Jama’a sun koka kan rashin inganci shinkafar Gwamanti a Kogi
Published: 15th, April 2025 GMT
’Yan Najeriya da suka rabauta da sayen shinkafar kasar waje da Gwamnatin Tarayya ta karya farashinsa sun koka bisa rashin ingancin wata wadda ake sayarwa a Jihar Kogi.
Wadanda suka sayi rukunin farko na shinkafar sun yaba da ingancinta da dandanonta, wasu kuma na korafi a kan yanayi da kuma dandanon wadda suka samu daga wani kamfani daga wata kasar Asiya.
Wasu suka samu shinkafar mai matsala sun yi ikirarin samun kwari a cikinta kuma tana yin kumfa idan ana dafa ta, sa’annan idan ta nuna tana yin danko sosai, sabanin yadda aka san shinkafar kasar waje.
Wani dan kasuwar shinkafar cikin gida a Najeriya ya yi zargin rukunin shinkafar da ta samu matsalar ta jima a ajiye ne kafin a fito da ita, shi ya sa ingancin ya samu matsala.
Duk da samun koma baya: Najeriya ce kasa mafi arzikin danyen mai a Afirka —OPEC Matashi ya yi yunƙurin soka wa mahaifinsa makami a KanoDon haka ya shawarci masu saya da su shanya ta a rana kuma su wanke ta sosai sa’annan su dan turara ta domin dawo da ingancinta.
A gefe guda kuma wadanda da suka amfana da wani rukuni na daban na shinkafar gwamnatin sun yaba da ingancinta ta fuskar dandano da kuma yanayi.
Kawo yanzu dai hukumomi ba su ce uffan game da korafin da jama’a ke yi kan wannan lamari ba.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: gwamnati
এছাড়াও পড়ুন:
Sakkwatawa na murnar kisan da sojoji suka yi wa mataimakin Bello Turji
Al’ummar ƙaramar hukumar Sabon Birni da ke jihar Sakkwato sun bayyana farin ciki bayan samun labarin kashe fitaccen ɗan bindiga da ya dade yana addabar yankin gabashin jihar, Kacalla Kallamu.
Rundunar Sojoji ta 8 ta hallaka jagoran ’yan bindiga, Kachalla Kallamu, a wani samamen haɗin gwiwa da aka kaddamar a ƙaramar hukumar Sabon Birni.
Dalibin jami’a ya rasu a hatsarin motar murnar kammala jarabawa Iya sojojin da ke tsaron Seyi Tinubu sun isa su samar da tsaro a Benin – SoyinkaWata majiyar soja da ta tabbatar da lamarin ga manema labarai a ranar Talata ta bayyana samamen a matsayin “babbar asara ga cibiyar ’yan bindigar Bello Turji,” tana mai cewa Kallamu shi ne babban na hannun daman Turji.
A cewar majiyar, an kashe Kallamu tare da wani daga cikin manyan masu samar wa Turji kayayyakin aiki a lokacin samamen da aka gudanar da safe a kauyen Kurawa ranar Litinin.
Majiyar ta ƙara da cewa aikin ya samu muhimmiyar gudunmuwar kungiyoyin sa‑kai na yankin.
“Mun dade muna bibiyar Kallamu. Kashe shi wata babbar nasara ce wajen raunana karfin ’yan bindigar da ke Sabon Birni da kewaye,” in ji majiyar.
Mamacin, wanda asalin ɗan Garin Idi ne a Sabon Birni, ya dade yana addabar al’ummar yankin.
Ana zargin ya gudu zuwa Jihar Kogi bayan ya tsere wa luguden wutar sojoji a watan Yuni 2025, amma ya sake shigowa yankin kwanan nan ba tare da an sani ba.
Majiyar ta yaba da ƙarin bayanan sirri da ake samu daga al’ummomin yankin, tana mai cewa haɗin kai tsakanin mazauna yankin da jami’an tsaro ya taka muhimmiyar rawa wajen nasarorin baya‑bayan nan.
Manema labarai sun ruwaito cewa an ci gaba da murnar labarin a Sabon Birni, yayin da mashawarcin musamman ga Gwamna Ahmad Aliyu kan harkokin tsaro, Kanal Ahmed Usman (mai ritaya), ya yaba wa dakarun bisa “ci gaba da jajircewa da ƙwarewa” wajen yaƙi da ’yan bindiga.
Mutanen garin Sabon Birni sun fito maza da mata suna murnar nasarar da aka samu, har suna cewa suna jin wannan rana kamar ta Sallah.
Sun yi fatan a ci gaba da samun nasarori irin wannan domin kawar da ’yan bindiga a yankin, a jihar, da kuma Arewacin Najeriya gaba ɗaya.