Zulum ya rage adadin tallafin rabon abinci da kashi 90% a jihar
Published: 27th, February 2025 GMT
Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya sanar da rage kashi 90% na tallafin rabon kayan abinci don ƙarfafa dogaro da kai a tsakanin mazauna jihar.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin da yake ƙaddamar da rabon kayan abinci ga magidanta 25,000 gabanin watan Ramadan a Maiduguri, Jere da sauran sassan jihar.
A cewar Zulum, gwamnatin jihar za ta ba da fifiko ga hanyoyin samar da ci gaba na tsawan lokaci a kan matakan agaji na gajeren lokaci kamar rabon tallafin abinci.
Ya kuma bayyana irin gagarumin jarin da gwamnatinsa ta yi wajen tallafa wa manoma sama da miliyan ɗaya da muhimman kayayyakin amfanin gona kamar irin su iri, taki, famfunan ban-ruwa, maganin ƙwari da magungunan kashe ciyawa.
“Wannan dabarar ba kawai za ta inganta dogaro da kai ba ce har ma da rage kashe kuɗaɗen gwamnati,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa, rabon kayan tallafin zai taƙaita ne ga ƙananan hukumomin jihar guda biyu kawai daga cikin 27 a shekarar 2025 saboda ƙalubalen da suke fuskanta.
“Ƙananan Hukumomin da za su sami tallafin abinci a shekara mai zuwa su ne: Ngala da Kala-Balge saboda yanayi na musamman.
“Waɗannan yankuna sun fuskanci mummunar ɓarna a gonakinsu daga giwaye kuma sun fuskanci ambaliyar ruwa. Don haka, a shekarar 2025, gwamnatin Jihar Borno za ta samar da kayayyakin tallafin abinci ga Ngala da Kala-Balge kaɗai,” inji shi.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Umara Zulum Umara
এছাড়াও পড়ুন:
Talauci Da Rashin Ilimi Ne Ya Sa Ayyukan Boko Haram Ke Dawowa – Gwamnan Yobe
Shugaban tawagar baƙin, Alhaji Ibrahim Abdullahi Yar’adua, ya ce sun zo Yobe domin nazarin halin tsaro da tattara bayanai da za su taimaka wajen tsara manufofin tsaron ƙasa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp