Tsohon Gwamnan Kaduna El-Rufai Ya Koma SDP
Published: 10th, March 2025 GMT
Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya fice daga jam’iyyar APC tare da komawa SDP.
Majiyoyi sun ce ficewarsa ta biyo bayan rashin gamsuwa da tafiyar jam’iyyar. A cewar El-Rufai, APC ta kauce daga ainihin manufofinta, don haka ba zai ci gaba da kasancewa a cikinta ba.
Ban Bar PDP Ba, Ina Gangamin Hadin Gwiwa Ne Don Tunkarar APC A 2027 – Atiku Ban Bar PDP Ba, Ina Gangamin Hadin Gwiwa Ne Don Tunkarar APC A 2027 – AtikuKoma wa SDP ya haifar da raɗe-raɗin cewa yana shirin tsayawa takarar shugabancin ƙasa a 2027, lamarin da ke nuna sauyar tsarin siyasa a Nijeriya, idan har za a samu ɗan takara daga arewa a 2027.
A halin yanzu, shugabannin APC na nazarin tasirin wannan sauyi, yayin da SDP ke maraba da zuwansa a jam’iyyar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
An sanya dokar hana fita a Kaduna
Gwamnatin Kaduna ta sanya dokar taƙaita zirga-zirga ta tsawon kwana guda a wasu sassan jihar.
Wannan na zuwa ne bayan wani hargitsi tsakanin jami’an tsaro da wasu ɓata-gari a yankin Kakuri.
Wuraren da dokar ta shafa sun haɗa da Kakuri Bus Stop, Kurmi Gwari, Monday Market, Afaka Road, da Kakuri GRA.
Wata sanarwa da Gwamnatin Kaduna ta fitar ta buƙaci mazauna da su kiyaye umarnin wannan doka.