DRC: Kungiyar M23 Ta Shelanta Tsagaita Wutar Yaki A Garin Goma
Published: 5th, February 2025 GMT
Kungiyar ‘yan tawaye ta M 23 ta sanar da tsagaita wutar yaki a garin Goma da take rike da shi, saboda dalilai na jin kai.
Kungiyar wacce take samun goyon bayan kasar Rwanda wacce ta kwace iko da birnin Goma da shi ne birni mafi girma a gabashin wannan kasa, ta sanar da tsagaita wutar yaki ta gefe daya saboda abinda ta kira samar da damar gudanar da ayyukan agaji.
Kungiyar ta ce, ta amince da tsagita wutar yakin ne domin amsa kiran da aka yi dangane da hakan, saboda a taimaka wa dubun dubatar mutanen da suke a tarwatse saboda yaki.
Ya zuwa yanzu dai babu wani furuci da ya fito daga gwamnatin kasar DRC akan batun tsagaita wutar yakin.
A ranar Litinin din da ta gabata kakakin MDD Stephane Dujarric ya yi bayani akan halin da ake ciki a kasar ta DRC tare da nuna damuwa akan matsalolin kiwon lafiya a cikin kasar.
Wani rahoto na MDD ya bayyana cewa, mutane 900 ne su ka rasu a cikin kasar ta DRC, yayin da wasu 2,880 su ka jikkata sanadiyyar tashe-tashen hankulan na bayan nan.
Daga farkon wannan shekara ta 2025, fiye da mutane 400,000 ne su ka bar matsugunansu a cikin kasar, kamar yadda hukumar MDD mai kula da ‘yan hijira ta bayyana.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Lebanon: Isra’ila Ta Kai Hari Akan Unguwar Dhahiya A Birnin Beirut
Jiragen yakin HKI sun kai hari a yankin Hangara dake unguwar “Dhahiya” a cikin birnin Beirut. Yankin da jiragen yakin na ‘yan sahayoniya su ka kai wa harin, yana cike da mutane da kuma makarantu biyu.
Jiragen yakin na HKI sun harba makamai masu linzami 3, da hakan ya haddasa tashin gobara.
A sanadiyyar wannan harin, an sami shahidi daya,yayin da wasu da dama su ka jikkata.
A ranar 1 ga watan Aprilu ma dai sojojin HKI sun kai wani harin a unguwar Dhahiya wanda ya yi sanadiyyar shahadar mutane 4 da kuma jikkata wasu da dama.
Tun bayan tsagaita wutar yaki a ranar 27 ga watan Aprilu 2025, HKI ta keta wutar yakin fiye da 2000.