Tawagar Kasar Saudiyya Ta Kai Ziyarar Ta’aziyya Jihar Jigawa
Published: 13th, February 2025 GMT
Gwamna Umar Namadi na Jihar Jigawa ya karbi bakuncin tawaga daga kasar Saudiyya karkashin jagorancin Sheikh Nuhu Idris Fallata shugaban hukumar Saudiyya mai kula da ciyar da Alhazai.
Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa, tawagar ta zo ne domin ta’aziyyar rasuwar mahaifiyarsa da dansa ya rasa.
Sheikh Fallata ya yi addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rasu.
Tawagar ta kuma yabawa tare da karrama Gwamna Namadi bisa kulawa da jajircewarsa wajen kyautata rayuwar Alhazai.
A cewar tawagar, jihar Jigawa ta yi fice mai ban sha’awa a lokacin aikin Hajjin shekarar 2024.
Shi ma da yake nasa jawabin babban daraktan hukumar jin dadin alhazai ta jiha Alhaji Ahmed Umar Labbo ya yabawa tawagar bisa karrama gwamnan jihar ta Jigawa.
Wadanda suka raka tawagar sun hada da babban daraktan hukumar jin dadin alhazai ta jiha, Alhaji Ahmed Umar Labbo, da daraktan ayyuka Alhaji Muhammad Garba, da Alhaji Isah Idris Gwaram da dai sauransu.
Usman Mohammed Zaria
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Jigawa Saudiyya Ta aziyya
এছাড়াও পড়ুন:
Tinubu ya bai wa ’yan ƙwallon Nijeriya mata kyautar kuɗi da gida da lambar yabo
Shugaba Bola Tinubu ya karrama ’yan wasan tawagar ƙwallon ƙafa ta mata ta Nijeriya da lambar yabo ta OON.
Shugaban ya bai kowacce ’yar wasa a tawagar ta Super Falcons kyautar gida mai ɗakuna 3 a rukunin gidaje na Renewed Hope da kuɗi dala dubu 100.
Haka kuma, shugaban ya kuma bai wa masu horas da tawagar kyautar dala dubu 50.