Trump ya yi barazanar korar Gwamnar Babban Bankin Amurka
Published: 26th, August 2025 GMT
Shugaba Donald Trump, ya yi barazanar sauke Lisa Cook, Gwamnar Babban Bankin Amurka (Federal Reserve), yana mai sukar yadda ake tafiyar da harkokin bankin, musamman batun bayar da bashi da tsare-tsaren lamuni.
A wata sanarwa da fadar White House ta fitar, Trump ya zargi Cook da gabatar da “bayanan ƙarya” kan sharuɗan bayar da lamunin gidaje (mortgage), yana mai cewa hakan ya jefa dubban Amurkawa cikin wahala sakamakon hauhawar kuɗin ruwa da kuma tsadar bashi.
Sai dai Lisa Cook ta mayar da martani da cewa shugaban ba shi da ikon sauke ta daga muƙamin da take riƙe da shi, saboda dokar da ta kafa Babban Bankin Amurka ta tanadar da cikakken ’yanci ga ’yan kwamitin gudanarwarsa.
Ta sha alwashin cewa za ta ci gaba da gudanar da aikinta ba tare da wani ɗar-ɗar ba, tana mai cewa manufarta ita ce kare tattalin arziƙi da talakawan ƙasar.
Cook ta yi suna tun lokacin da tsohon shugaban Amurka, Joe Biden, ya naɗa ta a shekarar 2022, inda ta zama mace baƙar fata ta farko ’yar asalin Afirka da ta taɓa zama mamba a kwamitin gudanarwa na Federal Reserve.
Wannan naɗin ya samu yabo daga masu fafutikar kare ’yancin mata da ’yan tsiraru, waɗanda suka ce hakan ya nuna ci gaba a fannin da mata ba su da yawa.
Sai dai tun bayan dawowar Trump kan mulki, gwamnar ta fuskanci matsin lamba daga sabuwar gwamnatin, wacce ke sukar manufofin Babban Bankin musamman kan hauhawar farashin kaya da matsalar gidaje.
Masu nazari kan harkokin tattalin arziƙi sun bayyana cewa wannan takun-saka tsakanin shugaban ƙasa da Babban Bankin na iya kawo ruɗani a fannin harkokin kuɗi a Amurka.
Masana harkokin siyasa kuma sun ce ƙoƙarin Trump na korar Cook na iya haifar da saɓani mai zafi tsakanin ɓangaren zartarwa da Babban Bankin, wanda ke da cikakken ’yanci.
A yanzu haka, an fara ganin tasirin wannan saɓani a kasuwannin hannun jari na ƙasar, inda farashin wasu manyan kamfanoni ya fara raguwa saboda rashin tabbas kan makomar manufofin kuɗi a ƙasar.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Federal Reserve
এছাড়াও পড়ুন:
Barazanar Amurka Kan Kisan Kiristoci A Nijeriya: Tinubu Da Trump Za Su Gana Kwanan Nan — Bwala
Da yake mayar da martani ga wannan zargin na Amurka, Bwala ya ce gwamnatin Tinubu tana jajircewa wajen kare dukkan ‘yan Nijeriya ba tare da la’akari da addini ba, yana mai cewa Amurka da Nijeriya sun dade suna hadin gwiwa a yaki da ta’addanci.
“Shugaba Bola Tinubu da Shugaba Donald Trump suna da kudiri iri ɗaya a yaƙi da ta’addanci da duk wani nau’in ta’addanci a kan bil’adama,” in ji Bwala.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA