Fina-Finai Na Sin Sun Gamsu Da Fina-Finan Da Aka Gabatar A Lokacin Hutun Bikin Murnar Ranar Kafuwar Sabuwar Kasar Sin Ta 2025 October 9, 2025 Daga Birnin Sin Sin Na Ci Gaba Da Goyon Bayan Kawo Karshen Rikicin Gaza October 9, 2025
A yayin da ake yawan samun ɓarnar dorinar ruwa a garuruwan Daɗin Kowa da Kupto da Malleri da Wade a yankunan Ƙananan hukumomin Kwami da Yamaltu Deba a Jihar Gombe ta kai ga samun asarar amfanin gona da rayuka. Hakan ne ya sa Ɗan majalisar tarayya mai wakiltar mazaɓar Yamaltu/ Deba a Jihar Gombe Inuwa Garba ya gabatar da ƙudiri a gaban zauren Majalisar Wakilai ta tarayya domin neman ɗaukar matakin gaggawa kan ɓarnar dorinar ruwa. ’Yan sanda sun ceto mutum 3 da aka sace a Kano da Kaduna Kwastam ta kama buhunan lalatacciyar fulawa 10,000 ana ƙoƙarin shigo da ita Najeriya Inda ya ce dorinar na yi wa manoma ɓarna sosai da ke janyo asarar rayuka, dukiyoyi da lalacewar...
Bugu da kari, an rufe shafukan hakar ma’adanai haramtacce 98 a fadin kasar. “An kiyasta cewa Nijeriya na asarar kusan Dala biliyan 9 a kowace shekara sakamakon haramtacciyar hakar ma’adanai. Wannan sata ta albarkatunmu da ya kamata ta bunkasa kasarmu ta wuce kima, kuma lokaci ya yi da za a kawo karshensa,” in ji Abdulraheem. A cewar sa, kwamitin na da alhakin hana asarar kudaden shiga, tabbatar da gaskiya da adalci a harkokin hakar ma’adanai, da tabbatar da cewa dukiyoyin ma’adanin kasar suna ba da cikakken gudunmawa ga ci gaban tattalin arziki. “Yayin da muke ci gaba, daya daga cikin manyan manufofin wannan kwamitin shi ne hana asarar kudaden shiga da haramtacciyar hakar ma’adanai da ayyukanta ke...
Rundunar ƴansanda ta Jihar Kano ta ce ta ceto mutane uku da aka sace a yayin wani aiki biyu da ta gudanar a Kano da Kaduna, tare da ƙwato babur da wasu shaidu. Mai magana da yawun rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Juma’a. A cewar Kiyawa, a ranar 7 ga Oktobar 2025, rundunar daƙile garkuwa da mutane (Anti-Kidnapping) tare da tawagar sa-ido daga ofishin ƴansanda na Bebeji sun gudanar da sumame bayan samun bayanan sirri kan wani mutum da ya tsere daga hannun masu garkuwa da mutane. Wanda aka sace, Abdul Hamid Bello, mai shekaru 21, ya taimaka wajen kai jami’an tsaro inda aka ceto wani mutum mai...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, ta samu nasarar ceto wasu mutum uku da aka sace, bayan wani samame da ta kai a jihohin Kano da Kaduna. Wannan na daga cikin ƙoƙarin da rundunar ke yi domin yaƙi da laifuka da tabbatar da tsaron jama’a. ’Yan sanda sun manta hularsu a motar dalibi bayan karɓar ‘cin hancin’ N99,000 NAJERIYA A YAU: Kalubalen Da Ke Gaban Sabon Shugaban Hukumar Zabe Ta Kasa A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar, ya bayyana cewa an gudanar da samamen ne tsakanin ranar 7 zuwa 9 ga watan Oktoba, 2025, bisa umarnin Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, CP Ibrahim Adamu Bakori. A cewar Kiyawa, samamen farko ya gudana ne a ranar...
“Akwai da yawa malamai marasa cancanta a cikin aikin. Muna da wadanda ke koyarwa a ajujuwa amma ba su da takardun shaidar koyarwa, musamman a makarantu masu zaman kansu,” in ji ta. Ta bayyana cewa, yayin da wasu mutane ke da sha’awar koyarwa da gaske, rashin horo na hukuma ya hana su shiga aikin koyarwa. Dr. Soyombo ta bayyana cewa TRCN a halin yanzu na da malamai masu rijista kusan miliyan 1.4, tare da shirin kara wannan adadi zuwa miliyan 20 cikin shekaru biyu masu zuwa ta hanyar dijital da saurin rajista. “Mun zamanantar da tsarinmu domin mutane da yawa su sami damar yin rijista,” in ji ta. “Kowane malami yana da bai wa ta musamman...
Hukumar Kwastam shiyyar bodar Najeriya ta Seme da ke jihar Legas ta ce ta cafke motoci biyar da ke maƙare da buhuna 10,000 na lalatacciyar fulawa da darajarsu ta kai Naira biliyan 1.2. Rundunar ta kuma ce ta tara jimillar kuɗin shigar da ya kai Naira biliyan daya da rabi a watan Satumba, wanda hakan ya nuna kari da kaso 182 cikin 100 idan aka kwatanta da Naira miliyan 531 da aka tara a watan Agustan da ya gabata. NAJERIYA A YAU: Kalubalen Da Ke Gaban Sabon Shugaban Hukumar Zabe Ta Kasa Tinubu ya yi wa Mamman Vatsa, Farouk Lawan da wasu mutum 173 afuwa Kwamandan rundunar a shiyyar, Wale Adenuga, ne ya bayyana hakan a taron manema labarai na...
Kazalika, tarihin Dimokiradiyyar kasar ya sha cin karo da kwam gaba kwam baya kusan za a iya cewa, tun bayan dawowar mulkin Demokaradiyya a 1979 da kuma sake dora kasar a wata turbar ta Demokiradiyyar a 1999. Alal misali, jamhuriyya ta hudu ta kasance ta jima sosai, amma kusan babu wasu ayyukan na inganta rayuwar ‘yan kasar da za a bigi Kirji a ce gasu an gani a kasar a zahiri. Idan aka dubi bangaren samar da hasken wutar lantarki kusan za a iya cewa, karni da dama da suka bace, har zuwa yau Nijeriya ta gaza samar da karfin wutar da kuma rabar da ita da ta kai karfin Megawatts 5,000 musamman duba da cewa, wannan adadin...
Rahotanni daga Gaza na cewa Isra’ila ta fara janye sojojinta daga wasu yankuna na zirin Gaza. Wannan dai na zuwa ne bayan da gwamantin Isra’ila ta amince da yarjejeniyar tsagaita wuta dake kunshe a shirin zaman lafiya na Trump da ta cimma da kungiyar Hamas. Daraktan Hukumar Ba da Agajin Gaggawa da Hadin Kan Kasa da Kasa ta Hukumar Tsaron Fararen Hula ta Gaza Mohammad Al-Moughayyir, ya ce sojojin Isra’ila sun janye daga yankuna da dama a cikin birnin Gaza da arewacin zirin da kuma wasu yankunan kudancin yankin. A Khan Younis da ke kudancin zirin Gaza, Motocin Isra’ila sun janye daga kudancin birnin da tsakiyar birnin zuwa yankunan gabashi. Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of...
Ma’aikatar baitul malin Amurka ta sanya takunkumi kan wasu mutane sama da 50 da hukumomi da jiragen ruwa da ake zargi da hannu a cinikin man fetur da Iran. A cewar sanarwar da hukumar ta fitar, ofishin kula da kadarorin kasashen waje (OFAC) ta kara matsin lamba kan Iran ta hanyar kakaba mata takunkumi ga mutane sama da 50, kamfanoni da jiragen ruwa masu saukaka sayarwa da jigilar danyen mai da iskar gas daga Iran. A cewar hukumomin Amurka, wadannan hanyoyin sun baiwa Iran damar fitar da mai da kayayyakin da suka kai na biliyoyin daloli. Sabon takunkumin ya shafi kamfanoni uku da ke Hadaddiyar Daular Larabawa, kamfanoni uku na bogi a Hong Kong, da wata matatar mai a China....
Gwamnatin jihar Zamfara ta yi gargadin cewa ba za ta lamunci duk wani aiki na sakaci ko zagon kasa da zai iya kawo cikas ga kokarin da take yi na gyara da inganta harkar ilimi. Shugaban hukumar kula da ilimin bai daya ta jihar Zamfara (ZSUBEB), Farfesa Nasir Garba Anka ne ya yi wannan gargadin a wata ziyarar bazata a makarantar firamare ta UBE, Low Cost da ke Gusau, biyo bayan rahotannin sace-sace da kuma lalata kadarorin gwamnati. Jami’in hulda da jama’a na hukumar, Ibrahim Maizare ya bayyana haka a wata sanarwa da ya ba rediyon Najeriya a Gusau. Farfesa Nssiru Anka ya nuna matukar damuwa kan rashin kyawun kayan aiki, ya kuma bayyana lamarin a matsayin...
Ofishin Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) reshen jihar Kano ya bi sahun sauran ofisoshi na kasa baki daya domin bikin Makon Hidima na 2025, wanda aka yi bikin a karkashin taken “Mai Yiwuwa”. Taron na yini biyu wanda Sashen kula da ingancin aiki wato SERVICOM na Hukumar ya shirya, ya gudana ne a ofishin NEMA Kano, inda aka mayar da hankali wajen kara inganta ayyukan hidima, da rikon amana, da hada kai wajen kai agajin jin kai. Da yake ba gabatar da takarda kan “Tabbacin Inganci da Biyayya a aiwatar da Agaji,” Sakatariyar Reshen Kungiyar Agaji ta Red Cross ta Najeriya, Musa D. Abdullahi, ya jaddada bukatar samar da manyan matakai, da rikon amana,...
Cibiyar Kula da Harkokin kasuwanci ta kasa ta bayyana kafa Cibiyar Gudanar da taron Kasuwanci na Najeriya a wani bangare na ganin ba a samarda cibiyoyi da ke da aiki iri ɗaya ba. Babban magatakardar Cibiyar Mista Victor Olannye, ne ya bayyana haka a lokacin da yake gabatar da takardar a yayin taron jin ra’ayin jama’a na kwamitin majalisar wakilai kan harkokin kasuwanci a Abuja. Mista Victor Olannye ya ce kudurin dokar da ke neman kafa sabuwar cibiyar ya ci karo da ayyukan Cibiyar Gudanarwa ta kasa da tuni Majalisar Tarayya ta 9 ta amince da ita wadda Shugaban kasar na wancan lokacin ya amince da shi. Ya yi nuni da cewa, babban makasudin kafa Cibiyar Kula...
Wata kafar labarai daban, Peoples Gazette, tun da farko a shekarar 2024, ta ruwaito labaran da ke zarginsa da yin jabun takardar shaidar NYSC. Sai dai Nnaji ya karyata labarin da Premium Times ta wallafa, yana mai cewa zargin aiki ne na abokan hamayyar siyasa a Jiharsa ta Enugu. Tsohon ministan, wanda aka nada a watan Agusta 2023, ya mika takardar murabus dinsa a ranar Litinin ga Shugaban Kasa, inda ya nuna godiyarsa kan damar da aka ba shi ta yi wa kasa hidima. A cikin wasikar tasa, tsohon ministan ya bayyana cewa ya zama abin kai hare-hare na “tsananin batanci” daga abokan hamayyar siyasa da ke neman bata masa suna. “Ina gode wa Shugaban Kasa...
Yawan mace-mace ta hanyar cutar kwalarar, na faruwa ne duk da biliyoyin Nairori da aka ce gwamnati da abokan huldar kasa da kasa suna kashewa, domin kokarin ganin an dakile ta. Wadannan kudade sun hada da kason kasafin kudi na shekara-shekara, wanda ya kunshi miliyoyin Nairori; akwai dala miliyan 700 da bankin duniya ya bayar domin samar da tsaftataccen ruwa sha, tsaftar muhalli a fadin kasa baki-daya, tallafin dala miliyan 2 daga Majalisar Dinkin Duniya, dubban daruruwan allurar rigakafin cutar kwalara da asusun kula da yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) suka bayar da sauran makamantansu. Alkaluman da aka samu daga cibiyar NCDC, sun nuna cewa a cikin 2020, kasar ta samu rahoton...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna ta kama mutum 26 da ake zargin masu garkuwa da mutane ne tare da kwato makamai da kudade daga hannunsu. Daga cikin abubuwan da aka samu nasarar kwatowar har da bindigogi na gida guda huɗu, makamai masu hatsari da kuma tsabar kuɗi Naira 546,000 da ake zargin wani ɓangare ne na kuɗin fansa. Tinubu ya yi wa Mamman Vatsa, Farouk Lawan da wasu mutum 173 afuwa Tinubu ya naɗa Amupitan a matsayin Shugaban INEC An kama waɗanda ake zargin ne a cikin jerin samame da aka gudanar daga ranar 3 zuwa 5 ga watan Oktoban 2025, a sassa daban-daban na jihar. Samamen ya haɗa jami’ai daga sashen ’yan sanda na Anchau, Hukumar Kula da Tsaro...
Dare ya jaddada cewa Nijeriya kasa ce mai addinai da dama, wacce aka gina bisa juriya, zaman lafiya, da girmama juna tsakanin mabambantan addinai, al’ummomin da ya ce Tinubu ya shugabanta. Dare ya ambaci maganar Shugaban Kasa inda ya jaddada cewa Nijeriya “kasa ce mai cikakken ‘yanci da girma, wadda aka gina bisa bangaskiya da juriyar jama’arta,” ya kara da cewa “Babu wani addini da ake zalunta, kuma babu wata al’umma da aka ware.” Yana nuna misali da rayuwar Shugaban Kasa a matsayin shaida ta juriya da fahimtar addinai, Dare ya bayyana cewa Shugaba Tinubu, Musulmi ne da yake auren fasto mai bin addinin Kirista. Ya kuma ruwaito Shugaban yana cewa, “Gaba da kiyayya ba su da gurbi...
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bukaci dukkanin bangarorin da su yi aiki da kuma mutunta yarjejeniyar da shugaban Amurka Donald Trump ya gabatar da kuma yin amfani da wannan damar. Da yake jawabi a wurin taron Majalisar Dinkin Duniya, Guterres ya bayyana cewa, “Ina kira ga dukkan bangarorin da su mutunta ka’idojin yarjejeniyar, da kuma rungumar damar da tke cikinta.” Duk da cewa dai a cikin kalaman nasa yafi nuna damuwa a kan fursunonin Isra’ila da ake tsare da su a Gaza, duk da irin mummunan kisan kiyashi da Isra’ila take yi a Gaza, amma mya ce Majalisar Dinkin Duniya ta shirya tsaf domin ba da cikakken goyon bayanta ga aiwatar da yarjejeniyar. A halin da...
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayar da afuwar Shugaban Kasa ga mutane 175. Daga ciki har da wadanda aka yi wa afuwar bayan mutuwa ga marigayi Manjo Janar Mamman Jiya Vatsa da ɗan gwagwarmayar kwato ’yancin kan Najeriya, Herbert Macaulay. An dauki wannan mataki ne bayan amincewa da shawarwarin da Majalisar Tsofaffin Shugabannin Ƙasa ta bayar a taronta da aka gudanar a ranar Alhamis a Abuja. Gwamnatin Kano ta shirya ɗaurin auren ma’aurata 2,000 Tinubu ya naɗa Amupitan a matsayin Shugaban INEC A cewar sanarwar da mai ba Shugaban Ƙasa shawara kan harkokin bayanai da dabarun sadarwa, Bayo Onanuga, ya fitar, Shugaba Tinubu ya kuma yi afuwa ga tsohon ɗan majalisa Farouk Lawan da wasu mutum uku, Misis Anastasia...
“Jami’an ‘yansanda na SIS, suka fara bincike kan rahoton, ta hanyar amfani da kaifin basira da fasaha, a hanyar filin jirgin sama, karamar hukumar Nassarawa, jihar Kano, jami’an sun kama wata mata mai suna Adama Hassan, ‘yar shekara 35 da ke da zama a karamar hukumar Deba, jihar Gombe, a ranar 6 ga Oktoba, 2025, yayin da take tuka motar da aka sace a kan hanyarta ta zuwa Jamhuriyar Nijar. Rahotanni sun bayyana cewa, wacce ake zargin ta amsa laifin karbar motar ne daga hannun wani mutumi da ke karamar hukumar Lafiyan Lamurde, jihar Adamawa, wanda a yanzu ake nema ruwa a jallo. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Jami’an Tsaro Sun Cafke Ɓarayin Kayayyakin Turakun Wutar Lantarki Na Hanyar...
Cikin darussan da wannan rikici ya tabbatar mana, akwai rashin tasirin amfani da karfin tuwo wajen warware duk wani rikici. Tabbas karfin soji kadai ba zai iya magance takaddama ko tashin hankali ba, ballantana ya wanzar da tsaro da walwalar bil’adama. Muna iya ganin hakan a zahiri, idan mun lura da yadda Isra’ila ta nuna a fili cewa hare-haren da ta kwashe shekaru biyu tana kaiwa sassan Gaza za su iya kawo karshen barazanar da ta ce kungiyar Hamas ke haifar mata, amma sai ga shi daga karshe sakamako ya nuna akasin haka. Har yanzu dai sannu a hankali ana komawa ga shawarar da kasashe masu son zaman lafiya suka jima suna bayarwa, wato a rungumi tattaunawa, da...
Gwamnatin Jihar Kano ta umurci Hukumar Hisba ta jihar da ta fara shirye-shiryen ɗaurin auren ma’aurata aƙalla 2,000 a ƙarƙashin shirinta na ɗaurin auren gata. Mataimakin babban Kwamandan hukumar, Sheikh Mujahid Aminudeen ya shaida wa kafar PUNCH a wata tattaunawa ta wayar tarho a ranar Alhamis, inda ya ce nan ba da daɗewa ba hukumar za ta fara shirin don ganin an samu nasarar gudanar da taron bikin. An kama 26 da ake zargin masu garkuwa da mutane Ma’aikatan jami’a sun yi zanga-zanga a Jami’ar Bayero “Muna shirin gudanar da ɗaurin auren wani rukunin ma’aurata guda 2,000 kamar yadda gwamnatin jihar ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta umarta,” in ji shi. Duk da cewa, babban kwamandan bai bayyana ainihin...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Nijeriya Ta Yi Asarar Ganga Miliyan 13.5 Na Ɗanyen Mai Ta Hanyar Sata Da Zagon-ƙasa – NEITI October 9, 2025 Labarai Batun Umarnin Kotu Na Kama Tsohon Shugaban INEC Ƙage Ne Kawai – Shugaban Jam’iyyar AA October 9, 2025 Manyan Labarai Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu Ya Zaɓi Farfesa Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC October 9, 2025

An Yi Tafiye-tafiye Miliyan 16.34 Da Suka Shafi Shiga Da Fita Daga Kasar Sin Yayin Hutun Kwanaki 8 Na Kasar
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Duniya Ta Kara Ganin Bunkasuwar Sin a Lokacin Hutun Murnar Ranar Kafuwar Sabuwar Kasar October 9, 2025 Daga Birnin Sin An Samu Karuwar Sayayya Yayin Hutun Bikin Kafuwar Kasar Sin October 9, 2025 Daga Birnin Sin Adadin Biyan Kudade Ta Intanet Yayin Hutun Bikin Kafuwar Jamhuriyar Jama’ar Sin Ya Kai Yuan Tiriliyan 13.26 October 9, 2025
Gwamnatin tarayya ta yi asarar jimillar gangar danyen mai miliyan 13.5 wanda kudinsa ya kai dala biliyan 3.3 sakamakon sata da fasa bututun mai tsakanin shekarar 2023 zuwa 2024, in ji wata kungiya mai fafutukar kare masana’antu ta Nijeriya (NEITI). Sakataren zartarwa na NEITI, Dokta Ogbonanya Orji, ne ya bayyana hakan a Legas a taron kungiyar masu ba da rahoto kan makamashi ta Nijeriya (NAEC) na 2025 a Legas ranar Alhamis. Ya koka da cewa, rashin gaskiya da rikon amana ne ya dabaibaye masana’antar mai da iskar gas, yana mai cewa akwai bukatar yin gaskiya da aiwatar da sabon tunani na fasaha wajen tafiyar da harkar mai da iskar gas a kasar. Orji ya lura cewa, kudaden da aka yi...
A bana, bikin Tsakiyar Kaka da Ranar Kafuwar Jamhuriyar Jama’ar Sin sun hadu, inda suka haifar da hutun tsawon kwanaki takwas. An yi hasashen cewa, adadin mutanen da suka yi tafiya a yankuna daban daban na kasar zai kai biliyan 2.432, tare da karuwar kashi 6.2% a kowace rana idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata. Adadin ribar da aka samu a manyan kantuna da gidajen abinci a cikin kwanaki hudu na farkon hutun ta karu da kashi 3.3% idan aka kwatanta da na bara, kuma har zuwa karfe 4:00 na yammacin ranar 8 ga watan, kudin shiga da aka samu daga kallon fina-finai yayin wannan biki ya wuce RMB Yuan biliyan 1.8 kwatankwacin fiye da dala miliyan 252....
Rahotanni sun bayyana cewa, karar mai lamba FHC/OS/194/2024, ta nemi umarnin tilastawa INEC da shugabanta na lokacin da su sanya sunayen wasu jami’an Jam’iyyar AA a shafin hukumar na yanar gizo bayan an cire su. Sai dai Udeze ya ci gaba da cewa, babu irin wannan hukunci ko umarnin kama shi (Yakubu), yana mai tabbatar da cewa, rahotannin ƙage ne kawai. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu Ya Zaɓi Farfesa Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC October 9, 2025 Labarai SSANU Da NASU Sun Yi Zanga-Zanga A Abuja Kan Rashin Cika Alƙawarin Gwamnati October 9, 2025 Labarai An Umurci Manyan Makarantu Su Mayar Da Kuɗaɗen TETFund Da Ba Su Kashe Ba October 9, 2025
Rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna ta kama wasu mutane 26 da ake zargi da yin garkuwa da mutane, tare da ƙwato bindigogi guda 4, da muggan makamai da dama. Ta kuma kama wani ɓangare na kuɗin fansa da ake zargin an biya masu garkuwa da mutane a wasu hari daban-daban a jihar. Nasarar kamen dai ya biyo bayan wasu jerin samame da jami’an ’yan sanda da na ’yan banga suka yi a tsakanin ranakun 3 zuwa 5 ga watan Oktoban 2025, inda suka yi ta kai farmaki kan gungun masu garkuwa da mutane da ke kai hari a ƙananan hukumomin Anchau, Ikara da kuma Makarfi. Tinubu ya naɗa Amupitan a matsayin Shugaban INEC Ma’aikatan jami’a sun yi zanga-zanga a Jami’ar...
Wata majiyar Falasdinawa ta bayyana cewa bayan amincewa da kawo karshen yakin Gaza,da ake tattaunawa a Sharem-Shiekh na kasar Masar, an fara aiki da tsagaita wuta a hukumance. Raidiyon HKI ya sanar da cewa, da karfe 12;00 na rana a yau Alhamis ne aka fara aiki da tsagaita wutar, don haka babu wani hari da sojojin HKI za su kai a yankin na Gaza. Majiyar Radiyon na HKI ya kuma ce; ‘Yan aiken Amurka biyu da su ne, Steven Charles Witkoff da Jared Corey Kushner sun halarci taron na Sheram-Sheikh a yau Alhamis. Jami’an Falasdinawa dai sun bayyana cewa aiki da wannan yarjejeniyar dai yana da alaka ne da yadda jami’an Haramtacciyar Kasar Isra’ila za su yi aiki da ita....
Mai Martaba Sarkin Nafada, Alhaji Dadum Hamza ya ƙaddamar da sabuwar doka ta rage tsadar aure a masarautarsa, a Jihar Gombe domin sauƙaƙa wa matasa yin aure da kuma magance matsalolin da ke hana sauƙin yin aure a cikin al’umma. Wakilin Sarkin, Alhaji Umaru Muhammad Baraya (Madakin Nafada), ne ya gabatar da dokar yayin taron ƙaddamarwa da aka gudanar a Unguwar Madaki da ke Nafada ta Tsakiya, tare da halartar jami’an gwamnati, Alƙalan kotun majistare da jami’an tsaro. ’Yan sanda sun kama waɗanda ake zargi da kashe ma’aikaciyar Arise TV a Abuja Najeriya ta tafka asarar tiriliyan 14.5 sakamakon rikicin Boko Haram – UNICEF Dokar za ta fara aiki daga wannan shekara ta 2025, inda aka gargaɗi matasa da su...
Rundunar ’Yan Sandan Babban Birnin Tarayya, sun kama mutum 12 da ake zargi da hannu a kisan ma’aikaciyar Arise TV, Somtochukwu Christella Maduagwu, a unguwar Katampe da ke Abuja. Rahotanni sun nuna cewa Somtochukwu, ta rasu bayan faɗowa daga bene mai hawa uku, yayin da ta ke ƙoƙarin tserewa daga hannun ’yan fashin, yayin da mai gadin gidan ya rasa ransa bayan harbin bindiga. Najeriya ta tafka asarar tiriliyan 14.5 sakamakon rikicin Boko Haram – UNICEF Majalisa ta yi watsi da zargin Amurka na yi wa Kiristoci kisan gilla a Najeriya Wata majiyar ’yan sanda ta bayyana cewa rundunar Scorpion Squad ƙarƙashin jagorancin ACP Victor O. Godfrey ce ta kama waɗanda ake zargin. Wasu daga cikin waɗanda aka kama sun...
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Kira ga tsayar da sallah wani aiki ne na wajibi ga hukumomin da’awar addini da malamai Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya jaddada cewa: Kira ga tsayar da sallah da koyar da ita, da bayyana ma’anonin da ke cikinta, da riko da ita, wani aiki ne na wajibi da ya rataya a wuyan hukumomin da’awar addini da malamai da ma’abuta addini. Dole ne a yi amfani da hanyoyin zamani domin watsa wannan fanni. A cikin sakon da Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya aike ga zaman taron cibiyar karfafa tsayar da sallah karo na 32 ya bayyana cewa: Taron karfafa tsayar da sallah yana daya daga cikin mafi...
Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci ya jaddada cewa: Duk wani kuskuren da makiya za su yi, za su fuskanci martani mai tsanani Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci (IRGC) Manjo Janar Mohammad Pakpour ya jaddada cewa: Duk wani kuskuren da makiya za su yi a mashigar tekun Farisa, da mashigar Hormuz da tsibirin Iran, za su fuskanci hukunci mai tsauri, nan take, murkushewa, da kuma nadama. A cikin sakon taya murnar zagayowar ranar sojojin ruwa na dakarun kare juyin juya halin Musulunci, Manjo Janar Pakpour ya bayyana cewa: “A jajibirin ranar sojojin ruwa na dakarun kare juyin juya halin Musulunci, yana mika sakon taya murna ga babban matsayi na kwamandoji da mayakan da suka yi...
Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya kaddamar da sabuwar cibiyar taro ta Ahmadu Bello da aka gina a Bauchi, inda ya bayyana ta a matsayin alamar ci gaba a gwamnatin Gwamna Bala Mohammed. Da yake jawabi a wajen taron, Obasanjo ya jaddada muhimmancin dunkulewar duniya, inda ya ce babu wata al’umma da za ta iya rayuwa a ware ba tare da yin hulda mai ma’ana da sauran kasashen duniya ba. Ya yaba wa Gwamna Bala Mohammed bisa ayyukan raya kasa, musamman a fannin samar da ababen more rayuwa, wanda a cewarsa hakan zai karawa Bauchi damar karbar bakuncin taron kasa da kasa da kuma jawo hankalin masu zuba jari. Tsohon shugaban kasar ya bayyana cewa irin wadannan...
An shawarci mata a karamar hukumar Kirikasamma da ke jihar jigawa da su kawo ‘ya’yansu domin yi musu rigakafin cutar shan inna, kyanda, da Gaida da sauran cututtuka masu ban tsoro. Uwargidan Shugaban Karamar Hukumar, Hajiya Fatima Maji Marma ta ba da wannan shawarar a lokacin kaddamar da shirin rigakafin cutar kyanda da na rigakafi na yau da kullum a fadar Hakimin Marma. Ta kuma jaddada aniyar karamar hukumar na bayar da tallafin da ake bukata domin samun nasarar gudanar da aikin rigakafin. Hajiya Fatima ta kuma yabawa gwamnatin jihar Jigawa bisa bullo da inshorar lafiya ga marasa galihu a matakin unguwanni a kananan hukumomin jihar 27. A nasa jawabin manajan hukumar kula da lafiya matakin...
Hukumar kiyaye haddura ta kasa reshen jihar Kano ta sanar da fara aiki a hukumance da sabon kwamandan hukumar, Kwamanda Idris Mohammed Lawal. Kwamanda Lawal ya karbi ragamar shugabancin hukumar ta Kano ne biyo bayan tura shi da hukumar FRSC ta yi a ranar 3 ga watan Oktoba. Ya gaji kwamandan Corps MB Bature, wanda ya yi ritaya a kwanan baya bayan ya kamala shekarun sa a aikin gwamnati. Kafin sabon mukamin nasa, Lawal ya taba zama shugaban aiyuka na shiyyar a hedikwatar hukumar FRSC shiyya daya da ke Kaduna. A jawabinsa na farko, sabon Kwamandan sashin ya nuna godiya ga rundunar Corps Marshal da Hukumar FRSC bisa amincewarsu. Ya yi alkawarin sadaukar da aikin...
Majalisar Wakilai za ta kaddamar da yakin kawo karshen Hakar Ma’adinai ba bisa ka’ida ba dake al’ummar kasar asarar sama da dalar Amurka biliyan 9 duk shekara. Shugaban Kwamitin wucin gadi kan hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba, Sanni Abdulraheem, ya bayyana haka ne a lokacin da yake gabatar da jawabinsa a lokacin kaddamar da kwamitin a harabar majalisar dokokin tarayya Abuja. Sanni Abdulraheem, wanda ya jaddada mahimmancin kwamitin ga tattalin arzikin kasa, ya bayyana hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba a matsayin wani bala’i da ke gurgunta kudaden shiga na kasa, da rura wutar aikata laifuka, da kuma zubar da muhalli. Shugaban kwamitin ya bayyana cewa, wani bangare na ayyukan kwamitin na toshe hanyoyin samun kudaden...

Kwamishinan Zamfara Ya Yabawa Yunkurin da Gwamna Lawal Ya Yi Na Jawo Masu Zuba Hannun Jarin Kasashen Waje.
Kwamishinan kasuwanci da masana’antu na jihar Zamfara, Abdulrahman Muhammad Tumbido, ya yabawa gwamna Dauda Lawal bisa jajircewar sa wajen tallata jihar Zamfara a matsayin cibiyar zuba jari. Kwamishinan, wanda ya bi sahun gwamna Lawal a wata tawaga ta hukuma zuwa bikin baje kolin kasuwanci da zuba jari na Canada–Africa da aka gudanar a Toronto, Canada, ya ce halartar gwamnan ya bude wa jihar sabbin damammaki na kasuwanci da bunkasar tattalin arziki. A wata sanarwa da jami’in yada labarai na ma’aikatar, Jamilu Bello, Tumbido ya fitar, ya tabbatar da cewa ma’aikatar kasuwanci da masana’antu za ta ci gaba da bin diddigin ayyukan hadin gwiwa da yarjejeniyoyin da aka kulla a wannan tafiya. A cewarsa, Gwamna Lawal ya baje...
Gwamnatin jihar Neja ta bayyana shirinta na yin hadin gwiwa da kungiyar injiniyoyin ma’adanai ta Najeriya a matakin jiha da tarayya domin tabbatar da aiwatar da kudurorin da aka cimma a karshen taron kasa da kasa karo na ashirin da hudu. Gwamnan jihar Mohammed Umar Bago ya bayyana haka a lokacin da yake bayyana bude taron shekara-shekara da taron kasa da kasa na shekara ashirin da hudu da aka gudanar a Minna babban birnin jihar Neja. Gwamnan wanda ya samu wakilcin shugaban ma’aikata Injiniya Idris Abubakar ya bayyana cewa hakan ya zama dole domin dorewa da aikin hakar ma’adanai na da matukar muhimmanci wajen kare shirin makamashi maras illa a matsayin Jigon gwamnatin sa. A nasa...
Hukumar Tsare-tsare da Cigaban Birane ta Jihar Kano (KNUPDA) ta jaddada aniyar ta na karfafa hadin gwiwa tsakanin hukumomi da inganta ci gaban birane ta hanyar hadin gwiwa da hukumar tsaro ta NSCDC. Tawaga daga KNUPDA, karkashin jagorancin Manajan Darakta, Arc. Hauwa Hassan T/Wada, ta kai ziyarar gani da ido hedikwatar hukumar NSCDC da ke Kano a wani bangare na kokarin fahimtar juna da hadin gwiwa tsakanin hukumomi. Da yake jawabi yayin ziyarar, Arc. Hauwa ta bayyana cewa ingantaccen tsare-tsare da ci gaban birane na bukatar hada karfi da karfe da manyan jami’an tsaro domin tabbatar da kare kadarorin gwamnati, tabbatar da doka da oda a cikin babban birni. Ta bayyana irin shirye-shiryen KNUPDA da ke ci...
Gwamna AbdulRazaq ya yabawa Shugaba Tinubu yayin da Sojoji suka tura cikakken birgediya domin fatattakar masu garkuwa da mutane daga dazukan Kwara. Hedkwatar sojojin Najeriya ta aika da cikakken birgediya da manyan kayan aiki a sassa daban-daban na Kwara ta Kudu, domin rage matsalolin tsaro a yankin. Wata sanarwa da sakataren yada labarai gwamnan, Rafiu Ajakaye ya fitar ta ce Tuni dai sojojin suka yi ta luguden wuta ta cikin kauyukan Oke Ode da Babanla, dukkansu a karamar hukumar Ifelodun. Har ila yau, rundunar ta kara da cewa, aikin ya zarce zuwa Edu da Patigi domin ratsa dazuzzukan da masu garkuwa da mutane suka fara kai hare-hare na matsorata a kan al’ummomi daban-daban tare da yin...
Majalisar Wakilai, ta yi watsi da zargin da Ƙasar Amurka, ta yi na cewa ana yi wa Kiristoci kisan gilla a Najeriya. Wannan martani na zuwa ne bayan wani Sanatan na Amurka, Ted Cruz, ya gabatar da ƙudirin doka a Majalisar Dattawan ƙasar, inda ya ce ana yi wa Kiristoci kisan gilla a Najeriya. Sauye-sauyen Tinubu ba su rage talauci a Najeriya ba — Bankin Duniya Fadar Shugaban Ƙasa ta ƙaryata rahoton Bankin Duniya kan yawan talakawa a Najeriya A yayin gabatar da ƙudirin ya buƙaci a ƙaƙaba wa wasu jami’an Najeriya takunkumi. Cruz ya ce: “ Ana kashe Kiristocin Najeriya saboda addininsu… lokaci ya yi da za a ɗauki mataki na gaske kan jami’an Najeriya da ke taimaka wa...
Ya kuma sanar da cewa an saka wa cibiyar sunan marigayi Sir Ahmadu Bello, Sardaunan Sakkwato, domin girmama jajircewarsa da hangen nesansa a shugabanci.Gwamnan ya ƙara da cewa Bauchi na da ɗimbin albarkatun ƙasa, kuma gwamnatinsa tana ɗaukar matakai don inganta yanayin kasuwanci domin jawo hankalin ‘yan kasuwa daga cikin gida da wajen ƙasa.Taron, wanda mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya wakilci shugaban ƙasa Bola Tinubu, ya samu halartar gwamnonin jihohi, Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, jakadu, sarakuna, da masu zuba jari daga sassa daban-daban na duniya. Ga hotunan:ShareTweetSendShareMASU ALAKA HotunaHOTUNA: An Tsaurara Tsaro A Gidan Buhari Da Ke Daura July 15, 2025HotunaHOTUNA: Yadda Bikin Al’adun Gargajiya A Masarautar Kaltungo Ya Gudana December 28, 2024HotunaHOTUNA: Yadda Abba Ya Raba...
Cristiano Ronaldo ya zama biloniya na farko tsakanin ƴan wasan kwallon kafa a duniya Bloomberg mai sharhi da kididdiga tarin dukiya tsakanin attajiran duniya, ta fayyace tarin kudin da mai shekara 40 dan kwallon tawagar Portugal mai taka leda a Al-Nassr ta Saudiya ke da shi. Ta ce yana da dalar Amurka biliyan daya da miliyan 400 daga kudin da yake samu na albashi da ladan wasa da tallace-tallace da zuba hannun jari. Ya samu albashin sama da dalar Amurka miliyan 550 tsakanin 2002 zuwa 2023 da kwantiragin da ya kai dalar Amurka miliya 18. Lokacin da Ronaldo ya koma Al-Nassr ta Saudiyya a 2022, ya zama wanda ke kan gaba da ake biya albashi mafi tsoka a tarihi. da...
Bankin Duniya ya ce har yanzu talauci na ci gaba da yaɗuwa a Najeriya duk da sauye-sauyen tattalin arziƙi da Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta aiwatar domin daidaita tattalin arziƙin ƙasar. A wajen ƙaddamar da rahoton ci gaban da aka samu a Abuja, Daraktan Bankin Duniya a Najeriya, Mathew Verghis, ya bayyana cewa aƙalla mutum miliyan 139 ne ke rayuwa cikin ƙangin talauci a shekarar 2025. Fadar Shugaban Ƙasa ta ƙaryata rahoton Bankin Duniya kan yawan talakawa a Najeriya NAJERIYA A YAU: Abin Da Dokar Kasa Ta Ce Kan Nada Shugaban Hukumar Zabe Ya ce duk da cewa tattalin arziƙin Najeriya ya ɗan bunƙasa, kuma gwamnati tana samun ƙarin kuɗaɗen shiga, yawancin jama’a har yanzu na fama da tsadar...
Adaidai lokacin da ake taron cika shekaru 2 da fara yakin Gaza Babban sakatare janar din Majalisar dinkin duniya Antonio Guterres ya sake yin kira da a gaggauta cimma yarjejeniyar dakatar da bude wuta ta din din din a yankin Gaza .inda ya bayyana yakin a matsayin babban bala’I da ba’a taba ganin irinsa ba Yakin ya jawo mummunar asarar rayukan mutane fararen hula da kuma lalata abubuwan amfani na jama’a , kuma ya jawo matsaloli masu yawa a ayyukan jin kai da yake bukatar kulawa ta gaggawa da kuma warware matsala ta hanyar siyasa Guterres ya halarci wannan taron ne inda yayi alkawarin ganin an kawo karshen yakin Gaza kuma ya amince da dukkan shawarwarin da Amurka ta bayar...
Fadar Shugaban Ƙasa ta yi fatali da sabon rahoton tattalin arziki da Bankin Duniya ya fitar, wanda ya kiyasta cewa mutane miliyan 139 na rayuwa cikin talauci. Fadar ta bayyana adadin a matsayin wanda ya saba da zahiri kuma ya kauce wa hakikanin halin tattalin arzikin ƙasar. SSANU da NASU za su yi wa gwamnati zanga-zanga kan rashin cika musu alƙawari 2027: Atiku, Jonathan da Obi ba za su iya kayar da Tinubu ba — Kalu Mai ba Shugaban Najeriya Bola Tinubu shawara kan harkokin yaɗa labarai da sadarwa, Sunday Dare, ya bayyana a shafinsa na X a ranar Laraba cewa dole ne a rahoton bai duba yanayin tsarin auna talauci na duniya ba. “Duk da cewa Najeriya na daraja...
Ƙungiyar Ma’aikatan Manyan Makarantun Najeriya (SSANU) da Ƙungiyar Ma’aikatan Ilimi (NASU), sun shirya gudanar da zanga-zangar gargaɗi ta rana ɗaya a yau Alhamis saboda Gwamnatin Tarayya ta gaza cika musu alƙawuran da ta ɗauka. Ƙungiyoyin, ƙarƙashin jagoranci Joint Action Committee (JAC), sun gudanar da taron gaggawa a ranar Laraba don shirya zanga-zangar. 2027: Atiku, Jonathan da Obi ba za su iya kayar da Tinubu ba — Kalu ’Yan sanda sun kama ɗan bindiga a kan iyakar Najeriya da Kamaru Sun ce za su gudanar da tattaki a cikin jami’o’i, tare da ɗaukar kwalaye masu rubuce-rubuce, sannan za su yi wa manema labarai jawabi domin bayyana ƙorafe-ƙorafensu. Sun zargi gwamnati da rashin adalci wajen rabon Naira biliyan 50 na alawus-alawus, ƙin...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A tsarin mulkin Najeriya, an bai wa Shugaban Ƙasa ikon naɗa shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) tare da sauran mambobinta. Wannan iko yana daga cikin muhimman nauyukan da ke hannun shugaban ƙasa domin tabbatar da cewa ana gudanar da zaɓe cikin tsari, gaskiya da adalci. Sai dai, kafin wanda shugaban ƙasa ya naɗa ya fara aiki, dole ne a nemi amincewar Majalisar Dattawa, domin tabbatar da cewa wanda aka zaɓa ya cancanci rike wannan muhimmiyar kujera. Wannan tsari yana taimakawa wajen tabbatar da cewa hukumar zaɓe ta kasance mai zaman kanta, ba ta karkata ga wani ɓangare na siyasa ba, kuma tana iya gudanar da aikinta cikin gaskiya...
Kakakin majalisar wakilai, Hon. Abbas Tajudeen, ya jaddada buƙatar ɗaukar ƙwararan matakai na kafa tsarin ‘yansandan jihohi a kasar nan domin magance kalubalen tsaro da ake fuskanta.Abbas ya bayyana haka ne a wajen taron jin ra’ayin jama’a kan kudirin dokar hukumar leken asiri da binciken sirri ta shekarar 2024, wanda kwamitin majalisar kan harkokin tsaro da leken asiri ya shirya a harabar majalisar dokokin kasar da ke Abuja ranar Laraba.Kakakin majalisar wanda ya samu wakilcin mamba mai wakiltar mazabar Ilorin ta Yamma/Asa, Honarabul Muktar Shagaya, ya ce, kawo sauye-sauye a fannin tsaro ya zama abinda aka fi mayar da hankali, kuma yanzu dole a tashi daga rubutu kawai zuwa aiwatar da cikakken tsari.Shugaban majalisar ya ce kafa ‘yansandan jihohi ta...
An kashe wani yaro ɗan shekara 13 mai suna Abubakar Wada da shanu 36, yayin da wasu ’yan bindiga sun kai wa makiyaya hari a kusa da ƙauyen Inzon da ke yankin Fan, a Ƙaramar Hukumar Barkin Ladi a Jihar Filato. Aƙalla shanu 49 kuma sun ɓace ba tare da sanin inda suka shiga ba. ’Yan sanda sun kama ɗan bindiga a kan iyakar Najeriya da Kamaru Kamfanonin rarraba lantarki sun tafka asarar biliyan 358 a cikin wata uku – NERC Shugaban ƙungiyar makiyaya ta Miyetti Allah (MACBAN), a Jihar Filato, Ibrahim Yusuf Babayo, ya bayyana cewa harin ya faru ne da yammacin ranar Talata lokacin da wasu makiyaya uku ke dawowa daga kiwo. Ya ce ’yan bindigar sun buɗe...
Gamayyar Jiragen ruwan ceto ko (FFC) ta bada sanarwan cewa sojojin HKI a yau Laraba sun kai faramaki kan wasu jiragen gamayyar a tazarar kilomitan ruwa 120nm kacal daga zirin Gaza. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar FFC tana cewa hotunan bidiyo da na tsaye, duk sun nuna lokacinda sojojin yahudawan suka farwa jiragen na ceton Gaza. Labarin ya kara da cewa sojojin yahudawan sun dakatar da wasu jiragen a ruwayen kasa da kasa, wanda bata da hakkin yin hakan. Jiragen ruwan ceton dai suna dauke da kayakin agaji wadanda suka kai dalar Amurka $110,000, kama hada da kayakin aikin likita da magunguna da wasu kayakin asbiti. Labarin ya nakalto kafafen yada labaran yahudawan na cewa...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe, ta kama wani mutum da ake zargin ɗan bindiga ne da ke aiki tsakanin iyakar Najeriya da Kamaru. Rundunar ta kuma ƙwato bindigogi ƙirar AK-47 guda biyu, harsasai 80 da wasu tarin makamai. Gwamnatin Gombe ta kafa hukumar bunkasa fasahar zamani da tattalin arziƙi Yadda Obasanjo ya ƙaddamar da cibiyar taron ƙasa da ƙasa a Bauchi Kakakin rundunar, DSP Buhari Abdullahi, ya bayyana cewa wanda aka kama, Adamu Adamu, mai shekaru 30, ɗan asalin Ƙaramar Hukumar Song a Jihar Adamawa. Amma wanda aka kama mazaunin unguwar Jauro Jatau da ke Akko, Jihar Gombe. An kama shi ne ranar 4 ga watan Oktoba, 2025, bayan samun sahihan bayanai da suka nuna cewa yana tare da wata...
ShareTweetSendShareMASU ALAKA Manyan LabaraiBoko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung October 8, 2025Manyan Labarai‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio October 8, 2025Manyan LabaraiDa Ɗumi-ɗumi: Yakubu Ya Miƙa Ragamar INEC Ga Agbamuche-Mbu A Matsayin Shugabar Riƙo October 7, 2025
Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya sanya hannu kan dokar kafa Hukumar Fasahar Sadarwa da Tattalin Arziki ta Zamani (GITDEC), domin bunƙasa ƙirƙire-ƙirƙire da ci gaban tattalin arziƙin jihar. Gwamnan ya ce kafa wannan hukuma wani muhimmin mataki ne da zai taimaka wajen sanya Gombe cikin jihohin da ke tafiya da zamani a ɓangaren fasaha. ’Yan bindiga sun sace shugaban malamai da wasu a Zamfara Yadda Obasanjo ya ƙaddamar da cibiyar taron ƙasa da ƙasa a Bauchi “Ayyukan hukumar sun haɗa da samar da cibiyar ƙirƙire-ƙirƙire, bunƙasa fasahar zamani, koyar da dabarun zamani, da kuma aiwatar da ayyukan gwamnati ta yanar gizo,” in ji gwamnan. Haka kuma hukumar za ta tallafa wa matasa da masu ƙirƙira, ta samu hannun...
Wasu da ake zargin ’yan bindiga ne, sun tare hanyar Gusau zuwa Gummi a Jihar Zamfara, inda suka sace mutane da dama. Wata majiya ta bayyana cewa, maharan sun tare motoci sannan suka yi awon gava da fasinjojin da ke ciki. Yadda Obasanjo ya ƙaddamar da cibiyar taron ƙasa da ƙasa a Bauchi Ban yi murabus don ina da laifi ba — Nnaji Wani shaida ya ce ’yan bindigar sun ɗauki lokaci suna sharafinsu kafin daga bisani suka tafi da mutanen da suka kama. Daga cikin waɗanda suka sace akwai Malam Sadis Isa, shugaban Majalisar Malamai ta Ƙaramar Hukumar Gummi, abin da ya jefa al’umma cikin tsoro da damuwa. “Da yammacin ranar Talata, ’yan bindiga sun tare hanyar Gusau zuwa...
Tsohon Shugaban Ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya ƙaddamar da sabon ginin Cibiyar Taron Ƙasa da Ƙasa, wadda aka sanya wa sunan Sir Ahmadu Bello a Jihar Bauchi. An ƙaddamar da cibiyar ne kafin babban taron zuba jari da nufin bunkasa kasuwanci da masana’antu a jihar. Ban yi murabus don ina da laifi ba — Nnaji Kamfanonin rarraba lantarki sun tafka asarar biliyan 358 a cikin wata uku – NERC A jawabinsa, Obasanjo ya yaba wa Gwamna Bala Mohammed, bisa irin ayyukan raya ƙasa da yake aiwatarwa, waɗanda ke inganta rayuwar jama’a. “Na yi farin ciki da abin da na gani da kuma abin da na ji. Ban zata cewa zan dawo Bauchi cikin ƙanƙanin lokaci don buɗe irin wannan katafaren waje...
Hukumar da ke Kula da Wutar Lantarki ta Najeriya (NERC) ta ce kamfanonin rarraba wutar lantarki guda 11 sun tara Naira biliyan 546.71 daga hannun abokan cinikinsu a cikin zango na biyu na shekarar 2025. Sai dai hukumar ta ce wannan adadi bai kai kaso 60 cikin 100 na wutar da aka tura musu daga babbar hanyar rarraba wuta ba, sakamakon matsalolin lissafin wutar da suka karɓa da kuma yadda aka raba wutar ga rukunan abokan ciniki daban-daban. Zulum ya ba ma’aikaciyar lafiya ’yar kabilar Igbo kyautar gida, ya ba danta aiki Matar aure mai ’ya’ya huɗu ta rataye kanta a Jigawa Hakan, a cewar hukumar, ya haifar da gibin biyan kuɗi na naira biliyan 167.25. kazalika, NERC ta ce...
Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya bai wa wata ma’aikaciyar lafiya ’yar ƙabilar Igbo kuma ‘yar asalin jihar Anambra, Marbel Ijeoma Duaka, kyautar gida mai dakuna biyu. Gwamnan ya kuma ba ɗan ma’aikaciyar aikin yi na dinidindin saboda jajircewarta da sadaukarwa wajen hidimtawa jihar na sama da shekara 20. Matar aure mai ’ya’ya huɗu ta rataye kanta a Jigawa Joash Amupitan na iya zama sabon shugaban INEC Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin rabon gidaje 72 ga malamai da ma’aikatan lafiya a ƙaramar hukumar Mafa. Zulum ya ce Marbel ta shafe fiye da shekaru 24 tana aiki a cibiyar kula da lafiya ta matakin farko da ke Mafa, kuma ba ta taɓa barin wurin ba ko...
Al’umma a kauyen Sumore da ke Ƙaramar Hukumar Dutse a Jihar Jigawa sun shiga cikin alhini bayan mutuwar wata mata mai shekaru 30, Adama Hannafi, wacce ake zargin ta rataye kanta. Lamarin, wanda ya faru a ranar Talata, ya tayar da hankulan mazauna kan ƙalubalen da ke tattare da rashin lafiyar kwakwalwa a cikin al’umma, musamman a yankunan karkara. ‘Akwai ɗaliban da ke yin digiri yanzu ba tare da sun taɓa shiga ɗakin karatu ba saboda AI’ Joash Amupitan na iya zama sabon shugaban INEC Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar, SP Lawan Shi’isu Adam, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa an samu gawar matar a rataye a jikin wata bishiya a kauyen. “Mun samu kiran...
Shugabar Cibiyar Nazarin Karatu da Ci Gaban Ilimi ta Najeriya (NCRRD) da ke Jami’ar Bayero Kano (BUK), Farfesa Amina Adamu, ta bayyana damuwa kan yadda dalibai ke ƙara gujewa amfani da dakunan karatu, tana danganta hakan da dogaro da kirkirarriyar fasaha ta AI. Da take jawabi a taron ƙasa da ƙasa karo na biyar kan nazarin karatu da nazari da aka gudanar a Jami’ar Bayero Kano, Farfesa Amina ta ce da dama daga cikin ɗalibai yanzu suna kammala karatun jami’a ba tare da sun taɓa shiga ɗakin karatu ko sau ɗaya ba. Yadda zargin mallakar takardun bogi ya yi awon gaba da kujerar Ministan Tinubu Joash Amupitan na iya zama sabon shugaban INEC “Muna da daliban da ke yin rajista...
Ya buƙaci jama’a suke bambanta “gaskiya da siyasa.”ShareTweetSendShareMASU ALAKA Manyan Labarai‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio October 8, 2025Manyan LabaraiDa Ɗumi-ɗumi: Yakubu Ya Miƙa Ragamar INEC Ga Agbamuche-Mbu A Matsayin Shugabar Riƙo October 7, 2025Manyan LabaraiYa Kamata Nijeriya Ta Ayyana Yaƙi Da ‘Yan Ta’adda — Tsohon Hafsan Sojin Ƙasa October 7, 2025
Shugaban hukumar makamashin nukiliya ta Iran ya jaddada cewa: Iran ba zata daina samar da magungunan da take yi ta hanyar fasahar makamashin nukiliya ba Kakakin Kwamitin Tsaro da Harkokin Waje na Majalisar Shawarar Musulunci (wato Majalisar Dokoki) Ibrahim Reza’ei, ya tabbatar da cewa ana ci gaba da samar da magungunan ta hanyar fasahar makamashin nukiliya a Iran, kuma ba a taba dainawa ba, kuma za a ci gaba da gudanarwa. Reza’i ya bayyana cewa: Kwamitin tsaron kasar ya gudanar da zaman hadin gwiwa tare da shugaban hukumar makamashin nukiliya ta Iran (AEOI), Mohammad Eslami, da wasu jami’an kungiyar. Islami ya gabatar da wani rahoto kan ci gaban da aka samu a fannin makamashin nukiliya, da hasarar da aka samu...
Dakarun bangaren sojin kungiyar Jihadul Islama ta Falasdinu Sarayal-Quds ta bayyana cewa: Fursunonin mamaya ba za su ga hasken rana ba har sai an sharuddan Falasdinawa Dakarun bangaren sojin kungiyar Jihadul Islama ta Falasdinu, sun jaddada cewa: Fursunonin mamayar Isra’ila ba za su ga hasken rana ba, sai dai ta hanyar tattaunawa da musayar ra’ayi da yahudawan sahayoniyya da suka kuduri aniyar kawo karshen yakin Gaza. A cikin wata sanarwa da dakarun Sarayal-Quds suka fitar, sun jaddada cewa su da dukkanin bangarorin gwagwarmaya ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen samar da hanyar kawo karshen yakin Gaza da kuma wahalhalun da Falasdinawan suke ciki. Har ila yau, sun tabbatar da cewa: “Makaman ‘yan gwagwarmaya makamai ne da aka...
Rahotannin daga Gaza na cewa Isra’ila na ci gaba da kai hare-hare a yankin Falasdinawa, a daidai lokacin da wakilan kungiyar da kuma masu shiga tsakani ke tattaunawa a Masar. Tankunan yaki da jiragen sama da jiragen ruwa na Isra’ila sun yi luguden wuta a wasu sassa na Gaza a ranar Talata. A cewar tashar Aljazeera, Hamas ta nunar da cewa ci gaba da kai hare-haren bama-bamai da Isra’ila ke yi a zirin Gaza, wani cikas ne ga sako mutanen da aka yi garkuwa da su. Qatar mai shiga tsakani a yakin Gaza, ta bayyana cewa, kamata ya yi Isra’ila ta dakatar da ayyukan soji a yankin Falasdinun, kamar yadda shugaban Amurka Donald Trump ya tsara, idan dai har ikirarin...
Uche Nnaji, Ministan Ƙirƙira, Kimiyya da Fasaha, ya yi murabus daga mukaminsa. Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ne ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar da yammacin ranar Talata. Joash Amupitan na iya zama sabon shugaban INEC Jerin ministocin da zargin takardun bogi ya tabaibaye su Nnaji na fuskantar zarge-zarge kan sahihancin takardun karatunsa, inda binciken da jaridar Premium Times ta gudanar ya gano cewa Jami’ar Najeriya da ke Nsukka (UNN) ta ce ba ta ba shi takardar kammala digiri ba. A cewar jami’ar, tsohon Ministan bai kammala karatunsa a cikinta ba, kuma ba ta taɓa ba shi takardar shaidar kammala ta ba. A cewar jaridar, Simon U. Ortuanya, Shugaban Jami’ar UNN, ya...
Geng Shuang ya jaddada cewa, kasar Sin kasa ce da ta’addanci ya yi wa illa. Ya ce kungiyar ETIM wadda kwamitin sulhu na MDD ya ayyana a matsayin ta ta’addanci, ta taba tada rikice-rikicen ta’addanci da dama a cikin kasar Sin, kana ta gudanar da ayyukanta a kasar Syria, da Afghanistan da sauransu. Ya jaddada cewa, kasar Sin na kira ga bangarori daban daban da su dauki matakai don yaki da kungiyoyin ta’addanci ciki har da kungiyar ETIM. (Zainab Zhang)ShareTweetSendShareMASU ALAKA Daga Birnin SinSauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi? October 7, 2025Daga Birnin SinDaukacin Mambobin Majalisar Kare Hakkokin Dan Adam Ta MDD Sun Amince Da Kudurin Da Kasar Sin Ta Gabatar Kan Kare Hakkokin Tattalin Arziki Da Zamantakewa Da...
Ya gargadi masu kafa kungiyoyi daban-daban a Arewa, yana kiran irin waɗannan ƙungiyoyi “barazana ga haɗin kan Arewa.” Haka kuma ya yaba wa sojojin Nijeriya bisa kokarinsu da sadaukarwa wajen yaki da matsalar tsaro. Alhaji Dalhatu ya kuma yi Allah wadai da “ƙungiyoyin marasa kishin ƙasa” da suka jawo rikicin baya-bayan nan a matatar mai ta Dangote, tare da kira ga Gwamnatin Tarayya da ta shiga tsakani. A cewarsa, kwanan nan an samu rikice-rikicen maganganu masu karo da juna daga wasu jami’an ACF a matakin kasa da jihohi, wanda hakan ya sa dole a kafa tsarin sadarwa mai tsauri. “Majalisar Amintattu tana da ikon da nauyin Ya bayyana cewa taron, wanda shugabannin jihohi, sakatarori, da mambobin Arewa 100% Focus Group suka halarta, zai...

Daukacin Mambobin Majalisar Kare Hakkokin Dan Adam Ta MDD Sun Amince Da Kudurin Da Kasar Sin Ta Gabatar Kan Kare Hakkokin Tattalin Arziki Da Zamantakewa Da Al’adu
Kasashe masu tasowa sun yi jawabi daya bayan daya, suna masu bayyana kudurin a matsayin wanda ya haska bukatar da daukacin jama’a ke da ita ta amsa kiraye-kirayen kasashe masu tasowa na kara zuba jari a fannin tabbatar da hakkokin da suka shafi tattalin arziki da zamantakewa da al’adu. Haka kuma bangarori da dama ciki har da Tarayyar Turai, sun yaba wa kudurin. (Fa’iza Mustapha) ShareTweetSendShareMASU ALAKA Daga Birnin SinFiraministan Sin Zai Halarci Bikin Cika Shekaru 80 Na Kafuwar Jam’iyyar WPK Ta Korea Ta Arewa October 7, 2025Daga Birnin SinHabakar Yin Sayayya A Lokacin Hutu Ta Nuna Kirkira Da Irin Ci Gaban Da Tattalin Arzikin Kasar Sin Ke Samu October 6, 2025Daga Birnin SinKaramin Ofishin Jakadancin Sin Da Ke Legas...