Babban Burinmu Shi Ne Tattara Naira Biliyan 100 A Bana – Dr. Zaid Abubakar
Published: 13th, February 2025 GMT
Hukumar tara haraji ta jihar Kano (KIRS) ta sanar da wani gagarumin shiri na kara yawan kudaden shiga na jihar zuwa sama da Naira biliyan 100 nan da shekarar 2025.
Shugaban hukumar Dr. Zaid Abubakar ne ya bayyana hakan a yayin da hukumar ke bitar ayyukan hukumar na shekarar 2024 da kuma tsare-tsarenta na shekarar 2025.
A cewar Abubakar, KIRS ta bullo da tsare-tsare na matsakaita da kuma na dogon lokaci domin bunkasa kudaden shiga na jihar.
Shirin tara kudaden shiga na matsakaicin zango na nufin tara sama da Naira biliyan 100 a shekarar 2025, inda ake sa ran za ta haura Naira biliyan 200 a shekaru masu zuwa.
Musamman ma, gwamnatin jihar tace tana son su hado hancin naira biliyan 75 a shekarar 2025, amma KIRS ta kuduri aniyar wuce wannan buri.
Ya ce don cimma wannan manufa, KIRS na da niyyar yin amfani da fasaha a matsayin wani bangare na kokarin da ta ke yi na aiki da dabarun zamani.
“Hukumar tana shirin amfani da fasahar zamani ta ICT don tsarin sarrafa bayanai da haɓaka tattara kudaden shiga da bin diddigi da ci gaba, da kuma tabbatar da ingantaccen gudanarwa.”
“Gwamnatin jihar Kano kuma tana shirin sake duba dokokin samar da kudaden shiga na jihar domin karfafa kudaden shiga.”
Abubakar ya lura cewa gwamnan ya amince da sake duba wadannan dokoki, wanda ake sa ran kammalawa kafin karshen watanni 3 na farko na shekarar 2025.
Abdullahi Jalaluddeen Kano/WABABE
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Haraji a shekarar 2025 Naira biliyan
এছাড়াও পড়ুন:
An Tsare Wani Mutum A Gidan Yari Kan Zargin Kashe Matarsa Saboda Ƙuli-Ƙuli A Kano
Mai shari’a Dahiru ya amince da buƙatar, ya kuma ɗage shari’ar zuwa ranar 12 ga watan Disamba, 2025, domin ci gaba da sauraron shari’ar.
Ƙuli-ƙuli dai nau’in abin ci ne mai taushi da ake yi da gyaɗa, ana soyawa har sai ya zama ƙura-ƙura ta yadda za a ci cikin nishaɗi.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA