Daruruwan ‘Yan Share Wuri Zauna Sun Kutsa Masallacin Kudus
Published: 15th, April 2025 GMT
A jiya Litinin daruruwan yahudawa ‘yan share wuri zauna sun kutsa cikin masallacin kudus, suna masu bayar da take na tsokana ga Musulmi. Har ila yau ‘yan share wuri zauna din sun kuma gudanar da na’u’oin ibadu na addinin yahudanci a cikin farfajiyar masallacin na Kudus.
Ma’aikatar da take kula da wuraren ‘wakafi’ na musulunci, ta bayyana cewa; Adadin yahudawa ‘yan share wuri zauna din da su ka kutsa cikin masallacin na Kudus sun kai 765,kuma ‘yan sanda sun rika yi musu rakiya.
A lokaci daya kuma jami’an tsaron na ‘yan sahayoniya sun tsaurara matakan kuntatawa Falasdinawa masu shiga cikin masallacin na Kudus domin yin salla.
Wannan tsokanar ta ‘yan share wuri zauna a masallacin Kudus, tana faruwa ne a lokacin da a can yammacin kogin Jordan, yahudawan suke lalata gonakin Falasdinawa da kankare kasar gonakin ta hanyar amfani da manyan motoci na buldoza.
Har ila yau ‘yan sandan HKI sun kutsa cikin garuruwa da dama na Falasdinawa a yammacin kogin Jordan, inda su ka kama mutane da dama. Haka nan kuma sanadiyyar harbe-harebn da su ka yi, sun jikkata Falasdinawa 4 a sansanin Jalzuna dake arewacin birnin Ramallah.
A birnin Tubas kuwa ‘yan sahayoniyar sun kutsa cikin unguwanni mabanbanta tare da tilastawa mazauna wasu unguwanni da su fice daga cikin gidajensu. Kwamitin al’umma na Falasdinu a yankin ya sanar da cewa a tsawon lokacin yaki adadin Falasdinawan da aka tilastawa ficewa daga cikin gidajensu, sun kai dubu 3 da 227.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: yan share wuri zauna
এছাড়াও পড়ুন:
Magajin Garin Birnin Tehran Ya Karyata Da’awar ‘Yan Sahayoniyya
Magajin garin birnin Tehran ya bayyana cewa: Karyar ‘yan sahayoniyya ya tonu na cewa ba su kai hare-hare kan fararen hula a yakin da suka kaddamar kan Iran ba
Magajin garin birnin Tehran fadar mulkin kasar Iran Ali-Ridha Zakani ya tabbatar da cewa: Karairayi da ‘yan sahayoniyya suke yadawa dangane da rashin kai hare-hare kan fararen hula a yakin da suka kaddamar kan Iran a fili yake karara. Yana mai nuni da cewa akwai kwarararn dalilai da ake da su wadanda suke fallasa karyar wadannan ikirari.
A cikin bayanansa, Zakani ya ce: Dalilai kan wadannan karairayi su ne kaburbura gawawwaki da suka hada da fili mai lamba ta 42 a makabartar Al-Jannar – Zahra da ke babban birnin Tehran. Ya bayyana cewa, duk wanda ya ga jerin sunayen wadanda suka yi shahada a lokacin yakin zai iya ganin karara irin karyar da ‘yan sahayoniyya suka shirga, kamar yadda kowa zai iya ganin gine-ginen da aka kai musu hare-hare a birnin Tehran.
Zakani ya kuma yi ishara da hare-haren baya- bayan nan da yahudawan sahayoniyya ‘yan mamaya suka kai kan wuraren fararen hula da suka hada da cibiyoyin kiwon lafiya, inda ya kara da cewa, gwamnatin ‘yan sahayoniyya sun kai hare-hare kan motocin daukar marasa lafiya da asibitoci da ba su bukatar wata shaida wajen tabbatar da karairayin ‘yan sahayoniyya.