Peter Obi na ganawar sirri da gwamnan Bauchi
Published: 13th, March 2025 GMT
Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa na jam’iyyar LP a zaɓen 2023, na ganawar sirri da Gwamna Bala Mohammed na Jihar Bauchi.
Taron na gudana ne a Ramat House da ke Bauchi, amma ba a bayyana manufarsa ba tukuna.
Da amincewar Buhari na fice daga jam’iyyar APC — El-Rufai ’Yan sanda sun hallaka hatsabibin ɗan bindiga a AbujaObi ya isa Filin Jirgin Sama na Abubakar Tafawa Balewa da misalin ƙarfe 10 na safiyar ranar Alhamis, inda Mataimakin Gwamnan Jihar Bauchi, Auwal Mohammed Jatau, ya tarbe shi.
Rahotanni sun nuna cewa Obi da Gwamna Mohammed za su yi magana da ’yan jarida bayan kammala ganawar tasu.
Wannan ganawa na faruwa ne a daidai lokacin da ’yan siyasa ke shirye-shiryen tunkarar zaɓen 2027.
Obi ya zo na uku a zaɓen shugaban ƙasa na 2023, wanda tsohon gwamnan Jihar Legas, Bola Tinubu na jam’iyyar APC, ya lashe.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Ma’aikatar Ayyuka da Sufuri ta Jigawa Ta Bada Kiyasin Kasafin Kudi na Sama da Naira Biliyan 161
Daga Usman Muhammad Zaria
Ma’aikatar Ayyuka da Sufuri ta Jihar Jigawa ta yi kiyasin kashe kudade miliyan dubu 161 da milyan 336 domin gudanar da ayyukan hanyoyin mota da harkokin yau da kullum a sabuwar shekara ta 2026.
Babban sakataren ma’aikatar, Malam Ahmad Isah, ya bayyana haka lokacin da ya ke kare kiyasin kasafin kudin ma’aikatar a gaban kwamatin ayyuka da sufuri na majalisar dokokin jihar Jigawa.
Babban Sakataren ya yi bayanin cewar, za a yi amfani da mafi yawan kudaden ne wajen gudanar da ayyukan hanyoyin mota tsakanin gariruwa da hanyoyin burji da kuma titunan cikin gari.
Yana mai cewar, haka kuma za a gudanar da ayyukan hanyoyi a manyan makarantun jihar ciki har Jami’ar Sule Lamido da ke Kafin Hausa da kwalejin fasaha da ke Dutse da cibiyar binciken aikin gona ta Kazaure, da kwalejin koyon aikin lafiya matakin farko da ke Jahun da sauransu.
Sai dai kuma babban sakataren ya koka dangane da bukatar daukar injiniyoyi domin aiki a ma’aikatar da hukumar gyaran hanyoyin mota JIRMA da kuma daukar sabbin jami’an duba lafiyar ababen hawa wato V.I.O, idan aka yi la’akari da karancin ma’aikata saboda masu yin ritaya.
Alhaji Ahmad Isah ya kara da cewar ma’aikatar tana kokarin cimma yarjajjeniya da makarantar koyon tukin jirgin sama ta kasa da ke Zaria domin amfani da filin jirgin sama na Dutse a matsayin sansanin koyon tukin jirgin sama.
Kazalika, ya ce makarantar koyon tukun mota da ke karamar hukumar Birnin Kudu za ta amfana da wasu ayyuka a sabuwar shekara.
A nasa jawabin, shugaban kwamatin ayyuka da sufuri na majalisar dokokin jihar Jigawa kuma wakilin mazabar Bulangu Alhaji Yusuf Ahmad Soja, ya yi addu’ar Allah Ya sa kasafin kudin ya karfafa cigaban jihar nan a sabuwar shekara.