Kasar Sin Ta Harba Taurarin Dan’Adam 18 Daga Cibiyar Harba Kumbo Ta Kasuwanci Ta Hainan
Published: 12th, March 2025 GMT
Da jijjifin safiyar yau Laraba ne aka harba rukunin taurarin dan’adam masu karamin zango daga doron kasa guda 18 a cikin roka kirar Long March-8 Y6, daga cibiyar harba kumbo ta kasuwanci ta lardin Hainan da ke kudancin kasar Sin.
Taurarin na dan’adam da aka harba, wanda rukuninsu shi ne na biyar a cikin nau’o’insa, sun shiga falakin da ake so cikin nasara, kamar yadda hukumar kula da kimiyya da fasahar sararin sama ta kasar Sin (CASC) ta bayyana.
Wannan aiki na bincike da aka kaddamar na farko daga sashe mai lamba ta 1 na tashar harba kumbon, bayan wanda aka kaddamar a sashen tashar mai lamba ta 2, a ranar 30 ga watan Nuwamban 2024, ya nuna yadda aka kimtsa tsaf a tagwayen shirye-shiryen da tashar sararin samaniya ta farko ta kasuwanci ta kasar Sin ke yi domin gudanar da ayyuka na gaba. (Mai Fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Sojojin Kungiyar “SADC” Sun Janye Daga DRC
Kusan sojoji 1,300 ne kungiyar kasashen gabashin Afirka ta SADC su ka fice daga kasar jamhuriyar Demokradiyyar Congo, a lokacin da mayakan kungiyar ‘yan atwaye ta M23 suke cigaba da kama yankunan kasar.
Wani mai sharhi akan al’amurran siyasar kasar ta Congo, Christian Moleka ya yi gargadi akan sake dagulewar al’amurra a gabashin kasar wanda dama can yana fama da matsalolin tsaro.
Janyewar da sojojin na SADC su ka yi daga cikin kasar tana a matsayin wani babban koma baya ne, alhali gwmanatin Kinshasha tana fatan ganin wadannan sojojin sun taka rawa wajen takawa mayakan M23 birki,kamar yadda su ka taba yi a 2023.
Sojojin na Congo suna fama da karancin kayan aiki da makamai, da hakan ya bai wa mayakan M 23 damar kwace iko da Goma da Bukavu.
Ana zargin kasar Rwanda da cewa ita ce ke taimaka wa ‘yan tawayen na M23, tare da aike sojoji 4000 da suke yaki a tare da ita.
A gefe daya, hukumar Agaji ta MDD tana yin kira ga kungiyoyi kasa da kasa da su taimaka su hana bullar babbar matsalar ‘yan gudun hijira da tabarbarewar harkokin agaji a cikin kasar.