Iran Ta Jaddada Matsayinta Kan Batun Tace Sinadarin Yuranium A Batun Tattaunawa Da Amurka
Published: 22nd, April 2025 GMT
Jamuhuriyar Musulunci ta Iran ta jaddada matsayinta kan batun tace sinadarin yuraniyo.
Mai magana da yawun gwamnatin Iran Fatemeh Mohajerani ta bayyana cewa, Iran na kokarin yin shawarwari ne domin samar da amana da samar da gaskiya game da shirinta na nukiliya domin dage takunkumi kanta.
A cikin taron manema labarai na mako-mako da ta gudanar a jiya litinin, Mohajerani ta mayar da martani ga wata tambaya game da tattaunawar da ake yi tsakanin Iran da Amurka, inda ta ce, shin bangarorin biyu sun cimma matsaya dangane da kasar da za a aike da hajojin uranium da Iran ta inganta? Shin Iran ta amince ta mika wadannan haja zuwa Rasha? Ta ce: Ina so in bayyana dangane da kashi na farko na tambayar cewa wasu daga cikin wadannan lamurra jajayen layukan Iran ne.
Wasu batutuwa a bude suke don tattaunawa, amma, kamar yadda aka ambata a baya, wasu daga cikin abubuwan da ake tattaunawa a kafafen yada labarai sun fada cikin jajayen layin Jamhuriyar Musulunci ta Iran ne, dangane da kasar Rasha, tana jaddada cewa, a matsayinta na mamba na dindindin a kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya tana da matukar muhimmanci a wurin Iran, kuma hadin gwiwar kut-da-kut da ke tsakanin Iran da Rasha, ya bai wa kasar Rasha rawar da ta taka wajen yin shawarwarin.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Majalisar Dinkin Duniya Ta Jaddada Wajabcin Komawa Kan Shirin Tsagaita Bude Wuta A Gaza
Majalisar Dinkin Duniya ta jaddada wajabcin komawa kan Shirin tsagaita bude wuta a Gaza
Wakiliyar babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya na musamman ta jaddada a yau Litinin cewa: Akwai tsananin bukatar komawa ga Shirin tsagaita bude wuta a Gaza.
A lokacin da take ba da shaida a zaman kotun kasa da kasa kan wajabcin da ya hau kan haramtacciyar kasar Isra’ila na kiyaye hakkokin mazaunan yankunan Falasdinawa, ta jaddada wajabcin isar da kayayyakin agajin na gaggawa ga Zirin Gaza, inda ta bayyana cewa: Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya António Guterres na yin duk wani kokari na kawo karshen matsalar jin kai da fararen hula ke fuskanta a yankunan Falasdinawa da aka mamaye da yankunan Falasdinawa da ba a mamaye ba amma suna fuskantar hare-haren wuce gona da iri.
Ta bayyana cewa kin bari a shigar da kayayyakin jin kai na yankunan Falasdinawa tun daga ranar 2 ga watan Maris ya kara ta’azzara wahalhalun jin kai a Gaza, tana mai bayanin cewa hukumomin Majalisar Dinkin Duniya na kokarin samar da muhimman abubuwan da ake bukata domin ci gaba da rayuwar al’ummar Falasdinu.