Gobara ta yi ajalin almajirai 17 a Zamfara
Published: 5th, February 2025 GMT
Wata gobara da ta tashi a wata makarantar tsangaya da ke Ƙaramar Hukumar Kaura-Namoda a Jihar Zamfara, ta yi ajalin almajirai 17.
Dukkanin almajiran sun ƙone ƙurmus, ta yadda ba a gane kowa a cikinsu ba.
Saura ƙiris Bello Turji ya zo hannu – Ministan Tsaro Tinubu ya ƙara kasafin kuɗin 2025 zuwa N54.2trnShaidu sun bayyana cewa gobarar ta farq ne cikin daren ranar Talata, kuma ta ɗauki kimanin sa’o’i uku tana ci.
Rahotanni sun bayyana cewar wasu almajirai 16 sun samu munanan raunuka a gobarar.
Wani mazaunin yankin, Abdulrasaq Bello Kaura, ya bayyana cewa gobarar ta fara ne sakamakon kamawar wasu itatuwa da aka ajiye.
Wani ganau ya shaida cewar, “Abin ya faru ne a makarantar Malam Ghali, a cikin ɗakin karatu.
“Akwai kusan almajirai kusan 100 a cikin gidan. Bayan da aka fitar da su, sai aka ɗauka babu kowa a ciki.
“Amma bayan gobarar ta lafa, sai aka dawo aka ga sassan jikin wasu kamar ƙafafu, hannaye, da kuma gawarwakin waɗanda suka rasu bayan sun ƙone ƙurmus.”
An yi jana’izar waɗanda suka rasu a ranar Laraba.
Shugaban Ƙaramar Hukumar Kaura-Namoda, Kwamared Mannir Muazu Haidara, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ya ce yana kan hanyarsa ta zuwa wajen da lamarin ya faru domin samun ƙarin bayani.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Almajirai Gobara Makarantar Tsangaya Zamfara
এছাড়াও পড়ুন:
‘Yan Bindiga Sun Yi Wa Hakimi Yankan Rago A Zamfara
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp