Leadership News Hausa:
2025-09-18@02:17:17 GMT

‘Yansanda Sun Kashe ‘Yan Bindiga 2 A Dajin Bauchi

Published: 5th, February 2025 GMT

‘Yansanda Sun Kashe ‘Yan Bindiga 2 A Dajin Bauchi

Jami’an ‘yansanda tare da hadin gwiwar mafarauta sun kashe wasu da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne a Dajin-madan, da ke karamar hukumar Alkaleri a jihar Bauchi. Da yake tabbatar da faruwar lamarin ga wakilinmu a safiyar ranar Laraba, Kakakin Rundunar ’Yansandan Jihar Bauchi, CSP Ahmed Wakil, ya ce an kashe ‘yan bindigar ne ta hanyar amfani da bayanan sirri da hadin gwiwa da masu sa ido da ke cikin al’ummomin da abin ya shafa.

Tinubu Ya Amince Da Naira Biliyan 80 Domin Sake Gina Madatsar Ruwa Ta Alau Da Ke Borno Masana Kimiyyar Sin Sun Kirkiro Sabuwar Fasahar AI Mai Hasashen Zuwan Mahaukaciyar Guguwa Ya kara da cewa, bayan artabun, wasu daga cikin ‘yan bindigar sun tsere da raunukan harbin bindiga zuwa dazukan da ke kusa. Wakil ya ce, an kwato bindiga kirar AK-49 guda daya da harsashi guda tara daga hannun ‘yan ta’addan a yayin artabun.

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Mummunan Hatsarin Mota Ya Kashe Fasinjoji 17 A Zamfara

A ƙalla fasinjoji 17 ne suka rasa rayukansu bayan wata motar haya ta faɗa cikin wata gada da ta ruguje a kan titin Gwalli da ke ƙaramar hukumar Gummi, jihar Zamfara.

A cewar hukumar kiyaye haɗura ta ƙasa (FRSC) reshen Zamfara, hatsarin ya faru ne a daren Lahadi lokacin da motar ɗauke da kaya da fasinjoji ta faɗa cikin gadar da ta ruguje. Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, SRC Isah Aliyu, ya tabbatar da lamarin a wata sanarwa da ya fitar.

Kwamandan FRSC na jihar, CC Aliyu Magaji, wanda ya ziyarci wurin hatsarin, ya bayyana matuƙar baƙin cikinsa da asarar rayukan, inda mafi yawansu mata ne. Ya ce hatsarin ya biyo bayan nauyin da aka ɗora wa motar fiye da ƙima da kuma tafiya da daddare.

Hukumar ta gode wa mazauna yankin da suka gaggauta taimakawa wajen ceto wasu daga cikin waɗanda hatsarin ya rutsa da su. Kwamanda Aliyu ya yi ta’aziyya ga gwamnatin Zamfara da al’ummar Gummi, tare da yin kira ga direbobi su rika bin ƙa’idojin hanya da kuma guje wa tuƙa mota da dare domin kare rayuka.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • ‘Yansanda Sun Kama Mutane 6 Kan Zargin Haƙar Ma’adinai Ba Bisa Ƙa’ida Ba A Neja
  • ‘Yansanda Sun Kama ‘Yan Ƙungiyar Asiri Da Ɓarayin Kifi A Jihar Neja
  • Kungiyar Human Rights Watch; Isra’ila Ta Kashe ‘Yan Jarida Fiye Da 30 A Kasar Yemen Ne Da Gangan  
  • ‘Yan Bindiga Sun Yi Wa Hakimi Yankan Rago A Zamfara
  • Burkina Faso: Masu Ikirarin Jihadi Sun Kashe Fararen Hula 50 A Cikin Watanni Hudu
  • ‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Kan Masallata Tare Da Garkuwa Da Mutane A Zamfara
  • Sulhu Da ‘Yan Bindiga Ya Fara Shan Ƙasa, Sun Yi Garkuwa Da Masallata A Zamfara 
  • Ƴan Bindiga Sun Sace Malamin Krista Na Ɗarikar Katolika A Kogi
  • Ƴan Bindiga Sun Kashe Sarkin Shuwaka Na Kanam A Filato
  • Mummunan Hatsarin Mota Ya Kashe Fasinjoji 17 A Zamfara