Ma’aunin Cinikayyar Ba Da Hidimomi Ta Sin Ya Zarce Dala Triliyan 1
Published: 4th, February 2025 GMT
Alkaluman da ma’aikatar cinikayya ta Sin ta fitar baya-bayan nan na cewa, a shekarar bara, darajar shige da ficen cinikayyar ba da hidimomi ta Sin ta kai kudin Sin RMB yuan triliyan 7.5, kwatankwacin dalar Amurka triliyan 1.034, wanda ya karu da kashi 14.4 cikin dari bisa makamancin lokaci na shekarar 2023, ma’aunin ya kai wani sabon matsayi a tarihi.
Shugaban hukumar kula da cinikayyar ba da hidimomi ta cibiyar nazarin hadin gwiwar ciniki da tattalin arziki na kasa da kasa ta ma’aikatar kasuwanci ta kasar, Li Jun, ya bayyana cewa, al’adun Sin masu kayatarwa na ci gaba da jawo hankalin masu yawon bude ido su zo kasar Sin don yawon shakatawa, da alamar zai inganta habaka ma’aunin cinikayyar ba da hidimomi ta Sin, tare da inganta da maido da aikin ba da hidimomin yawon shakatawa na kasa da kasa.
Bugu da kari, abubuwa da dandamalin da suka shafi al’adun dijital na kasar Sin sun taka rawar gani sosai a ketare. Misali, tun lokacin farko da aka fitar da shi a shekarar 2024, wani wasan kamfuta mai suna “Black Myth: Wukong” cikin sauri ya zama jagoran tallace-tallace a kan dandamalin wasannin kamfuta masu yawa kamar Steam da WeGame, kuma ya sami lambobin yabo da yawa.
Bisa rahoton binciken ci gaban adabi na intanet na kasar Sin a shekarar 2023, yawan labaran adabi na yanar gizo da ‘yan kasar Sin suka rubuta da kansu a ketare a shekarar 2023 ya kai kusan dubu 620, tare da masu karantawa da suka kai fiye da miliyan 230 a ketare.(Safiyah Ma)
এছাড়াও পড়ুন:
Sabbin ‘Yan Saman Jannatin Kasar Sin Sun Shiga Tashar Sararin Samaniya Ta Kasar
Ofishin kula da zirga-zirgar kumbuna masu dauke da mutane na kasar Sin ya ce, an harba kumbon Shenzhou-21 mai dauke da ‘yan sama jannatin kasar Sin 3 cikin nasara, a daren jiya Juma’a, agogon Beijing.
Daga baya kumbon ya sarrafa kansa wajen hade jikinsa da na tashar binciken sararin samaniya ta kasar Sin, ta yadda ‘yan saman jannatin suka shiga tashar, inda tsoffin ‘yan saman jannati 3 da suka dade a cikin tashar, suka yi musu maraba. Hakan ya shaida haduwar sabbi da tsoffin ‘yan sama jannatin kasar Sin karo na 7 a tashar binciken sararin samaniya ta kasar.
Bisa shirin da aka yi, wadannan ‘yan sama jannati 6 za su kwashe kimanin kwanaki 5 suna aiki tare a cikin tashar, kafin tsoffin ‘yan saman jannatin 3 su kama hanyar dawowa gida.
Zuwa yanzu, kasar Sin ta riga ta tura ‘yan sama jannati 44 zuwa sararin samaniya. (Bello Wang)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA