Fararen Fatar Kasar Afirka Ta Kudu Sun Yi Gangamin Nuna Goyon Bayan Trump
Published: 16th, February 2025 GMT
A jiya Asabar ne da wasu kungiyoyi na fararen fata a kasar Afirka ta kudu sun yi gangami a bakin ofishin jakadancin Amurka dake birnin Pretoria suna masu nuna goyon bayansu ga kalaman da Donald Trump da ya riya cewa, gwamnatin kasar da bakaken fata masu rinjaye tana nunawa fararen fata wariya.
Daruruwan masu gangamin sun daga kwalaye da aka yi rubuta a jikinsu da su ka kunshi yin godiya ga Donald Trump da ya yi Magana akan abinda ce, damuwarsu ce.
Wanda ya shirya gangamin Willem Petzer, ya ce, yana son fadawa kasashen turai cewa, suna da kawaye a cikin kasar Afirka ta kudu.
Da dama daga cikin mahalarta gangamin sun fito ne daga al’ummar Afirkana da Trump ya ce, gwamnatin kasar ta yi dokar kwace musu filaye.
Shi kuwa Heinrich Steinhausen ya bayyana cewa; A cikin shekaru 30 na bayan nan an sami rabuwar kawuna a cikin kasar saboda abinda ya kira siyasar gwamnati.
Tuni dai gwamantin kasar Afirka ta kudu ta yi watsi da wadannan zarge-zargen na Donald Trump.
Masu bin diddigin abinda yake faruwa suna ganin cewa Amurkan tana yin matsin lamba ne akan kasar Afirka ta kudu saboda ta shigar da kasar “Isra’ila” a gaban kotun duniya ta manyan laifuka da ta yanke hukunci akan Isra’ila da yi wa Falasdinawa kisan kiyashi.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: kasar Afirka ta kudu
এছাড়াও পড়ুন:
Uganda Ta Sanar Da Kawo Karshen Ebola Da Ta Barke A Kasar
Ma’aikatar kiwon lafiya ta kasar Uganda ta sanar da cewa, an kawo karshen Ebola da ta bulla a kasar bayan da aka dauki kwanaki 42 ba tare da an sami mutum daya wanda ya sake kamuwa da ita ba.
A wani bayani da ya fito daga hukumar kiwon lafiya ta duniya ( WHO), ta bayyana cewa, a lokacin bullar cutar an gabatar da mutane 14 masu dauke da ita, an tabbatar da 12 daga cikinsu, sai wasu biyu da ba a same ta a tare da su ba.”
Haka nan kuma hukumar lafiyar ta ce, an sami mutuwar mutane 4 daga cikin wadanda su ka kamu da cutar ta Ebola, wasu mutane 10 kuma sun warke.”
Watanni 9 da su ka gabata ne dai aka tabbatar da bullar cutar a birnin Kamfala bayan da wani mutum da yake dauke da ita ya rasu.
Dajukan da kasar ta Uganda take da su, suna a matsayin matattarar cutar ta Ebola ce, wacce a karon farko ta bulla a cikin kasar a 2000.
A yankin yammacin Afirka cutar Ebola ta kashe fiye da mutane 11,000 a tsakanin 2013 zuwa 2016.