Aminiya:
2025-05-01@00:00:08 GMT

DAGA LARABA: Yadda Al’adun Aure A Ƙasar Hausa Suka Koma ‘Event Centre’

Published: 5th, February 2025 GMT

More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba

A da akan kwashe kwanaki ana bukukuwan aure a ƙasar Hausa, kama daga kamu, zuwa sa lalle, yinin biki da zaman ajo zuwa buɗar kai da sayen baki.

Sai dai waɗannan al’adu sannu a hankali suna ta gushewa.

Ko mene ne dalilin wannan sauyin?

NAJERIYA A YAU: Hanyoyin Noma Ba Tare Da Kashe Kuɗi Da Yawa Ba DAGA LARABA: Dalilan Da Mutane Suke Son Haihuwar Maza Fiye Da Mata

Wannan ne batun da shirin Daga Laraba zai duba a wannan makon.

Domin sauke shirin, latsa nan

উৎস: Aminiya

এছাড়াও পড়ুন:

Shugaba Tinubu Ya Taya Sabon Firaiministan Kanada Mark Carney Murna

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya Mista Mark Joseph Carney murna bisa zaɓensa a matsayin Firaiminista na 24 na ƙasar Kanada, bayan nasarar jam’iyyar Liberal a zaɓen majalisar dokokin da aka kammala kwanan nan.

 

A cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai Bayo Onanuga, ya fitar, Shugaba Tinubu ya bayyana zaman Carney a wannan matsayi a matsayin wani muhimmin ci gaba, musamman a wannan lokaci da Kanada ke bukatar gogaggen shugaba domin fuskantar ƙalubale da dama.

 

Carney, wanda fitaccen masani ne a fannin tattalin arziki, ya taba rike mukamin Gwamnan Babban Bankin Kanada daga shekarar 2008 zuwa 2013, sannan ya ci gaba da zama Gwamnan Babban Bankin Ingila daga 2013 zuwa 2020.

 

Shugaba Tinubu ya bayyana kwarin gwiwar cewa ƙwarewar sabon shugaban Kanada a fannin kuɗi da shugabanci za ta taka muhimmiyar rawa wajen gina makomar ƙasar. Haka kuma, ya sake jaddada kudirin Najeriya na ƙarfafa dangantakar diflomasiyya da Kanada, musamman a fannonin ilimi, sauyin yanayi da hijira.

 

Shugaban Najeriya ya ƙara da cewa yana fatan kafa kyakkyawan hadin gwiwa da gwamnatin Carney, yayin da ya nuna godiyarsa ga kyakkyawar alakar da aka kula a tsakaninsu  a zamanin tsohon Firayim Minista, Justin Trudeau.

 

Bello Wakili

 

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Yadda ’yan Tifa da baƙin direbobi ke haddasa haɗari a Abuja
  • Sojoji Sun Daƙile Harin ‘Yan Bindiga , Sun Ceto Fasinjoji 6 A Taraba
  • DAGA LARABA: Asarar Da Hausawa Ke Tafkawa Sakamakon Bacewar Tatsuniya
  • Shugaba Tinubu Ya Taya Sabon Firaiministan Kanada Mark Carney Murna
  • Gwamnatin Jihar Jigawa Ta Shirya Fara Tantance ‘Yan Fansho
  • HOTUNA: Yadda aka dawo da ’yan Najeriya 203 daga Libya
  • NAJERIYA A YAU: Dalilin karyewar farashin shinkafa a kasuwannin Najeriya
  • Sin Za Ta Aiwatar Da Matakan Daidaita Samar Da Guraben Ayyukan Yi Da Raya Tattalin Arziki
  • Yadda matar gwamna ta sa mata gasar haihuwar ’yan uku
  • Gwamnatin Tarayya Ta Umurci WAEC, NECO Su Koma Amfani Da CBT Nan Da 2026