Isra’ila ta kashe Palasdinawa 17 ta jikkata 69 a awa 24 a Gaza
Published: 15th, April 2025 GMT
Isra’ila ta kashe Palasdinawa 17 tare da jikkata wasu 69 a cikin awa 24 a yankin Gaza, inda ta kai harin sama a wani asibiti da ke yankin Khan Younis.
Ma’aikatar Lafiyar Gaza ta sanar cewa jiragen Isra’ila sun kashe wani jami’in lafiya tare da jikkata wasu tara a Asibitin Kuwaiti da ke yankin Al-Musawi da ke Khan birnin Younis da ke Gabashin Gaza.
Mai magana da yawun asibitin, Saber Mohammed, ya bayyana cewa wadanda harin ya rutsa da su sun hada da marasa lafiya da kuma jami’an kiwon lafiya.
Isra’ila ba ta uffan a game da harin ba a halin yanzu, amma wasu rahotanni sun nuna jami’an tsaronta sun yi awon gaba da wasu Palasdinawa 14 a yankin Yamamcin Kogin Jordan.
Matashi ya yi yunƙurin soka wa mahaifinsa makami a Kano Sojoji sun ceto mafiya 16 da aka yi garkuwa da wasu a Filato NAJERIYA A YAU: Dalilan Rikice-Rikice A Jihar FilatoOfishin Kula da Fursunoni na Palasdinawa ya bayyana cewa yanacin mutanen an kama su ne a yankin Birnin Kudu, inda aka kama mutum uku a unguwar al-Issawiyya da ke Gabashin Birnin Kudus da wasu uku a garin Anata.
A yankin Ramallah kuma na jami’an Isra’ila sun kama Palasinawa uku a garin Al-Mazarra’a Ash-Sharqiya da kuma wani mutum guda a kauyen Kobar.
Sun kuma kama wani mutum guda a unguwar Ezbet al-Jarad da ke birin Tulkarem da wani guda kuma a Ezbet al-Tayah.A yankin Nablu kuma Isra’ila ta kama Palasdinawa uku a yankunan Beit Furik da kuma birnin Nablus.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Isra ila Palasdinawa
এছাড়াও পড়ুন:
Mutum 6 sun rasu, 13 sun jikkata a hatsarin mota a Kogi
Aƙalla mutum shida ne suka rasu, yayin da wasu 13 suka jikkata, bayan wata bas ɗauke da nakasassu ta yi hatsari a kan hanyar Lokoja zuwa Okene.
Waɗanda abin ya shafa suna komawa Okene ne bayan halartar bikin Ranar Nakasassu ta Duniya ta 2025 a Gidan Gwamnatin Jihar da ke Lokoja.
Jirgin fadar shugaban ƙasa ya ƙi sayuwa wata 5 bayan saka shi a kasuwa ’Yan sanda sun kama mutum 28 kan zargin lalata mata da yara a YobeAn garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa asibitoci daban-daban a jihar, inda suke ci gaba da samun kulawa.
Kwamishinan Harkokin Sadarwa na Jihar Kogi, Kingsley Femi Fanwo, ya ce wannan hatsari abun baƙin ciki ne ga gwamnati da jama’a.
Ya ce Gwamna Ahmed Usman Ododo ya umarci gwamnatin jihar da ta biya dukkanin kuɗin maganin waɗanda suka jikkata kuma ta tura jami’ai zuwa asibitoci don tallafa wa waɗanda abin ya shafa da iyalansu.
Fanwo ya ce: “Gwamnatin Jihar Kogi tana jimami sosai tare da iyalan waɗanda suka rasu guda shida, kuma za ta tallafa musu.”